Sashe 24
Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau kuma da ya ji gobe zai yi baƙi sai yake da na sani, tun da, da a ce bai cewa Saddiqa Zulaiha sati biyu za ta yi ba, da tau tun da Zulaiha ta cika sati ɗaya da Saddiqa ce za ta karɓi girki, kuma baƙinsa za su zo a girkin Saddiqa ne ya fita kunya, sai dai su je su gaisa da Zulaiha.
Amma ganin abin yana damunsa, kuma ba ya so ya kunyata a gaban abokai a je ana masa dariya ana gulmarsa, tun da shi ma ana haɗuw da shi a yi ta wasu, amma shi da yake Saddiqa ta fitar da shi kunya shi ya sa wancan karon bai kunyata ba, don haka yanzu ma ya ce a ransa zai je ya lallaɓa Saddiqa ta shiryawa baƙi girki su sauka a wurinta yana fatan Allah ɗora shi a kanta.
Zaune take a kan kujera tana duba hadisin bulugul maram, ya shigo da sallama, amsawa ta yi tana shaƙar wani dummm daga jikinsa, sai ta ji duk warin yana neman hargitsa mata ciki amma a haka ta dake tare da danne mamakinta na ganinsa yana washe mata jajayen haƙoransa da basa samun wanki, tana ta tunanin ko ya amarya take yi? Bata san cewa duk kanwar ja bace, da shi da amaryar zani ce ta tarar da mu je mu.
ÆŠan murmushi ta saki ta ce
"Barka da yamma" Ƙurr ya mata da ido sai ya ga kamar an ƙara mata kyau, haƙoranta ya kafe da ido yadda suke tas a wanke gasu nan a jere kamar masara, ƙamshin da yake tashi a jikinta da kuma ɗakin sai ya ji har wata hamma ta fara suɓuce masa, yana kallonta kamar yau ya fara ganinta ko dai hakan bai rasa nasa ba da kwana biyu da bai ganta ba wai shi mai sabuwar amarya ya ce
"Barka dai Hajia Saddiqa mutanen gayu da tsafta" Wata dariya ce mau sauti ta kuɓuce mata jin sunan da ya kira ta da kuma kirarin da ya mata ta ce
"Yau É—in kuma" Ta faÉ—a a ranta tana mamakin ashe dai tsafta tana da rana, tun da shi ya tsani tsaftar da take komai ta yi bata iya ba amma yau ga shi yana yabawa, kawar da tunanin ta yi da sake faÉ—in
"Ko dai ɓatan hanya ka yi, nan fa ba ɗakin amaryarka ba ne" Maganar da ta faɗa ta gane kamar ta ɗan sosa ransa don har a fuskarsa sai da ta fuskanci hakan, amma ta nuna kamar bata gani ba. Shi kuma kawar da maganar tata ya yi ya ce
"Don Allah alfarma na zo nema wajenki" Da mamaki take kallonsa wai ita Saddiqa ce Aminu zai nemi alfarma a wajenta, saurin kawar da tunanin dalilin hakan ta yi ta ce
"Allah sa zan iya" Cikin sanyin murya ya ce
"Dama baƙi ne zan yi, kin gane Bulhari abokina soja?"
Ta ce "Eh na gane shi"
Sai ya ce" Shi ne ya zo gari, to gobe zai zo shi da Kabiru da Lawan shi ne za ki musu abinci" Wata Æ´ar dariyar rainin hankali ta yi ta ce
"Ni É—in? Gaskiya bani da lokaci" cike da mamakin kalamanta ya ce
"Baki da lokaci, ni mijinki kike faÉ—awa haka Saddiqa? Kin manta zamana kike?"
Tsaye ta miƙe daga zaunen da take, kafe ta ya yi da ido ganin body hug ɗin jikinta ta kama ta ga ɗan cikin nan da ba a gani sosai ya zauna ɗas kamar a wajen yake tun asali. Taku ɗaya biyu ta yi ta sauya wajen zama don hamamin hammatarsa ya dame ta, sai da ta koma ɗan nesa da shi ta zauna cikin haɗe fuska ta ce
"Ka manta ba bakina bane? Kai fa ka ce amarya sai ta ci amarcin sati biyu, don haka wallahi ko ruwan zafi babu wanda zan dafawa" Tana kaiwa nan ta hau gado ta naɗe ƙafa ta shiga latsa waya, ɗiff ya yi ya kasa cewa komai don ji yake ya shiga tara ba ma uku ba, din abin ya fi ƙarfin uku sai dai uku sai uku.
Siyam-siyam ya tashi ya fita, da harara ta bi bayansa tana ƙarewa rigar jikinsa kallo, duk saitin hamatar gumi ne daga ganin rigar ma babu wanki.
Yana dawowa ɗakin Zulaiha, ya ganta, zaune tsakiyar gado da ɓawon lemon fata a kan gadon, lemo uku ta yanka da ayaba biyu ta cinye amma ɓawon a kan gado. Wani ɓacin rai ya ji ya linku da wanda Saddiqa ta masa amma ganin so yake ya lallaɓata ta wa baƙi abinci sai ya danne ɓacin ran ya zauna ya ce
"Amaryata, bakya laifi" Kallonsa ta yi tana mai kai hannu tsakiyar kanta da babu kitso ta sosa, garin susar ribom É—in ya faÉ—o ai kuwa ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da susa, tana mai cewa ina jinka
"Baƙi zan yi gobe abokaina" Ta ce
"Sai aka yi yaya" Danne takaicin da ya ji na maganarta ya yi ya ce
"Dama sun ƙosa su zo su ganki" Ta ce
"To baka nuna musu hotona, ai ba sai sun ba kansu wahala ba" Shiru ya yi ya ce
"Don Allah ki taimaka abinci suka ce za su ci a nan fa" Ya faɗa yana son ya ce ta taimaka ta musu mai daɗi don ya san babu abin da ta iya dafawa ko jiya sai da ta yi ɗanwake ya narke a ruwa, haka ya dawo sai wani ɗanmalili wanda ake yi da masa a ci da manja da yaji ta yi suka ci ai kuwa ya ɓarke da gudawa, yana tuna abincin Saddiqa baiwar Allah, da ba ya gode mata.
"Allah kawo su lafiya" Ta faɗa tana saka hannu a bireziya ta ringa susa, kallo ɗaya ya mata ya san ba komai bane yake mata ƙaiƙaiyi sai ƙazantar rashin wanka, yau sati guda da zuwanta gidan amma bata taɓa wanka da sabulu ba, wai wankan baƙin ruwa ya wadatar, sai ta ce fatar da za a mayar da ita cikin ƙasar kabari mene ne na wanke ta da sabulu.
Nan dai ya lallaɓa ta, ta ce za ta musu tuwon shinkafa miyar kuka, sai ya ce zai siyo zabuwa ta musu farfesu. Da wanann suka bar maganar.
Washe gari da safe tun da suka yi wankan tsarki, suka yi sallah, ta koma gado ta kwanta, tsintsiya ya ɗauka ya shiga share ɗakin saboda ya san dai a nan baƙin za su sauka, ita kuma ba gyarawa take ba, tana baccin ya shiga share ɗakin, ya sunkuya yana sharo ƙasan gado sai ya hango wani plate da mamaki ya janyo ya ga abinci aka ci aka suɗe kuma aka tura ƙasan gado saboda tsabar ƙazanta, da ganda ba za a fita da shi waje ba.
Kai ya girgiza yana jin ya gamu da gamonsa, fita ya yi da shi ya dawo ya cigaba da sharo ƙasan gadon, abin mamaki sai ya sharo pad, wacce aka yi amfani da ita, ko a leda ba a saka ba, jinin jiki har ya yi wani baƙi-baƙi kore-kore. Da tsintsiya ya janyo pad ɗin har tsakiyar farin tiles ɗin da ya ci uban datti kasancewarsa fari, tamkar ba sati ɗaya ta yi a ɗakin ba, a ƙufule ya shiga faɗin
"Yar aljanna, ƴar aljanna, Zulaiha ke" Idanu ta runtse da ƙarfi jin kitan har tsakar kanta ta tashi a zuciya tana cewa
"Ni fa a kan wasu banzayen abokanka, ba za ka damu rayuwata ba, wallahi in ka taɓo ni sai na fasa mutu tuwon" Ɗif ya yi jin za ta shuka masa salalan tsiya, idan ta ƙi karɓar abokan nan ai ta jaza masa raini da dariya a cikin abokai.
Kai ya karkata gefe kamar maraya ya sassauta murya ya ce
"Ba wannan maganar ba ce, haba Zulaiha leƙo ƙasa ki ga abin da na gani nake kiranki" Fuska ta yatsina tana cewa
"Ka san bana so ake tashina " Ta faɗa tana leƙowa, ya ɗauka za ta nuna wani yanayi in ta ga pad ɗin amma cikin halin ko in kula ta ce
"Lah wai wannan abar ce dama, ai ranar nan ina kwance na ji ta ishe ni, kuma dai na ji kamar jinin ya bar zuba, shi ne na fisgo shegiya na jefa ƙasan gado, na cigaba da baccina" Tana kaiwa nan ta koma ta kwanta ta cigaba da bacci abin ta.
Sakaka yake kallon pad ɗin yana kallonta ita ma, a ransa yana raya cewa ya gamu da gamonsa, tabbas ya auro wacce ta dame shi ta shanye a ƙazanta.
Pad É—in ya É—auka a makwashin shara, fita ya yi ya jefa a shara, ya dawo ya cigaba da share É—akin, dama rabar da ta yi kwana biyu ne priod É—in ya zo kuma kwana uku ta yi, sai ta yi wanka.
Mopping ya yi ya yi goge -goge, ya kunna turaren tsinke ya saka a kusurwa-kusurwa.
Banɗaki ya shiga, wanka yake so ya yi don ya ga yanzu goma ma ta yi, babu sabulu don tsawon satin nan daga shi gar amarya babu wanda ya yi wanka da sabulu, fitowa ya yi ya zo ya ɗan taɓa ƙafarta yana tsoron ta tashi ta ce an tashe ta, sa'arsa ɗaya bata yi ƙorafi ba ya sasaauta murya ya ce
"Don Allah ina sabulun wankan nan na cikin lefe" Sai da ta tashi ta zauna ta ce
"Sabulun wanka kuma? Dama kana wanka da sabulu ne"
Ya ce
"Kin san baƙin nan za su zo shi ya sa gwara na yi wanka, don Allah ke ma ki taso yau ɗaya dai ki yi wanka da sabulu, kar su zo ni wari ke wari abin zai yi yawa shege da hauka" Ya faɗa yana ɗan lallaɓa ta.