← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI

MAMAN AFRAH
09013181851
[4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/DHHvkSDbSKeFqXeWD4p37a

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

BOOK 1

PAGE 5

ÆŠif ta yi kamar ruwa ya ci ta gabanta yana tsananta bugu, tana fatan Allah ya sa wani abu ne da ban ya kawo su ba waccan maganar ba.

Tana jin sa ya amsa musu ciki-ciki shigowa suka yi, tashi ta yi ta lallaɓo take ɗan leƙowa ta tsakanin labule. Kwance yake reran ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Bai bar danna wayar ba kuma bai tashi zaune ba har suka zauna dama sun san hali duk gidan su bashi da kunya ba ya girmama mutane.

"Baka ga mun shigo ba? Kana kwance kenan shigowar tamu ɓangaren ka bashi da wani amfani tun da ga shi ka nuna da shigowar mu da rashin ta duk ɗaya" Yaya Shafi'u da ya ƙulu ya ce yana kallon sa. Ɗan dim ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma dai ya tashi ya zauna ya ajiye wayar yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

"Akwai maganar da ta kawo mu shi ya sa ma ka ganmu a tare don haka kawai ba za mu zo ɓangaren ka ba" Yaya Sule ya ce

"To" Kawai ya ce a taƙaice.

"Kai yanzu Aminu ka yi aure ma ba za ka sauya ɗabi'un ka ba? Mutum yana da iyali amma in kana yin wani abu tamkar dai ƙaramin yaro wani abun ma da kake ƙaramin yaro ba zai yi ba" Yaya Sule ya faɗa.

"To in ban da ma ɓacewar basira ba, kai ma fa yanzu watarana uba ne kana so ƴaƴan ka su taso suke...

"Haba don Allah wai ya za ku zo kuke mini magana a rufe ai gwara ku faɗa mini asalin mai yake tafe da ku amma kuna magana a ƙudundune ina zan gane manufar ku" Ya katse Yaya Shafi'u

Saddiqa da take laɓe tana ganin abin da yake wakana gabanta yana dukan uku-uku, duk mamaki ya cika ta saboda ita sun saba girmama na gaba da su ko yaya mutum in ya girme ka to fa ko da baka san shi ba kana daraja shi amma shi ga shi yayunsa na jini ma tamkar dai shi ne gaba da su ta jinjinawa lamarin ƙurr ta musu da idanu tana jira me zai biyo baya.

"Maganar rashin sallah da baka fita, ko da asuba dukanmu sai mu je masallaci amma kai kaÉ—ai ne baka zuwa" Yaya Shafi'u ya ce

"Kuma batun ƙazantarka dai ashe baka sauya ba sai abin da ya cigaba? Duk faɗan da aka maka ashe bai shige ka ba ta bayan kunnenka ya bi ya wuce..

"Allah na gode maka, yanzu a ce mutum ba zai makara sallaha ba har sai an tuhume sa? Ƙazantar me kuma?" Wannan tambayar da ya yi yana wani kallon jikin sa ita ce ta saka hanjin Saddiqa hautsinawa, tana addu'a Allah sa kar su ce ita ce ta faɗa don yanayin yadda ta ga yana musu magana kamar wasu sa'annin sa ta san ba ma lallai ya ɗauki maganar su ba bare har ya yi aiki da ita.

"Ƙarya za a maka ne, na ce ƙarya za a maka to matarka ce ta kawo ƙaranka a kan a maka maganar kake tsafta ka ga kuwa dole a faɗa maka don ba za a zuba maka ido ka cutar da ƴar mutane ba saboda ƙazanta ai cutar da abokin zama ne" Yaya Shafi'u ya faɗa cikin hargowa.

'Subhanallah! Shikenan sun saka ni a maganar' Saddiqa ta faÉ—a a zuciyar ta.

"Saddiqa?" Ya tambaya mamaki kwance saman fuskar sa.

"Eh ko kana da wata matar bayan ita?" Yaya Sule ya tambaya yana kallon sa.

"To ko da a ce matarsa bata kawo ƙaransa ba ai ko yanzu komai ya aka kalla wataƙila rabonka da sallaha tun ta asuba ko ma a ce tun ta safe tun da baka je masallacin asuba ba, amma yanzu bari a kira ta waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin ji" Cewar Yaya dama in za a yi sulhu mutum biyu ake haɗawa a ji ta bakin kowa abin da ya sa ma muka maka maganar kai kaɗai saboda wannan sulhun ba ya buƙatar ma sai an ji ta bakin wani don abu ne a bayya ne" Cewar Yaya Shafi'u.

"Wai ni baku san yanzu da kuma da ba ɗaya ba ne? Ni ma yanzu na yi aure don haka a daina biyo ni ana mini wani faɗa don na girmi faɗa, sallah kuma ai Allah ake yi wa ba mutum ba batun tsafta kuma ita Saddiqar za ta faɗa mini sauran bayanan" Ya faɗa a ƙufule yana komawa yadda yake tun farko wato ya kwanta ya ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tare da fara latsa wayar sa.

Lamarin Aminu ya fara basu tsoro ganin haka suka bambame shi da faɗa kamar za su ari baki don yadda ta musu ma in suka kira matar tasa wataƙila su ji kunya don ba ƙaramin aikinsa ba ne ya tsinkasu a gabanta duk da sun san tana ji tun da dai sun san tana cikin ɗaki, basu ƙara ma kallon inda yake ba suka tashi suka fita

Saddiqa da gumi ya gama wankewa tsabar tsoro ta juya da sauri ta koma bakin gado ta zauna, kamar jiran tafiyarsu yake sai ga shi ya faÉ—o É—akin kamar an jefo shi.

"Ashe baki da hankali?" Ya faɗa tamkar zai kai mata duka. Furucin nasa ya bata mamaki duk da ta tsammaci wasu abubuwan amma bata zaci har zai iya alaƙantata da rashin hankali ba.

"Aminu ni kake ce...

"An faɗa miki na ga alama baki san wa kika aura ba, har ni za ki je ki haɗa da ƴan uwana? Har kin kai ki fara bibiyar ƴan uwana kina kai musu maganganu ?Yaushe aka yi daren da har gari zai waye? Yaushe aka yi auren ma, tabbas hakan ya nuna mini ke ba matar rufin asiri ba ce kuma baki da riƙe sirri, tun da har kin kasa jure abubuwan nan tun tafita bata yi nisa ba" Ya tari numfashin ta yana magana kamar zai kai mata duka.

"Aminu ni ce ba matar rufin asiri ba?" Ta tamabaya ranta yana ƙuna tare da nuna kanta da yatsa.

"To matar rufin asirin ce? Har ni za ki je ki samu ƴan uwana ki musu maganar banza kina son ki shiga tsakanin mu ki haɗa mu dama ana cewa wasu matan idan suka auri miji burin su bai wuce su raba shi da kowa nashi shi ya dawo mallakin su su kaɗai. To ki sani ba dai ni Aminu ba har yau baki fahimci wa kike aure ba kuma ina so ki sani tun da har ni kika yi wa haka ƙazanta yanzu na fara babu sauyi ba irin mu ake yi wa abu ta ƙarfi ba"

Tun da ya fara maganganun ranta yake ƙuna ji take tamkar dai ta buɗe ido ta ga mafarki take, wai Aminun ta wanda yake lallaɓata tamkar ƙwai wanda yake son ta shi ne yau yake jifanta da munanan kalamai wai ita ce take son ta raba shi da ƴan uwan sa.

'Ashe dama gyara kayanka yana zama sauke mu raba?' Ta tambayi kanta a zuciyar ta idon ta har ƙwalla ya ciko ta takaicin maganganun sa.

Zuciya ce ta ɗauke ta don ta ga lamarin ya yi tsamarin da sai ta turbuɗawa idanunta toka, idan ta bari abun a haka zai ƙara girma ne ya bunƙasa tun da shi bai ɗauki ma abin da yake yi a matsayin kuskure ba.

"Aminu bari ka ji ni ban auri kafiri ba musulmi na aura don haka dole ka cigaba da amsa sunanka na musulmi ta hanyar kiyaye sallah da kuma tsafta ce jikin ka, shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne kana ganin har akwai matar da za ta jure wannna halayyar? A ce mutum ba zai tsafta ce jikinsa ba wanka wannan ba za ka yi ba bare wankin baki kayanka in wanke maka amma ba za ka saka ba na gaji da maka alkunya dole in fito maka a mutum...

"Kin gaji? To in har kina gani za ki ƙwaci abin da kike so ta ƙarfi ga fili ga mai doki, ko an faɗa miki ana haɗa gudu da susar ɗuwawu ne? Babu gyara haka na ga dama sai lokacin da na ga dama zan yi wanka sannan sallah ina yi kiyaye lokacinta kuma wannan tsakanina ne da wanda ya yi umarnin a yi sallah shi kuma yana gafara amma dai ki sani ba gudu ba ja da baya...

"Wallahi ba zan yarda ba don ƴaƴana ba za su taso su ga wannan rayuwar marar kai da ƙafa...
Fuuu ya juya ya bar mata ɗakin, ji take ranta yana ƙuna wai ita ya ce ba matar rufin asiri ba ce, wannan maganar ta fi ƙona mara rai da kuma yadda ya tabbatar mata ba zai canja ba.
Chapter 7 · 0% Book details