← Book details Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 93

Sashe 9

Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

lawyers will put you through everything kuyi signing papers, nagama dakai you can excuse me Maheer yay maganan yana nunamai kofa kallonshi Senator yayi yadauka kodan hannu Maheer zai bashi su gaisa amman ina, ashe dai duk labaran dayaji hakane, yaron akwai wulakanci da rashin mutunci sannan harka dashi akwai bala in tsada just imagine fa bayan yabiya kudi yasayi kaya sannan still zai kawo 5% a profit dayay making na kayan daya saya but still haka mutane ke rushing nashi sabida kayanshi akwai kyau baka taba saya kafadi ba saikaci riba saisa zakaga kaman 5% daga profit din daya demanding is nothing compare to kalan riban dakake samu, tashi yayi ahankali yana gyara malummalum din jikinshi yace to godiya nake Pablo zan karasa dasu kaman yanda kace saida yakai kofa sannan kaman barawo yasake juyowa yakalli Maheer daya lumshe idanu yadaga kanshi sama yana huro hayakin taba in circles yadaura kafa daya kan daya sannan yajuya tareda bude kofan yafita Dan dake wajen yace are you in or out sir ? Dasauri senator yace wani kofa awajen Dan yabude yace to come with me Kusan 10min Dan yayi adakin daya kaisu sannan yafito yana daddana IPad saida ya knocking office din da Maheer keciki sannan yabude kofa yashiga yace Sir is time for the meeting kallon Dan yayi dayake tsaye a tsakiyan dakin, da yatsu yamai alamu daya karaso ya kawomai iPad din gabanshi sannan yakarashe zuke ragowan taban ya ijiye karan kan ashtray yakalli IPad din da wasu maza guda biyu kekan screen din daya Inyamuri daya bayerabe shikuma Dan yajuya yafita daga dakin. Sai wuraren 9 yagama meeting din tashi yayi harzai fita saikuma yakalli kofan bathroom na dakin ahankali yakarasa zuwa wajen yabude kofan yashiga alwala yadauro yafito dadduma dake cikin drawer desk din shi yadauko ya shimfida yayi sallan asuba yana sallamewa yamike yafito daga dakin su Dan da securities nashi na tsaye gaban dakin suna gadinshi cikin gida yawuce direct bude kofa yayi yashiga falon Nas yagani a falo zaune dagashi sai gajerren wando da singlet ajikinshi yahada cereal a bowl yanaci yana kallon AIT, ganin Maheer yasa dasauri ya ijiye bowl din yace Escobar gaskiya ayi hiring chef agidan nan nagaji da yunwa bansan mesa Boss tace kar adauko chef mace ba ita batason mata agidan nan, to tunda har yan aiki maza garemu akanme chef dinma bazamu dauko namiji ba, tunda maza ma yanzu sun kware a girki eh Pablo yay maganan yana kallon fuskan Maheer ganin idanunshi nakan tv kyam yana kallo a tsayen yasa dasauri Nas shima yajuya yakalli tv yace ohh wai kaji IG yacire tsohon CP yau ana nada sabo wannan Ibrahim Ibrahim din nan, he s 45, dan Bauchi ne fulanin Bauchi amman girman nan Abuja ne achan dutse, ance he s a very stubborn strict man but banwani damuba tundadai yaron CP da aka cire ne I am sure yasanmu da CP bazai bamu matsala ba ko Pablo wucewa Maheer yayi yafara hawan stairs saikuma ya tsaya chak kafin yajuyo yakalli Nas dake kallonshi yana tauna cereal na bakinshi yace if he dares mess with me i will mess with him right back yana maganan yawuce sama murmushi Nas yayi yace idanma baisan waye Pablo ba zaka gwadamai kallon Dan yayi dake tsaye kikam yace kaje kahadamai cereal ka kaimai cikin gurbataccen hausanshi Dan yace ba lallai yaci ba Oga, abincin wannan small eatry din kadai yake iyaci, sai anjima zamuje mu sayo cikin son kokarin tunawa Nas yace ohh wannan eatry nagane shi yama sunanshi I think ahhhhh yasa hannu aka yana kokarin tunawa yace something kaman Maman In Dasauri Dan yace Maman Intee s bite nunashi da yatsa Nas yayi yace yes correct, kai matan nan ta iya girki koni I love komi datake dafawa kusayo dani idan kunje KYALKYALIN KAUNA
Chapter 9 · 0% Book details