Sashe 18
Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba wani nan dauɗar rashin wanka ce wanann" Tsaki ya daka ya ƙara juyawa taku ɗaya biyu ya yi maganar da ta fara kamar haka ita ta katse masa tafiyar.
"Idan dai har kana ganin akwai macen da za ta juri zama da kai a wannan halin da kake ciki, to ga fili ga mai doki" Ko kallo bata ishe shi ba ya juya da nufin zuwa ya ɗauki gajeran wandonsa, saboda yana so ya saka sai ya kwanta tun da ya ga alamar haƙƙin nasa ba zai samu ba, kayan jikinsa ya cire duka don gajeran wandon zai saka ya kwanta.
Saddiqa da take jiran ganin abin da zai yi idanunta suka sauka a kan gajeran wandon da ya nufa zai ɗauka, cikin zafin nama ta ɗare kan gado ta dira sai gata ta riga shi zuwa wajen suka miƙa hannu kusan a tare za su ɗauka cikin rashin sa'a Aminu ya riga ta ɗauka, baki ta damƙe da haƙori ganin ya yi wa wandon riƙon sakainar kashi ta yi saurin tankwaɓe hannun wandon ya faɗi, duk da bai san dalilinta na son ɗaukan wandon ba amma dai ba ya so ta ɗauka.
Tana ɗauka yana tsaye sai gani ya yi ta ɗan sunkuya ƙasa, bai ankara ba sai ta bi ta tsakanin ƙafafunsa, cikin jin haushi ya ce
"Wai mai za ki yi da wandon nan" Ya ƙarasa faɗa rai a ɓace. Cikin hakin da take na cin nasarar zuwan wandon hannunta ta ce
"Aminu tun da wannan wandon ba shi kaÉ—ai ne gajeran wandonka ba, daga yau ka rasa shi" Jin furucinta sai da gabansa ya faÉ—i, don shi babu wandon da yake so a duniya sama da wannan wandon nasa da ya mallaka tun kafin ya yi aure Cikin tsantsar mamaki ya ce
"Sakawa za kike?" Ya tambaya don shi a ganinsa in ba sakawa za ta yi ba mene ne na cewa ya rasa shi" Ko uffan bata ce ba sai ta juya ai kuwa ya take mata baya yana faÉ—in
"Wallahi kika sake wani abu... Bai ƙarasa ba ganin ta zura da gudu shi ma ya bi bayanta da gudun, har falo suka fito ganin ta nufi hanyar ƙofa sai lokacin ma ya lura tsirara yake, ga shi gida ba su kaɗai ba.
Da gudu ya juya É—aki ya sako rigarsa jallabiya ya fito da sasaarfa, yana fitowa tsakar gidan ya hange ta ta yi hanyar kicin Sumayya da take hangensu daga windown tsabar tsegumi har É—aÉ—É—age take. Kafin ya cim mata har ta shige kicin, Saddiqa kuwa tana shiga kicin ta shiga neman ashana da yake a rikice take sai ta rasa ina take jin takun gudu-gudu sauri-saurinsa ya sa ta shiga waige sai sannan ta hangi ashanar a saman loka.
Da sauri ta ɗauka ta fito daga kicin ɗin, yana shirin shiga ya ga ta fito tamkar an jefo ta, har bangaje shi ta yi, can ta yi wajen haryar bayin tsakar gidan ta jefar da wandon ta ƙyasta ashana t jefa masa a take ya kama da wuta. Aminu da sai lokacin ya fahimci abin da ta yi idanu ya zaro a guje ya ƙarasa ya saka ƙafa ya taka wandon wutar ta mutu da wata uwar harara ya bita ya nufi ɗaki saboda ba ya so ya fara mata a tsakar gidan.
Yana zuwa falo ya ɗaga wandon nan ya ga saitin mazaunai ne daga baya ya ƙone, sai ya fito ƙunar har gaban wandon kamar ya yi kuka ya ji saboda soyayyarsa da wandon nan, ɗaki ya shiga ya saka wandon ya cire jallabiyar ta mudubi ya juya ya hangi yagar mazaunan ya ga ana ganinsa, ya duba gaban ya ga mafitsararsa ta fito daga yagar.
Wani takaici ne ya turnuƙe shi amma bai ji zai iya cire wandon ba, yana nan tsaye sai ga Saddiqa ta shigo da mamaki ta kalli wandon a jikinsa ita kuwabta ƙiyasta ba zai sake saka wandon nan ba. Baki ya buɗe zai mata masifa ai kuwa bai kai ga magana ba ya ji ta saka hannu ƙiiii ta fisgi wandon da yake ba wani ƙwari gare shi ba ya tsufa ga dauɗa ta kashe masa ƙarfi kullum shi yake sakawa kamar rai, cikin yahar ta saka hannu ɓetttt yana ja tana ja saida gabaɗaya ta yaga shi shammatarsa ta yi ta fice da wanda ta riƙe ta bar shi sanye da wajen ƙafar wandon ɗaya wacce ta zamo wajen cinyarsa.
Tana fita ta ƙyasta ashanar sai da ya ƙone ƙurmus, Sumayya da take ganin komai sai dariyar mugunta take dukmda bata gane mene ne aka ƙona ba amma dai ta fahimci rigima suke.
Tun da ta dawo ɗakin yake masifa kamar zai cinye ta ɗanya, bango ta ba ajiyarsa ta hau gadon ta kwanta, shi kuma yana tsaye tsirara wai ba zai saka wani wandon ba sai ta maido masa da wanda ta ƙona, cikin bala'i ya ce
"In na saka wani wandon shege nake wallahi ki tashi tun dare bai miki ba ki dawo mini da wandona" Kallonsa ta yi ta ce
"Sai ka ɗaura zani in ba za ka saka wandon ba" Ta ce tana kallon yadda yake tsaye babu kaya kamar wani ƙaramin yaro. Tun da ta bashi baya bata bi ta kansa ba, yake ta masifa ƙarshe bata san yaya ya ƙare ba don bai kwana a gadon ba a ƙasa ya ajiye katifa ya kwanta.
Tun da ta ƙona gajeran wando kamar ta ƙona ɗan mutum sai ya zamana ya ɗauki wata muguwar gaba da ita, sannan kuma wandunan nasa ba ya amfani da su tun da ya nuna bata isa saka shi abin da bai yi niyya ba. Gidansu ya koma a ɗakinsa wani bakko da ya ajiye wasu kaya ya sake ɗakko wasu wandonan biyu wanda sun fi wanda ta ƙona tsufa, ya kawo su gidan yake sakawa sai idanu ta zuba masa.
*BAYAN SATI BIYU*
Jinya take zazaaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani, ga bata cin abinci sai abubuwan kwaɗayi yawan tashin zuciyar da take shi ya fi damunta dole sai lemon tsami take ajiyewa tana lasa, hakan yake kwantar mata da tashin zuciyar.
Aminu ganin haka sai ya tsiri takura mata sannan magana ɗaya ce a kan cewa ba dai ciki ta yi ba, wannan kalmar tana ƙona mata rai sai ka ce ita ta yi wa kanta cikin da zai ke faɗin ba dai ciki ta yi ba.
Dakyar ya bata kuɗin zuwa asibiti yana cewa ya san ma ba ciki bane, don haihuwa ba yanzu ba shi a shekara biyar ma babu tsarin haihuwa a tsarinsa. Wannan dalilin nasa ya sanyata fargabar sakamakon asibitin tun da ta san dai bata ganin proid ɗinta, sakamakon farko da ya fito ya nuna cikin wata biyu kwance a mararta . Bayan ta dawo gida gabanta yana tsananta bugu ta miƙa masa takardar sai da ya taɓe baki bai karɓi takardar ba ya ce
"Ba panadol bane aka rubuta miki idan na fita zan sayo, ko ba shi kaɗai bane aka rubuta?" Ya faɗa yana maida hankalinsa kan wayar da yake charting da ƴar aljanna. Wani ƙululun baƙinciki ne ya tokare ta ta kalles shi ta ce
"An ce ina ɗauke da cikin wata biyu" A kiɗime ya tashi tsaye har wayar tana faɗuwa ƙasa ya kalle ta da mamaki cikin ɓacin rai ya ce
"Wane irin ciki wai? Ko dai suna nufin kina da fama da ciwon ciki" Wani kallo ta masa na takaici kafin ta ce
"Ba ciwon ciki ba ina da ciki na haihuwa... Tun kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"Wanann wasa ne ma, sannan idan har gaske ne ina so ki sani zan sayo miki magani ki sha cikin ya zube don ni haihuwa bata cikin tsarina a yanzu" Da tsananin tashin hankali shimfiÉ—e a koÉ—aÉ—É—iyar fuskarta irin ta marar lafiya ta ce
"Zubarwa? Cikin sunnar? To ni wallahi ban shirya yi kisan kai ba, kuma wannan cikin sai na haife shi, ka san baka shirya haihuwa ba ka aure ni? Ko ka san baka shirya haihuwa ba ka neme ni ka biya buƙatarka shin baka san cewa cikin zai shiga ba dama? To wallahi ko mai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa zubar da ciki ba ko da na shege ne bare ɗan sunna" Cike da takaicin shigar masa hanci da ƙudundu ne da take ya kalle ta ya ce
"Ki shirya zama cikun uƙuba kuwa a gidan nan" Kallonsa ta yi tana jin haushin kasancewarsa mijinta kuma uban ƴaƴanta ga ƙazanta ga jahilci ga rashin tsoron Allah, duk da bata da ikon tare ƙaddararta amma ta yi da na sanin auren Aminu!.
Tun daga wannan rana kamar yadda ya faÉ—a hakan ce ta faru kwata-kwata bata jin daÉ—in zaman gidan, duk wani abu da take so na kwaÉ—ayi sai dai ta nemawa kanta taimakonta É—aya idan ta je gidansu Abbanta yana bata kuÉ—i tun da ba wata sana'a take yi ba, da wannan kuÉ—in take samu ta sayi abu in tana sha'awa.
Bayan wannan siraɗin sai kuma wasu abubuwa suka fara fitowa lokacin cikinta yana da wata biyar ya fito amma ba sosai ba kasancewar cikin fara bai fiya girma ba. Ƙazanta dai sai abin da ya cigaba saboda shi dai mai hali ba ya canjawa.
Yanzu abin da ya tsiro da shi, ba ya siyan sabulun wanka tun da shi dama ba damuwa ya yi da sabulu ba wankan farin ruwa ma sai lokaci zuwa lokaci, sabulun wanki ba ya siya mata bare a zo ga turaren shafawa ko freshner makilin kuwa ba a ma batunsa duk waÉ—annan kayan ita take saya amma kuma in ta saya shi kuma zai yi amfani da su idan amfanin hakan ya taso.
Ganin hakan sai take ɓoyewa tun da shi ma da haƙƙin hakan yake kansa bai siya ba, babu dalilin da zai sa ta sarawa jaki ciyawa.
Abin da ta lura kawai ya tsane ta ne saboda cikin da take ɗauke da shi wanda ya so a zubat tun yana ƙarami ta ƙi.