← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 44

Sashe 26

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita ya kamo sunan MAMUDA ya doka kira, wajen sau uku wayar tana shiga amma ba a É—auka ba, ba ya raba É—ayan biyu ya san fushi take da shi. Kiranta ya cigaba da yi a ransa yana cewa

'Mata biyu da alama zama da su zai yi wahala, ga shi dai kowacce bata san da zaman ɗaya ba amma a hakan suna haɗa mini zafi, ina ga na haɗa su waje ɗaya a matsayin matana, lallai akwai badaƙala, ni kuwa yanzu ba zan iya rabuwa da Salaha ba, kin ga Amina kenan taki kishiyar tana tafe kema, tun da har kina yin murna za a yi wa wata, shi dama ramin mugunta gajere ake ginawa' Yana wanann zancen zucin ya ji ta ɗauka, amma bata ce komai ba, cikin ɗan karya murya ya ce

"Baby nah, fushi da ni?" Nana ma shirun ne, amma tana jinsa, ya cigaba da faÉ—in

"Amma ai gimbiyar tawa ta bani dama, na kare kaina ko? Amma in aka ƙyale ni sai abin ya mini yawa wai shege da hauka" Dariya ce ta ƙwace mata jin karin maganar da ya yi, wani sanyi ya ji a ransa jin ta yi dariya ya san tana dab da sakkowa. Sai da ta tsagaita dariyar ta ce

"Dama ka iya karin magana amma baka mini?" Wani murmushi ya saki cikin zaƙuwa ya ce

"Ni in kullum ma kike so zan ke miki" Shiru ta yi sai kuma ta ce

"Yanzu ni za ka kira da MAMUDA? Bayan kiran da na maka ka ƙi ɗagawa, har da wanda ka katse" Dimmm gabansa ya faɗi, nan ya shiga haɗa kalaman ban baki yana cewa

"Kin san ya aka yi?" Bai jira ta amsa ba ya É—ora da faÉ—in

"Lokacin da kika kira da farko ba na kusa, da na zo kuma garin in ɗauka na katse, sannan kuma lokacin da na ɗauka, kiran MAMUDA ne ya shigo, ni kuma duk tunanina shi ne kuɗi ne da yake so in ara masa, sai bayan na gama magana na gane katoɓarar da na yi, sanin za ki yi fushi sai na kashe wayar ma baki ɗaya, na ce bari in bari sai kin ɗan huce in zo bada haƙuri, kar in zo ranki a ɓace ki ƙara tunzura" Shiru ta yi tana jinsa, tana kuma nazarin maganarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo sautin ta wayar, sa kuma ta ce

"Allah sarki, ashe duk gudun ɓacin raina ne ya sa ka kashe wayar ma, ba komai na fahimce ka" Daɗi ya ji sosai a ransa, nan suka shiga hirar soyayya, sun daɗe suna magana cikin so da ƙaunar juna, kafin daga bisani suka yi sallama suna masu yin kewar junansu.

Sai da ya ƙarasa shago ya siyo lipton ɗin, sannan ya dawo gida, Amina ko a jikinta da ta ga ya daɗe don bata kawo komai ba, hankalinta yana waya tana gulmar za a a yi wa facalarta kishiya.

Tun da aka yi haka shi ne fa Aminar, take yi wa Saddiqa wani gani-gani tamkar dai ita ce ta jawa kanta kishiyar, shi ya sa ko ranar auren Aminun ma ta rinƙa shiga ta alfarma tana fita, don murna take a ranta tana rayawa saura Sumayya ma, amma ita ta san ita da kishiya sun yi hannun riga.

*AMINU*

Kunya ce ta rufe shi gabaɗaya, yana jin tamkar dai ya je ɗakin Saddiqa ya ɗakko ta ta zo ta maye masa gurbin Zulaiha, ta karɓi baƙin nasa in ya so idan suka tafi ita Zulaihar ta zo.

Amma sai dai bakin alƙamai ya bashe, bai san ledar lemukan hannunsa ta suɓuce ba sai da ya ji Kabiru yana faɗin

"Aminu lafiya dai" Ya lura basu gane abin da yake gani ba, don ya san babu wanda zai yarda cewa Zulaiha matarsa ce, duba da cewa babu wata amarya da za a gani a yanayin da take yanzu. Sanye take da wani zanin atamfa roba, wanda ya ci uban datti tamkar na mai siyar da mai da ƙuli, don yadda ta zo da shi dama babu wani wanki zaninta ne tun tana gida, ita kanta t shirt ɗin da ta daka duk maiƙo ne a jiki ita ma babu wankin kan nan ,nata bucai da shi babu kitso amma ribom ɗin yana jikin gashin, wanda reto ribom ɗin yake kamar zai faɗi saboda gashin ba ya haɗuwa ya yi parking. Tun da ta zo dama bata yi kitso ba, ga kuma uban ruwa da kan yake sha na wankan tsarki.

Wainar fulawa ce a farantin take ci, ta wani barbaje. Haƙori ya saka ya danne leɓansa na ƙasa, yana ƙoƙarij saisaita nutsuwarsa, Lawan ne ya ɗauki ledar da ta faɗin ya riƙe.

Aminu kuwa tunani yake, mai ya sa ta cire les ɗin da ya saka ta saka a jikinta. Ki yake kamar ya je ya yi ta dukanta ko ya huce amma babu dama haka suka ƙaraso shi da abokan nasa yana dariyar yaƙe wacce ta fi kuka ciwo.

Ita kuma ganin suna dab da zuwa, sai ta haɗa tafukan hannayenta ta murza tamkar mai shafa mai, bata nufi ko ina da hannun ba sai kanta, ta shafe maiƙon a jikin gashin kan nata, sai kuma ta mulke ragowar maiƙon a jikin zanin nata ta janyo wata hularta da take gabanta ta saka a kan nata, sai dai wani daga cikin gashin kan nata ya fito daga gefe ɗaya a gaban hular, sai ya yi tamkar doron zabuwa.

Kuka ne kawai Aminu bai saki ba, shu damuwarsa ma Bukari don ya lura Bukarin bai gane cewa wannan matarsa ba ce amaryar da yake ta musu kurin za su je su gani ya yi babban dace, kuma ya yi babban kamu don ya auri muradinsa wacce ƙaddara ta sako Saddiqa a matsayin matar farko kafin ita.

Zulaiha kuwa tana gama saka hular ta miƙe tsaye, tana washe baki tana musu sannu da zuwa, don lokacin har sun zo barandar. Kallonta Aminu ya yi yana jin wani takaicin ganinta da abokansa suka yi a shiga marar kyan gani shiga ta ƙazanta wata irin kunya ta rufe shi yana jin dama bai kawo su ba.

Sai a sannan ya lula tunanin ranar da Khady ƙawar Saddiqa ta zo, yana rayawa a ransa kenan haka Saddiqa ta ji kunya da ƙawarta tw gan shi a haka? Lallai ya yarda cewa baka gane abu har sai an maka shi, amma dai ba za ka gane ciwonsa ba sai in kai aka yi wa.

Sai sannan ya ji ashe bai yi wa Saddiqa adalci ba. Maganar Bukari ne ya katse masa tunani da faÉ—in

"Wai ina amaryar ne" Kallon kallo aka shiga tsakanin Lawan da Kabiru, don su sun gane cewa wannan ta tsaye a gabansu ita ce amaryar.

"Gani kuwa" Zulaiha ta faÉ—a tana Æ´ar dariya irin ta amare, har da wani É—an kauda kai irin tana jin kunya. Washe baki Aminu ya yi cikin wayancewa yana Æ´ar dariya ya ce

"Eh mana, ita ce, ai ka ji ma ta baka amsa, dama masu magana sun ce waƙa a bakin mai ita tafi daɗin ji" Bukari kallonta ya yi yana ɗan jinjina abin a zuciyarsa ya ce

"Sannu amarya" Ta ce

"Yawwa" Aminu kuwa ya ga alamar suna son su raina masa hankali, don sun ga amaryarsa cikin shiga marar kyau, ga kuma abin da ta yi na goge maiƙo a tsakiyar kanta da jikin zaninta, shi ya ma rasa mai ya sa ƙazanta ta zaunawa Zulaiha.

Ya É—auka yadda ta cigaba da karatun nan, zai samu wayewa da tsafta ta fitar hankali, amma dai sai ya ga tana abu kamar dai bata shiga ajin ma kwata-kwata ba.

Ya ƙagara su shiga cikin ɗakin, don su gane ita fa ta rasa giɓi ne ta wani ɓangaren, amma ta fannin girki za su gane yau kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Gaba ya yi yana cewa

"Bismillanku" Suka take masa baya, ita kuma Zulaiha sai ta koma gefe suka wuce. Suna shiga ɗakin suka zazzauna a ƙasa inda ta shimfiɗa table mart ta jera abinci, Aminu sai washe baki yake yana so ya mantar da su abin da suka gani, dai da suka zazzzauna kamar an ce ya kalli gefe kusa da Bukari ya hangi breziyar Zulaiha yashe a wajen, gata ta ci uban dauɗa, hannun breziyar daƙwa-daƙwa kamar mai tallar kalwa, ganin hakan Aminu ya shiga faɗar hakan a zuciyarsa

'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakil, kin kashe ni Zulaiha'

Babu wanda ya lura da breziyar, shi ya sa yake fatan ya samu nasarar kawar da ita daga wajen, ba tare da idanun É—aya daga cikinsu ba ya gani.

Amma dai ya san da wuya hakan ta kasance, sai a sannan ya tuna ranar da Saddiqa ta ce ya bar mata gajeran wando a falo, amma ya nuna ko a jikinsa ashe dai ko da kai ƙazami ne akwai abin da baka so a gani, bai ankara ba ya ji Lawan ya ce

"Abokina wai ya duk ka yi shiru ne?"

Yaƙe ya yi yana sosa ƙeya, amma hankalinsa yana kan breziyar nan ta Zulaiha, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangi kan gadon ma duk ta cukurkuɗa shimfiɗar, ga kayan da ta cire nan yashe a kan gadon. Sai ya ji dama dai ko durƙusawa Saddiqa ne ya yi ya roƙe ta a kan ta karɓi baƙin nan a wajenta, ya san ko ledar pure water ba za ta jefae a ɗakinta ba, bare kuma wata breziya, a zuciyarsa ya ce

'Allah na tuba breziya ko wankakkiya ce matarka ta jefar abokanka suka gani ai da kunya, bare kuma wannan daƙalƙalar ta ci datti ta more' Cikin kawar musu da tunanin ya ce

"Lah ba komai fa, da yake yau na tashi da ciwon kai" Ya faɗa yana ƴar dariya, tare da kallon Bukari yadda ya ga duk ya yi kamar dai a takure yake, da alama dai ganin Zulaiha ko ya sa ya ji ƙyanƙyami kasancewarsa mai tsantsani.
Chapter 26 · 0% Book details