Sashe 41
Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai dama na san za ki yi farinciki, ni ma yadda za mu yi ta shige sa fice shi ya sa na yi É—inkunan" Tana É—aya leshin ta ce
"Kai amma leshin nan ya tafi da ni wallahi, amma mai É—inkina ka ba ya É—inka mini ko?" Amsa mata ya yi da eh kafin ya ta ce
"Kai amma naka ma sun yi kyau, na yaran ma haka, bari na zaɓa maka wanda za ka saka ranar dinner da kuma ɗaurin aure" Ta faɗa tana duba kyan kayan har ta hango yadda za su masa kyau ta ce
"Dan Allah Abban Yusuf kar ka kalli kowacce mace a wajen bikin nan, kuma kar ka shiga hoton abokai in dai da mata a ciki, ban amince ba, sannan kake sunkuyar da kai in ka ga mata za su wuce" Cikin zolaya ya ce
"Ke kuma da za ki je naki bikin ƙawayen waye ya saka miki dokar kallon maza?" Ƴar dariya ta yi ta ce
"Ai ni duk mata ne" Dariyar shi ma ya yi ya ce
"Mu ma duk mazan ne" Su duka suka yi dariya, haka ta zauna ta ware kayan nasa tana ta yabawa da kyawun su, ta É—auki nata da na yaran shi ma ya É—auki nasa, har wata ajiyar zuciya ya sauke ganin bata zargi komai ba.
Ranar alhamis haka ya saci jiki ya je wajen ƙauyawan da su Salaha suka shirya, har aka je ka yi hotuna aka tashi ya dawo bata fahimci komai ba, tun da ya ce mata suna hidimar bikin abokin ne ita kuma da yake dama shirme ne da kishin kawai a ranta bata damu da mijin ba, hakan ya sa bata zargi wani abu ba.
Ranar juma'a da ya kasance ranar kamu, tun wajen ƙarfe goma ta shirya ta ɗauki yaran a cewarta, wai gidansu za ta kai yaran, sai a lokacin ma take ce masa ta je za a yi wa wata ƙawarsu kishiya, gidan su Saddiqa kuma sai ranar ɗaurin aure za ta je musu, tana son ta je ta jajanta mata in ta fita, kuma daga gidansu za su wuce gidan wacce za a yi wa kishiyar saboda aikin abin da za a raba gobe ɗaurin aure. Shi ma da yake dama haka yake so ta kama gabanta sai ya amince har da bata kuɗi masu kauri, duk da wani ɓangaren yana jin tausayinta a ransa amma in ya yi duba da cewa, laifinta ne zai saka shi ƙara aure, yadda ya rasa wasu abubuwan da ya faɗa halaka gwara ya yi aurensa, sannan yana ganin ma hakan izna ne a gare ta, da bata da aiki sai bibiyar gidan wanda za a yi wa kishiya ko da basu da wata makusanciyar alaka, kawai don ta je ta kashe ƙwarƙwatar idonta.
Da yamma lokacin da ya yi wanka ya shirya, abokansa suna ta kiransa a kan cewa suna jiransa domin tafiya wajen kamu, ga amarya ma tana ta doka masa kira a kan cewa su zo a tafi wajen kamun don tuni mutane sun kun ƙagu a tafi saboda wajen kamu ya gama kankama, jere kuwa dama tun ranar laraba suka je suka yi.
Fitowar da ya yi yana cikin rufe ƙofa ya ji, an saki wata uwar guɗa, gabansa ne ya yanke ya faɗi yana tunanin waye kuma zai saka shi a matsala, duk da ya san Amina bata nan amma dai guɗa ta hautsina masa ciki yana waiwayowa ya ga Sumayya ce sanye cikin wani koran leshi mai jajayen fulawoyi an sha uban jambaki, tana riƙe da hannun Ruma. Sai danya ɗan waiwaya ya ga babu kowa.
"Irin wannan guÉ—a haka kamar za ki cire hanci" Ya faÉ—a cikin wasa. Dariya ta yi ta ce
"Ango ka sha ƙamshi, mijin mace biyu ka fi mai mace ɗaya, mai mace ɗaya ya fi gwauro" Ta ce tana dariya. Shi ma dariyar ya yi yana sauri ya juya ya fita tana cewa a gaishe mata da amarya.
Sumayya ta shiga tunano ranar da za su je gidan Ummar Aminu su gaishe ta, da ta biyawa Zulaiha don kafin su bar gidan ƙawance ya ɗinke a tsakaninsu, lura da ta yi ita Saddiqa bata iya gulma ba kuma dai ta ga kamar Saddiqar bata son take shigar mata ɗaki, kuma ita ma Saddiqar ba zuwa ɓangaren Sumayyar take yi ba sai da dalili, abin da ta fahimta kamar dai Saddiqa tana gudunta ne saboda tsantsanin ƙazantarta hakan ya sa yanzu sai suka haɗe kai da Zulaiha amma ba wai ta daina kulata ne bane kwata-kwata.
ta tuno lokacin da ta shiga É—akin Zulaiha ta nufa ta shiga da sallama, aka amsa mata, tana shiga É—akin Zulaiha ta tashi da sauri bakin nan fal cike da yawun da ya taru a bakin, dama a hakan ta É—aga bakin dama gudun kar yawun ya zubo ta amsa sallamar. BanÉ—akin ta shiga ta tofar ta dawo tana É—an kiran sunan Ruma ta koma ta zauna, Sumayya ta kalle ta ta ce
"To ke baki shirya ba mu wuce gidan Ummar" ÆŠan yatsina fuska ta yi ta ce
"Yanzu zan saka kayana" Kallon ƙafarta Sumayya ta yi ta ga furu-furu kamar ta yi tsere a sahara ta ce
"Yau ɗaya dai ki mulke ƙafar nan da mai kar mu je ake mana kallon ɗaya saura kwata" Kallonta ta yi ta ce
"Shiga zan yi ai in wanke ƙafafu da fuska da hannuna, sai na shafa mai ai dama ni ina ni ina watsawa jikina ruwa, taɓ ni na yi sati ma ban yi wani abu wanka ba, in kinga ruwa ya taɓa jikina to alwalar sallah ce, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, dama can bana ƙaunar wanka kuma yanzu sai abin ya haɗu da cikin nan da na samu sai in ji babu abin da yake saka ni sai ƙyamar wanka" Dariya Sumayya ta yi ta ce
"Dama fa wahala da rai ne wanka, ni yau kwanana tara ban yi ba wallahi Shafi'u har ya gaji da mita ya zuba mini ido yo dama wankan dai na tsarki ne aka fiya yi, yanzu kuwa ya tsiri wani hali in zai kusance ni sai ya ce sai na yi wanka na wanke baki in na ƙi sai ya haƙura har falo ya ƙaura saboda ba ya son haɗa makwanci da ni, ni kuwa na ce ta fi nono fari gaba ta kaini gobarar titi, bare yanzu da nake fashin sallah ma kin ga ba zai wani zo neman buƙtarsa ba" Baki ta taɓe Zulaiha ta yi tsaki ta ce
"Rabu da gulmammu shi ma wannan sarkin ƴan rainin wayon Aminu, sai yake cewa wai in watsa ruwa ko ba zan saka sabulu ba ., ni kuwa in ce ya daɗe bai ga wanka ba, don ko sabulan kayan lefe na na saka na datse da mukulli na ɓoye mukullin, sai rai ya kai in na sauka lafiya, nake mulkawa in rabu da ƙarnin jego" Tana faɗar haka suka kwashe da dariya, ta shiga bayin ta yi wankin jiki, tana cikin wankewa ta ji wani hamami daga bakinta wanda ita kanta sai da ta ɗan runtse ido, hakan ya sanya ta lakuci makilin a yatsanta ta ɗan goga ta kurkure bakin ta fito, mai ta shafa ta saka atamfa riga da zani ta yafa mayafi suka fito. Da wannan tunanin ta bar gidan.
A ɓangaren Amina tun da ta shirya da yamna ta nufi gidan ƙawar tata, wacce ake yi wa ƙawar kishiya, haka suka wuce don uwar gidan tana ta musu waya a kan su iyi sauri saboda hall ɗin da ake kamun amaryar mijin za su je, don za su je su rawa su yi liƙi su nuna ko a kwalar rigarsu, dama kuma da sanin mijin uwar gidan za ta je.
Shi ma gudun fitina ya amince kuma da yake lallaɓata yake a rabu lafiya. Mota biyu suka cika da ƙawayensu, suna ta hira da zage-zage suna tsinewa maza wata ta ce
"Ai mazan ƴan buhun uba ne, sai sun hango wata za su aura su isheka da cewa ƙaddara ce" Wata kuma ta ce
"Ai ba za ki gane namiji munafuki ne ba sai ya É—irka miki kishiya, shikenan fa sai ya shiga raina miki wayo, a wajenki ya nuna ke ce a gaba ita ma a nata wajen hakan ce za ta faru ai maza munafukan mata ne" BuÉ—ar bakin Amian cikin cika baki ta ce
"Ai ni Allah ya taimake ni, kuma na taimaki kaina, na nunawa mijina babu ni babu zama da wata, shi ma kuma ya amince da hakan, yanzu ko sha'war kallon mace na ya yi bare a kai ga soyayya" Wacce ake yi wa kishiyar ce ta ce
"Raba kanki da namiji wallahi duk ƙarya ce, kawai suna raina mana wayo ne, nima nawan ba da haka ya fara ba, ban san da maganar auren ba sai da aka saka rana, shi ma auren ya rage sati uku" Kallonta Amina ta yi ta ce
"Naki mijin da ban nawa da ban, yo ni aka mini haka kuma ai sai gawata!" Uwar gidan ta ce
"Ko mushe za ki yi namiji babu ruwansa, in ma bai haÉ—a miki da saki ba in ya ga za ki tada masa hankali... Katse ta Amina ta yi da faÉ—in
"Ya isa wasa ya yi wasa ban da, tsikarin uwar miji"Da haka suka ƙaraso wajen da za a yi kamun, wurin guda biyi ne a jere kuma dama sun lura ana ta shiga kowanne kuma ba a buƙatar kowane get pass.
Da suka rasa wanne ne nasun, sai suka fito suka bi ayarin wasu ƴan mata, suna shiga ashe wajen kamun su Yaya Sule ne amma ango da amarya basu riga da sun iso ba, wajen dai an shriya komai gwanin sha,awa. Ana cikin wanna halin wayar uwar gidan ta yi ƙara, mijin ne yake sanar mata cewa ga sunan wajen idan sun zo, nan suka gane ba inda suma shiga bane suka fito domin zuwa ɗayan.
A daidai nan ne motoci suka zo reras, da alama motocin amarya da ango ne da kuma ayarinsu, amma dai mamallakan hall É—in da su Amina suka shiga. Tun da a daidai wajen suka tsaya.