← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aminu to ƙwarƙwata ce a cikin kanka cunkus, gata nan har wata ta zo wuyanka daga cikin kan kuma ta ganganro" Da sauri Aminu ya cire hannuwansa daga kan nasa yana mai miƙewa tsaye a kiɗime, don maganar da dake shi matuƙa ya ce

"Kwarkwata Umma? Dama kwarkwata tana fitowa maza na shiga uku" Ya faÉ—a har lokacin yan tsaye hankalinsa a tashe. Cikin halin ko in kula Umma ta ce

"To mene ne na kiɗimewar? Abin mamaki ne don an samu shazumamu a wajen da aka zubar da suga? Ai ba zai zama abin mamaki ba, tun da in dai an ga zara za a ga wata, in har an zubar da suga ko abu mai zaƙi dole shazumamu ya baibaye wajen, to haka ma tun da kwarkwara ƙazanta ce take kawota ka ga babu ruwanta da kan mace ko kan namiji, duk inda ta samu ƙazanta ta samu mafaka kenan" Umma tana mas wannan jawabin shi kuma ya tafi tunani kamar wanda ya tuno wani abu ya ce

"Wallahi Umma wannan kwasa mini aka yi, tun da Zulaiha ta tare take soshe-soshe a kanta da jikinta, wallahi sai dai in ita ta kwasa mini"Sheƙeƙe Umma ta kalle shi ta taɓe baki ta ce

"Abubya haɗu dai guda biyu, dama can kwarkwatar ta samu mafaka ne saboda tsabar taka ƙazantar" Komawa ya yi ya zauna ransa yana ƙuna, yana hango yadda za su kwashe da Zulaiha don sosai ya ƙara tunzura. Umma ta ɗora fa faɗin

"Yanzu Aminu kana magidanci da mata har biyu, É—aya tana da ciki amma a ce wai an samu kwarkwata a cikin gashinka? Shin ya kake so in yi da kai? Ka mallaki hankalinka ma sai ina maka faÉ—an ka gyara jikinka, ko so kake in ke binka gidan naka ina maka wanka ina saka ka gyara jikinka, don Allah dubi kanka kamar tukufar tsire, babu aski babu gyara wari jir ko yanzu baka ji wurin nan yadda yake tashin wari ba, ina amfanin baÉ—i babu rai, yanzu wa ya san tsawon lokacin da ka kai baka yi aski ba, kuma wa ya san lokacin da ka kwashe baka yi wanka ba...

"Jiya da abokaina za su zo na yi wanka wallahi Umma, ni fa kawai gani nake wankan nan don a ji sanyi da iska ake yi, kuma tun da Allah ya kawo mu, lokacin sanyi ba sai mutum ya huta ba" Tsabar takaici ma sai ta rasa bakin magana, ganin bata ce komai ba ya É—ora da faÉ—in

"Maganar aski kuwa Umma yanzu ai zamani ya sauya, ba a wani aske gashi, duk mai askewa ma kallon kidahumi ake masa wanda bai waye ba" Baki kawai ta saki tana kallonsa jin bata ce wani abu ba ya É—ora da faÉ—in cewa

"Ko kuma a yi wa lan wani gyara ki ga kamar kalba, duk ya dunƙule waje-waje haka ake yi... A tsawace ta ce

"Wayewa ko ƙazanta, ai gashin da ake bari wanke shi ake tas a shafa masa mai a taje, amma ba naka ba kai da baka yi wanka ba ma za ka wanke kai? Yanzu a haka ma gashinka ya samu kwarkwata bare aka maka gyaran curi-curi ai ina ga har ƙudan cizo sai an samu a cikin kanka" Yana kallonta yana susa hannu bibbiyu. Ta cigaba da faɗin

"Ka gyara halinka, ƙazantarka kaɗai za ta sa mace ta rainaka, yanzu a ce miji ba zai yi wanka ya saka kaya a wanke ba, kalli haƙoranki har wani iri suka yi kamar mai cin goro, don Allah wace mace ce za ta ji daɗin ganinka a matsayin mijinta?" Shiru ya yi yana wani harhaɗa rai ya ce

"Ni fa Umma babu wata mace da ta isa ta ja da ni, ko ta kawo mini raini a cikin gidana, in kuwa ta ce haka za ta yi wallahi Umma sai ta gwammace kiÉ—a da karatu... Katse shi Umma ta yi da faÉ—in

"Dalla rufewa mutane baki, shi ya sa ai na ga yanzu ma matsalar gidan naka ce ka kawo, kuma shi ya sa na ga tsabar isarka ce gashi nan matarka a gidanka ta bika har ɗakin matarka ta maka ihun kwarto" Shiru ya yi yana tuna yadda ya so yau ya kwashe ganima a wajen Saddiqa da jikin nan nata tsaftatacce mai daɗin ƙamshi amma kuma Zulaiha ta katse masa hanzari har yanzu in ya tuna ji yake kamar ya je ya yi ta bugunta har sai ya ladabtar da ita, amma duk da haka yana nan a kan bakarsa na ba zai yarda da raini a gidansa ba, dole duk wacce ta so ta taka shi ya taka ta son ransa.

Jin ya yi shiru Umma ta cigaba da faɗin, ban maka baki ba Aminu amma na tabbata ba za ka taɓa samun mai hankali da nutsuwa haɗe da haƙuri da juriya kamar Saddiqa ba, amma yanzu kai wannan kwarkwatar ma ina za ka je da ita, cunkus a kanka wace mace ce za ta yarda ka raɓe... Shigowar Fatima ce ta katse maganar da Umma take, gabaɗaya Fatima ta ji abin da Umma ta ce, hakan ya sanya ta zaro idanu haɗe da toshe baki ta ce

"Umma kwarkwata kuma a kan Yayan? Na shiga uku wayyo Aunty Saddiqa kin gamu da jarab... Hararar da Umma ta bita da ita ce ta sanya ta haÉ—iye sauran maganar.

Aminu kuwa jin furucin ta sai ya tashi tsaye a ƙufule yana nuna ta da yatsa ɗaya ɗayan kuma yana susa ya ce

"To magulmaciya, wallahi kika sake wannan maganar ta fita sai na sauya miki kamanni, don wallahi dukan tsiya zan miki" Fatima da sauri ta koma bayan Umma ta raɓe tana cewa

"Umma ni fa ba wani na ce zan faÉ—awa b... Katse ta Aminu ya yi da faÉ—in

"Ki faÉ—a mana, uwar shgen shishshigi" Umma ganin yana kumfar baki ta ce

"Fatima fita ki ba mutane wuri" Fita ta yi tana kallonsa ƙasa-ƙasa da sakin dariya a ɓoye, da sauri ya bita zai kai mata duka Umma ta ce

"Dawo nan, wai kai yaushe za ka nutsu yanzu ƙarya aka maka kalli yadda kake sosa kai, ai abin kunyar ya yi yawa ni takaicin ma kamar in yi kuka nake ji na rasa ya zan yi da kai Aminu, tun kana ƙarami nake fama da kai, amma har yanzu ka kasa gyara rayuwarka da tsafta, komai ƙazanta bakya jon kunya, ko kaɗan" Jin tana faɗa ya koma ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai amma fa har zuciyarsa shi bai ga abin da ya yi wanda za a ke masa wannan maganganun ba tun da gani yake a kan daidai yake.

Suna nan tana ta masa faɗa, har ta koma masa nasiha don abin ya fi ƙarfin faɗa, da a ce Aminu yana jin faɗa da an wuce wannan wajen, shi kaɗai ne Allah ya bata ƙarami a cikin ƴaƴanta kuma marar jin magana, ga taurin kai tun yana ƙarami yake bata wahala, amma har yanzu ana fama da rashin tsaftarsa ta ɗauka idan ya yi aure abij zai yi sauƙi amma ga shi abu yana cakuɗewa har kai da kwarkwata.

Ranta duk a ɓace ta shiga tunanin tun yana ƙarami, kowa zai yi brush amma shi ba zai yi ba, in har zai yi wata da watanni bai wanke baki ba to bab ruwansa sai dai an ce ya wanke, wani lokacin ma sai Umma ce za ta saka masa makilin a brush ɗin, amma in ya faki idanunta sai ya saka ruwa ya wanke makilin ɗin daga jikin brush ɗin a ajiye. Ta sha fama amma a banza, mai ya fi takaici a ce mutum da iyali amma kana masa faɗan wanka. Ɗagowa ta yi idanunta sun i ja ta ce

"Yanzu Aminu kalli farcenka, zaƙo-zaƙo kai baka san cewa farce inuwar shaiɗan bace? A jikinka kai to mene ne kake gyarawa? A haka za ka ji daɗin gabatar da ibada anya kuwa?" Shigowar Baba da sallama shi ya katse maganar da suke yi.

Waje ya samu ya zauna, yana kallonsu Aminu yana ta faman susa, Aminun ne ya gaishe da shi ya amsa, yana kallon yadda yake sosa kai, duk da Aminu yana ƙoƙarin danne ƙaiƙayin kar ya yi susar amma abin ya ci tura.

Kafin Baba ya fara magana Umma ta ce

"Gashi nan ya kawo ƙaran matansa" Nan ta kwashe komai ta faɗawa Baba, buɗar bakin Baba sai cewa ya yi

"Aminu da yardar Saddiqa ka ƙarawa amaryarka kwanaki?" Ƙoƙarin saita kansa ya yi ya ce

"Eh, eh, eh Baba" Shiru Baba ya yi Umma kuma ta shiga aikawa Aminu harara yana sadda kai ta ce

"Ƙarya yake" Nan Umma ta shiga faɗawa Baba dalla-dalla. Baba ya rufe shi da faɗa ya ce ba ya son rashin adalci in rashin adalci zai yi to gwara ya sawwaqewa ɗaya, jin haka sai Aminu ya yi zuruf ya ce

"Amma Baba banda Saddiqa ko? Sai dai Zulai... Katse shi Baba ya yi da cewa

"Aminu gatse na maka fa, ni yanzu kana ganin zan iya saka ka saki matarka babu wani dalili? To ka buɗe kunneka ka jini, tun da ka aure su su duka mutuwa ce za ta rabaku, sannan ina so ka sani duk rashin adalcin da ka yi musu ko ka dannewa wata haƙƙinta Allah ba zai barka ba" Kai ya sunkuyar Baba ya masa tas ya ce da Yamma Umma ta je gidan ta sasanta matsalar.

Umma ta faɗawa Baba maganar kwarkwatar Baba kaɗan bai kai masa duka ba saboda haushi. Nan ya ƙara masa gargaɗi a kan tsafta ya ce ya kama hanya ya tafi kasuwa, haka ya musu sallama ya fita Umma tana cewa idan ya je kasuwa ya saya maganin kwarkwatar ya kai wa ita Zulaihar sannan shi ma ya yi wanka kuma ya wanke kan nan tas ya saka magani, da to ya amsa ya fito.

Yana cikin tafiya a tsakar gidan Fatima ta leƙo tana danne dariyarta ta ce
Chapter 34 · 0% Book details