← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 44

Sashe 2

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amarya ta ango to a taho a fara aikin lada" Bata tanka masa ba ta ɗauki qur'ani da yake irin mai izu goma-goma ne mai guda shida a ciki. Tasowa ta yi ta miƙa masa. Da mamaki yake kallon ta cikin ɗan diriricewa ya kalle ta don yana fatan dai ba ɗori za ta ce ya mata ba don idan haka ne ta ɗakko dala ba gammo.

"Ka karɓa ka karanta ko izu biyu ne" Amon muryar ta ya katse shi. Idanu ya kafe ta da su yana kallon ta ya ce

"Wai karatun ma sai kin saka ni Saddiqa? Lokacin muna yara muna zuwa islamiya in ban manta ba a hadisi na ɗaya da ake mana ana cewa dukkan ayyukan ibada basa iyuwa sai da niyya" Ganin ya hayyayƙo mata sai ta juya jiki sanyi ƙalau ta koma kan sallayar ta zauna tare sa yin bismillah ta fara karatun suratul yasin a bayyane.

Aminu da ya koma ya kwanta ya ja bargo ya ji karatun nata zai hana shi bacci ya É—ago ya ce

"Wai kike yi a zuciyar ki mana" Ko juyowa bata yi ba ta fara karatun a hankali don ta ga abin nasa ya fara wuce gona da iri a ce mutum hatta sautin qur'ani ba ya so.

"Ki rufe qur'anin nan ki zo mu kwanta" Maganar sa ta katse ta

HAJIYA BAKI DA LABARIN HAJIYA MEERAH ME KAYAN MATA KUMA LIKITAR MATA? IN KINA DA ZAN ƘARA MIKI SANI IN KUMA BAKI DA ZAN SANAR DA KE. BAKI TAƁA GANI ANA TALLAR KAYANMU A AREWA 24, KO TAURARUWA KO HIJRA BA? KAYANMU BABU INDA BASA ZAGAYAWA A FAƊIN DUNIYA MUNA AIKAWA KO INA SAYEN ƊAYA KO SARI HAUSAWA SUKA CE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA🤗
GA LIST ƊIN KAYANMU KAWAI IN KINA SO KI MINI MAGANA SANNAN AKWAI GRP DA MUKE TURA KAYAN GA MASU SON SHIGA DON SU GA HOTUNAN KAYAYYAKIN MU👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

MAMAN AFRAH
09013181851
[4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/L3FON3yJGYpBg3fVdxikGe

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

PAGE 2

Babu yadda ta iya haka ta yi addu'a ta naÉ—e sallayar ta mayar da qur,anin ta je wajen nashi.

Gari yana fara haske ta shiga ƙoƙarin raba jikin ta da nashi, amma ya riƙe ta ya hana ta yinƙurin hakan. Jin bata daina kiciniyar ƙwatar kan nata ba a hankali ya buɗe ido ya ce

"Ina za ki je?"

"Wanka zan yi in yi gyaran É—aki sai na dafa abinci" Galala yake kallon ta.

"Don wankan tsarki dai da ba wani wahala gare shi ba Saddiqa sai ki bari kya yi anjima, kuma yanzu ɗakunan nan sabbi ina suke buƙatae shara, kuma abincin sai mu ci kaza da lemon jiya in kuma bakya son ci ko waina sai na siyo "

"Ai har wankan sabulu zan yi ni dama daga gari ya waye nake wanka, don ni a ƙalla sai na yi wanka sau huɗu watarana har biyar ma" Cike da mamaki yake kallon ta can dai ya yi ƙarfin halin cewa

"Wai a wata kike wankan sau biyar ko a shekara?"

"Wata? Shekara?"

"To ai na san dai ko a sati ba a yi wanka sau biyar ba"

"To a rana nake nufi" Sai da ya É—an É—ago yana kallon ta sosai.

"Wankan ne kike sau biyar kamar baki da aikin yi"

"Rashin aikin yi ne? Tsafta ce fa"

Bata ƙara magana ba ta shige bayi ta yi wankan tsarki ta ɗore wankan sabulu, yana ta jin tana ta dirzar jikin ta tamkar wacce ta yi wata jikin ta bai ga ruwa ba.

Sai da ta gama ta fito.

"Wai amma sabulu a gidan ku ba ya wata ko Saddiq"

"To ajiyar sa za a yi dama ba don a yi wankan aka siya ba" Shiru ya yi bai ce komai ba shiryawa ta yi ta saka doguwar rigar atamfa ta sha ɗauri sai bulbula ƙamshi take. A bakin gadon ta zauna tana ɗan jifan sa da kallon soyayya.

"Wai Bab... Bata ƙarasa ba ta tuno ya hana ta kiran sa da Baby.

Sai da ya tashi yana shiga bayin ta yi saurin gyara kan gadon ta É—akko tsintsiya ta shiga sharewa kafin ya fito ta share É—akin ta dawo falo tana sharewa sai ta ji ya fito kamar yadda ta zata hakan ce ta faru domin kuwa iya wankan tsarki ya yi.

Tana son cewa mai ya sa bai yi wankan sabulun ba amma tana jin kunya.

"Tun jiya nake wanka wannan ne na uku ita ƙazantar da kanta ta san bata isa tsayawa a jikina ba, ba sai na sanya sabulu ba" Ya faɗa tamkar ya san tunanin da take.

Ita dai tana ɗan mamakin a ranta amma sai take tunanin ko sai daga baya zai yi, kaya ya saka bayan ta gama gyaran ɗakin ta ɗakko sauran kazar jiya ta je ta ɗumama musu, tana ta ƙarewa gidan kallo, tana hango ɓangarorin facalolin nata.

Da yake dama ta taɓa zuwa gidan sau ɗaya amma sai dai da daddare ne da ya kawo ta ta yi musu sannnu da shan ruwa a ramadan, to ta shiga ɓangaren kowacce sun gaisa sannan da za ta tafi sun rako ta, wannan ne sanin junan da suka yi.

Haka suka yi ta hirar su sai wajen sha biyu ya fita zuwa gidan su. Bayan fitar sa ne tana zaune rana ɗan danna waya Sumayya ta shigo da sallama amsa mata ta yi suka zauna suna ɗan taɓa hira, cikin hirar tasu ne kamar an ce ta kalli kafaɗar Sumayya abin da ta gani ne ya bata mamaki, hannun bireziyar Sumayya da ya leƙo ne baƙiƙƙirin da shi daga gani kuma fara ce bireziyar amma tsabar datti duk ta dafe.

'Ikon Allah, ita kuwa wannan mai ya sa take saka abu da datti haka?' Saddiqa ta faɗa a zuciyar ta tana jin wani iri don ita a duniya ta tsani ƙazan ta, abin bai tsaya a nan ba tana sauke idanu a ƙasan zanin ta ga shi ma ya ci uban datti da alama ma an yi ta saka a atamfar. Mamaki take da tunanun ita kuwa bata jin kunya mijin ta ya ga hannun bireziyar ta ko ƙasan zanin.

"Amarya an kwana a baƙon waje" Muryar Sumayya ta katse mata tunani. Murmushi ta yi ta ce

"Wallahi kuwa, ni ina Ruma?" Ta tambayi Æ´arta.

"Ruma bacci take ne"

"Amina fa?"

"Ban ji motsin ta ba tana ɓangaren ta" Haka suka cigaba da taɓa hira daga ƙarshe ta tafi.

Da yamma ta yi ta yin baƙi maƙota da ƴan uwa masu zuwa ganin gidan amarya, da yake shi ma angon tun da ya zo ya ci abincin rana ya fita ganin tana ta yin baƙi.

Sai bayan sallar isha'i ya dawo gidan.

*BAYAN KWANA BIYU*

Da yamma tana zaune tana yankan farce sai Ruma ƴar gidan Sumayya, da Yusuf da Albani ƴaƴan Amina suna wasa. Kallon yaran Amina ta yi tastas da su gwanin sha'awa amma Ruma hancin ta maji duk ta bushe ga kan nata duk kalbar da aka mata ta tsufa wandon ta kuwa sai zarnin fitsari yake, kwata-kwata ƙazantar jikin yarinya ta yi yawa ba don kar a ga baƙin ta ba da ta kora yarinyar wajen uwar ta don ita ba mutum ba ce da take son ƙazami ya raɓe ta, don ko tana gida in dai yaran maƙota suka shigo to kuwa indai kai ƙazami ne gidan ku take kora ka.

Da sallama ya shigo ta amsa, don dama danta masa maganar ya ɗan huta ko sati guda ne sai ya cigaba da zuwa kasuwar cewa ya yi babu wani hutun amarci da zai ɗauka ai maza ƴan su fita su nemo a ci ne. Jikinsa buɗuɗu da fulawa, da yake sana'ar sa aunar da filawa ce, a can kasuwa gaban wasu shaguna yake buɗe buhun filawa yana aunarwa, idan ya ƙare sai ya sake buɗe wani. Sannu da zuwa ta masa ta karɓi ledar hannun sa, sai kallon ta yake yadda ta masa kyau ta yi kwalliyar ta cikin baƙar abaya sai ƙamshi take bakin nan nata yana sheƙin lipstic.

Kicin ta nufa da ledar ta ware kayan miya ta saka a kwando ɗaya ledar kuma kayan marmari ne sai ta saka a frige, ta wanko wasu ta yanko a plate ta zo ta ba yaran, suna karɓa da murna suka fice.

Kayan abincin ta É—akko ta ajiye masa a falon tare da ruwa sai ta nufi bedroom É—in, kwance ta same shi a kan gadon. Ta ji babu daÉ—i ganin jikin sa babu yadda yake duk filawa amma ta hau kan gadon danne abin da ta ji a ranta ta yi, bayi ta nufi tana shirin shiga maganar sa ta katse ta.

"Baki yi sallah ba ne?"

"Sallah kuma?"

"Eh na ga kin nufi bayi" Ya faÉ—a yana kallon ta shi tana birge shi yadda take Æ´ar gayu.

"Ruwan wanka zan haÉ—a maka" Shiru ya É—an yi sai kuma ya ce

"Wane irin wanka da la'asar É—in nan, bakya ganin sanyi ake ai sai mura ta kama mutum" Da mamaki take kallon sa kawar da kai ya yi gefe ya kuwa maje.
Chapter 2 · 0% Book details