Sashe 5
Kyalkyalin Kauna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR AMMNUR APHRODISIAC is home of lafiyayyun kayan mata na ban mamaki, kayan matsi, kayan gyaran nono, kayan gyaran amarye dana maijego da abubuwan mallaka kome kikeso zaki samu awajensu. Chat them up by clicking on this link; wa.me/+2349080070762 EPISODE 3 Fitowa daga wanka tayi tana tafiya ahankali sabida yanda tagaji dan yau ta taku, Farida tagani adakinsu tana kokarin cire Hijabin islamiyya itakuma Sa a bata dakin tana dakin Maman su (Yaya) Farida dake kallon Yasmeen din dataga gajiya karara akan fuskanta tace Anty Miemie mekika kawo mana yau daga bakery dinku Chef ? Wata doguwan riga Yasmeen taciro daga drawer dakin tasaka sannan tajaye igiyan w ankan daga jikinta ta shanya akan kofan dakinsu ahankali tace anjima zan baki gashinan a leda yanzu muyi salla kafin Baba yazo dasauri Farida tace ni banayi Gyadamata kai Yasmeen tayi tadauki hijabi tasaka ta kabbarta salla, saida Baba yafito yasa dukansu matan suje suyi salla sannan yawuce yatafi masallaci shida yara mazan gidan. Babban gida ne wanda iyayensu suka rasu suka banmusu bayan sun haifesu su uku suka, Baffa wanda shine Babba mijin Yaya kuma, kowa na gidan Yaya ake cema matarshi, dan kasuwa ne Baffa yana saida kayan hatsi akasuwa, Yaya ce kadai matarshi ta haifamai yara biyar guda 4 maza wanda uku sunyi aure suna aiki agaruruwa daban daban Abba kawai yaragemai da Sa adatu da basuyi aure ba, dukansu na university Sa a na 200 level shikuma Abba na 300level, sai Baba shi dan sanda ne yaranshi uku duka mata, Yasmeen ce Babba, sai Farida dakuma Nanah, sai kanninshi da ake cema Baba Karami mijin Hajjo yaransu kananu hudu maza biyu sai yan biyu Hassana da Husaina. Bayan sallan magrib gabaki dayansu mazan suka shigo gida duka yaran zuwa sukayi gaidasu banda Yasmeen da tana sallan magrib ta bingile da bacci danta bala in gaji, anatse Baba yakalli Farida dake zaune kusada Ammi akan tabarma yace ina Yasmeen ? Dan ita kadaine bata tsakar gidan, ahankali Farida tace tayi bacci Baba bai damu da abincin da aka kawomusu da zasu fara ci ba tashi yayi ahankali yakalli Yayanshi yace ina zuwa Baffa ku faracin abincin idan da sabo kowa na gidan yasaba da yanda Baba yake da yaran gidan ma gabaki daya bawai nashi kadaiba gyadamai kai kawai Baffa yayi, direct dakin yaran yawuce wanda shine atsakiya dakinsu wanda yakenan ciki da falo da bayin wanka da dakin Baffa shima ciki da falo da bayin wanka sai akama yara matan dakinsu awajen babban daki guda daya, da sallama chan kasa yadaga labule yashiga dakin, kwance yaga Yasmeen din akasa tai shane shane tana bacci ga hijabin datai salla dashi agefe babu hula akanta sai kitson kanta dakenan all back dayay tsufa amman gashin baki sidik sai uban tsawo tana shakan bacci, ahankali ya tsugunna akanta hannunshi yakai yadaura asaman kan goshinta jin jikinta ba zafi yasa ahankali yakai hannunshi yabugi kafadarta yace Yasmeen Yasmeen cikin bacci murya chan ciki tace uhn Baba dan shiru yayi yana kallonta saikuma ahankali yatashi gadonsu katon gaske dan su uku ke kwana adakin, wani zubin kuma Nana nazuwa tace ita wajen Anty Yasmeen zata kwana ba wajen Ammi ba sai su zama su hudu, hijabinta dake wajen Baba yadauka ya kakkabe gadon sannan yadawo yaduka yadagata ahankali yace tashi kihau gado cikin bacci yadagata tamike tsaye kana ganin yanda take kasan ta bala in gaji dan har layi layi take kaman zata fadi da taimakonshi yasata akan gadon tana lumshe idanu cike da bacci sannan yakashe wutan dakin dayake kunne yawuce yafito tsakar gida daga Yaya har Hajjo kowa yabishi da kallo anamai harara ciki ciki itadai Ammi ko kallonshi batayiba dan sosai yau yabata mata rai, zama yayi wajen yayinshi yasa hannu suka cigaba da cin tuwon duk wanda zai shigo gidan saisun bashi sha awa sabida yanda family suke three brothers da iyalansu suna zaune agidan da iyayensu suka bar musu da iyalansu zaman lafiya kuma kansu ahade. Saida suka cinye tuwon sannan yakalli Yayan nashi anatse yace Yaya gobe za amini karin girma awajen aiki zan koma Commissioner of Police CP duka gidan hatta Ammi saida takalleshi cikeda farin ciki yaran sukahau cewa Baba Allah ya sanya alheri murmushi yamusu yace Ameen su Yaya da Hajjo ma sukace Allah sanya Alheri Allah tayaka riko anatse yace Ameen nagode murmushi Baffa yayi yace Alhamdulillah Alhamdulillah shi daman duk wanda yarike Allah haka Allah ke daukaka shi, mutane na yawan cewa ai duk Dan sandan da baya karban cin hanci baya kaiwa ko ina, ko akasuwa idan ana hiran nan nakan cemusu uhm uh kada suce haka, inada kani da tunda yashiga aikin yan sanda yau kimanin shekaru kusan sha takwas kenan daidai da cin hancin naira biyar baitaba karba ba kuma ahankali ahankali anata karamai girma gashi yau za a nadaka CP maiyafi haka? Nan gaba saidai muji an maidaka IG gabaki dayama Baffa yadanyi shiru tareda daukan ruwa ya kurba sannan anatse yace a kullum ina fadamaka kowani matsayi kasamu arayuwan nan kayi amfani dashi wajen magance matsalolin al umma gabaki daya, wajen yaki da rashin gaskiya da kafa gaskiya, wajen taiwakama addinin musulunci, wajen tsare hakkin dan adam da saman da zaman lafiya adoron kasa, ta hanyar kawo karshe sata, kidnapping, shaye shaye, fyade, kisan kai da sauransu, Allah ubangiji yabaka sa a yakuma tayaka ruko sannan kasani wannan position din amana ce, karkaci amanan sabon seat din nan kaji Ibrahim anatse Baba yace naji Baffa nagode sosai dafashi kanninshi mai binshi yayi Baba Karami wanda shine mijin Hajjo yace Allah yatayaka riko Yaya murmushi yayi yace Ameen tashi Baffa yayi yace to kumu tashi mutafi masallaci, kukuma matan sai kuyi naku sallan dan juyawa Baba yayi yakalli Ammi dake kallonshi cikeda farin ciki dauke kai tayi dasauri ganin sun hada ido dan haushin shi takeji wani kalan murmushi yayi yabi su Baffa suka wuce mosque batare dayace mata komiba. As usual daman gidan ana sallan isha i kowa ke shigewa daki dan yara anje school angaji, weekends ne dama yaran gidan basu cika bacci da wuri ba dan ranan baaje boko ba, Ammi na idar da salla tadauki Nanah datai bacci asaman gadonta tafito waje tashigo dakin su Yasmeen tagansu duka sun kwanta dudda ba bacci Sa a da Farida keyi ba amman Yasmeen tadade da bacci, kwantar da Nana tayi tareda su tana kallon Yasmeen tace kin gaji ba dole kiyi bacci ba cikin dare kya tashi kiyi ishan kukuma baraku kashe wutan bane dasauri Sa a dakejan lullubi tace Ammi dan Allah kikasha mana dan hararansu tayi sannan takashe musu tajawo musu kofan tafito tashiga nata dakin, maida kofan falon tayi tarufe sanan tashiga uwar dakinsu, dan matsakaicin bayinsu da wanda kadai ake aciki ta shiga ta watsa ruwa sannan tafito ta shirya cikin kayan bacci ta fesa yan turarukanta ta kwanta. Wuraren 10 su Baba suka shigo gidan, direct dakin yara yawuce, shikuma Baffa yana kulle gate, ahankali yatura kofansu yashiga wayan hannunshi ya kunna saida ya dudduba su ganin duk sunyi nisa abacci sannan yasake Tofa musu addu a yafito tareda maida kofan nasu ya kulle sannan yama Baffa sallama duk kowa yashige dakinshi maida kofan dakinsu yayi yarufe sannan yawuce uwardaka, jallabiyan shi yashiga cirewa yana kallon Ammi dako sallaman shi bata amsaba kuma yasan ba bacci take ba, bayi yashiga bakinshi ya wanko tareda dauro alwala wanda wannan haka yake kullum sannan yafito ya kashe wuta taredayin bismillah yahau gadon, ahankali ya matsa kusada Ammi yakai hannunshi yana kokarin juyoda ita cikin wata kalan murya yace juyo kimin Allah sanya alheri dan ke kadai ce kika rage baki samini albarka ba kabarda hannunshi tayi cikin fushi da rashin son yin magana dashi tace stop touching me dan shiru yayi saikuma chan yace kiyakuri to kaman jira take wani kalan juyowa tayi saikuma ta tashi zaune cikeda masifa amman bamai karfi sosai ba gudun kar ajinsu tace nagaji da hakurin dakeke bani kullum saikagama cimini mutunci agaban uban kowa sabida yara saika biyoni da daddare kana cemin nayakuri yau bazanyi ba kaji Ibrahim bazan yi ba shiru Baba yayi jin takira sunanshi yau kai tsaye yasan ranta yabaci, cikin wani yanayi na nuna kunci tace Ibrahim ka manta cewa nine mahaifiyar yaran nan, nine nadaukesu wata tara acikina, nine nai laulayinsu, haka kuma nine nan nikadai nashiga labour room nasha nakudan yaran nan nahaifosu maisa kake treating dina kaman banson yarana kaine kadai ke sonsu why? Inda ba nine na haifesu ba sai ace eh dama banice mahaifiyar su ba but this girls are mine, nine mahaifiyar su, mesa kakemin abinda kakemin akansu eh Baban Nanah ? Shiru Baba yayi baice komiba baki Ammi tabude zatai magana sai kawai kuka ya kufce mata kawai tafashe da kuka sosai dan abinda yake mata na kona matarai ainun, wani kalan sanyi jikin Baba yayi ahankali yajawota zuwa jikinshi batai musu ba tashige bayanta yashiga shafawa cikeda lallashi yace kiyakuri bazan karaba, I know you love our girls beside yaranmu ne nidake muka haifesu sometimes ina miki fadane sabida sakaci, Maryam yara mata muka haifa guda uku, hakki ne su akanmu nida ke we have to protect them, support them, musa idanu akan lamarin su, mu tarbiyantan dasu da kyau kinsan idan ka tarbiyantan da yara mata da kyau ka aurar dasu Allah zai bamu aljanna ranan gobe kiyama? Hadisai daban daban daga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi inda yake nuna falalan da iyaye suke samu ranan gobe kiyama dasuka tarbiyantan da yara mata da kyau, Please understand me kidaina fushi dani, inaso kiyi tsayin daka kaman ni akansu that s all stop crying matata, I am simply doing the right thing yay maganan yana bubbuga bayanta, da kyar tai shiru ta dago daga jikinshi sannan takalleshi dudda cikin duhu ne tace I understand abinda kake kokarin yi kan yaran nan perfectly well but is too much! You are overreacting, Yara mata garemu kana tareda yaran nan 247, kana yawo dasu kana rike musu hannu a anguwa, anguwan nan kap babu wanda baisan how protective you are towards this kids ba, wazai taba zuwa ya aure su kowa tsoron tinkaranka yake, Yasmeen dinmu is 20yrs kasan mates nata guda nawa sukai