Sashe 51
Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bama zata iva lissafawa ba komi nashi na mutuwan burgeta kara wayanta yayi dasauri tabude idanubta lallabawa tayi ta mike dagakan dadduma tawuce wajen jakanta data rataye tabude taciro wayanta message taga tanada shi dasauri tashiga bude messege din gain daga bakuwar number ne, wani kalan ijiyan zuciya ta sauke takara natsuwa kafin ta kalli sakon tana kara bude manvan idanunta danta karanta da kyau. "Sw..." tadanyi shiru Farida dake rubutu akasa tana kwafe note tace "me kike kokarin karantawa nazo na karanta miki"? For the first time in her entire life tai rejecting akaranta mata abu dasauri tace "'a" kwanciya tayi da gudu kan gado taja bargo tarufe har kanta Farida takalleta saikuma tai murmushi tacigaba da rubutunta. Daga wayan Yasmeen tayi cikin bargo tana kallon sakon ahankali sabida kar muryanta yafito ma sosai tace "Swe.. saikuma dasauri tace "sweet! Eh sweet ne" kafin ta kalli next kalman tace ....dr..." dasauri tace "dreams" ahankali tace "sweet dreams. MM" wani sweet smile tasaki ta manna hancinta kan wayan akunyace mistakenly tai dialing number kawai duu duuu taji alamun ringing, dawani irin sauri tazare wayan dagakan fuskanta ahaukace ta yaye bargon tafito tace "Wayyoo Allah" tashiga daddanna call din tana katse kiran Farida tasaki baki tana kallonta, wurgar wayan tayi chan gefe bayan takatse kaman ta fashe da kuka, daidai kira na shigowa wayan zaro idanu tayi kaman zasu fado kasa. Maheer dake kan couch adakin Hamad ne yadan lumshe idanu kafin yasaci kallon Hamad dake gefenshi yana aiki a system, tashi yayi ahankali yazura slippers yawuce yafita daga dakin Hamad yabishi da kallo kafin ahankali yace "munafikin miskili kawai your MM doesn't just stand for Maheer Maheer, harda Munafikin Miskili" last room din dake corridor Maheer yawuce yashiga, dakin a gyare tsaf kashe wutan akin yayi ya kunna AC dakin yawuce yahau kan gadon ya kwanta daidai Yasmeen nacewa "Hello, waye"? Ita adole so take ta nunamai bata gane waye ba, dan murmushi yasaki kadan kafin cikin wani soft calm voice yace "idanunki ne" dudda yadan gaban Yasmeen ke dari dari amman saida maganan yasa tasaki dan murmushi tana kara satan kallon Farida dake rubutun ta abinta taga ko tana kallonta, murguda baki tayi cikin murya yar karama chan kasa ta yanda ko Farida dake dakin barataji metake cewa ba tace "me kake kirana ni"? Dan murmushi kadan Maheer yayi jin vanda takemai tsiwa cikeda son shima yakara tunzurata yace "ai ke kika kirani" jitayi kaman zata nitse akasa takasa magana, murya chan kasa yace "why are you feeling bad?" Dan shiru yayi kafin cikin murya mai bala'in dadi yace "zaki iya kirana anytime afterall very soon zan zama mitinki" hararanshi tayi kaman yana gabanta cikeda kulewa tace "ni bazan aureka ba" "nikuma zan aureki Fateema!" Faduwa gabanta yayi sosai tarasa mesa duk idan yakirata sai gabanta yafadi hakan yasa takasa magana hawaye ya fito daga idanunta dasauri tasharesu da bayan hannu. "Mesaki kuka yanzu"? Yay tambayan ahankali bin dakin tayi da kallo ko yasa camera ne yake ganinta dasauri tace "kasa camera ne adakin muma yanzu?" Dan murmushi kadan yayi yace "idan naso zan iva sawa but no bansa ba" adan hankali tace "to ya kayi kasan ina kuka"? Shiru yayi baice komiba harsaida tacire wayan daga kunnenta takalli screen di ganin yanakai still yasa ta maida wayan kunnnenta tace "hello" cikin tattausiyan mura batare daya amsa hellon taba yace "my soul is connected to yours saisa nasan u were crying" shiru tayi batasake cewa komiba, murya chan kasa yace "ina mai kukan nan kaman ke Nana Aisha?" At this point tafara tunani mavbe aliani ne mutumin nan vasan duka sunansu na gaskiya, shiru tayi saikuma tace "meruwanka da ita" murya chan kasa yace "she's now my sister in law, itada Farida da Sa'adatu, Fateema kuma itace matata" shiru kawai tayi tana saurarinshi tana lumshe idanu wh kaman karya daina magana muryanshi dadi sosai, turo baki tayi tace "nidai saida safe" cikin dan kakkausan murya babu alamun wasa yace "nasallameki ne"? ahankali tace "a'a" dan shiru yayi kusan 1min baice komiba ahankali vace "have u had ur dinner?" Ahankali tace "eh" "mekikaci"?Kwanciya tayi ahankali daidai zata bada amsan taji muryan Baba yana magana da Baffa zai shigo dakin atsorace tace "Baba yazo bye" tura wayan karkashin pillow tayi ta runtse idanunta tai lamo daidai Baba yay sallama yashigo Farida tace "Baba sannu da zuwa" karasawa gaban Farida yayi yace "yauwa Farida ya akayi bakiyi note a school ba" adan tsorace gain yanda ya kafeta da ido tace "Baba kaine na ciwo ne lokacin a class" dan sassauta mura yayi yace "dakika dawo kin fadama Mamanki kanki na ciwo kinsha magani"? Gyadamai kai tayi ahankali tace "nasha" hannunshi yakai yataba goshinta kafin yakai wuyanta jin ba zafi yace "idan yasake damunki gobe lemme know zan kaiku hospital kiga Dr" anatse tace "to Baba" tashi yayi yakalli Yasmeen datai lamo itama Farida faduwa gabanta yake dan kada yakamata karasawa gaban gadon yayi yakalleta ganin kaman tai nisa abacci yasa yajuyo yakalli Farida yace "Ina Sa'adatu"? "Tana wajen Yaya" Gyadamata kai Baba yay cikeda gamsuwa Yasmeen yakara kallo yabi dakin da kallo kaman nai neman wani abu sannan yajuya yafita yace "saida safe kiyi addu'a kafin ki kwanta" "to Baba" Farida Farida tafadi ahankali tareda sauke jjiyan zuciya ganin yafita takalli Yasmeen tace "Allah yasoki bai kamaki kina waya ba hope dai kin katse wayan"? Dasauri Yasmeen tasa hannu taciro wayan daga kasan pillow ga mamakinta Maheer nakan layin dasauri takai wayan kan kunnenta tace "daman ban kasheba kai mesa baka kasheba" ahankali yace "ban sallameki ba" "to me kakeso?" Yasmeen tai maganan tana kallon kofan su jin antaba gain Sa'a ne tashigo yasa tasauke ijiyan zuciya, jin shiru baice komiba yasa ta turo baki cikin kunkunai tace "ni zanyi bacci" almost 10secs baice komiba kafin chan yace "bakida kunya ko" dan dariya kadan tayi mara sauti tace "toka barni na kwanta baccin" yanda taja baccin saida yaji aranshi, anatse yasauke ijiyan zuciya cikin tattausan murya yace "good night Fateema" kasa magana tayi tai shiru tama rasa takamaimen metakeji danji tayi inama baice good night ba, anatse yace "zanzo ranan Sunday by 3, 4 zan tafi" cikeda tsiwa tace "karka sake kazo gidan mu ni, kuma bara'a aureka ba din, bye" dip ta katse wayan. Ta tura wayan karkashin pillow dasauri tareda lumshe idanu wh batasan mesa ba bala'in dadin wayan dasukeyi takeji har aranta itadai tabani meke damunta ne haka, fuskanshi tafara gani ahaka daga baya bacci yay awon gaba da ita. Yau tunda ta tashi gabanta faduwa yake ita tunda take bata taba shiga irin wannan vanayin arayuwanta ba, wani bangare na zucianta na toron mutumin nan da shakkan shi sabida tasan criminal ne, koba komai ya gwada mata kadan daga halinshi, wani bangare na zucianta najin wani iri game dashi tun ranan Friday dasukai waya basu kara ba sotake yasake kiranta suyi magana taji muryanshi, tabude message nashi takaranta yafi sai dari na Sweet dreams din nan, tabude number shi takalla harta haddace akanta tsabagen yanda take tunaninshi she's just dying to hear from him, kewanashi infact babu abinda bamataji game dashi, wani bangaren na zucianta bayaso yazo gidansu yau amman har kasan ranta wh wl takosa taganshi, tarasa mezatai tunani to idan yazo su Farida suka ganeshi fa suka fadi koda yake Farida tace ita bata iya ta kalli fuskanshi ba Nana wannan daman kuka take batasan shi ba harsuka dawo daga hadda wuraren 1 tarasa meke mata dadi mix feeling takeji sosai daman gashi sunyi test bata iya tayi komiba. Wuraren 1 aka bude labulen kofanta dasauri ta dago kanta Baba tagani yana sanye da manyan kaya dasauri ta tashi ta zauna tana jawo dankwalinta dan rufe kanta, Baba dake kallonta ganin tamai wani iri yace "kinyi salla"? Gyadamai kai tayi ahankali, Baba dake kallonta ganin duktai wani iri yace "baki da lafiva ne?" Baki tabude zatai magana saiga hawaye sharrr sun zubo dasauri Baba yasaki labulen yawuce yashiga dakin, abakin gadon su yazauna yana kallonta baice komiba itama kallonshi tayi kaman tafadamai abun da ya tsayamata awuya amman bazata ivaba batason tazama sanadin dazaisa akashe mata iyaye hannayenta kawai tadaura kan fuskanta tafashe da kuka sosai, Baba yakai cikakken 1min yana kallonta bai hanata kuka ba chan yace "Yasmeen" cikin kuka tace "naam Baba" hannunshi yakai saman fuskanta yazare hannayen taredakai bayan hannunshi yashare fuskanta tsaf yace "meke damunki"? Dan yasan kukan damuwa takeyi bana ciwo ba, vanda Baba ya tsareta da ido yasa ahankali cikin murya Mai balain rauni tace "muni test a hadda ko daya ban iyaba Baba, zasu karamin repeating ko halama nan gaba Nana tazo tafini aji, Baba maisa banda ilimi maisa har yanzu bana iya rubuta kowani kalan baki, nasan amsan tambayan but ban iya narubuta ba banda kokar...." " kuka vakaracin kartinta dasauri Baba yasata ajikinshi kankameshi tavi bayanta ya bubbuga yace "shiti kada ki kara cewa bakida kokari, kinada kokari kini bari akwai wata Malama da akamin maganan ta zan daukota tadinga zuwa gida tana miki all abubuwan kinji now stop crying" kara sosuwa zuciyanta yayi all Baba ever did was to support her daidai da sau daya Baba baitaba complaining cewa batada kokari ba dudda kowa na gidan nan yayi, baya gajiya da nema mata ilimi, baya gajiya da sata a makaranta daban daban, tayaya itama yanzu lokaci yayi bazatama mahaifinta hallaci ba, ta ceceshi koda mutuwa zatayi ta hanyar haka daya taba iyayenta gwara ta aureshin kome zaiyi yayi da ita idanma kasheni zaiyi yayi amman ya kale Baba yasa adaina binshi ya kyale yan uwanta. Sallama Ammi tayi tashigo ganin Baba dakin saida abin yabata mamaki baki tasaki tana kallon Yasmeen dataga idanunta sunyi ja dasauri itama tazo wajen tace "Yasmeen meya sameki"? Takai hannunta tana cirota daga jikin Baba, ahankali tace "muni test ban rubuta komi ba Ammi" Ammi jitayi zuciyanta ya sos dasauri ta rungumeta tana kallon fuskan Baba dake kallonta tace "stop crying a karatu the most important thing shine kanka yarike and Alhamdulillah kanki yarike was dan haka ki barma Allah komi watarana sai labari kinji saisa gara kiyi aurenki kihuta da wannan bakar wahalan dakike a makarantu" wani mugun harara Baba yama Ammi itama ta maida mishi hararan back, tashi yay