← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 44

Sashe 21

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saddiqa bata yi wata gayyata ba, daga Khady ƙawarta sai Noor ƙanwarta sai kuma Fatima ƙanwar Aminu, sai Amina da kuma Sumayya. Leshi ta ɗauka na lefenta aka mata doguwar riga buba, wacce ta karɓe ta don gabaɗaya sai ya ƙara mata kyau, kasancewar cikin girmab jiki ya ƙara mata, ta ƙarw cikowa ta yi kyau, ga ƙirjin nan nata da duk ya cika bra, kamar ita ce amarya in ba wanda ya lura ba babu mai cewa tana da cikin wata shida.

Bayan an kawo amarya, kowa ya watse bayan wata Auntyn Saddiqa da suka zo, su ne suka mata nasiha haÉ—e da bata baki. Bayan kowa ya tafi tana zaune a kan kujera, tana jin shigowar Aminu da abokansa amma babu wanda ya shigo É—akinta a cikinsu, tana jin suka wuce É—akin amarya, duk da faÉ—an da su Yaya Sule da Yaya Shafi'u suka masa amma bata ga alamar zai saduda ko ya sakko ba, don yanzu a yadda ta lura da ita da rashinta uwar ubansu É—aya a wajensa.

Ɓangaren amarya da ango kuwa, tun da abokansa suka tafi, ya shiga rawar ƙafa a wajen amarya, haka suka sha amarcida amarya duk da cewar wannan ne karo na farko da namiji ya kusance ta, amma dai sai ta ga kamar akwai gyara a lamarin angon nata.

A nashi ɓangaren sai ya ji ƴar aljanna, bata kai Saddiqa a komai ba na ɓangaren ƴa mace. Abin da ya bashi mamaki bai wuce yadda ya yi buzigir babu wankan tsarki ba ita ma haka ta kwanta ko a jikinta, haka ma da asuba babu wanda ya tashi yin sallah, da gari ya waye tangararai ya yunƙura ya tashi da yake ta saka pant da suka gama sunna, idanunsa ƙirrrr a jikin pant ɗin tun da bacci take, yadda ya ga datti a jikin pant ɗin ne ya bashi mamaki ganin pant ɗin ba sabo bane kuma akwai dauɗa a jiki.

Tambayar da ya yi wa kansa ta farko ita ce, ina panties É—in da ya saka a kayan lefe har dozin biyu? Kanta ya kalla wanda babu kitso da alama shamfo aka yi don ya ga ribom É—in kanta shi da ban gashin da ban saboda kan nata da alama dakyar ya yi parkin. Da wannan É—an al'ajabin ya sauka daga gadon ya nufi bayi karon farko da ya ji Saddiqa ta faÉ—o masa, wacce bata kwanciya sai ta tsarkake jikinta sannan har shi take yi wa faÉ—an kawar da najasa, amma yau ga shi ita wannan sai bacci take hankali kwance.

Wankan tsarki ya yi ya fito bayan ya yi alwala, da yake ma ko sabulun wanka bai gani a bayin ba, yana fitowa ya ɗan taɓa Zulaiha ganin har takwas ta gota. Idanu ta ɗan buɗe tana yatsina haɗe da doka tsaki ta ce

"Haba Aminu ya za ka tashe ni, ka san ni ko a gida in ana son ganin ɓacin raina to a tashe ni daga bacci" Kasake ya yi yana kallonta, ya fara tunanin to wa ta yi wa tsakin? Sannan ina ɗan aljannan da take kiransa. Dannewa ya yi ya ce

"Ki tashi ki yi wanka da sallah mana" Ko gizau bata yi ba sai kuma dai ta ce

"Goma ta yi?" Da mamaki ya kalle ta ya ce

"Goma kuma?" Kallonsa ta yi tana daga kwancen ta ce

"To a gidanmu sai tara nake sallah, yanzu kuma nan gidan mijina ne ka ga sai goma ta yi na yi" Bakinsa ne ya ƙi rufuwa a zuciyarsa ya ce

'Yasin wannan ta fi ni jahilci da wasa da sallah, duk tsiya bana kaiwa goma ban yi sallaha ba, yanzu wannan ya kwaso a matsayin mata turƙashi'

Dakyar ya lallashe ta, ta shiga bayi ko minti uku bata rufa ba sai gata ta fito, kallonta ya yi tana ɗaure da tawul, fatarta sai sheƙin rashin fitar wanka take ya saba da ganin fatar Saddiqa ko tsayawa ruwa ba ya yi saboda fita a wanka ya ce

"Babu sabulu a banaɗakin ko?" Ya faɗa yana fargabar amsar da za ta bashi, don ba ya so ya gano wani abu na cewa ƙazama ce don ya ga alamomi sun fara bayyana. Fuska ta ɗan yatsina ta ce

"Sabulu kuma, kar ka damu kanka ni ba baƙuwar zafi ba ce, don a gidanmu kowa da sabulunsa, na kowa sai ya ƙare nawa yana nan" Wani yawu ya haɗiye ya ce

"Mai ya sa?"

"Wallahi sai in yi sati ban yi wanka da sabulu ba, ni a na yi amfanu da sabulu watarana na goga sau ɗaya a hannuna na wanke fuska, uban jiki kuwa idan na kwara baƙin ruwa ya wadatar, ai ni dama ina cewa mijina ya huta da siyan sabulu" Shi kaɗai ya san yanayin da ya shiga da ta furta kalmar baƙin ruwa ya wadatar, ashe dai ko kai ƙazami ne baka son ƙazamar mace? Wannan yake ta saƙawa a ransa sai dai ya dake ya ce

"Wai ni kuwa ina panties da aka saka a lefe, na ga na jikinki kamar ba wanda aka saka ba ne? " Tana saka riga ta ce

"Na rabar da dozin ɗaya, dozin ɗayar yana nan cikin akwatin, tun da ina da wanda nake amfani da su a gida ai ba sai na ɓata wani ba, shi wando da a ciki yake a rufe ba gani za a yi ba" Tana faɗar haka ta hau sallaya hankali kwance ta kabbara sallah, ba tare da ta sake cewa komai ba, shi kuma ta ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa saboda ya ga yanzu ma wandon jiyan ne ta mayar ta saka riga bata sauya wani ba.

Tun da ya ja tasa sallayar ya kabbara sallah, har ya idar bashi da nutsuwa sosai yana ta tunanin dama Zulaiha kura ce da fatar akuya ko yaya?.

Ko da ta idar kwanciya ta yi tana danna waya, shi kuma ya shiga tunanin ranar farkon aurensu da Saddiqa gyaran ɗaki ta shiga yi washe gari har yana hanata. Wai ita amarya ba za ta shiga kicin ba, haka ta saka shi zuwa ya dafa shayi ya ɗumama kazar ya kawo musu, ta hanƙare ciki tana ci tana korawa da shayi.

Inda suka gama break fast ɗin, a nan ta bar kayan, shi ma bai ɗauke ba yana son ganin gudun ruwanta. Wajen sha ɗaya ta ce ya siyo mata kati, haka ya fita ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Saddiqa yana ta waiwaye, don da ya zo giftawa ma sai da ya shaƙo ƙamshin turaren wuta. Zulaiha kuwa yana fita garin tashi za ta shiga banɗaki, ta tuntsurar da kofin da ta sha shayin ya zube, ko ta kanta bata bi ba ta shiga
bayin.

Aminu da ya dawo daga siyen kati, yana shigowa bai lura da shayin ba ya ɗora ƙafarsa, ji kake suuuuu santsin sabon tiles da na shayi ya kwashe shi, sai da ya yi gaba-gaba ya yi baya, yana ta baza hannu inda zai dafa wani abu amma sai da ya je ƙasa, zaman ƴan bori ya yi yana jan salati.

Zulaiha jin faɗuwar abu ta fito daga bayin, ganin Aminu yashe yana riƙe da ƙudu sai kuwa ta fashe da dariya ta ce

"Ango garin yaya?" Wani haushinta da takaicin ƙazantar ta ya tsaya masa a maƙoshi, yana ganin ban da ƙazanta da ta goge ai da bai faɗi ba, tsabar takaici bai san ya yi suɓutar baki ba ya ce

"Saddiqa!!!"

*INA SANAR DA KU WTSAPP SUN RUFE MINI LAYINA 09013181851 YANZU DUK MAI NEMANA ZAI MINI MAGANA TA 09025576222*
[5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09025576222*

BOOK 1
PAGE 12

*AMINA*

Tun daga ranar da ta faɗawa Saddiqa cewar ta kai ƙaran Aminu, wurin su Yaya Sule a kan ƙazanta, shikenan ta ƙara ɗaura ɗamara a ranta cewa dama a ce ƙazami ta aura da babu ruwanta da fargabat ƴanmata. Amma yanzu gashi nan wannan mijin nata mai shegen muguwar tsafta da gayu ta san dole yake birge ƴan mata suna son shi, duk yana cika bakin cewa shi babu shi babu wata ƴa mace amma dai bata yarda da hakan ba don ta san namiji baka raba shi da ƴan mata.

Bayan an yi hakan da kwana biyu, da daddare suna zaune kowa ya duƙufa yana danna waya, wayar Yaya Sule ce ta yi ƙara, idanu ya shiga ciccicirawa gabansa yana faɗuwa, ta wutsiyar idanu ya kalli Amina da take latsa waya ya ga hankalinta bai kai kan wayar da ake masa ba. Da sauri ya kai hannu ya katse kiran, yana shirin mayar da wayar silent wani kiran ya shigo a karo na biyu, a wannan lokacin ne hankalinta ya kai kan wayar da ake masa, barin abin da take ta yi ta maida kallonsa gare shi ta ce

"Baka ji ana ta maka waya ba?" Alamomin rashin gaskiya ne suka bayyana a fuskarsa, duk da ya yi ƙoƙarin danne hakan amma sai da ta fahimta, ganin za ta harbo jirginsa ya yi saurin faɗin

"Wani abokina ne ya dame ni da kira, wai rancen kuÉ—i yake so ni kuma bana so in bashi saboda taurin bashi gare shi" Ya faÉ—a yana fatan ta yarda da maganarsa saboda ba zai iya da wannan É—an banzan kishin nata ba, domin kuwa ya san muddin ta gane budurwa ce ya yi sai ya fi naman cikin oven gasuwa.

Kallon rashin yarda ta bishi da shi, don lokacin kiran ya cigaba da shigowa a karo na uku, wayar kuma tana hannunsa abin da ya ƙara bayyana mata cewar ba gaskiya yake faɗa ba yadda hannunsa yake karkarwa. Wayarta ta ajiye a kan kujerar da take zaune, ta ce

"Yanzu abokin naka ne zai rinƙa kiranka sai ka ce wanda ya baka ajiya? Rance ka ce yake nema fa, to a kan mai zai ke maka kira a jere- a jere kamar dai ya baka ajiya ko kuma shi ne yake binka bashin?" Ta faɗa don har ranta ya fara ƙuna don ta san ƙarya yake, addu'a ya fara a zuciyarsa yana cewa
Chapter 21 · 0% Book details