Sashe 31
Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunta ne ya fara karkarwa jin zuciyarta tana ɗarsa mata wani zargi, duk da ta ƙaryata zuciyarta amma dai sai ta ji tana son sanin dalilin kiran da MAMUDAN yake yi wa mijin nata.
Tana ɗaga kiran sai wayar ta mutu, da ta duba sai ta ga cajin ne ya ɗauke gabaɗaya. Jin ƙaran sheƙa ruwan Sule a banɗaki da alama ya gama wankan ma, sai ta ajiye wayar, tana shirin barin gaban madubin sai ga shi ya fito daga bayin, abin da ya ɗaure mata kai shi ne yadda ta ga alamomin razana a tare da shi, wannan ya sanya ta ji hankalinta ya tashi, tana tambayar zuciyarta shin idan har babu wani abu da yake ɓoyewa a wayar mai ya sa da ya ganta a kusa da wayar zai razana.
Kafe shi ta yi da idanu tana son gano gaskiyar lamarin, shi ma Sule a nasa ɓangaren tsorata ya yi, don tunaninsa ko ta masa bincike a wayar tasa amma kuma tunowa da ya yi cewa yau da safe ya canja passward na buɗe wayar sai ya ji daɗi a ransa, hakan ya sanya ya yi saurin kawar da tsoro daga fuskarsa, matsowa ya yi yana zuwa sai ya riƙo ta tare sa rungumota jikinsa ya sanya lemar hannunsa ya shafe mata fuska tare da juyo da ita suke fuskantar juna, ita kuma da bata gama dawowa daga nisan kiwon tunanin son sanin alaƙarsa ta yawan kira da MAMUDA yake yi ba, sannan uwa uba dama ita ta tsani soyayya sai kishin tsiya ne kawai da ita amma mijinta ba ya samun kulawarta, ko soyayarta wanda hakan ya sa shi kuma yake cutuwa, har ya sa ya fara tunanin mafita wato ya auro wata macen ko ya samu yadda yake so.
Hannunta ta fincike saga riƙon da ya mata ta ce
"Na sha faÉ—a maka ni ba ma'abociyar soyayya bace, amfanin soyayya aure ne, kuma mun yi aure to mene ne saura?" Da kallo ya bita duk da ya saba jin kalamanta masu tsauri irin wannan, amma bai san mai ya sa yau suka masa zafi fiye da kullum, kafin ya ce wani abu har ta É—ora da faÉ—in
"Shin waye MAMAUDA?" Tambayar ta zo masa a bazata, tunanin ya fara kan cewa ko dai ta samu damar buÉ—e passward É—in wayar ne, har take tuhumarsa kuma ba a kan kowa tuhumar ba sai a kan Salaha(MAMAUDA) Idanunta ya kalla yana son tantance tambayarta domin ya san irin amsar sa ya kamata ya bata, yana cikin wannan halin ta katse shi da faÉ—in
"Magana nake maka fa, waye MAMUDAN nan wai yanzun nan ma na ga yana kiranka" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya san dama sai dai in kiran ta gani amma da bincike ta masa a wayar ta gano abubuwa da dama na soyayyar da suke zubawa da Salaha ai ya san ya kaɗe har ganyensa kuwa, don irin musayar zantukan soyayyar da suke masu tsayawa a zuciya ya san da wataƙila ta suma in da gani. Jarumta ya aro ya ce
"Kai Amina, wallahi ni na É—auka ma wani abu ne ya faru, yanzu a kan MAMUDA ya kira ni kika tsare ni da tambaya haka, kamar dai wata macen... Wani kallo ta aika masa kafin ta katse shi da cewa
"Kar ka ma fara, don ba a haifi macen da za ta kira ka ba, kuma har abada ba za a haifeta ba, kai nawa ne" Murmushi ya yi yana jinjina kishi irin nata ya ce
"Maganarki dutse, ai ni kaina na san babu wacce za ta kira miki ni, kisha kuruminki amanarki ta riƙu, MAMUDA dai ni ban san me ya sa yake damuna ba, shi bashi da aiki sai neman rancen kuɗi... Katse shi ta yi da faɗin
"Amma ranar nan cewa ka yi za ka yi blocking É—insa" Dakyar ya samu dabarar faÉ—in
"To ai bayan na yi blocking É—in da wata lambar ya kirani yana cewa, ya gode da na rufe hanyar da zai sameni, don na ga bashi da kuÉ—i, wannan dalilin ne ya sa na sake saved sabuwar lambarsa" Shiru ta yi tana nazari shi kuka ganin maganar ta yi tasiri ya sake cewa
"Babu daɗi din baka da shi a gujeka" Ajiyar zuciya ta sauke mau ƙarfi ta ce
"Haka ne kuma, amma dai kiran koyaushe bashi da wani amfani, ni sai in ke jin faÉ—uwar gaba" Ya ce
"Ki kwantar da hankalinki ni naki ne har abada, ko ana ruwa ana iska, ana ruwa da ƙanƙara daga ke babu daɗi na kulle ƙofa tuf da mukulli" Wata dariya ta saki mai sauti, don ta ji daɗin yaudararrun kalaman da ya tsarata da su bata san cewa rami ya mata ta faɗa ba don MAMAUDA ba kowa bane sai matar da yake son aura, yana ta tunanin wannan cakwakiya ta yaya zai sanar da amarya cewa akwai uwar gidanta har suna da yara biyu, sannan ita mai gayya mai aikin sarkin ƴan kishi Amina ta wacce hanya zai faɗa mata yana neman aure, ya san duk ranar da ƙwan nan ya fashe tabbas akwai ɗan jijjiɓin rikici, shi ya sa ma ya iya takatsantsan, sannan ya iya takunsa don ko da a ce zai sanar da su, su duka biyun to sai aski ya zo gaban goshi, wanda bahaushe yake cewa aski in ya je gaban goshi ya fi zafi.
Tun da ya fahimci Amina ta gama gane yawan kiran da MAMUDA yake yawan yi masa, gashi shi kuma ba zai iya sanar da Salaha cewa ba koyaushe za take kiransa ba, tun da bata san yana da iyali ba duk da wasu ƴan matan ko sun san namiji yana da mata basa fasa kiran wayarsa koyaushe, domin wata a lokacin da ta san namiji yana da mata a sannan ne za ta buɗe ƙofofin rashin mutunci ba za ta tsiri kiransa ba sai yana gidansa don haɗa fitina da husuma. Idan aka samu uwar gidan mai ƙarfin zafin kishi shikenan sai a rinƙa bala'i da miji wata daga wanann har saki a gifta tsakaninta da mijin, don abu guda da mata basa ganewa shi ne, duk lokacin da namiji yake neman aure idanunsa rufewa suke ba ya ji ba ya gani, ko a mutu ko a yi rai.
Goge sunan MAMUDA ya yi ya maryar da shi MARAINIYA, bayan an yi hakan da sati biyu, wayarsa tana caji ya jona, sai kuwa ta fara ƙara, ya tashi da ɗan hanzari zai ɗakko Amina ta ce
"Bari in yi aikin lada in miƙo maka, ba sai ka tashi ba" Murmushin yaƙe ya saki yana komawa ya zauna gabansa yana faɗuwa, Amina tana ɗaukan waya ta ga sunan MARAINIYA da manyan baƙi yana yawo a kan screen ɗin waya.
A ɓangaren Sule kuwa yana ta addu'ar Allah sa wani ne daban yake kiransa ba Salaha ba, yana wannan halin sai ta ji Amina ta ce
"Sule wace ce kuma MARAINIYA" Gabansa ne ya faɗi, shi a nashi ɓangaren ya saka sunan ne don yana ganin ba lalai hakan ya ɗauki hankalinta ba, amma ganin hannunta har karkarwa yake wayar tana neman suɓucewa cikin dakiya ya ce
"Wai dama MARAINIYA na saka?" Ta ce
"Ban sani ba, kai za a tambaya" Sai ya ce
"Kai amma fa typin error sai ya haɗa maka ɗan jijjiɓin faɗa, MARAYA fa zan rubuta, wani abokinmu ne tun muna primary babansu ya rasu to shi ne fa kullum aka masa abu sai yake cewa, don mun san shi maraya ne, shikenan daga nan sunan maraya ya bi shi" Yana kai wa nan ya kafe ta da ido, idanu ya ga ta runtse, tana jin yadda ƙirjinta yake bugawa, sai kuma ta buɗe a hankali tana shirin miƙa masa wayar wani kiran ya shigo, wayar ta kafe da ido har sai da ta ji ta gamsu da maganarsa, ta miƙa masa tana faɗin
"Wallahi na tsani abin da za a ke saka mini shakku" Karɓa ya yi yana cewa na sha faɗa miki ki kwantar da hankalinki" Komawa ta yi ta zauna tana faɗin
"Ba dole gabana ya faÉ—i ba, na ga an sanya MARAINIYA. Idanunta ya faka ya danne wayar ta mutu gabaÉ—aya, sai ya kara a kunne yana cewa
"Babu MARAYA sai rago" Yana faɗar hakan ya ɗan yi shiru alamar kamar amsa ake bashi daga ɗaya ɓangaren. Sai kuma ya ce
"Allah sarki kowa lpia" Daga haka ya shiga yin Æ´ar hira yana dariya, tamkar da wani yake yi, yana gamawa ya tashi ya mayar da wayar caji.
Daga haka suka ɗan shiga hira da ita, yana ƙara faɗa mata babu ita babu kishiya a gidan duniya, tashi ta yi daga jinginen da take ta ce
"Mene ne nufinka? Kenan a lahira ba da ni kaÉ—ai za ka zauna ba?" Tambayar ta so bashi dariya, amma ganin haka sai ya dake ya ce
"Baki san akwai matan aljanna ba?... Tun kafin ya kai ƙarshen maganar ta ce
"Ni a aljannar ma ni kaÉ—aice " Dariya ya yi ya ce
"To Aminatu sarkin Æ´an kishi, wato har da matan aljanna ma" Ita ma dariyar ta yi ta ce
"Yo su ma ai mata ne" Bai ce komai ba ya É—an yi murmushi a zuciyarsa yana cewa
'Iska tana yawo da mai kayan kara, ni da nake son mace ƴar soyayya wacce za ta shagwaɓani ta tarairaye ni, in ɗanɗani zumar soyayya da ta lobayya, ni ma in nuna mata tawa kulawa da soyayyar, amma ke kin zo kin mini dikim, in an yi batun soyayya ki ce ba haka ba, amma batun kishi ke ce a gaba, baki san ya za ki ɗauke hankalin mijinki ya dawo kanki ba' Ya faɗa a zuciyarsa yana yi wa Yusuf magana ganin yana ɓarna.
Yana fita daga gidan ya sauya sunan Salaha daga MARAINIYA zuwa, ABOKINA washe gari kuma sai ya sha kwalliya tare da fesa turare ya cewa Amina zai je wajen walima da abokinsa ya shirya musu saboda yana ƙara aure, Amina jin haka ta washe baki don ita a rayuwarta tana so ta ji an ce za a yi wa wata mace kishiya amma ban da ita.