← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 44

Sashe 28

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan halin ne Bukari da ya ɗora ɗaya hannunsa a kan breziya bai, ɗanɗanon naman ya sa ya ɗago hannun ashe hannun breziyar ya maƙale a jikin links ɗin hannun rigarsa, sai ga breziya tana reto a hannun soja, su duka ukun da kallo suka bi hannun soja, banda Aminu da ya yi saurin sadda kai ƙasa, a zuciyarsa yana cewa

"Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahilmazim"

*ZAN BAKU BOOK 1 A FREE BOOK 2 GA MAI HALI YAKE DA BUƘATA ZAI BIYA 500 ZAKU IYA FARA PAYMENT DAGA YANZU ZUWA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222*

*INA SANAR DA KU WTSAPP SUN KULLE MINI WANNAN NO 09013181851 YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI 09025576222*

*AKWAI MAGUNGUNAN MATA, NA KAMFANIN MEERAH B HERBS,AKWAI NA GYARAN BREST AKWAI NA SANYI AKWAINSET NA AMARYA HAÆŠIN ME JEGO MALLAKOKI, LABULAYE ZANNUWAN GADO LESUNA, ATAMFOFI, LAFFAYA TAKALMA MAYAFAI MASU BEAD WORK DA NA SHAGO KAYAN YARA DA SAURANSU MAI SO YA MINI MAGANA TA 09025576222*
[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BkaHPj3RyI1JJmiwfXfnAA

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su *09025576222*

BOOK 1
PAGE 14

Bakin Bukari kamar ƙofar gari haka ya buɗe tsabar mamaki, tamkar wanda aka ratayawa igiyar kashi hake yake ganin breziyar tana reto a hannunsa, ga wani tsantsani da ya hana rai da zuciyarsa sukuni.

Kabiru shi har wani idanu yake zarewa don son tabbatar da cewa breziyar ce a hannun soja, ganin duk sun raja'a a kallon breziyar hakan ya sa Kabaru fahimtar babu wanda ya lura da nasa gamon da ya yi. Hannunsa ɗayan ya sanya ya fincikon ƙusar daga jikin haƙarƙarin nan da ta yi nutso cikin tsoka, tana cake jiki kamar an buga ta a katako duk da har a wani lanƙwashe take.

Kabiru yana zaro ƙusar ya ɗagata sama, har lokacin Aminu kansa yana sunkuye a ƙasa ya kasa ɗagowa, Lawan salati ya kwasa ganin ƙusar da aka zaro daga jikin nama, shi Buƙari ya rasa bakin magani ji yake tamkar ya shaƙo Aminu ya yi ta duka saboda takaici.

Aminu kuwa jin an ɗauki salati duk sai ya ɗauka har lokacin, suna jimamin breziyar ne hakan ya sanya ya ƙara sunkuyar da kai ƙasa, idanunsa kafe da cinyar zabuwar da take riƙe a hannunsa, ga cinya har cinya saboda girma amma ɗanɗano da rashin dahuwa ya hana ya ci naman cikin kwanciyar hankali, uwa uba ga wannan tashin hankalin abin kunyar da Zulaiha ta jaza masa.
A ƙufule Kabiru ya ce

"Aminu dama kawo mu gidanka ka yi don a kashe mu?" Wanann tambayar ta ba Aminu mamaki don ya zaci a kan breziya ake magana, kunya ta hana shi É—agowa amma dai duk da haka bai zaci har za a É—auki abin da zafi a sako maganar kisan kai.

Bai É—ago ba kuma bai ce komai ba, sai cewa yake a zuciyarsa.

'Allah ka ji tausayina, ka sa breziyar nan ta ɓace, sai in ce dama aljannu ne suka kawo'

Lawan ne ya ce

"Alamomi da dama sun nuna hakan, miya ɗaci firit ga kuma baƙar breziya a ajiye kusa da mu, sannan yanzu ga guba an tsinta a cikin nama" Dummm gaban Aminu ya buga, don dama da aka ce baƙar breziya har sai da ya runtse ido, yanzu kuma jin an ce guba sai gabansa ya tsannata bugu yana tunanin hallaw wace masifa ce Zulaiha ta jaza masa, da za a ce guba a nama, shi da ya san zai haɗu da wannan ƙaddarar a baƙar ranar nan da bai kawo su gidan ba.

"Aminu magana ake maka fa" Kabiru ya ce yana wani huce kamar zai kai masa duka.

A hankali ya ɗago kansa, gumi ya gama jiƙa shi, a kan zarɓeɓiyar ƙusar ya sauke idanunsa, kafin ya mayar da akalar ganin nasa zuwa hannun Bukari da yake rataye da breziyar, basu ankara ba sai suka ga Aminu ya fara gwala idanu yana cewa

"Jama'a duhu nake gani, bana ganin komai fa, jama'a a kawo ɗauki ko dai baƙar iska ake yi yau" Ya faɗa yana baza hannuwa kamar mai zancen kurame, sannan sai gwale idanu yake yana runtsewa ya buɗu.

Su duka da kallon rashin fahimta suka bi shi, shi kuma ya yi wannan dibarar ne saboda ya tsira daga jin kunya. Tun da dai ya san in ya ce ba ya gani dole su masa uzuri ko ma hankalinsu ya tashi, dole su manta da batun ƙusa da breziya tun da ya ga alamar babu sauƙi wai ciwon arne.

"Lawan ne ya karkata kai ya ƙare masa kallo, cikin hargagi ya ce

"Wallahi ƙarya kake mu za ka rainawa hankali, a'a ka manta ba baƙar iska ba ce ta taso, guguwa ce mai haɗe da ƙasa" Ɗif Aminu ya yi a ransa yana tunanin kar dai sun hango lagwansa.

Hannayen ya fara miƙawa saitin Bukari wansa yake a ƙufule, ya cika fam kamar zai fashe, yana miƙa hannun yana gwale idanun, yatsunsa ne masu zato-zaton farce da hannun yake riƙe da cinyar kaza ya kusa nutsawa Bukari a ido.

Lawan ne ya ce

"Kabiru nutsa masa ƙusar nan a idon da yake gwalewa, wataƙila idanun su washe ya daina ganin duhu" Da sauri Aminu ya ja baya, da jan mazaunai ya koma daga can gefe yana cewa

"Haba ku tausaya mini ga cutar makanta ga ta ƙusa ai sai ku tsiyayar mini da idanun" Bukari cikin kakkausar murya mai cike da takaici idanunsa sun kaɗa sun yi jajur yana jin amai yana yunƙuro masa in ya kalli breziyar hannunsa ya ce

"Aminu wallahi ka buɗe idanunka ka ɗauke mini wannan abar daga hannuna, in ba haka ba to wallahi zan manta matsayina na Bukari abokinka, in koma Bukari soja in lakaɗa maka na jaki, hatta ita matar taka ba zan barta ba" Ƙwuitttt wata ƙaramar tusa marar ƙara ta suɓucewa Aminu, don shi fa a duniya yana tsoron soja, dama abin da ya sa yake sakin jiki da Bukari ma saboda ya san abokinsa ne, kuma dai ba da unifoarm yake ganinsa ba, don ganin idanun Bukari sun yi ja sai ya fara tunanin ko allurarsa ce ta soja ta motsa, jin wannan batu sai ya saki wata ƴar dariya mai ɗan sauti ya ce

"Wallahi idanun nawa ma sun washe, yanzu kam ina gani raÉ—au-É—au, subhanallahi wannan abar fa? "Ya ce yana kallin breziyar. Bai jira cewar kowa ba ya ce

"Wannan da gani aljannu ne suka mana ajiya, wataƙila ma yanzu suna zaune a ɗakin nan, donn wannan breziyar ko kusa ba ta amarya ba ce, kuma ko ƙusar cikin naman bata rasa nasaba da aljannu"

Kallon ka raina mana wayo suke yi masa, kunya yake ji har lokacin, bai taɓa zaton zai kunyata haka ba, tun da suka shigo gidan ake cin karo da abubuwan al'ajabi da bashi kunya ba zai gaji da faɗin Zulaiha ta tozarta shi yau ba. Bukari yana jefa masa wani kallo ya ce

"Ka É—auke mini ita daga jikina, don wannan kayan nawa ma na gama saka su har abada" Ya faÉ—a yana wani irin yatsina fuska.

Ana cikin wannan yanayin ne, amarya Zulaiha ta shigo, har lokacin zanin leshinta yana yafe a jikinta sai dai wannan lokacin iya wuyanta ta yafe bata rufa har kai ba. Wata ƙaramar roba ce a hannunta mai ɗauke da yajin daddawa, dama tun daga gida aka niƙo mata shi, to sai ta manta bata kawo ba hakan ya sa ta shigo da sallama tana mai cewa

"Ga yajin daddawa, duk da na san ai yanzu tuwon ma kun ci ƙarfinsa, an ji miyar amarya zaƙwaiƙwai" Ta faɗa ba tare da ta lura da yanayin da suke ciki ba, da yake tana ɗan sunkuyar da kai ne, ta sunkuya ta ɗago kenan ta yi arba da naman kowa a hannu, sannan ga tuwo nan duk ba a ci ba, cike da ɗan mamaki ta buɗe baki ta ce

"Haba abokan ango abin har da zari kuma, wato bakwa bari ku gama cin tuwon ba ku ci naman, shi ne ake hannu baka hannu ƙwarya" Ta faɗa cikin sigar wasa irin na matar abokinsu. Bukari cije leɓe ya yi yana jin wani haushinta, a ɓangaren Aminu ma hakan ce ta kasance amma babu wanda ya bi ta kan Zulaiha, Aminu ne ya miƙa hannu ya ciro breziyar hannun Bukari wacce warin gumi da na dauɗa yake tashi daga jikinta.

Karaf idanun Zulaiha suka sauka a kan breziyar, cike da ɗan jin kunya tana ƴar dariya ta miƙawa Aminu hannu tana cewa

"Lah faɗowa ta yi, wallahi da na cire tare da kayan nan na ɗora ta a kan gado" Aminu da ya yi fosta jin ta ƙara tona masa asiri, shi da yake wayincewa yana cewa ta aljannu ce, amma ta gama faɗar komai. Har ta karɓi breziyar Aminu bai samu bakin magana ba, tana karɓa ta ɗauki rigar leshin da ta cire ta saka breziyar a ciki ta tuƙunƙune, ta ajiye tana cewa

"Ga yajin naku nan, ni bari na fita, sai ku ce gaba da gashi" Har ta juya Kabiru ya ce

"Amarya ni sai na samu ƙusa a cikin nawa kashin nama" Juyowa ta yi tana dariya irin ko a jikin nan nata ta ce

"Ayyo, wallahi kasan zabuwa da wahalar dahuwa, shi ne aka ce ana saka ƙarfe ko cokali, to shi ne na saka tsohuwar ƙusar nan don ta yi saurin dahuwa" Idanu Lawan ya ƙanƙance jin amsar da ta ba Kabaru, Kabiru kuwa zuciyarsa ce ta tashi saboda har ya fara hango inda aka samo ƙusar zai iya kasancewa waje ne marar tsafta.

Ganin hankalinta kwance za ta fita, Lawan ya ce

"Naman ma zaƙi cai" Shiru ta ɗan yi tana nazari, jin an ce zaƙi, sai sannan ta tuna waje ɗaya ta ajiye robar suga da ta gishiri kuma robobin iri ɗaya ne, sannan gishirin ma ba mai laushi sosai ba ne.

A zuciyarta ta ce

'Cakwakiya lallai kuna cin daÉ—i' A fili kuma sai ta yi dubarar faÉ—in
Chapter 28 · 0% Book details