Sashe 50
Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bakin balarabe Masha Allah tubarkallah shewa sukayi, jin Baffa na kwala musu kira yasa duk suka saka hijaban su suka daddauki su drinks da ruwan gora suka fita dashi, anatse Baffa yace ga iyayen Fateema nan gaggaishe su sukayi Maheer yakasa dagokai suka wuce suka koma daki sannan Baffa yace to bismillan ku Gyaran murya Baba Makaho yayi yace to godiya ya tabbata ga Allah ubangiji daya hallice mu ya raya mu sa an nan ya nuna mana wannan rana, dafarko dai sunana Alhaji Maheer Makaho, haka aka haifeni da makanta, gaskiya dana taso iyayena basu da shi ahaka ahaka dai nasamu wata makauniya irina marigayiyi mukai aure Allah yamata rasuwa yanzu atare kowa yace Allah gafarta mata ahankali yace Ameen sannan yace bazan muku karyaba dalilin d ana ne nazo gidan nan yau, yarana biyu da Hamad wanda shi likita ne saikuma Maheer pharmacy yakaranta amman bai sami aiki dashi ba Allah yabashi aikin koyarwa english kaman yanda nafadi, banda shi duka yaran nan nawa da scholarship sukai karatu akasan waje Alhamdulillah Baba yasakeyin shiru kafin chan yace yaran nan yarane dasuka taso na koya musu ladabi biyayya natsuwa da bin Allah ma aiki, Maheer yasameni da maganan yaga wata daliba a makaranta sunanta Fateema yanaso soyayya irin ta aure bawai soyayyan da akeyi a zamanin nan ba, saidai yabukace ni dana fara ganawa da iyayenta amai izini yanemeta tukunna dan bai dace yatari yarinya a school yana mata magana ba karatu tazo yi a school ba soyayya ba jinjina kai Baffa yayi maganan na shiganshi, cikeda dattaku Baba yace to gani ga babban aminina da yarana gakuma Liman shima aminina ne kuma zai iya wakiltata ako ina munzo mu nemama danmu iznin neman auren diyarku idan babu kowa, idan suka daidaita nan bada jimawa ba ayi aure da izinin Allah to mekuka ce ? Shifa Baffa yasan halin kaninshi to bazai taba bari yakori mutanen arziki da mutunci haka bane dake neman Yasmeen ba, anatse Baffa yay gyaran murya yace a gaskiya naji dadin wanna halin karamcin irin naku da sannin amfanin iyaye, sannan babu wani wanda ke neman aure Yasmeen wato Fateema dan haka nabashi izinin nemanta idan har komi ya daidaita saimu hada bikinsu taredana yayarta Sa adatu da za ayi nan da wata daya In sha Allahu murmushi kowa yayi ana Alhamdulillah, Baba da tunda suka zauna Maheer yake kallo atsanake yace Fateema is AS genotype dinta, menene genotype dinka ? Kowa bin Baba yayi da kallo Baffa kaman ya make Baba dan baisan what s all this ba yanzu aka fara magana za azo kan genotype nan gaba, dan dagokai Maheer yayi yakalli Baba kafin ya sunnar da kanshi kasa dasauri, cikeda kamala yace ni AA ne Abba hamdala Baffa yayi hakanan yaji yanason Maheer wlh dan yaron ga kunya ga sanyi ga rashin magana, daukansu Baba bazaice komiba yace I need general blood test naka from a well known hospital saikuma yadanyi shiru bai damu da yanda kowa ke kallonshi ba Baba yace ban yarda ka taremini yarinya a titi ko a school ba ban yarda ba, Fateema karatu nakeso tayi banson tai loosing focus, ranan lahadi zan iya baka kadinga zuwa har nan daki a falon mahaifiyarta ka ganta kuyi magana na tsawon awa daya gyadamai kai Maheer yayi ahankali, Baba yace banson yawan kira, kira once in a day ya isa sake gyadamai yayi Baba zai kara magana Baffa yatareshi da sauri ta hanyar cewa to Masha Allah, yanzu dai in sha Allahu tunda yau juma a ranan lahadi saiyazo shida yarinya su zanta zamu kira yarinyar mu tambayeta idan tai na am dashi zamu danyi yan binciken mu kafin mukiraku mu sanar daku kuzo asa rana da izinin Allah dasauri Baba yace zata cigaba da karatu wannan karan Baba Makaho bai bari Maheer ya amsaba dan kafin yay magana yace In sha Allah ai ilimi gatan bawa ne, ilim adon diya mace Fateema zata cigaba da karatu harsaitaji ya isheta Baba zai kara magana Baffa yace to bismillan ku muci abinci badan Baba yaso ba ya kalli Baffa sannan yadauke kai. Sosai su Baba Makaho suka saki jiki sukaci abinci Hamad ma vaci dan abincin gidan dadi Maheer nedai vakasaci sai wasa yake da spoon har aka gama, gaggaisawa akayi Baffa bai kara bama Baba room to talk ba suka shishigayin sallama Baffa na karban nambobin wayansu dakuma adreshin gidansu, sannan Baffa yakalli Maheer daketa sussunar dakai yace "muna jiranka ranan lahadi" gyadamai kai ahankali Maheer yayi sannan suka fiffice suka tafi.Koda suka dawo gida Baffa bai karabi takan Baba ba, Baba yatafi office kawai dan baiso abinda Baffa yamaiba kawai babu yanda ya iyane dan bazai iya ja dashi ba.6 dot suka fito daga lectures fitowa tayi daga class ga mamakinta Baba tagani gaban ajinsu yana kallonta kuri, ahankali tace "Baba, ina yini" dan murmushi yasakin mata yasa hannu yakarbi jakan nata tareda kama hannunta kaman yar yarinya yace "mutafi" awani kalan kunyace ta gyadamai kai tareda binshi har zuwa inda yay parking sai kallonsu ake, budemata mota yayi tashiga ta zauna yasamata jakan ajiki yarufe yazagaya ta dayan side din yazauna yaja motan, sundanyi nisa suna tafiya kaman daga sama yace "wani yataba miki magana a school din nan kan soyayya"? Dasauri takalli Baba gain hankalin shi nakan tuki vasa ahankali tace "a'a Baba" bai karace mata komiba agaban wani shagon abubuwan Habib yoghurt ya tsaya fita yayi yace "kijirani" kusan 13k ya kashe a shagon ya damo fura dayawa for kowa na gidan Nana kadai yasayama zallan yoghurt dan ita bata iyashan yoghurt mai hade da furaba har yanzu sannan yadauko ledan yazo yabude motan yabama Yasmeen karba tayi yamaida kofan yarufe yazagayo yashiga yatada motan suka wuce gida suna kaiwa bai shiga gida ba yawuce mosque dan anfara salla a masallaci itakuma Yasmeen tawuce cikin gida, babu kowa a tsakar compound dan kowa na daki yana salla sallama tayi ta shiga dakin Ammi daidai Ammi na sallame Salla Nana agefenta jiye ledan yoghurt din tayi gaban Ammi tareda zare hijabin ta yar akasa ta kwanta tadaura kanta kan kafan Ammi dakekan dadduma tace "wasshhh Ammi nagaji wh, Nana kawomini abinci na naci" tashi Nana tai dasauri ta wuce tafita dan zuwa dakinsu tadauko kulan abincin Yasmeen fuskan Yasmeen Ammi tashafa tace "yau wasu mutane sunzo neman aurenki" wani kalan faduwa gaban Yasmeen yayi dasauri takalli fuskan Ammi tareda tashi zaune kirjinta nawani kalan rawa, dan dariya kadan Ammi tayi tace "to matsoraciya relax Babanki yagansu yace yaron yazo yaganki jibi lahadi, saikin ganshi kafin ayanke decision kinji" gyadama Ammi kai tayi ahankali daidai Nana tashigo da kulan tace "Anty Yasmeen gashi" karba tayi ahankali itama tajawo ledan yoghurt din tace "Baba yasayo mana fura" karba Ammi tayi ta shiga rarrabawa adaddafe Yasmeen taci abincinta duk yunwan datakeji kasaci tayi sosai takarbi fitan ta tafita daga dakin zuwa dakinsu ijiye komi tayi tafita tayi alwala tadawo salla tayi sanan tajuyo takalli su Sa'a da tunda tashigo suke kuskus ganin taki tajuyo yasa suka kwashe da dariya Sa'a tace "wayaga Yasmeen amarya, ni wl naji dadi sosai Allah sa ahada bikinmu tare" wani mugun harara Yasmeen tamata baki tabude zatai magana sai kuka baki daga Farida har Sa'a suka saki baki suna kallonta yanda hawaye ke sauko mata tana kai bayan hannu tana gogewa da sauri sunki tsayawa dudda ba kuka take da karfi ba, Farida dasauri ta rarrafo zuwa wajenta kaman itane babba ahankali cikeda so tace "Anty Yasmeen bakiso kiyi aure kibar gidan nan saisa kike kuka"? Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali dan bazata taba iya fadin abinda ke damunta ba dasauri Farida ta rungumeta tace "kidena kuka please kinji Anty Yasmeen babu inda zaki nima banso kibarni wazai dinga dafa mana indomie da abinci mai dadi, wazai dinga kawomana su cake da zobo daga shago eh" itama Farida tahau kuka, tsaki Sa'a tasaki tace "wIh kunci kun koshi ne van iska to dan kuji dukanku har Nana saitayi aure wata rana tabar gidan nan" sake rushewa da kuka sukayi daga Yasmeen har Farida babu mai lallashin wani hakan yasa Sa'a tamike tace "wlh bani zakusa a trouble ba dan Baba yashigo yaganku kuna kuka kunga tafiyata wajen baabata' ficewa tayi daga dakin abinta, da kyar Farida tai shiru sannan tadago kanta fuskanta ta share tass sannan takalli Yasmeen dake kuka, hannunta takai kan fuskanta ta sharemata hawayen tass tace"kidaina kuka, ba ance ran Sunday zaizo ba tunda bakison Auren saiki fadama Baba kinji" Gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali, Farida tace "tashi to muyi salla idan mun idar saikiyi raka'a biyu ta istikhara ki nemi zabin Allah" batai musu ba tashi tayi suka fice sukayi alwala sukai isha'i sannan tayi istikhara abinta tagama takwanta kan dadduma tai shiru tunani yamata yawa, she's thinking of Maheer kaman ba gobe, koyaya tai numfashi shine kawai takeji azuciyanta, she's afraid of him, tana tunanin yanda zata aureshi bayan tasan criminal ne, tana tunanin abinda Zaima su Baba da duka yan gidansu idan tafadi dan tasan zai iya tunda har ya iya kidnapping dinsu duka, yasan makarantan su yasan ajinta yasan wajen aikinta yasan number a number ta daga yan gidansu sai Maman Intee kedashi ya akayi yasamu oho yasan gidansu ta tsinke da lamarin shi yanda yace zai kashe su baba zai iva data zama sanadin da iyayenta zasu mutu gwara tazama sanadin dazasu rayu all abinda tasani shine idan har akeai next life bazata taba bari Baba yazama police ba infact she hates the job sabida kana haduwa da criminals daban daban dazasu addabeka da family ka gashi yanzu she's the only one day can save Baba da duka yan gidansu, all this aside shi Maheer din ko Pablo nema oho akwai wani iri datakeji azuciyanta gane dashi first of all tanason yanda yake kamshi bata tabajin kamshin turare aduniya kai dadin nashi ba, saikuma yanada bala'in kyau saisa bataso tana kallonshi bata taba ganin namiji Mai kalan kyanshi ba, manyan idanunshi, digon hancinshi, bakinshi da pink lips nashi, bakin cikakken giranshi da gashin kanshi dana saje bala'in mata kyau suke, tsayinshi na burgeta sosai, saikuma everything about yanda yake magana da yanda yake share mutum da yanda yake daukan lokaci kafin yabada amsa da kuma muryanshi ita