← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 44

Sashe 3

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu haka za ka zauna kalli jikin ka fa, jiya ma fa da na haÉ—a maka ruwan cewa ka yi la'asar ta yi ba za ka yi ba, kuma fa akwai ruwan É—umi ba na sanyo ba ne"

"Haɗa" Ya ce a taƙaice. Juyawa ta yi ta shiga ta zuba ruwan ta fito ta ɗakko na zafi ta haɗa masa, brush ɗin sa da ta goga masa makilin da safe ta gani bai yi ba ta wanke brush ɗin ta sake tatsa masa makilin ɗin ta fito.

"Na haɗa maka" Da to ya amsa da kamar ba zai tashi ba sai kuma ya tashi ya tuɓe kayan jikin sa daga shi sai gajeran wando ya shiga bayin ya rufo. Ya ɗan jima da shiga amma bata ji alamar kwara ruwa ba jim kaɗan ta fara jin alamar taɓa ruwa, can sai ga shi ya fito amma abin mamaki fuska, hannaye sai ƙafafun sa ne kaɗai suka san ya taɓa ruwa da alama wankin jiki ya yi ba wanka ba. Wani takaici ta ji a ranta ta rasa mai ya sa Aminu ba ya son yin wanka ta lura ko kaɗan ya ƙi jinin zuba ruwa a jikin sa.

Ita kuma tana É—an jin kunyar sa shi ya sa ba ta iya faÉ—a masa hakan yana damun ta. Shi kuwa yana fitowa ya wani haÉ—e rai yadda ba za ta ga fuska ba bare ta ce wani abu mai ya É—auka ya shafa abin sa ya É—auki singlet É—in da ya cire ya mayar ya É—akko wata jallabiya ya saka.

"Mu je ki zuba mini abincin" Ya ce bai jira cewar ta ba ya fita falon, shiru ta yi tana zaune a wajen, ita da a gida idan Noor bata yi wanka ba in za ta kwanta ta ringa mata bala'i a kan ba za ta kwana shimfiÉ—a É—aya da ita ba sai ga shi jiya ta kwana da wanda bai yi wanka ko sau É—aya da sabulu ba a rana, yau ma kuma da alama tarihin jiyan zai maimaita kansa.

Kamar wacce aka tsikara haka ta tashi bayin ta nufa ta leƙa brush ɗin sa yana nan kamar yadda ta ajiye wai don ma kar ya ce bai gani ba a kan buta ta ɗora masa kusa da kwandon wankan amma bai yi ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin babu daɗi.

"Saddiqa" Ta jiyo muryar sa yana kiran ta. Amsawa ta yi ta nufo falon tana ƙirƙirar murmushin yaƙe.

"Amarya, amarya" Ya ce yana kallon ta. Bata ce komai ba ta zuba abincin ta tura masa, ya fara ci ruwa ta É—akko ta zuba masa ta koma gefe tana É—an tunani, ita yanzu damuwar ta bai wuce rashin wankan sa ba.

A daddafe ya gama ana magriba har ya miƙe a falon sai da ta masa maganar sallah sannan ya tashi yana ɗan jin kunya ya shiga bayi zai yi alwalar ita kuma ta fito da kayan zuwa cikin. Shafi'u ta gani ya fito daga part ɗin su ya zo da fita da alama masallaci zai je don a kallo ɗaya da ta masa ta ga alamar ruwa hakan yana nuni da alwala ya yi. Farin yadin da yake jikin sa wanda a kallo ɗaya ta gama tantance wanke yake tas ga karin guga, wani ƙamshin turare da ya buɗaɗe hancin ta mai sanyin ƙamshi ya sa ta ji a ranta ina ma Aminu mijin ta ne yake gyara kansa haka.

Tun zuwan ta gidan bata taɓa jin wani nau'i na ƙamshi daga jikin sa ba, ko da a ce ta ɗakko turaren ta ta ce ya shafa ko kuma ta yi ƙoƙarin shafa masa in zai fita wajen sana'a sai ya ce shi ba ya son asarar abu, wanda zai je ya sha rana wajen sana'a ina shi ina wani turare, haka idan za su kwanta tana ƙoƙarin ya shafa sai ya ƙi ko ya ce wai turaren juya masa kai yake ko kuma ya kawo mata wata hujja marar madogara.

"Yaya Shafi'u ina wuni" Ta gaishe da shi. Shafi'u kuwa tun da ya fito ya hango fitowar ta ya ƙura mata idanu haka kawai ya ji ta birge shi ganin ta cikin tsafta da kwalliya. Amsawa ya yi ta yi gaba tana jin yadda idanun sa yake yawo a jikin ta.

Ko da ta dawo shi ma ya fito É—aure da alwala. Kayan da ya dawo da su daga kasuwar su ya mayar sai dai yanzu ta ga babu farin fulawar a jiki sosai da alama ya karkaÉ—e ne.

Murmushi ya sakar mata, bata ankara ba sai ji ta yi ya zo ya kawo mata wata wawar sumbata a kunci kusa da bakin ta, idanu ta ɗan runtse jin wani gumus ɗin bakin sa da ta shaƙa. Bakin sa ya janye yana ƴar dariya ya ce

"Kin ƙi sakin jiki da ni sai kike jin kunya, ina mijin ki mene ne na runtse idanu. Murmushin yaƙe ta ƙaƙaro ya juya da sauri jin an fara sallar, ɗaki ta shiga ta yi alwalar ta gabatar da tata sallar.

Haka da dare ma ya zo mata tashin wani hamamin gumi don ban da warin rana babu abin da yake tashi daga jikin sa, haka ya zo neman haƙƙin sa ita kuma tana ƙamshi ta tsaftace jikin ta da bakin ta, rungumar da ya mata kanta a wajen hamatar sa sai da ta ji har wani juyawa kanta yake saboda wari, da ya haɗe bakin su kuwa gabaɗaya numfashi ma sai da ya gagare ta tamkar an saka hancin ta a wurin kashi haka ta ji tabbas warin baki babu daɗi ga shi Aminu yana da rami a haƙorin sa irin abin nan da ake kira da kogon haƙori wanda wasu suke cewa tsutsar haƙori ce take cinye wajen.

Abincin yana shiga wurin idan har mutum ba ya wanke baki tare da fitar da abincin da ya maƙale to kuwa warin da bakin sa zai yi sai dai Allah

KAYAYYAKIN MU NA KAMFANIN MEERAH B HERBS 👇

*Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* .

*Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.*

MAMAN AFRAH
09013181851
[4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf

*KAZAMIN MIJI*

NA

MAMAN AFRAH

First Class Writer's Asso.📝

Daga marubuciyar:
Bonono rufin ƙofa...
Ruɓaɓɓiyar igiya
Ƴan adaidaita sahu
Ungozoma
Ƴar zaman wanka
Ƙara'in inna delu
Beelal
Jalli joga
Da sauran su.
*09013181851*

PAGE 3

*SUMAYYA*

Zaune take a falo ta yi zaman dirshan sanye take da zanin falle ɗaure a jikin ta sai wata riga t-shirt , Ruma tana waje zaune a foo tana kashi, shigowar Ya Shafi'u falon sai da ransa ya yi mugun ɓaci ganin falon duk datti ga wata takarda da leda nan duk ya yaga ƙanana da alama Ruma ce ta yayyaga, gefe ɗaya ga farantin abincin da Rumar ta ci, ita ma kuma Sumayyar da nata kwanon a gabanta da alama abincin ta gama ci ko hannu bata tashi ta wanke ba.

"Ummi na gama" Ruma ta ce tana daga wajen. Wata uwar gyatsa ta saki ta ce

"Ki zauna zan zo in wanke miki"

"Wai mai ya sa Sumayya kullum lamuran ki gaba suke ba baya ba? Kin ga yadda ƙuda yake bin yarinyar nan kuwa, maimakon ki je ki raba ta da kashin shi ne...

"Dakata malam wai kai kullum a ganin laifina kake, komai na yi ban iya ba, shi wankin kashin ibada ne da za a ce lallai daga faɗa na tashi na wanke mata " Ta katse shi a zafafe, kallon ta yake da takaici falon duk ya haɗe da warin gumin ƙazanta in ba mantawa ya yi ba rabon da ta yi wankan yau kusan kwana uku kenan haka ma bata wa Ruma ba.

"Ya kamata ki wa kan ki faɗa duk abin da kike yi idan yaran ki suka taso su ma shi za su yi, yanzu ki dubi ƴaƴan Amina gwanin sha'awa tas da su kullum amma ke ƴarki sai ta kwana uku jikin ta bai ga ruwa ba daga ta zo kusa da mutuk sai zarnin fitsari, idanun ta kwantsa bakya wanke mata baki haba wannan wace irin ƙazanta ce Sumayya?" ,Wani uban tsaki ta ja, ta tashi tare da saka ƙafa ta ture kwanon gabanta da ta ci abinci bata bi ta kansa ba ta shige ɗaki ko hannu bata wanke ba ta je ta hau gado ta kwanta take danna waya.

Rumar ya ɗakko ya je ya wanke mata kashin ya yi floshin, hatta banɗakin sai tashin zarni yake duk bango da ƙasan tiles ɗin sun dafe.

"ÆŠakko wandon ki a falo in saka miki" Ta ce wa Ruma hankalin ta a kan waya. Wandon ta É—akko ta kawo mata, ta saka mata, shi kan sa zarnin yake duk ga wamdunan yarinyar nan babu wanki ga kayan wanki kamar su yi magana, ta gwammace ta zazzaga musu mai datti su saka idan ta ga banu hali sai ta tsakuri kaÉ—an ta wanke.

Falon ya dawo ya haɗa plate ɗin Rumar da kwanon Sumayyar ya fita ya je kicin kayan wanke-wanke tari guda ƙuda yana bi abin tsantsani tsayawa ya yi ya kama tsantsa.
Chapter 3 · 0% Book details