Sashe 84
Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wanda Maheer kawai take kallo aciki bawani ba, anatse Hamad yace "duba sauran" nabiyun tazaro takalla Maheer ne shikadai zaune akasan gada wani bridge haka ya daure fuska tamau kaman wanda ke shirin dambe nan ma da mutane lokacin akalla zaikai shekara bakwai haka nan ma kayan jikinshi yagaggu ga majina bushashe a hancinshi, sai kuma last picture data kalla wanda kaman ma Maheer baisan anyi hotonba yana karkashin wani bishiva shi kadai vadaura hannunshi akan fuskanshi yana kuka sosai, dasauri tadago kanta takalli Hamad ga mamakinta hawaye tagani akan idanun Hamad yasa hannu dasauri ya share, Hamad is a very emotional person gashi da tausayi, ahankali Hamad yace "Yasmeen inason kanina sosai, duk wanda zai cutarmin dashi kova wahalar mini dashi tsananshi nake sosai wh, dan Allah kada ki cutarmini da kanina kema" Hamad yay maganan was sababbin hawaye na zubomai dasauri ya sharesu Yakalli Yasmeen anatse ace "naso Maheer shine zai baki tarishinshi dakanshi but I guess bazaitaba iyawa ba dan baida surut baida magana ko kadan Maheer" Hamad vasakeyin shiru kafin ahankali yace "inaso nabaki labarin Maheer ne sabida ki sassauta kowani kalan hukunci kikemai ko kikeso zakimai Hamad yasakeyin shiru kafin ahankali yace "bantaba gain yaron daya taso cikin kunci dakuma lonely life kaman Maheer ba, toro, damuwa ba kaman Maheer, dudda ni iyayena duka biyu makafi ne suka haifeni, dudda mahaifiyata tarasu amman nafi Maheer jin dadin ravuwa nesa bakusa ba" yasake yin shiru kafin ahankali yace "mahaitiyar Maheer was a criminal yar fashi ce though shi karan kanshi baisan labarin ta ba but dai yar fashi ce bayan an kamata aka kaita gidan yari KIRIKIRI FEMALE PRISON a lagos sunanta Hafsatu, Mahaifin Maheer was a guard a prison din sunanshi Aliyu Maheer, yaya akayi oho rana daya akaga mahaifiyar shi da ciki agidan yari matan datai kusan 2vrs a prison din rana dava aka ganta da ciki, dudda taso tai abortion but ba halinyi agidan yari, investigation wayamata ciki aka fara tafada Aliyu ne dalilin dayasa aka sallameshi a aiki kenan aka koreshi daga aikin gidan yarin, itakuma tacigaba da rainon cikin dabataso dudda taso takashe dan cikin ta hanvar kin shan magungunanta da sauransu ahakadai ta haifi Maheer anan gidanyari, ba'a rabata dashi ba haryay shekara daya da rabi tareda ita dudda bawai wani kula dashi takeba wani zubin idan yana kuka ba sai prison guards mata sunzo sun danneta tabashi nono da karfi dayaji, kafin 6month Maheer nacin komi inii Maman dan ita keba da labarin a area mu, akarshe dai sabida Maheer data haifa gwamnati tayafe mata laifinta tafito nan sukai connecting da mahaifin Maheer kulle dan sabida shine aka yafemata tafito ta raini danta da kyau so hakanan ta yarda sukai auren yadawo da ita nan Abuja cikin chan wani kauye a maraba dasu axis na nyanya dan sufara rayuwa afresh" Hamad yadanyi shiru nakusan 2min kafin ahankali vace "Fateema a asalin ghetto side na nyanya muka girma, area da thugs, criminals, waye waye ke zama, tunda nake bantaba ganin iyayen dazasu haifi yaro amman kaman basu suka haifeshi ba sai akan iyayen Maheer, kallonshi suke a mistake child, basason haihuwa to babanshi agbero mahaifiyarshi ma haka, basa bashi abinci, basamai wanka, basamai wanki, basu sashi makaranta ba, baida ma takalmin kafa, kusan mahaifiyarshi tamafi tsaneshi ne sabida gane take sabida shi takasa cigaba da rayuwanta, takasa komawa past life dinta, gashinan tazauna batada kudi kuma bata isa tabarshi ba kada asake maidata prison, sannan kullum mahaifin Maheer da ita bala'i suke, dambe, dambe, dambe kaman yan gidan dambe makota harsun gaji da shigowa ana rabasu, ke amsa sansu kina shigowa cikin layinmu kikace gidan dambe zaa kawoki gidan mu danmu makotansu ne duk haya muke agidan, Maheer na yaro but he is such a sad boy sabida vanda kullum mamanshi da babanshi dambe sukeci har kofar gida kuma basu rabu ba, wani zubin dambe babanshi har Riga yake cirewa a titi, Maheer tsoron iyayenshi ma yake kaman yaga doddanni, kaman baya cikinsu idan zaiyi kwana biyu basu ganshi ba bazasu taba nemanshi ba, kullum dare saidai varaba yashiga ya kwanta kusada kofa yay bacci akasa, sannan kusan kullum akan Maheer karami suke juve anger su bayan fada suma yaron nan shegen duka saisa yake mutuwan tsoronsu yaron yazo yanada bakin zuciya da taurin ral, Maheer has been a traumatized little boy kinsan mesa Maheer baida magana sannan baya dariya kullun zakiga fuskanshi ahade"? Dasauri Yasmeen ta girgiza kai Hamad yace "sabida iyayenshi, kinsan ya akayi muka zama friends"? Girgizama kai Yasmeen takarayi shiru Hamad yayi hawaye suka kara fadomai daga idanu yashare dasauri yace "Mamanshi bata bari yay magana da kowa agidan mu da area mu, idan suka fara fada suna dambe toro saiyasa yafito vana kuka vana neman inda zai bove vadaura hannuwanshi biyu haka akunne" Hamad yadaga hannayenshi yana nunama Yasmeen vace "yahau kuka sosai yana juye juye da neme neme munada wani babban cage na kaji Maman mu lokacin" Hamad yadanyi shiru kafin ahankali muryanshi narawa sosai dan he's damn emotional yace "cage din kajin nan, nan Maheer kezuwa yashiga ya boye tareda kaji yataushe kunnenshi yana kuka sosai tun safe har dare ba ruwa ba abinci, duk idan naje kaima kajinmu abinci naganshi yana kuka yasa hannu akan lips dinshi vana kallona alamun nai shiru kada in nuna yana nan Maman shi tazo ta dakeshi, ragowan abincin mu dana kawoma kaji zai karba vahauci yana kuka ahaka daganan abincina sainaki ci nakawomai yaci Nima sainashigo cage din dagani sai shi sai muyita wasa yadaura kanshi kan kafadanta yay bacci kaman baya bacci agidansu yana munshari ya rikemin hannu gam irin kaman kada natafi na barshi" hannayenshi Hamad yadaga yadaura kan idanunshi yanadan huci mai zafi sabida kuka itama Yasmeen tasa bayan hijinta kan idanunta kawai sabida kuka labarin na wani kalan sosamata rai, kusan 3min Hamad yayi ahaka sannan yazare hannayenshi yasauke ijiyan zuciya ahankali ace "watarana fada yay fada agaban Maheer suka kunna wuta adakinsu wai saidai sumutu dukansu dan Baban Maheer yace mata zai kara aure, Maheer yagudu yafita daga dakin yana taushe kunnenshi yana kuka yashiga cage na kaji yalabe as usual, dakinsu yakama da wuta kafin kice me wuta yakama duka gidan ma yan gida aka fara fitowa waje kowa dagudu, nadawo daga makarantan allo kenan da allo a hannuna naga wuta yakama gidanmu gasu Baba duk awaje naji ana cewa ai mutanen prison dinnan ne suka sa wuta wato iyayen Maheer, dasauri najujjuya banga Maheer adandazon mutanen wajen ba, dudda ana ihu ana kirana saida nafada gidanmu da wuta keci dagudu naje wajen Maheer daketa tari cikin cage dan nasan nanne wajen buyanshi na goyashi muka fito cikin ikon Allah ko wuta daya baitabamu ba dagani har shi, Yasmeen" Hamad yakira sunan Yasmeen ahankali ace "iyayen Maheer sun mutu kaf anguwan mu da masallatan mu ana tambayan wanda zai dauki Maheer dan ba'asan yan uwansu ba baasan usulin iyayenshi ba balle akai Maheer amman kowa yaki wai basason irin tsiya, yaron bai fito daga tsatso Mai kyau ba yaron criminal dasukai zaman gidan yari suka haifeshi, anguwanmu kakap babu wanda baisansu da dambe ba, Babana baida komi gashi lokacin mahaifiyata batada lafiya but yanda yaga inason Maheer har nashiga cikin wuta sabida shi vace shi zai dauki Maheer vadawo danshi dagayau baba yahadamu gashi gidan damuke haya yakone yashiga nema mana wani gida da yan kudaden davake dashi sabida yadauki Maheer akaki bashi haya hakan vasa muka koma kasan gada musami makwanci dan Mama batada lafiya sosai, Maheer dakika gani yau has always been like this dudda yanda Babana da Mamana ke sonshi shi bayason mutane, murdadden yaro ne tun yana yaro, baya zama inda suke bava zama inda mutane suke, ko akasan gadan haka zaie yanemi wani lungu ko sako shi kadai yaboye, ni kadaine komi na Maheer, idan kinaso kiga murmushin shi saiyana tareda ni, idan kinaso kiji muryan Maheer kimasan yanda yake magana kiji kalan maganan shi to salyana tareda ni, idan aka aikeni nadawo banga Maheer ba all I need to do is naie naduba maboya lunguna, waje mai shitu shiru daba mutane to zanga Maheer, is as if nine Mamanshi, nine babanshi, nine abokinshi, nine kuma komi nashi aduniya, wlh koda za'a bashi naira biyar ko irin mutane sunga yaro da yagaggun kaya haka su bashi abu bazai tabaci ba saiya ganni zamuci, ahaka da karfi da yaji na jashi munakai Baba bara dan Mama nata ciwo sosai kudadenmu sun kare tass, koda munsami kudin kama gida asibitinta keciyewa dan cancer gareta na jini hakan yasa muka dage da bara dan babu mai taimakonmu, [7/24, 4:46 PM] SAFIYYA: livan zuciya tasauke cikin kuka tanuna kanta tace "ban damu naji anything else ba dudda he wanted to explain things to me ban bashi listening ears ba, ban saurareshi ba, idanuna sun juya banji ban gani I said nasty things to him, I said terrible things to him, Ya Hamad am even worse than matan data cutar dashi dan nima na cutarda shi Yasmeen tafashe da kuka zuciyanta har nauyi yake mata sabida tausayin Maheer da bala'in damuwa dakuma that guilt feeling a abubuwan daya gayamai dakuma wayanda tamai harda marinshi, dan tsugunnawa Hamad vavi agabanta vace "stop crying pls" cikin kuka tace "I can't, How do I make up for my mistakes Ya Hamad kifadamin pls, ban kyautama Maheer ba at all please help me Ya Hamad" dan murmushi Hamad yayi ganin how much Yasmeen keson Maheer yace "goge idanunki to" da kyar ta tsayar da kukan datakeyi takai hannayenta ta goge idanunta tass takalli Hamad da shima idanunshi sunyi ja sabida kukan dayayi dan murmushi yayi yace "dukanku kannina ne dagake har Maheer, yanzu inaso yau ki koma gidanki flat dink kada kisaka kwanan anan, amman before that you are the lady kada ki koma just like that saiyazo yakara baki hakuri ya lallabaki which I know definitely zaizo, I know kin hakura har ranki but kidania aji but bada vawaba kuma kada ki wahalar mini da kani" Hamad vadan harareta yana murmushi vace "yanzu kidan ja aji dan ficici saiku shirva karki nunamai u know all this pls, kada ki nunamai u know anything bazaiji dadi yasan nagaya miki ba, saisa dagani har Baba