Sashe 47
Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da sauri dudda already shi yasan wace girl Maheer yake nufi, sake shiru Maheer yayi kafin chan yace Fateema you mean Yasmeen? Yarinyar dakai kidnapping nazo namata treatment ? Murya chan kasa Maheer yace eh, yarinyar comissioner of police dasauri Hamad yace yarinyar da Babanta ya kwace kayanku ai tafadamin ranan shiru Maheer yayi bai kara cewa komiba sai danna waya dayake wanda Hamad yasan bawai wani abun kirki yake dannawa ba, yadade yana kallon Maheer saikawai yasauko daga table din yakaraso gabanshi hannu yasa ya karbi wayan hakan yasa Maheer yadago kanshi dasauri, sa wayan Hamad yayi a aljihunshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda seriousness yace Maheer kasan what u are telling me kuwa? Yarinyar comissioner of police dayake nemanka ruwa a jallo yay arresting kakeson ka aura? How? Tayaya? Did you even know abinda kakeyi? Maheer kanaso kaje prison ne? Eh ? Hamad yay maganan cikeda damuwa, dan shiru Maheer yayi yana kallonshi idanunshi sunyi ja anatse yace I don t care about anything I just wants to marry her dasauri Hamad yace is she the reason dayasa ka nemi lecturing a school dinsu ? Gyadama Hamad kai Maheer yayi ahankali, sake yin shiru Hamad yayi yana kallon Maheer din kaman yanda yake kallonshi kafin anatse yace Maheer son yarinyar kake ne? Shiru yayi yakasa magana Hamad yace talk to me, are you in love with her ? Lumshe idanu Maheer yayi kafin yabude murya chan kasa yace I don t know, I don t understand myself, I don t even know the meaning of all this things danakeyi, I don t know anything again, all I know, all I see is just her dudda Hamad so yake yayi murmushi daurewa yayi yace to tayaya zaka dumfari wannan dan sandan kace zaka auri yarshi kaima kasan bazai taba bakaba wannan ma super story ne, sokake asirinka ya tonu yarinyar ai she will tell Baban ta wayekai girgixamai kai yayi cikeda damuwa anatse yace he will never know nine, I will handle the girl dasauri Hamad yace tayaya? Wai Maheer kasan me aure kuwa? Aure is not one of your tricks fa? You can t handle aure kaman yanda kake handling harkan cocaine, Maheer wai kakosan wat you are getting kanka into kuwa? Lumshe idanu Maheer yayi saikawai yasauko daga bakin gadon azuciye zai wuce yayi kofa hannunshi Hamad yarike yace ina zaka muna magana ? Azuciye Maheer yajuyo cikin tsananin fushi yace why are you asking me all this questions? Kasan menake going through? Kasan meke damuna? See Hamad I don t believe in Marraige you know that but nima bansan meke damuna ba this girl has become like parasite tazo tashiga jinina she s everywhere in me, the thought and everything is driving me mad, Hamad I see her in my dreams, I see her idan nabude idanu, I see her in everything danake, tunda tashigo rayuwana I can t handle anything again, not me not my empire, what do you want me to do inba in aureta ba? Maybe if she s close to me bazan dingajin abinda nakeji ba but why do you keep questioning me Hamad why why why ? Bakaramin baci ranshi yayi ba yayi shiru saikuma chan yanuna kanshi yace kasanni sama da kowa d normal Maheer daka sani it will take me not less than 2hrs I will kidnap this girl nadauketa tadawo wajena har abada and nothing will happen but no banyi all this ba I want to marry her legally base on addini nasan tana taredani ne amatsayin matan aure not yarinyar danai kidnapping wrongly but why are you asking me all this questions is it because I come to you I can do this myself kasan dahaka ko ? Kafadanshi Hamad yakama anatse yace calm down Maheer kaima kasan I will always support you, you are the only brother danake dashi aduniya uhmm tambayoyin danake maka is just to look out for u Maheer yanzu mekake so ? Lumshe idanu Maheer yayi Hamad yabishi da kallo wato idan Allah yatashi kamaka baya maka da kyau rana daya Allah ya jarabi Maheer da mahaukacin son yarinyar mutumin dakeson kaishi gidan yari. Bude idanunshi Maheer yayi ahankali yace inaso karakani muje nama Baba maganan aje a nema mini aurenta sannan mu taushe any loophole dan nasan kafin ya bada auren yarinyar nan saiyay binciken sama da kasa shiru Hamad yayi yana kallonshi anatse yace yarinyar fa ? Ahankali Maheer yace I will handle her ita jimm Hamad yayi yana kallonshi saikuma yace wacchan matar fa yazakai da ita dan yatsine fuska Maheer yayi yace batama cikin lissafi na she s not relevant and she will never know ahankali Hamad yace Maheer kallonshi Maheer yayi baice komiba, shiru Hamad yayi yana kallon idanun Maheer din all abinda yagani is sincerity da tsantsan so, gyadamai kai yayi yace shikenan I will support you nadawo gida anjima sai muje muma Baba magana idan yaso shida Mallon Sani sai suje gidan su ko gyadamai kai Maheer yayi kafin ahankali yasaki dan murmushi yajuya yafice daga office din Hamad yabishi da kallo har cikin ranshi yasan this is first step na shiryuwan Maheer, idan ta wannan sanadin Allah yakeso ya gyarashi to Allah ya tabbatar da Alkhairi yakara raba shi da matan nan dan she s not Khair in his life. EPISODE 4 https://www.instagram.com/p/CtwFCtXITwD/?igshid=YjgzMjc4YjcwZQ== Yasmeen na zaune a shagon Maman Intee dan tunda tashigo tazauna Maman Intee nata mata hira, tana bata labarin yanda customers din nan nata suka daina zuwa yanzu bata ciniki sosai, bata iya magana kawai bin Maman Intee take da idanu da abinda ke damunta yafi karfin tunanin ta, harsaida Maman Intee tace Kodai har yanzu bakiji sauki bane tace a a taji kanta kedan ciwo tasa hannu suka fara filling na samosas datakeyi. Tana cikin hada salad wayanta dake cikin jaka yahau ringing faduwa gabanta yayi takalli agogo dasauri this is just 2:15 na rana Baba ne ke kiranta amman normally yau 5 zata gama lectures sabida duniya dataji yamata zafi ne yasa tazo nan shagon Maman Intee kota manta damuwanta, dasauri tagoge hannunta tawuce wajen jakanta tabude wayan taciro takalli screen din, wata bakuwar number ke kiranta ba number Baba bane hakan yasa ahankali tace waye wannan number kuma ? Maman Intee dake bama Intee nono tana jinta tace ki dauka kiji ko waye gyadama Maman Intee kai tayi ta danna wayan takai kunnenta cikin sassanyar muryanta tace hello har tsakiyan kanshi yaji dadin zakin muryanta, cikin wani irin cool romantic voice yace inajin yunwa sosai Fateema, am outside shagon ku, bring food for m dawani kalan sauri Yasmeen tazare wayan daga kunnenta ta shiga daddanna screen din tana kokarin katse wayan harsaida Maman Intee tace ke lafiya? Waye kika kashe wayan da gudu haka ? Rasa abinda zatace gabanta na faduwa sosai yasa tace .wani mutumi ne yanda tabada amsan zakasan tasan waye, dasauri Maman Intee tace wani mutumi kuma ? Rasa abinda zatace tayi saitai shiru tana zaro manyan idanunta tana kallon Maman Intee tana maida wayan jaka da sauri, Maman Intee yar gari ce tasan whatsupp dan dariya tayi da shewa tace yaushe kikai saurayi Yasmeen ? Zaro idanu Yasmeen tayi sosai tanuna kanta tace dariya sosai Maman Intee tayi ganin yanda tayi tace kwarai kuwa ke, watanki nawa kina zuwa shagon nan inhar wayanki tai ringing kodai Baban ki ko Mamanki ne ke kira, bantabajin wani ya kiraki ba, yarinya har yarinya gaki kyakkyawan gaske black beauty abinki amman baki kula samari ni nasan duk sabida Baban ki ne yanzu dai waye wannan ? Rasa abinda Yasmeen zatace yasa tace lecturer mu ne wani kalan kecewa da shewa Maman Intee tayi tace to meyake so ? Ahankali tace uhmmmm cewa yayi yana waje wai yunwa yakeji zaro idanu Maman Intee tayi tace shine kika barshi tuntuni hannu Maman Intee tasa tajawo Hijabi dagakan kofa tabata tace maza saka kije ki shigo dashi nan wani kalan miyau Yasmeen ta hadiye tana zaro idanu gabanta nafadi baki Maman Intee takama tace ohh ni jama a duk wanda yaganki yasan sabon shiga ce ke a harkan samari, idan tsoron Baban ki kike kinsan dai bazai taba kamaki anan ba ko menene amfanina idan bazanyi guiding naki ba, wuce jeki shigo dashi idan naganshi mai hankali ne dakaina zan kira Ammi ki namata wannan sanarwan, wuce kije kishigo dashi Gyadamata kai Yasmeen tayi duk atsorace take ya akayi yasami number ta, ya akayi yayi tracing nata zuwa nan wannan wani kalan takadirin maye ne? Da gaske babu inda bazai iya samota ba, ahankali take tafiya kanta akasa har zuwa waje motan ita kadaice pake awajen hakan yasa takara hadiye wani kullutun abu awuya tawuce wajen motan kafin takai taga an bude kofar baya alamun nan zatazo hakan yasa takarasa wajen, ko cikin motan bata kalla ba kanta akasa tana wasa da dogayen yatsunta ahankali kaman yar yarinya tace ance .ance kashigo tunda tafito yake kallonta hartazo wajen, hannayen ta datake wasa dasu ya kalla kafin yasaki dan murmushi softly yace wayace in shigo ? Dan dagokai kaman barauniya tayi danta kallai karaf suka hada ido dasauri tasauke kanta kasa, murya chan kasa kaman mai shirin fashewa da kuka tace Maman Intee tana maganan tajuya da sauri tawuce ciki yabita da kallo wani irin sweet smile yasaki ganin dukya kara firgitata ganinshi datayi yazo nan kuma yakira number ta, ga mamakin Dan saukowa yayi daga motan tareda gyara zaman suit nashi ya da bakin glass na idanunshi yafara tafiya ahankali yawuce cikin shagon tana tsaye chan wajen kanta, kujerun dake wajen tanunamai da yatsa ahankali tace kazauna murya chan kasa yace okay Wifey dasauri takalleshi shima ita yake kalla tareda zare glasses na idanunshi daidai Maman Intee tafito tace laaaa shine tabarka bata baka ruwa ba kaga shirmen Yasmeen ko tajuya takalli Yasmeen dake rakube awajen kanta tace wuce kije ki dauko ruwa sai kizo ki tambayeshi mai zaici yafito daga aiki keda kikasan harka da dalibai da wuya imaza juyawa tayi tashige ciki itakuma Maman Intee takaraso wajen kan Maheer akasa kaman bashi ba yace Ina yini Hajiya washe baki Maman Intee tayi tace ina Hajiya ai kirani da Maman Intee na ai yanzu an dawo daya, to