← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 44

Sashe 42

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amin tana riƙe da hannun ƙawarta, kamar an ce ta kalli cikin ɗaya daga cikin jerarrun motocin amarya da angon da suka tsaya a abin da ta gani ne ya hautsina hanjin cikinta, wanda ya so zautar da ita, jikinta ya kama rawa tamkar mazari cikin karkarwa baki ta shiga ƙoƙarin haɗa wasu haruffa....

*AMINU*

Ya yi gyara murya yana ƙara dakewa don kar su gane yana ɗan fargabar gabatar musu da ƙudurinsa, ya fara magana yana cewa

"Dama na tara ku ne domin in sanar da ku cewa, na kama mana wani gidan haya, kafin in samu in yi ginina in koma gidan kaina" Wani shu'umin murmushi ne ya suɓucewa Zulaiha jin za a sauya musu gida tana fatan dai can ba ɗaki ɗai-ɗai bane kamar wannan, don dama tana tunanin yin taron suna a gidan idan ta haihu, to yanzu faɗuwa ta zo daidai da zama. Saddiqa kuma bata ji komai ba a kan maganarsa don ta san ruwa dai ba ya tsami banza. Bai jira ta cewarsu ba ya ɗora da faɗin

"Ɓangare uku ne a gidan, kowacce tana da ciki da falo fa banɗaki, sannan abu na gaba ina sanar da ku cewa zan ƙara aure nan da sati uku... Dididimmm gabansu ya faɗi amma dai Zulaiha ta fi shiga ruɗani don Saddiqa dannewa ta yi tare da majewa duk da abin ya ɗaure mata kai. Zulaiha bata san lokacin da ta ganta a tsaye ba ranta yana mata ƙuna, Saddiqa kuwa wani shu'umin murmushi ta saki irin na an zo wajen, cikin hargagi Zulaiha ta shiga faɗin

"Au me? Aure fa ka ce, mafarki kake ko a falke kake, to idan bacci kake ka falka daga nannauyan baccin da kake don bani da kishiya" Ta faÉ—a tana tada jijiyoyin wuya kamar za ta kai masa masa duka. Kallon baki da hankali ya mata ya ce

"Kar ki nemi ki mini rashin kunya, dama mun yi da ke ba zan auri wata ba bayan ke? To idan mun yi ma na janye bare kuma ni babu wacce na taɓa yi wa alƙawarin ba zan mata kishiya ba, don haka ki shirya kishi da ƙabila ma kuwa" Saddiqa jin ya ce ƙabila sai da ta ƙanƙance ido tana mamakin wani sabon salo, Zulaiha kuwa kuka ta fashe tana mai yin kukan kura ta yi kan Aminu, wanda ganin haka ya miƙe tsaye yana taka mata birki da faɗin

"Kar ki fara haukar kishi fa, don in aika ki gida zuwa wani lokaci ba abin mamaki bane a wajena" Cike da jin haushinsa ta ce

"Wannan ai wulaƙanci ne wato an ci moriyar ganga za a yada korenta, daga yin auren har za a fara taryata da kishiya bayan wacce na tarar a gidan" Ta faɗa tana huci. Kallon sakarya ya mata ya ce

"Ita wacce kika tarar ba mutum bace, ko ita bata yi magana ba sai ke, ko ke kaɗai ce matata, to aure babu fashi ki yi duk abin da za ki yi" Kallonsu Saddiqa ta yi ta taɓe baki ita su duka ma tsantsaninsu take ji, ta rasa ma mai ya sa Zulaihar take wannan tsantsar kishin, iya wani lokacin idan ta tsaya ta ƙarewa Aminu kallo sai ta rasa abin so a jikinsa ko abin kishi, don yanzu ta fi karkatar da lamarin aurenta da shi a matsayin ƙaddara. Sai dai ita Zulaiha kishinsa take haiƙan, ko don ita ɗin ma ƙazamar ce oho, ita yanzu ai sallama musu Aminu za ta yi su jiƙa su sha ita yanzu hankalinta ya fi karkata ga yadda za ta ba ƴarta tarbiya.

Zulaiha ce ta ce

"Ai ita don ba ita za a yi wa kishiya ba, ni za a yi wa ai ita ni ce kishiyar ta wacce za a auro yanzu kuma kishiyata ce" Tsaki ya ja ya ce

"Ke kika sani, in ma mene ne ita ma haka ta jure, ke ma ba zai gagare ki ba ita da har kwana bakwai na ƙara miki daga cikin kwanakin bakinta, ashe babu daɗi... Jin hakan sai Zulaiha ta harzuƙa tana faɗin

"In ka isa ka ƙarawa amaryar da za ka auro kwanakina shegiya uwata ta haifeni, na rantse da Allah uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho... Saddiqa ganin abin nasu yana neman wuce makaɗi da rawa ta kalli Aminun cikin sanyin murya ta ce

"Ni dai ina maka fatan alkairi, Allah sa a yi a sa'a amma don Allah ku ita mini daga ɗaki na gaji da jin wannan hayaniyar" Zulaiha jin wannan furucin ranta ya ƙara ɓaci ta harzuƙa ta ce

"Wato ga dabbobi suna faɗa ko, dama ai gajiya za ki yi da hayaniya tun da daɗi kike ji ba ke za a ƙarowa ba" Ko kallo Zulaiha bata ishi Saddiqa ba, ta koma kujera ta zauna ta harɗe ƙafafu, wannan abin ya yi wa Zulaiha ciwo, don ta so Saddiqa ta biya ta ta sauke fushinta a kanta, amma Aminu daɗi ya ji don haka sai ya fara bubbuɗawa ya fara tafiya da niyyar barin ɗakin, Zulaiha taku ɗaya biyu ta yi ta damƙo wuyan rigarsa ta shaƙe shi, yana ta faman ta saka amma ta ƙi dakawa wai sai ya fasa aure ai kuwa ya ɗaga hannu ya kwashe ta da wani gigitaccen marin da ta sakar masa wuyan da ta shaƙe babu shiri, tana sakinsa ya gyara rigarsa ya fita daga ɗakin, ita kuma ta buɗe baki tana sheƙa kuka, tamkar wacce aka yi wa mutuwa har da su Allah ya isa take ta faman yi.

Saddiqa ganin abin babu tsari, sai ta kama hannunta za ta fitar da ita daga É—akin don hamamin da suka sanyawa É—akin ya haifar mata da ciwon kai, wani irin cisge hannunta Zulaiha ta yi tana aikawa Saddiqa mugun kallo. Dariya ma abin ya ba Saddiqa ta kalle ta ta ce

"Shi fa rashin mutunci da kike gani biki ne, idan aka maka ramawa kake, amma ni bani da lokacin ramawa sai dai in ce ki je ki sha ruwan sanyi, amma ki saka a ranki auren Aminu babu fashi gwara ki kwantar da hankalinki ko don abin cikin ki" Harara ta aika mata ta ce

"An ƙi a kwantar ɗin, kuma da kika ce zai ƙara a bakinki" Tana kaiwa nan fuuuuu ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakinta, nan ta tarar ashe Aminu ficewa ma ya yi daga gidan.

Ta É—aga hankalinta amma bata sauya zani ba, don sai abin da ya cigaba, Sumayya ta ji babu daÉ—i jin za a yi wa Zulaiha kishiya don dama yanzu ita ce abokiyarta dama an ce abokin damo guza.

Amina kuwa daɗi ta ji musamman ma da ya kasance an ce za su tashi daga gidan da zama. Shafi'u ya ji babu daɗi jin Saddiqa za si bar gidan, ɗan kwallin ganinta da yake yana jin shauƙi sai ya ji zai yi kewa, amma ya saka a ransa cewa duk runtsi zai ke zuwa gidan da sunan ziyara.

Ana saura kwana goma bikin suka kwashe kayansu suka koma gidan da ya kama haya, Zulaiha har lokacin bata huce ba tana ta hancini tana kuma mugun jin haushin Aminu. Da yake ɗakinsa da ban yanzu bashi da burin da ya wuce Aisha amarya ta tare domin hankalinsa ya yi kanta yana ganin da wuya a samu wata mace da za ta kaita ko ta fi ta don yana ganin ta mallaki komai, duk da ƙiba da kuma faɗin mazaunanta yana ɗan bashi fargaba sai dai ya sanya a ransa shi ba zai ɓata mata rai bama bare wani faɗa ya haɗa su, don ya lura tana da faɗa, gashi abu kaɗan ta hayayyaƙo shi tun kan a je gidan amma dai ya saka a ransa cewa wuyarta ta shigo gidan ne dole zai gyara mata zama kamar yadda ya ladabtar da sauran.

Yau ya kama asabar aka É—aura auren Aminu da Aisha. Rawar kai wajen Aminu ko kallo su Saddiqa basu ishe shi ba, saboda yana cikin maza masu mayar da macen gida ba kowan kowa ba a lokacin da suka samu wata matar.

A yau ne za ta tare gabaɗaya ɓangaren amarya ya sha jere kasancewar suna neman na kansu daga ita har mahaifiyarta sai aka mata kaya na kece raini tamkar aurenta na fara, kujeru farare, kayan gado farare, labulayen Aisha ma farare ne. Kasancewarta mace mai son farin abu.

Da yake Aminu yana da ɗakinsa amma saboda tsantsani irin na Aisha tun daga gida ta faɗa masa cewa ita fa ba za take kwana a ɗakinsa a kan katifar da yake kwana da matansa ba, saboda tana da ƙyamar ƙazanta hakan ya sa take ganin kawai sharing ɗin katifar ba za ta iya ba, wannan lamari ba ƙaramin daɗaɗawa Aminu rai ya yi ba, don dama wani uban shirgin kayansa ne mararsa wanki da ya tare da tarkacen tsuffin takalmansa wasu ma tun nasa ne na gida, don tun da ya gabya samu turakarsa ya je ɗakinsa na gidansu ya kwaso sauran kayansa, duk ya libge daɗin dabya ji kuwa ba ya so Aisha ta fahimci halayyarsa ta ƙazanta tun da wuri don ya lura irin masu tsaftar nan ne ta innanaha.

Bayan kowa ya watse tana zaune a ɗakinta da ya sha turaren wuta, farar laffaya ce a jikinta mai flower golding, ɗakin fanka tana kaɗa ko ina. Bayan Aminu ya shigo ta ga yana ta ƙoƙarin rufe ƙofa nan take sanar da shi ya bata ga ya haɗasu da sauran matansa ya gabatar da ita ba, Aminu kuwa da ya san Zulaiha tana tamfa sai ya ce wai sai zuwa gobe. Haka dai ta ƙyaleshi

Bayan sun ɗan ci kayan maƙulashe, ta tashi ta buɗe wata jaka ta ɗakko sabon brush tana mai cewa

"Na hutar da kai siyan brush na taho da kayana, saboda ni bana son brush mai laushi na fi son mai tauri" Dariya ya yi abinsa, yana ganinta shiga bayi ta fito sai kawai ta tarar da shi ya yi mata saƙamƙam a kan gado, da mamaki take kallonsa don ita ta saba indai ta ci abu sai ta wanke baki amma shi ta ga ko bakin bai kuskure ba bare ya wanke da brush.
Chapter 42 · 0% Book details