Sashe 27
Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zulaiha kuwa da suka shige ta koma ta zauna, har ta zauna ta tuna ba ta kai plate da cokula ba, tashi ta yi ta tafi kicin É—in amma plate É—in wainar fulawa yana nan da É—an guntun yaji a kan farantin.
Riƙe ta taho da plate ɗin da colula a ka, sai kuma kofuna a kan wani plate ɗin, da sallama ta shigo tun da ta shigo wani haushi ne ya turnuƙe Aminu yana aika wa zanin jikinta harara ƙasa-ƙasa, sai lokacin ya ƙure ƙirjinta da kallo ya ga ashe dai breziyar da ya gani cirewa ta yi babu wata a jikinta.
"Barkan ku da rana ina wuninku" Ta faɗa tana daga durƙushen da ta yi, ganin Aminu ya yi fuska sai muzurai yake, ana haka Bukari ya ɗaga hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan breziyar Zulaiha, ya juya zai kalli wajen da sauri Aminu ya ce
"Ni Bukari baka bamu labarin wajen aiki ba" Wannan maganar ce ta É—aukewa Bukari hankali, bai ga breziya ba, shi kuma Aminu sai tunanin yadda zai yi ya kawar da ita ba tare da sun ankara ba. Zulaiha kuwa bayan ta gaishe su, ta É—auki zanin less É—inta a kan gado ta yafa a kanta kamar mayafi don sai lokacin ma ta tuna suturcr jikinta tun da a gaban abokansa ne.
Aminu kuwa sai signa yake mata, a kan ta gyara gaban goshinta, wato hular nan inda gashi ya fito, don ganinta yake kamar bararoji.
Tana fita aka Lawan ya matso da plates É—in yana faÉ—in
"Ya kamata mu fara cin abincin nan" Kowa da to ya amsa suka ma manta da batun Zulaiha, sai Aminu da yake kallon breziya lokaci zuwa lokaci yana fatan Allah sa kar su gani, shi ya manta yadda Khady ta ga gajeran wandonsa, Kabiru ne ya ce
"Ni fa a rayuwata ina son cin girkin amare, ban san mai ya sa girkin amarya ya fita da ban ba, shi ya sa ina son abokina ya gayyace ni cin abincin amarya" GabaÉ—aya suka kwashe da dariya, aka shiga buÉ—e flaks.
Lawan ne ya buɗe flaks ɗin tuwon, ganin tuwon bai mulmulu ba, alamar dai ruwa bai ishi shinkafar ba, sannan ina iya ganin shinkafar raɗo-raɗo alamar rashin tuƙuwa, lura ne ma basu yi ba da sun ga yadda wata take fari tas alamar tana ɗanyarta.
Lawan sakawa kowa tuwo guda É—aya, a plate É—insa, Kabiru har ya ce
"Wannan ai zubin rowa ne, ni na fi son malmala biyu" Sai suka fashe da dariya, irin ta abokai, nan kowa ma ya ce biyu za a zuba masa, amma saboda tsokana sai Lawan ya ce
"Kai ango guda ɗaya za a bar maka, tun da kai kullum kana cin abincin amarya" Dariya ya yi, Kabiru ya buɗe flaks ɗin miya ta yi kauri kirtif saboda yadda aka kaɗa kukar da yawa, ga ɗan ƙarnin kifin da ta saka a miyar yana tashi, kasancewar bata saka corry da sauran kayan ƙamshin da zai kashe ƙarnin ba.
A haka dai aka zubawa kowa miya, basu damu da ƙarnin ba ko yadda miyar take koriya tsarrr tun da wani abincin a ido ne bashi da kyan gani amma a baki sai ka ji yana da ɗanɗano.
Kabiru ne ya gyara zama ya ja nasa farantin gabansa, da yake table mart É—in tana da girma ya ce
"Gwara na jingina da kujera, kar na fara ci na yi santi ku ce a saka mini waigi" Ya faÉ—a yana haÉ—iye yawu. Lawan ne ya yi dariya ya ce
"Yo dama santi ai sai dai in baka fara ci ba" Bukari ya ce
"Ni dai na san da wuya in koma gida da kunnena, wataƙila a cin abincin zan cire kunne ɗaya" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, Aminu ya ce
"Idan kuka fiye yabawa ƴar aljannata abincin ta, ba zan ƙara kawo ku cin abincin ba" Aminu ya faɗa don yadda suke ta zuzuta abincin sai ya ji tamkar dai sun ci ne, a ransa ya san dai yau in suka ci za su kusa tsinke yatsa, Kabiru ya ce
"Kishi ne ya motsa Aminu, baka so a yabawa amaryar taka" Bukari ya ce
"Surutun ya isa haka, a ci abinci" Kowa cokali ya ajiye wai ba za su ci tuwo da cokali ba.
Aminu ne number one wajen gutsurar tuwo ya haɗo da miya, kafin kowa ya kai nasa ne ya fara isa bakinsa, wani irin ɗaci ne ya ziyarci bakinsa gabaɗaya bakin ya game da ɗaci tamkar ya tauna magani filajin, idanu ya ƙwalalo yana kallon abokan nasa a fakaice yana addu'ar Allah sa wani abu wanda zia dakatar da su daga saka tuwon nan a bakinsu ya bayyana, ko da a ce a waje ne za a yi ihun gobara a kawo ɗauki tabbas zai yi yadda zai yi ya sa su tafi taimako amma dai ba ya fatan su ci.
Haka ya daure yake mumulmumultu da tuwon a bakinsa, tamkar tsohon da babu haƙori a bakinsa, yana cikin wannan halin ya ga Lawan ya ɗago idanu ya kalle shi yana riƙe da tasa lomar tuwon da ya yi wa wanka da miya, da sauri Aminu ya yi yaƙi da zuciyarsa wajen sauya akalar fuskarsa, daga yamutsewar jin ɗaci zuwa walwala, muduk ya haɗiye tuwon babu shiri, gabaɗaya ɗacin har maƙogwaronsa. Maganar Lawan da Kabiru ce ta dawo da shi daga suman ɗacin da ya yi jin sun haɗa baki wajen faɗin
"Bismillah" Kafin wani yunƙuri sun kai lomar a kusan tare, Bukari ne na ƙarshe, yana sakawa ya yi fosta da lomar tuwo a bakinsa, shi bai haɗiye ba shi bai tofar ba. Wani tari ne ya ƙwacewa Lawan bakinsa da tuwon da sauri ya ce
"Kabiru lalumo ledar lemon can ka miƙo mini kashina" Kabiru kamar jira yake ya warto ledar ya ɗakko lemon, maimakon ya miƙawa Lawan sai ya buɗe robar ya kafa kai dakyar ya samu ya kora tuwon nan da lemo, yana zare idanunsa da suka yi jawur saboda tsabar wahalar ɗaci.
Kafin Kabiru ya gama shan lemon Lawan da yake ganin ba zai iya jumurin buɗe wata robar ba, ya warce sauran ya shiga kwankwaɗa, sai da ya ji faɗawar nashi tuwon bidik sannan ya shiga dawowa hayyacinsa, bai ankara ba Bukari soja ya karɓe saura lemon don shi ya fi kowa shiga tashin hankali saboda ya tsani abu mai ɗaci ko yaya, bare wannan ɗacin mai ɗaga hankali, Aminu kuwa shi a dole sai wayincewa ya yi da faɗin
"Kai gayu kuna yarfa ni fa, so kuke amarya ta shigo in ji kunya, ga lemuka nan kala-kala amma kun zauna kuna fasin-fasin da guda ɗaya kamar kun samu ƙwallon ball" Ya faɗa yana daurewa ya suri wata lomar amma wannan karon ƙarama ya ɗauka, su duka ukun kallon inda zai kai lomar suke, suna mamakin to ko shi bai ji abin da suka ji ba, haka Aminu ya yi shahadar aika lomar nan bakinsa, wani amai yana neman tahowa, haka ya daure ya haɗiye.
Abin ya haɗe goma da ashirin, tuwo ɗanye duk ɗanyar shnkafa a ciki, ga miya ƙarni ga kuma wani ɗaci mai shiga harshe.
Dakyar ya samu lomar ta shige cikin, a take cikinsa ya ji yana murɗawa. Yana ankare da sauran babu wanda ya sake gigin kai wata lomar bakinsa, sai juya hannu suke a farantin to shi ma da aka bashi malmala ɗaya da yaya, bare su kuma masu malmala bibbiyu. Ya san tabbas kara ce suke masa, basa so su nuna wani aibi daga tuwon shi ya sa kuma don kar ya ji babu daɗi suka ƙi ajiyewa. Cikin wayincewa ya ce
"Gayu dama fa basu son tuwo, gwara mu fara da zabuwar can da ta dha dahuwar amare, kuma dai na ɗan ji kamar hannun amarya ya ɗan goce a miyar nan wataƙila miyar ta ɗan kama ne, shi ya sa take ɗan ɗaci" Ya faɗa yana ture plate ɗinsa gefe, su duka ukun kamar jira suke suka turo nasu, fita ya yi zai ɗakko musu ruwan wankin hannu, don ba ya ƙaunar ƴar aljanna ta sake dawowa ɗakin, bare da ya ga ta ɗauki wani uban zanin leshi ta sha lulluɓi da shi.
Yana fitowa ko inda take bai kalla ba, kicin ya je ya É—akko ruwa a wata roba mai É—an faÉ—i, da ya dawo fuskar nan tasa a haÉ—e yana dab da shigewa É—akin ta ce
"ÆŠan aljannata, ya kuka ji tuwon? Amma fa don Allah kar ku cinye duka wallahi ban É—auki nawa ba" Wani takaici ne ya sa ya kasa magana, kaÉ—a kansa ya yi a zuciyarsa yana cewa
'Indai wannan tuwon naki ne, mai kama da maɗaci ga shi nan an bar miki har na ɗumamen safe ma kya samu' Ya faɗa a zuciyarsa yana shigowa falon, da ya ji suna zance ƙusƙuƙus amma yana zuwa sai aka yi ɗif, kunya dai yau ya san ya kunyata daɗinsa ɗata ma sa ci naman ba sa zauna da yunwa ba, ko dai su zo basu ci komai ba.
Kowa hannunsa ya wanke suka ɗan fatsar, farantin da ta ɗoro kofuna ya sauke ya jirkice musu naman a ciki, sai turiri yake tuni kowa ya ɗan murmusa, suna jin daɗi an raba su da alaƙaƙai wato miyar maɗaci, don wanna sunann ne ya dace da miyar duk da babu wanda ya san dalilin da ya sa miyar ta yi ɗaci, wannan amsar sai Hajiya ƴar aljanna.
Wani ya ɗau cinya, wani haƙarƙari, wani kwankwaso, kowa dai da abin da ya ɗauka, a baki suka luntuma a tare, kowa ya shiga kokawa da naman da sai an yi yaƙi zai gutsuru saboda tauri, idanunsu ya ƙanƙance jin wani ɗanɗanon da ya bambanta da na miyar tuwo, ɗanɗanon da duk cikinsu su huɗun basu taɓa cin karo da shi a cikin nama ba, ba a nan gizo yake saƙar ba jikin haƙarƙarin hannun Kabiru wata ƙatuwar ƙusa ce wacce romon naman da ya baibaye ta, bai hana a ga tsatsar da ta yi ba.