← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 44

Sashe 15

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa ta yi za ta gabatar da sallar asubar sai kawai ta ji wani haushinsa ya cika mata rai, tana tunanin a ce su uku a gidan kowacce mijinta ya tafi masallaci amma nata a kwance, shi ba da zuwa masallacin ba kuma bai yi a gida ba. A zuciye ta nufe shi tana zuwa ta cire masa bargon da ya ƙudunduna, can gefe ta warɓar da bargon sai ga shi ya bayyana tsirara, ita kuma sai ta kama ƙugu ta fara jijjiga jiki don ta ga alama sai ta yi da gaske gwara ma tun kan ta fara haihuwa ta yi wa tufkar hanci, kafin yara su zo su ga halin da ake ciki.

A ƙufule ya buɗe idon jin iskar da ta fara shiga jikinsa suuuu ya gane buɗe masa rufar ta yi, zaune ya tashi ya shiga ƙarewa kansa kallo ganinsa tsirara cikin dakakkiyar murya ya ce

"Wai ni Saddiqa sa'anki ne ni, ko don kinnga makwancina ne raini ya shiga tsakaninmu? Sabosa kina matata kin saba ganina babu kaya har hakan ya zama raini? Ina rufe ki zo don ƙarfin hali ɓarawo da sallama ki buɗeni tsirara ki tsaya a kaina?" Ya faɗa yana wani huci kamar kumurcin zaki.

Ganin haka ita ma ta maje ta ce "Mene ne na rainin a ciki? Ni ban ga wani abin rainaka ba, tun da wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, da kake cewa na buÉ—e ka tsirara shin dama ba haka ka kwanta ba? Ai ni ce dama na suturta maka jikin naka amma dama hakan ka kwanta ai"

Wani kallo ya jefe ta da shi ya ce

"Don kin rufa mini bargo shi ne kika buɗe, ai da kin barni na kwana a haka tun da ba roƙar ki na yi ki rufe ni ba" Ya faɗa yana waige-waige, bata san mai yake dubawa ba sai ta ga ya leƙa can gefen gado, sai kuma ya shiga ɗaga filillikan bata ankara ba sai ji ta yi ya ce

"Ina kika kai mini gajeran wandona?" Ji ta yi kamar ta yi kuka amma sai ta ce

"Tun da baka bani ajiya ba a kan mai za ka tambaye ni"

Kai ya jijjjiga alamar lallai wuyanta ya isa yanka tun da suka fara musayar yawu da ita, ɗaya gefen gadon ya leƙa inda wandon yake sai kuwa ya hango shi yamushe a ƙasa, ɗakkowa ya yi ko karkaɗewa bai yi ba ya saka kayansa ya koma ya kwanta yana mai gargaɗinta da cewa

"Wallahi kika kuskura kika ƙara tashina sai kin raina kanki" Yana faɗa ya kwanta. Hannu ta kai ta ja babban yatsan ƙafarsa, yadda ya tashi a fusace ya sa ta yi saurin ja da baya ganin ya miƙe tsaye a kan tsakiyar gadon. Tsalle ɗaya ya yi ya dira a gabanta, da baya ta ja don ta fara tunanin kar ya wanka mata mari, da hanzari ta ƙara matsawa har sai da ta jingina da bango sai da ya je dab da ita ya tura ƙirjinsa ya tokare ta idanunta ta ɗaga ta sauke a fuskarsa kasancewar ya fita tsawo. Baki ya buɗe ya fara magana cikin gargaɗi ya ce

"Saddiqa kar ki fara bari in ke sauke fushina a kanki, ina so ki sani ni rashin mutunci gaba na bashi ba baya ba in har kika ce ni za ki shigewa hanci da ƙudundune to za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke ne,na lur har yau baki san wa kika aura ba to ina so ki sani a cikin halaye na ko kashi ɗaya baki sani ba a cikin ɗari gwara ki lallaɓa amma in har kina so mu shiga zaman doya da manja ga fili ga mai doki" Tun da ya fara maganar gabanta yake faɗuwa da sauri da sauri don ita tsoronta ɗaya kar ya kai mata hannu, kawai kallon fuskarsa take mai ɗauke da farin abin yawun bacci da ya bushe sawun yawun baccin har haɓarsa, ga bakinsa da ya buɗe yana mata magana sai ta ji ta ƙosa ya bar kusa da ita. Cikin dauriya ta buɗe nata bakin ta ce

"Ka yi haƙuri" Ta faɗi hakan ne don ya janye jikinsa daga gare ta, don bata ƙaunar warin da take shaƙa daga gare sa" Hannu ya ɗaga ya kaɗa mata yatsunsa a saitin fuskarta ya ce

"Wannan ne karo na ƙarshe" Kai kawai ta iya gyaɗawa. Ƙwafa ya yi haɗe da jan wani gajeran tsaki ya juya ya shiga bayi ya banko ƙofar da ƙarfi. Wata ajiyar zuciya ta sauke, kasancewarta mutum marar son tashin hankali ita in ba bango aka kaita ba bata son yin faɗa ma sai dai in raina mata wayo aka yi.

Tana jin ƙaran ruwa a bayin ta juya ta hau sallaya ta shiga gabatar da sallarta, a raka'arta ta biyun tana sujjadar ƙarshe ya buɗe banɗakin ya fito dama wankan tsarkin ya yi ta ɗauro alwala, bayan ta gama addu'a za ta fara karatu ya ce

"Fita falo ki yi, zan yi sallah a sallayar" Bata ce komai ba siyam-siyam ta busawa rigarta iska. Yana saka jallabiyarsa ya kabbara sallah yana idarwa ya koma ya kwanta don daga sallama ko azkar bai yi ba ya tashi.

Tana karatun amma duk ta damu da halayen da Aminu yake yi, saboda karatun da ta yi ne ma zuciyarta ta yi sanyi da ta gama ta je ta ajiye ta dawo falon ta kwanta a kan kujera tunani barkatai yana adabar zuciyarta.

Ko da gari ya waye haka ta tashi suƙuƙu, ɗanwake ta kwaɓa ta yi don shi ta ji tana son ci haka ta musu ta soya manja ta ci da shi, shi kuma sai ta soya masa farin mai. Bayan fitarsa ta gyara ko ina ta shiga yin goge -goge sai da ta gama tas sannan ta shiga ta wanke bayin za ta yi wanka, amma yadda ƙasanta yake raɗaɗin karcenta ɗin da ya yi da farce jiya sai ta ji tana buƙatar shiga ruwan zafi ta gasa jikinta, ruwan ɗumin ta shiga sai kuma ta yi wankan saboda shi gogan kaya kawai ya saka saboda wannan wankan da ya yi ta wadatar a wajensa, ko ta kan brush ɗinsa bata bi ba domin ta san idan ta duba ma ranta ne zai yi ƙuna saboda ta san da wuya in ya wanke bakin.

Don ta ga ya sauya mata fuska ma duk da ta san hakan ba ya rasa nasaba da abin da ya faru a tsakaninsu.

Wajen shida na yamma tana zaune falo wayarta ta yi ƙara tana ɗakkowa ta ga Khady ce, cewa ta yi

"Assalama alaikum ƙawata ta kaina" Daga ɗaya ɓangaren Khady ta ce

"Ni na yi fushi, da alama angon nan ya sauya mini ke kin san na ce yau zan taho amma maimakon ki kira ki ji ko na taho shi ne baki kira ba" Ta faÉ—a cikin sigar zolaya, dariya ta yi don ta san da alama rigima take nema sai ta ce

"Yi haƙuri ta hannun damana ni na isa, kawai dai abubuwa ne suka sha kaina" Baki ta taɓe kamar Saddiqae tana ganinta ta ce

"To shikenan gani a gida na dawo"

Cike da murna Saddiqa ta ce

"Don Allah da gaske ko wasa" Dariya mai sauti Khadyn ta yi jin duk Saddiqar ta ruÉ—e da murna ta ce

"Wallahi da gaske nake don É—azun nan na dawo"

"Amma na ji daÉ—i, ji nake kamar na zama tsuntsuwa in zo in ganki My Khady" Dariya ta fashe da ita ta ce.

"Haba amarsu ta ango ai ni zan kawo miki ziyara, in sha Allah gobe a gidanki zan wuni, mu sha hira in zo in ga soyayyar nan taku ke da Babynki Aminu ko na yi kwas nima" Ta faɗa cikin tsokana don ta san irin so da ƙaunar da suka shuka a neman auren.

Dimm gabanta ya buga jin wai za ta zo ta ga soyayyarsu, bata san tun tuni komai yana neman ya zama tarihi ko ma ya zama. Sai ta yi arfin halin cewa

"Sai kin zo kuwa" Haka dai suka yi sallama suna ta tsokanar juna. Tun bayan da suka yi sallama sai ta shiga taraddadin zuwan Khady tana fatan Allah daidaita tsakaninsu kar ta zo ta gansu, ba ma wannan ba tana addu'a da fatan Allah ya sa har ta zo ta tafi kar su haɗu da Aminu, don wannan tsaf sai ya ja mata raini wannan ƙazantar a yadfa take ƴar ƙwalisa a ce wannan ƙazamin ne mijinta daga ya gifta sai warin rana daga ya buɗe baki kamar ana kwasar kwata ai abin kunya ne wallahi.

Ko da suka zo kwanciya ma kadaran kadahan, domin baya ma ya juya mata. So take ta sanar masa za ta yi baƙuwa amma tana tsoro sai dai ta yi ƙarfin cewa

"Aminu gobe fa Khady ta ce wunin gidan nan za ta yi" Ta ƙarasa faɗa cikin sanyin murya. Banza ya mata har ta cire ran zai yi magana sai kuma ya ce

"Allah kawo ta" Haka kawai ya ce bai ƙara magana ba amin kawai ta ce ita ma bata bu ta kansa ba ta kwanta.

Ko da safe da ya tashi jugum ya yi ba dariya ba murmushi ba magana, duk sai ta ji ta rasa ya za ta yi, ko da ta kawo masa abinci ma sai cewa ya yi a ƙoshe yake haka dai da zai fita ta ce masa kayan miya ya ƙare babu a frige buɗar bakinsa sai ya ce

"Ki yi wake da shinkafa da mai da yaji" Shiru ta É—an yi sai ta ce

"Amma ka san na ce maka zan yi baƙuwa ai da an kawo na mata wani abu amma kuma babu abu mai ɗan daɗi sai a ce wake da shinkafa" Kallo baki da hankali ya mata sai ya ce
Chapter 15 · 0% Book details