← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saddiqa ina son sanar da ke wata magana, gabanta ne ya faɗi bata san dalili ba, amma hakan ba ya rasa nasaba da rashin sabo a ce Aminu ya zauna ya ce za su yi magana, cikin nutsuwa haka. Kofin ta ajiye ta saka cokali ta bashi hankalin ta, yana wani ɗaɗɗaga kai irin na rawar kan da ango yake idan zai yi ƙara aure ya ce

"Dama ba wata magana ba ce, ina so abin da zan faɗa ki ɗauke shi ƙaddara, idan kuma baki ɗauka ƙaddara ba, za ki iya ɗaukansa duk yadda kika ga dama" Kallon mamaki ta masa haɗe da na rashin fahimta kafin ta furta komai ya ce

"Aurena nan da sati huɗu" Gabanta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta danne ta ƙura masa ido tana mamaki, hanzarin katse ta ya yi da faɗin

"Za ki zaɓi guda ɗaya, ina nufin ko bedroom ko falo, don ɗaya za ki haɗe kayanki ɗaya ita ma ta zauna" Dummm kunnuwanta suka yi, ta ji zafin maganar amma sai ta mayar da komai ba komai ba, saboda ita yanzu ta rasa a wajen Aminu mene ne za ta yi alfahri da shi a tare da shi ɗin? Wanda har zai sanya ta ji kishinsa, duk wani abu ya toshe hanyar sai dai abin da ba a rasa ba.

"Kai ma sha Allah, amma na ji daɗi, kuma na taya ka murna matuƙa Allah sa abokiyar arziƙi ce" Ta faɗa hankali kwance tana mai ɗaukan kofin ta cigaba da shan garin, duk da tana jin garin a yanzu tamkar maɗaci take sha. Tsaye ya tashi da sauri sai kuma ya koma ya zauna, baki sake yake kallonta yana son gano maganarta da gaske take ko kuma ƙarfin hali ne, saboda abokinsa ya ce masa yau babu zaman lafiya wataƙila ma Saddiqar ta shaƙe masa wuya. Ransa ne ya ɓaci ganin bai gano komai ba a fuskarta sai kwanciyar hankali alamar dai maganar bata ɗaɗata da ƙasa ba, cikin ɓaci rai ya fara magana yana cewa

"Saddiqa anya son Allah da annabi kike mini? Ya za a yi bayan an ce kishi kumallon mata amma ke in zo miki da maganar kishiya ki mini addu'a, sona ne bakya yi ko kuwa? Don duk inda so yake akwai kishi" Daƙyar ta ci nasarar danne dariyar da take taho mata, ganin ya haƙiƙance yana faɗa da tada jijiyoyin wuya amma sai ta kalle shi ta yi fari da ido haɗe da murmushin fatar baki ta ce

"Kamar ya? Tambaya kake ko neman sani? "

Wannan yanayin da ta yi furucin ya sake harzuƙa shi ya ce

"Cewa na yi anya kina sona?" Wannan karon dariyar da ta yi sai da kyawawan haƙoranta suka bayyana ta ce

"Shafa ka ji" Tsaye ya ƙara tashi ganin ita ma ta miƙe, yana huci ya ce

"In shafa ina? Ai so a zuciya yake ke ya kamata ki faɗa mini" Kallon sheƙeƙe ta masa ta ce

"Ni ma ban sani ba, abu ɗaya dai na sani ni matarka ce, sanna kai mene ne damuwarka da ina sonka ko ba na sonka, kai da za ka kawo sabuwar amarya? Abu na gaba ka kira amaryar ka tambaye ta tsakanin falo da bedroom wanne take so, duk wanda ta zaɓa sai ka faɗa mini na ɗauki wanda bata zaɓa ɗin ba" Tana gama faɗar haka ta fice daga falon ta tafi kicin za ta kai kofin da ta sha garin.

Tsaye ya yi yana riƙe da ƙugu da hannu biyu, ransa ƙuna yake shi da ya zo ya ɓata mata rai, amma ido ya juye da mujiya tun da ga shi, shi ne yake tsaye ransa yana ɓaci. Kallon jikinsa ya yi yana rayawa a ransa to shi kuwa bai kai a yi kishinsa ba ko me? Shi da ake bashi labarin yanzu zai zama kamar ƙwai a wajen matan nasa, kowacce tana ririta shi, kowacce za take son shi ana rububinsa amma tun ba a je ko ina ba Saddiqa ta nuna shi bata kishinsa?.

Yana cikin wannan halin wayarsa ta fara ƙara, ɗakkowa ya yi ya ga sunan abokinsa, a ƙufule ya ɗaga daga ɗaya ɓangaren abokin ya ce

"Ango ka sha ƙamshi, ango ɗan gatan amarya da uwar gida" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare masa wuya, tsabsr haushi kasa cewa komai ya yi ya katse wayar, don ya san yanzu yana faɗa masa yadda suka kwashe da Saddiqa da ya sanar da ita auren, shikenan ya samu abin tsokana.

Saddiqa kuwa tana zuwa kicin ta ajiye kofin, wani irin ɓacin rai ne yake dabaibayar zuciyarta, ita ganin yaushe ma aka yi aurenta, yaushe ma ta ji daɗin zaman gidan mijin da har za a kawo mata wata abokiyar zama?.

Ta jima tsaye a kicin ɗin har sai da ta ji ta samu nutsuwa ta hanyar yin addu'a sannan ta dawo falon, bata same shi ba baki ta taɓe tana ƙarewa falon kallo, bedroom ɗin ta ƙarasa tana ƙare masa kallo ta tabbatar duka biyu babu wanda zai iya ɗaukan kujeru set da kayan gado, dole sai dai an rage kujerun.

Bakin gado ta je ta zauna, ta É—auki wayarta ta kira, Mamyn ta, bayan sun gaisa ta shiga labarta mata abin da Aminun ya sanar da ita, sosai Mamy ta kwantar mata da hankali, duk da ta ji ciwon abun kuma ta lura tun ba yau ba Saddiqar tana cikin damuwa amma dai babu yadda za a yi da abin da Allah ya tsara.

Noor ƙanwarta ma da ta karɓi wayar, sai da ta kusa kuka jin za a yi wa Auntyn ta kishiya, gabaɗaya ma ita sai ta ji aure ya fita ranta, tun da dai tana ganin soyayyar da take tsakanin Aunty Saddiqa da Yaya Aminu amma tun ba a je ko ina ba zai mata kishiya.

Bayan sun gama ta kira Khady take faɗa mata, haushi ne ya turnuƙe Khady ta ce

"Ai gwara ma ya yi auren, kya samu salama ta wani fannin, ki yi haƙuri ƙawata mahaƙurci mawadaci, in dai aure ne ga wurin nan in kika yi haƙuri kwana nawa ne, maye ya yi amarya ya cinye kayarsa da sannu watarana za ki gan su a rana ke dai ki kame kanki ban da ɗaukan cin fuska ko raini" Sosai Khadyn ta kwantar mata da hankali hakan ya sa ta ji ƴar salama a ranta.

Ummar Aminu har gida ta zo ta lallashe ta, tare da bata haƙuri sosai Saddiqa ta ji daɗin kulawarta, ko ba komai ta ƙara kima da daraja a idanunta.

Aminu tun daga ranar ya shiga muzurai, shi a dole Saddiqa bata son shi, hakan ya sanya duk abin da zai yi da gayya yake don ranta ya ɓaci, amma ita sai ta yi kamar bata san yana yi ba.

Da yake Zulaiha ya tambaya ta zaɓi bedroom, hakan ya sa Saddiqa aka mayar mata kujerarta guda ɗaya gida, da yake bata samu waje a falon ba, ƙofar bedroom ɗin kuma ya rufe ta, aka fasa wata daga waje aka fara aikin amarya haiƙan duk da yana jin ciwon fitar da kuɗin amma ina ya tuna gwangwajewa zai yi da amarya, sai ya da dama-dama kibiya a ido.

Wani sabon salon wai kiran sallah da usur, Zulaiha ta ce ita ba za ta zauna a ɗaki mai siminti ba, dole sai an saka mata tiles har jikin bango, haka Aminu ya yi ƙuri ya saya aka gwangwaje ɗakin amarya uwar gida kwa ko oho.

Kasancewar bayin a bedroom yake sai ya zamana ya zama a ɓangaren Zulaiha hakan ya sa aka yi wa Saddiqa wani bayin a waje, tun da wanda yake tsakar gidan na kowa da kowa ne. Saddiqa duk da ta ga yadda yake kashe kuɗi ana aiki amma bata ɗaga hankalinta ba.

Sumayya da Amina suna gefe suna mata dariyar ƙetar za a mata kishiya, lamarin sosai ya tsorata Amina ganin Aminu zai yi aure, ita da take sha'awar miji ƙazami saboda tsabar kishinta amma sai ga shi ƙazamin zai yi aure.

Tun da bikin ya ƙarato yawancin kullum yana gidan su Zulaiha ƴar aljanna, ɗakin amarya kullum in zai fita ya garƙame da mukulli, sai dai ba a raba musu kicin ba don wannan guda ɗayan ne hakan ya sa Saddiqa ta tattara kayan kicin ɗin ta saka a lokokin kicin ɗin ta bar wanda za take amfani da su kawai.

Ganin bikin ya zo, sai Aminu ya fara É—aga mata wani kai, yana jijji da kansa ki gidan ya dawo sai ya buÉ—e É—akin amarya da aka gama ya shiga, wani lokacin ma sai dai in ta je kicin ta ga ya zuba abincinsa ya je É—akin amarya ya ci, wai tun kafin amaryar ma ta tare.

Tun saura kwana biyu É—aurin aure aka zo aka yi jere a É—akin amayar, ango sai giggiwa yake yana bada faÉ—i shi ala dole mai amarya.

A ɓangaren amarya Zulaiha babu ya ita, don magungunan matan MEERAH B HERBS masu kyau da inganci, da farko maganin sanyi Mamarta ta saya mata na kamfanin MEERAH B HERBS, saboda duk wani abu da ya shafi maganinmata ba ya aiki, in har akwai sanyi a jikin mace. Magungunan mata da na hips, duk na MEERAH B ne suka saya a wajen Maman Afrah ga number ta mai buƙata ya tuntuɓe ta 09025576222, don kama daga set na kayan uwar gida, set na amarya, set na mai jego babu abin da basa siyarwa.

Zannuwan gado da labulaye, tumtum da frame, duk a wajen Maman Afrah akansiyawa Æ´ar aljanna, jin yadda magungunan suka fara saukar mata da ni'ima ya sa ta gane tabbas magungunan kamfanin MEERAH B HERBS suna da kyau.

Yau ya akama asabar a yau aka É—aura auren Aminu da amaryarsa Zulaiha.
Chapter 20 · 0% Book details