← Book details Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 44

Sashe 38

Kazamin Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da ta cika sarin biyu ne, Saddiqa ta shiga kicin za ta dafa ruwan zafi, abin mamaki sai ta ga Zulaiha ta ɗauki tukunyarta ta dafa indomie, da alama girkih da dare ta yi, cike da mamaki ta ga har fork da plate ɗin duk nata ne, sannan kuma da ta gama amfani sai ta kwasa cikin jibgin kayan wanke-wanken ta. Amma haka Saddiqa ta ware su ta wanke ba tare da ta ce komai ba. Da yamma kuma ta shiga kicin ɗin za ta ɗakko plate da wuƙa za ta yanka mangwaro tana shiga ta samu Zulaiha ta yi ɗanwake a tukunyarta, ta kwashe a robarta sannan tana zubawa a plate ɗinta sannan fork da spoon ɗin ma na kai duk nata ne.

Mamaki al'ajabi suka saka kanta ya É—aure, ta ma rasa ta ina za ta fara magana, tana tunanin cewa wani abu amma sai ta ga ita Zulaiha ko a jikinta hasalima ta nufi wajen robobin Saddiqa wanda take zuba yaji da su maggi ta buÉ—e robar jan yaji ta saka cokali ta É—akko za ta zuba a É—anwaken da Saddiqar take yi kallon É—anye, saboda kana kallonsa za ka gane bai dahu ba. Har Zulaiha ta zuba yajin ta É—akko plate É—in ta zo za ta gota Saddiqa, cikin dakakkiyar murya Saddiqa ta ce

"Wai ni malama mai yake faruwa a wannan kicin É—in ne? " Yatsina fuska Zulaiha ta yi cikin rashin sanin manufar Saddiqa ta ce

"Ban gane ba mai kike tambaya" Zulaiha ta faɗa tana ƙarewa Saddiqa kallo ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake tashi daga jikin Saddiqar wanda ƙamshin ya haɗe wajen, saɓanin jikin Zulaiha da yake bada wani nau'in warin dauɗa da ban.

Saddiqa ta ce

"Shin bakya bambance tsakanin fari da baƙi ne?" Cike da wani kishin Saddiqa da ya tokare Zulaiha cikin zafin zuciya ta ce

"Wai mai kike nufi ne, ya za ki tare ni kina mini wani bayani marar kai da ƙafafu?Idan za ki tambayi abu ki yi da hausar da zan gane" Ɗan ƙanƙance ido Saddiqa ta yi ta ce

"Ina nufin ke bakya gane kayanku da kayan da ba naki ba? Ina nufin kwanuka, ya za kike ɗaukar mini kwanuka kina ɓatawa, sannan abin bai tsaya a nan ba har kike buɗe mini robar yaji kina ɗauk... Tun kafin Saddiqa ta kai ƙarshen maganar Zulaiha ta katse ta da faɗin

"Sai mai to? Idan ba a so kowa ya taɓa kayan kowa a kicin ake warewa, ke kuma naki mijin saboda tsiya ya haɗamu a kicin ɗaya kamar wasu sakarkaru, kwanukan da na ɗauka kuma wanda na gani a wanke ne, shi kuma yaji na ji daka da ɗanɗanonsa ya mini kin ga babu buƙatar sai matar gida ta san mini tun da ba almajiranci na zo gidan ba, gidan mijina ne, sannan kwanukan nan da suka taru na wanke-wanke za ki iya haɗawa da naki ki wanke, don ni wanke-wanke da shara basa ma cikin tsarina" Saddiqa ta ce

"Sannu zaƙaƙura wannan sai dai ki faɗawa wanda ya ajiye ki, ko shi yake wankewa ko ya ɗauka miki mai yi, don ni na fi ƙarfin bautawa kishiyar da za ta yi gadara da ni, batun yaji kuma wanda kike taƙamar da shi ba shi ya saya ba, ba shi ya daka ba don haka karki ƙara gigin taɓawa don sai na saka kin gwammace kiɗa da karatu" Tsaki Zulaiha ta ja, ta ce

"Ke banza ce sakar... Tun kafin Zulaiha ta ƙarasa sai ji ta yi ƙiii Saddiqa ta warce farantin hannunta wajen kwanukan nan mararsa wanki ta nufa ta ɗauki wani faranti a wajen ta ɗaga ɗanwaken za ta juye, da sauri Zulaiha ta ce

"Kar ki kuskura don wallahi ba zan yar... Kafin ta ƙarasa Saddiqs ta juye a kan farantin marar wanki ta nuna Zulaiha da yatsa cikin kalami na wanda ya san abin da yake faɗi ta ce

"Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, domin babban goro sai magogin ƙarfe, iya gani iya ƙalewa ki sani duk nisan jifa ƙasa zai faɗo, ni na fi ƙarfin ki kirani sakarya, ina so ki sani wanda ya rigaka da kwana ya rigaka da tashi, domin wanda zai je sama ya taka dutse haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya" Saddiqa tana kaiwa nan ta wuce ta ɗauki plate da ƙaramar wuƙar cokula ta juya za ta tafi, har ta kusa fita ta koma ta haɗa kayanta da Zulaiha ta ɓata a waje guda.

Ran Zulaiha ƙuna yake tana ji kamar ta shaƙe Saddiqa ta mata dukan tsiya. Tana juyawa ta hangi ɗanwakenta a faranti marar wanki, bayan ta shirya cin ɗanwaken, Saddiqa tana zuwa za ta wuce sai ta ji Zulaiha ta ja rigarta ƙiii ta dawo da ita baya saitinta. Rai ta haɗe tana aikawa Zulaiha wani kallo ta ce

"Daga yau kar ki ƙara kai hannunki jikina" Zulaiha tana jin wani tuƙuƙin ɓacin rai ta ce

"Mai ya sa kika zuba mini É—anwakena a kwano marar wanki?" Cikin halin ko in kula Saddiqa ta ce

"Saboda shi wancan marar wankin shi ne mallakiinki kuma halaliyarki, kuma ai hausawa sun ce guntun gatarinka ya fi sari ka bani, sannan idan har tsafta da daÉ—i ka ga abu mai kyau ya baka sha'awa, to ya zamana dole ka koyi kintsa naka da tattala naka, ba wai ka mayar da kayan wani naka ba" Saddiqa tana kaiwa nan ta juya ta fito daga kicin É—in, hakan ya yi daidai da shigowar Aminu gidan, wanda yau yake cike da murnar komawa É—akin Saddiqa da kwana.

Wani ƙaramin kukan kissa Zulaiha ta rushe da shi, wacce ko sannu da zuwa bata masa ba ta shiga faɗin

"ÆŠan aljannata, ka ga matarka tana mini wani irin cin kashi" Aminu da yanzu kawai dama cike yake da ita, jin ta kirashi da É—an aljanna sai ya ce

"Ni fa bana son tashin hankali, ya tun da sanyin safiya na fita neman abin rufawa kaina asiri amma daga zuwana zan tarar da wani makararran faɗanki?" Bai jira cewarta ba ya juya zai tafi ɗakin Saddiqa rai cike da haushi Zulaiha ta bi bayansa da harara. Saddiqa ma baya ta take masa tana jin wani abu yana yunƙuro mata don zuwansa wajen ya sauya iskar da take kaɗawa.

Zulaiha ɗakinta ta nufa ranta yana ƙuna, ta ɗauka a matsayinta na amarya Aminu zai ƙuntatawa uwar gidansa saboda ita amma ta zo ta ga saɓanin yadda ƙawaye suke zugata sai dai bata gane cewa ko dai ita ce bata kai matsayin da za a ƙuntatawa wata dalilinta ba, don yanzu ta lura Aminu kamar an sauya mata shi.

A ɗakin Saddiqa kuwa Aminu ransa fari ƙal ya shiga, jin wani ni'imtaccen ƙamshi ya mamaye ɗakin, wani yadi ne ruwan toka a jikinsa saboda yadin bai cika nuna datti ba sai ya maimaita shi ya fi a ƙirga don shi dama bai damu da haske ko dauɗar abu ba. Yadda ya sha rana a kasuwa ya sanya bayansa jiƙewa hakan ya sa rigar har mannewa take yi. Yana ƙarewa ɗakin kallo ya ƙarasa bakin gadon ya zauna. Saddiqa da tun da ya doshi ɗakinta annaurin zuciyarta ya sauya ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Tamkar ya ari baki haka ya shiga amsa mata cike da ɗokin ganinta yana faɗin

"Saddiqa amaryar kuma uwar gida" Bata amsa masa ba ta ƙarasa ta zauna a ƙasa tana janyo wankakken mangwaron da za ta yanka, ranta yana ƙuna don ganin Aminu ya zauna a kan gadonta ta san zanin gadonta fari ya tashi daga aiki, don ko shigowarta ɗakin kaɗai ta san akwai wanda datti ya yi wa kanta a ɗakib nata. Bai damu da yanayin fuskarta ba ya ce

"Saddiqa ina mukullin banɗakin ki" Wani daɗi ta ji a ranta duk da tana taraddadin shigarsa banɗakin nata, amma dai duk tunaninta wanka zai ce zai yi bata san cewa har yau Aminu yana nan yana taka matsayinsa na Aminu kuma yana amsa sunansa ya ƘAZAMI ba, tana cikin tunanin hakan ya ce

"Ina son zan tsugunna" Dimmm ta yi jin wai kashi zai yi, ta fara tuno yadda banɗakin yake a wanke tass, yadda take amfani da kayanta ita kaɗai. Kallonsa ta yi tana tuna yadda ba ya ploshing wani lokacin da yadda yake ɓata shaddat kanta in ya tsubunna kamar wani ƙaramin yaro, ita dai ba don ba don ba da ta ce ta yafe Aminu a matsayin miji, sai dai ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta akan hakan cikin jikinta yana taka muhimmiyar rawa, duk da hausawa suna faɗin da babbar budurwa a gida gwara ƙaramar bazawara sai dai yanzu ta fara taraddadin komawa gida zawarci da ƙaramin ciki, har ta haife ta raine shi, sannan ta yaye in ma ta samu mai aurenta shin ya makomar rayuwar abin da za ta haifa zai kasance.

Mukullin ta miƙa masa, yana ta ƙoƙarin son ganin fuskarta amma ta ƙi bashi dama, fita ya yi yana rawar ƙafa ya nufi bayin. Zulaiha tana hangoshi ya shige bayin bayan ya buɗe, tana jin wani kishinsa yana taso mata. Ya daɗe a bayin kafin ya fito bayan ya yi wankin jiki haɗe da yin alwala ya rufe banɗakin ya fito. Ko kallon inda Zulaiha take bai yi ba, yana ganin lokacin da ta tashi ta nufi ɓangaren Sumayya.

Saddiqa tana zaune tana shan mangwaron ya dawo ɗakin, a ranta tana ta addu'ar Allah sa wanka yake da ta ga ya daɗe, sai dai yana shigowa ta gane jikinsa bai san da zaman wani abu ruwan ba, a ranta tana ƙiyasta mai hali ba ya sauya halinsa. Kabbara ya yi tana gani ya yi azahar da la'asar, tana hango a ce wannan uban ƴaƴanka ne shin mene ne wanda yaran za su koya a bayyane daga mahaifinsu, ƙazanta ko rashin kiyaye sallah a kan lokacinta, ko uwa uba rashin kula da addinin kansa, babu wani abin koyi daga Aminu, sai dai abin Allah wadai.
Chapter 38 · 0% Book details