← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 44

Sashe 16

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi ba abinci ba ne?" Bata ma samu damar bashi amsa ba, da yake dama yau bai fita da wuri ba lokacin ma wajen ƙarfe sha ɗaya da wani abu. Yana dab da bakin ƙofa ta tsinkayi muryar Khady tana sallama, kallonsa ta yi ta ɗan langaɓar da kai alamar ya saki fuskarsa kar a gano wani abu a tsakani, banza ya mata ya juya don yau da yake basu gabatar da sunna da dare ba ankan baƙin ruwan ma bai yi ba kaya kawai ya saka taimakonta ɗaya kayan a wanke, duk da cewa idan har aka ɗora kaya a kan dauɗa to duk ɗaya ne an ce wa makaho ga ido.

Fitowa ta yi tana amsa mata, shi ma sai ga shi ya fito abin mamaki sai ya washe jajayen haƙoransa suka gaisa da Khady tana ta musu tsiya wai sun yi aure sun manta da ita. Yana dariya yake tsokanarta kafin ya musu sallama ya tafi su kuma suka shige falo suna ta murnar ganin juna.

Zaunawa Khadyn ta yi Saddiqa ta zauna a kusa da ita suna ta hirar yaushe gamo, cewa ta yi bari ta ɗakko mata ruwa ta fita zuwa kicin. Khady fitar Saddiqa ke da wuya ta shiga ƙarewa falon kallo ganin yadda ya sha gyara ko ina sai ƙamshi yake sai dai abin da yake bata mamaki wani ɗan hamami da take ji yana tashi daban da ƙamshin.

Ɗan hura hanci ta yi amma sai ta ji warin har yana ɗan shigar mata maƙoshi, kamar an ce ta duba bayanta daga saman kujerar da take zaune ta yi ido huɗu da wani talallan gajeran wando wanda ya gaji da tsufa har ta fara tauyewa daga ƙugu, ya haɗa uban datti waiwayawar da ta yi ne ta ji warin har wani dumm ya sa ta ji a kanta da sauri ta tashi ta bar kujerar ta koma wacce take ɗan nesa da ɗayar. Mamaki take mai ya kawo wannan wandon haka amma jin takun Saddiqa sai ta kawar da wannan tunanin.

Saddiqa da ta shigo bata kawo komai ba da ta ga Khady ta sauya wajen zama ruwan ta akiye mata har da fruit da ta yanko mai sanyi.

Hira suka shiga yi tana cin fruit É—in can ta ce

"Wai ƙawata kin ganku kuwa kamar ba amarya ba, maimakon in zo in ga kin yi ƙiba kin yi jawur dake amma sai in ga kin rame kin yi baƙi kamar wacce aka yi wa auren dole, ni gani nake babu abin da zai sa in yi rama in har masoyina yana kusa da ni" Ta ce tana kallon Saddiqa.

'Allah sarki Khady baki san mene ne zaman aure ba, a haka muje ganin gidan aure kamar babu matsaloli amma kowane gidan aure cike yake da matsaloli da ƙalubale birjik sai dai na wani ya fi na wani, babu sabon aure babu daɗɗe' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya ta ce.

"Kin jiki da wani abu, rashin lafiya fa nake fama" Idanu Khady ta zaro ta ce

"Don Alla da gaske? Ki ce an samu ɗan baba" Dammm ƙirjinta ya buga don sai yanzu ma ita ta tuna cewa wannan watan bata yi priod ba, kallon yanayin da ta shiga Khadyn ta yi ta ce

"Ya dai" Murmushi ta yi ta ce

"Babu komai"

Suna nan suna hira bayan ta ɗora abincin, lokaci zuwa lokaci tana fita kicin ta dubo, amma dai ta ɗan ji ɗan bashi-bashi a falon sai dai bata kawo komai ba, dama sai ta fita ne idan ta dawo sai ta ji falon ya sauya. Bayan an kira sallah Khady ta fita banɗakin tsakar gidan za ta yi alwala, ɗaki ta shiga ta ɗakko sallaya ta zo ta shimfiɗa mata kamar an ce ta ɗaga kanta saman kujerar da Khady ta fara zama ta tashi, aikuwa ta yi arba da gajeran wandon Aminu daƙyal-daƙyal da shi gabanta ne ya faɗi shiru ta yi tana ɗan nazari a nan ne ta ƙiyasta a zuciyarta cewa wannan wandon ne ya saka Khady tashi daga kujerar.

Wani takaici ne ya saka ta danne leɓen bakinta tana jin haushi da takaicin ajiye mata wandon da ya yi bata san ma ya ajiye ba. Jin takun Khadyn ya sa ta yi saurin ɗaukan wandon ta shige ɗaki tsabar haushi cilli ta yi da shi wajen drower Aminu, wandon kamar an nuna masa wajen zama sai kuwa ya maƙale a jikin hannun drower yake reto yana ta lilo.

Ƴar guntuwar freshner tata da ta rage ta ɗakko ta feshe a falon, ita ma Khadyn tana shigowa ta sauke idanunta a wajen gurbin wandon sai ta ga wayam hakan ya nuna cewa Saddiqa ta kawar da shi.

Sun idar da sallar ta zubo musu abinci har da sauran kabeji da albasa ta yanka musu, za su fara ci kenan kamar daga sama ta jiyo muryar Aminu yana rafka sallama, hatta Khady sai da ta lura da sauyin da fuskarta ta nuna, shigowa ya yi yana washe baki firi-firi da shi da fari fulawa yana shigowa falon ƙamshin freshner ɗin ya sauya zuwa wani abun daban saboda ya kwaso rana, kuma abin haushin yana zuwa ya yi wa kansa masauki a falon.

Murmushin ƙarfin hali Saddiqa ta yi ta ce

"Sannu da zuwa" Amsa mata ya yi ita ma Khadyn ta masa ya amsa sai ya ce

"Ai yau na ce tun da muna da baƙuwa gwara na dawo da wuri ni ma asha hirar da ni kar a yi babu ni kawo mini abincin nima" Ya ce yana dariya.

Tashi ta yi tana sakin murmushin yaƙe ta fita kicin, tsayuwa ta yi tana jin kamar ta nutse don kunya ya dawo daga kasuwa amma bai san ya je ya tsaftace jikinsa ba, zai zo ya saka su a gaba. Abincin ta zubo masa ta dawo.

Suna gefe guda suna ci shi ma ya cin nasa, ana haka sai kuwa ya yi wani kaki, ya kako majina sai kuwa ya tashi su duka da kallo suka bishi ƙofar ɗaki ya nufa yana zuwa ya ɗaga labule ya tofar a ƙofar ɗakin, don daga inda suke ma suna hango inda ya tofar da majinar, yana sakin labulen kuwa da yake labulen har ƙasa yake aikuwa iska ta ja labulen ya tsunduma cikin kakin majinar da ya tofar!

TIRƘASHI!!!

09013181851

Kina neman zannuwan gado? Ko kuwa labulaye, kina son siyen frames, ko takalma, kina son siyan mayafai masu beat work ko leshi da atamfa kike so? Ina da kamfala sannan har da laffaya.

Hijabai kike so ko kuwa sarƙa da ɗankunne agogo ko warwaro, ina siyar da magungunan mata masu inganci har da na sanyi da basir babu abin da bana siyarwa har da wanda ban zana ba ki dai tuntuɓi

MAMAN AFRAH 09013181851

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

PAGE 10

Aminu dawowa wajensa ya yi ya zauna hankali kwance ya cigaba da cin abincinsa, Khady kuwa zuciyarta ce take ta tashi ganin abin da ya yi domin tun da ya tofar da yawun nan bata kai ko da loma ɗaya ba bakinta sai jujjuya cokalin take, Saddiqa kuwa kunyar duniyar nan ce ta ishe ta duk da ita ma abincin ya fice mata rai amma kuma tana jin kunya da nauyin abin da ya yi a gaban ƙawarta.

Ganin duk sun yi jugum-jugum bakinsa da abinci ya kalle su da mamaki ya ce

"Ƙawayen juna ya kuka dakata da cin abincin, ai ni wallahi Saddiqa yau kin biyani da wake da shinkafar nan, ya yi daɗi sosai" Ya faɗa yana ƙara cika cokali ya kai bakinsa, Saddiqa bata ce komai ba sai Khady ce ta yi ƙarfin cewa

"Ai kam ya yi daɗi ni da yake dama ban cika cin abinci sosai ba, yanzu ma ƙoshi na yi ba don abincin ya isheni ba" Ta faɗa tana sakin dariyar yaƙe.

Bai sake magana ba sai da ya cinye abincin nan tas, lokacin Saddiqa ta haɗa kwanukan ta fita da su tsintsiya da klin haɗe da ruwa ta ɗakko ta wanke ƙofar ɗakin ta ɗakko wani labulen ta cire wancan ta saka ta kai bayi ta saka a bokiti ta wanke ta fito ta je ta shanya.

Kiran sallar la'asar ne ya saka Khady cewa bari ta je ta yi alwala, tana fita Saddiqa ta kalle shi jin yana sakin gatsa haɗe da miƙe ƙafa a kan kujera bashi ma da niyyar tashi yin sallah ta ce

"Yanzu Aminu kai sai ka ce ƙaramin yaro a ce a ƙofar ɗaki za ka tofar da yawu? K...Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya katse ta da faɗin

"To sai aka yi yaya wai ku mutane mai ya sa ba a iya muku ne? Yanzu yawu ma don na tofar sai an tuhume ni? Idan ba a ƙofar ɗaki ba a ɗakin kike so in tofar hallaw cibi ya zama ƙari? To ni da gidana babi wanda zai mini wani iyayi wai ke sarkin ƴan tsafta" Idanu ta runtse tana jin takaicin maganarsa amma sai ta danne ta buɗe idanun da tuni sun yi jajur saboda takaici, ta ce

"Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah tun da mu ma sallah za mu yi" Shiru ya yi bai ce komai ba sai kuma ya ce

"Ko dai in yi alwalar in zo in ja ku jam'i?" Wani haushi ta ji ita da take so ya fita a falon ko sa samu damar shaƙar iska mai daɗi amma wai zai ja su jam'i ɗan rausayar da kai gefe ta yi ta ce

"Kamar na ga baka yi azzahar ba fa, kuma ta yaya za ka ja mu sallar la'asar" Shiru ya yi don tabbas ya san bai yi É—in ba sai kuma ya ce

"Na rama ta daga baya" Kallonsa ta yi tana jinjina jahilci irin nasa ta ce

"A'a azzahar ai ita ya dace a fara yi sannan la'asar, wai ni kuwa anya Aminu ka yi islamiya?... Tun kafin bakinta ya rufu ya hayyyaƙo mata tamkar zai kai mata duka ya ce
Chapter 16 · 0% Book details