← Book details Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 93

Sashe 22

Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kankame idanunta tana kwakume Yasmeen gamgam ta bayanta kaman zata barka mata riga irin yanda yara keyi din nan idan sunga wanda suke tsoro tace Anty Yasmeen Ammi Ammiii tana maganan tana makyarkyata tana sakin fitsari bin fitsarin fitsarin Maheer yayi da kallo datakeyi tana kuka cikin fushi yakalli Wike yace why did you bring this child to my house bayan kasan how much I hate children haaaa, shoot her idan batai shiru ba! Dawani kalan sauri Yasmeen tadago kanta takalleshi tana boye Nanah abayanta da kyau gabanta na bugawa ita bama tasan ko kallonta yake koba kallonta yakeba sabida glasses na idanunshi but dai fuskanshi na kan kallonsu ne, cikin wata kalan muryan dake cike da tsoro mai kuma mugun sanyi tace s just a child that is very scared, idan da wacce zakasa a harba adakin nan should be me! Not my sisters for the first time Maheer zubama Yasmeen manyan idanunshi yayi dudda ta cikin glass ne kasa jurewa tayi tadauke kai da sauri ta tsugunna tareda kallon Nana da idanunta ke kulle gamgam kaman na Farida ahankali tashafa kanta da fuskanta tace kiyi shiru Nanah kinga Uncle bayason kukan yara, please Nanah zan kaiki wajen Ammi idan mungama kinji yi shiru to Nana na gyadama Yasmeen kai tayi ahankali ta rungume Yasmeen da sauri, ahankali Yasmeen ta mike tsaye tareda sauke Nanah taboyeta abayanta sannan tasauke kanta akasa tana wasa da yatsunta kirjinta bugawa kawai yake kaman tashin aradu, da hannu Maheer yama Dan alamu yabasu wani takarda da Dan ke rikeda shi hakan yasa Dan yataho gabansu baya Yasmeen tayi dasauri a tsorace ganin wani ya nufota, Maheer duk yana zaune inda yake yana kallonsu, tsayawa daidai gabansu Dan yayi yana kallon fuskan Yasmeen din ganin kaman yataba ganinta amman yakasa tunawa yabata paper tana wani kalan nishi kaman zata shide ta amsa tana kallon paper, Dan yace wannan sakone zuwa ga Baban ki da zaki karanta yanzun nan zan muku video idan zaki fara karantawa dazamu aika mishi, let s hope he listens yasaki kayanmu muma musake ku yay maganan yana komawa baya itakuma Yasmeen na kallon rubutun takardan da takasa gane komi ciki ko abin yahadu da she s under stress da tsoro ne oho but word na farko kadai ma takasa karantawa ballantana sauran, waya Dan yaciro yakunna video yakalli Yasmeen din yace kifara nafara video gyadamai kai tayi ahankali takalli paper tana ware manya manyan idanunta dasuka kara haske tass sabida safiya ne kwaiduwan idanun sunyi gray sosai tana kokarin karanta word na farkon ma takasa, ahankali Maheer dake shan taba yadago kanshi yadaura mayun idanunshi akan fuskanta yana kallonta tundaga kan hannayenta data rike paper gamgam yatsunta na motsi sosai da dan tiny little red lallen daya rage a kumbunanta, zare hannunta daya tayi daga rikon datama paper takai yatsanta dasauri tadaura akan letters din kaman mai koyan ABCD tace ..Paaaaa tasake kakarewa dakin yay tsit ana kallonta, kafin takara daddagewa da duka karfinta hawaye na taruwa a idanunta tsabagen yanda take fama ta karanta tace Paaaa .boooo Daidai nan hawaye ya sauko daga idanunta dasauri takai bayan hannunta ta share kwallan tana kara ware manyan idanunta trying to read it by fire by force kowa na kallonta na dakin, ahankali Farida dake bayanta tafito gently tasa hannunta akan paper tareda kallon Yasmeen murya chan kasa tace kawo na karanta Anty Yasmeen gyadamata kai Yasmeen tayi ahankali gwanin ban tausayi sannan tasakin mata paper karba Farida tayi tadan dagokai takallesu kasa kasa dan takasa kallon fuskan kowa kafin tasauke kanta dasauri cikeda tsoro tace my sister nada matsalan hada baki so I will read sosai Maheer ke kallon Yasmeen data tsaya gefen Farida innocently har lokacin kwayan idanunta na kyallin hawaye sabida hawaye dasuke ciki, anatse Farida tafara karanta takardan. Pablo Escobar yabaka 1hour kasaki his shipment da drivers nashi yasaki maka yaranka inba hakaba zaka tsinci gawawwakin yaranka ukun nan dakake gani akan video agaban police station dinku Fashewa da kuka sosai Farida tayi cikin wani kalan muryan tsoro da tsantsan tashin hankali ganin sunce zasu kashesu tace Baba dan Allah ka basu abunsu we are scared Baba katse video Dan yayi yajuyo yakalli Maheer dake kallon Yasmeen har lokacin cikin glass nashi yace s done Sir gently Maheer yamike tsaye ganin zai juya yasa cikeda Yasmeen tace kaine Ogansu ko ? Chak Maheer ya tsaya batare daya juyoba hakama yaranshi, Dan yakalli Yasmeen datai magana yace ke are you okay kike tambayan sir ko shine Ogan mu wani kalan kallo tama Dan adake cikeda damuwa dakuma jarumta tace da Oganka nake magana bada kaiba wani kalan juyowa Maheer yayi kaman zaki jin yanda yarinyar tai magana da saida Yasmeen din tai baya da sauri sannan ta tsaya takalli hayakin taban daya huro tasa hannu ta kakkabe kafin takalleshi tace inaso kasaki kannena su koma gida ni ku barni anan har lokacin da Baba zai saki kayanku da direbobin ku dakuke so yasaki sosai Maheer yake kallonta yanda takemai maganan kaman tana bashi command, ganin yanda yake kallonta yasa Dan yabude baki zaiyi magana yadagamai hannu alamun kar yayi, yadda karan taban hannunshi yayi akasa cikin wani kalan husky voice yace are you commanding me ? Cikin yanayi na matukar bacin rai ganin yanda Ogansu keda rainin wayo yasa tace I don t know! All I know is kannina basuda lafiya, kabarsu sutafi niku rikeni bakada imani ne dazakai kidnapping 4yrs old little girl ? Hannun Yasmeen Farida takama cikin tsoro fizge hannunta Yasmeen tayi cikin zafin rai tai ihu tace ki barni, yadauka tsoronshi akeji ne the worse zai iya shine ya harbeni namutu ko yadade baiyiba, baka da Imani ne ? Sosai abin yabashi mamaki tunda yake babu wacce ta taba kallonshi tamai magana kwatankwacin haka ballema rashin kunya irin na yarinyar nan, wani makirin murmushi yayi tareda shafa sajenshi yana kallonta still kafin cikin wani dan iskan takadirin murya yace bani dashi ko kadan yajuya mata baya tareda kallon Dan yace take this lousy girl and lock her up a study Maheer yay maganan azafafe tareda juyowa yana kallon fuskan Yasmeen din, zaro idanu tayi tana komawa baya tana kallon sauran mazan dakin dake dumfarowa inda take, Farida tafashe da kuka suna kankame ta, ganin da gaske suke dauketa zasuyi yasa dasauri Yasmeen tace kayakuri dan Allah karka sa akaini wani waje daban da kannena please please please dan Allah juyawa Maheer yayi fuuuu yafice daga dakin, Dan da Nas suka bishi abaya, su Farida suna ji suna gani daukanta akayi aka fita da ita daga dakin suna kuka sosai suna kururuwa itama Yasmeen na kuka sosai tana kururuwa aka kallesu itakuma aka wuce da ita wani waje. KYALKYALIN KAUNA M SHAKUR EPISODE 1 For your original Egypt Abayas,home decor, Gold (new and used), shoes that are qualitative and unique at affordable price , siyen daya ko sari (wholesale and retail) contact +201123302418 Instagram @Shopper_topia WhatsApp group *Maryam s Egypt abaya * Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj Ita bama tagane inda akai da itaba kokawa take sosai tana tutturjewa tana kokarin kwace hannunta tana kuka sosai tana waigawa tana kiran Farida da duka muryanta da Nana, batasan ta ina akabi da itaba wani babban mahaukacin falo suka shigo da ita akai wani corridor da ita sai chan aka bude wani kofa daganan bakin kofa aka jefata cikin dakin saida ta buge dan kwalin data rufa dashi ma fita yayi daga kanta bata damu da bamata bi ta dankwali ba tashi tayi da gudu tai kofan tana kuka sosai tashiga kiciniyar bude kofan amman arufe hakan yasa tafashe da kuka sosai tana bubbuga kofan tace dan dan Allah, dan Allah ku budemini kofan, wlh Nanah da Farida zasuyita Kuka please please dan Allah kuji tausayina dasu Nana kubude mini gajiya tayi da bubbuga kofan ahankali ta tsugunna jikin kofan tareda kife kanta akofan tana wani kalan kuka mai tsuma rai ashe tun jiya batai kuka bane sabida tana taredasu Farida tana ganinsu, yanzu da aka rabasu sai taji duniyan gabaki daya yamata zafi kawai Nanah kefadowa ranta da Farida ga tausayinsu da yanda zasuyi yanda batanan din nan takeji, tai kuka tai kuka harta godema Allah, takai kusan awa biyu awajen kofan kuka take once in a while tana roko abudeta, chan same kamshin turaren nan dataji dazun ne yadaki hancinta hakan yasa tamike tsaye dasauri tana wani kalan bubbuga kofan tana jijjiga kofan tana kuka. Dan Allah kace su bude ni dan Allah, kayakuri please please please, Nanahhhhhh, Faridaaaa, Ammiiiii . Dan Allah kayakuri baran karaba bude kofan dataji anayi yasa tai shiru tashiga kallon kofan da sauri takoma baya, shigowa Maheer yayi dakin yana sanye dawani 3quater navy blue na Fendi sai off white t-shirt mai gajeren hannu dayamai wani kalan mahaukacin kyau dan kunnen diamond dake makale a kunnenshi yana wani kalan shinning yana sheki hannunshi rikeda wayanshi, kafafunshi sanye dawasu fararen crocs designers, yana zuba wani kalan kamshi kaman wanda yafito daga kogin turare, wavy gashin kanshi na kyalli da sajenshi, lips nashi sunyi pink sosai looking so moist and succulent, wannan karan baisaka bakin glasses ba hada idanu sukayi wani kalan faduwa gabanta yayi dasauri ta sauke kanta kasa ganin yanda yakeda dogayen gashin idanu kaman mace, takai bayan hannunta tana share fuskanta, dauke kai yayi yawuce cikin office din shikuma Dan dayake tsaye ata waje yarufo kofan dasauri tai wajen kofan tashiga bugawa tanajan kofan ganin ba a budeba yasa takife kanta jikin kofan tafashe da kuka sosai kaman wata marainiya da aka kulle adaki tanaso tafita. Ahankali yazauna kan kujeranshi yaja system yabude ya kunna kafin gently yadago kanshi yadaura manyan idanunshi akanta yanabin tundaga gashin kanta dayake abude da kallo wanda wani shuku dayay tsufa ne akanta but baihana kaga silky black long hair nata ba, gashin ma sun zazzaro waje dan tanada tsantsin gashi gasu kuma so coily, ganin duka gidan nan babu mai imani ko tausayin Nanah karama ma dake kuka balle ita babba yasa tawani juyo da sauri karaf suka hada idanu yahade rai tamau ya tsuke fuska, wani kalan wankamai wani uban harara tayi tareda kai bayan hannunta tashare fuskanta tass tass tawuce wajen dan kwalinta datagani akasa ta dauka takai
Chapter 22 · 0% Book details