Sashe 5
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba komai, wata ƙawata ce aka ce ta rasu. Zan kiraka gobe idan zan je ganin Asiya"
Daga Haka ta rolling glass ɗin ta kunna motar ta fara reverse. Yaya Bello ya bita da ido yana mamakin wannan lamari dan bai yarda dalilin kukanta ba kenan akwai wani abu a ƙasa...
Ƙarfe taran dare ta kira shi a waya tace ya kawo mata irin abubuwan da yake sha yake manta damuwarsa.
"Hajiya Halima anya lafiyarki kuwa?. Abinda nima ke ƙoƙarin dena sha kike son sha"
"Ya zan yi Yayanmu. Ya zan yi?. Har yana da bakin yi min gori saboda zai aurar da 'yarsa. Ba zan taɓa yafewa ba, ko a lahira ba zan yafe masa ba" ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka.
Yaya Bello yai shiru yana sauraron kukanta. Ya ma rasa mi zai ce, duk da a da haushi take bashi amma yanzu ji yake inama yana da abinda zai share mata hawaye, ya yaye mata matsalarta.
Kusan minti ɗaya kafin aka kashe wayar, ya sake kiran numbar amma ba a amsa ba, ƙarshe kuma daya kira ya ji wayar a kashe.
Hankalinsa ya tashi, tunda ta fara maganar kayan maye kada fa ta je ta aikata abinda bai dace ba.
Isuhun ƙauyensu ya taɓa rataye kansa a jikin bishiya aka dinga cewa hauka ce ta kama shi, wasu kuma suka ce damuwa ce ta mai yawa.
Kasa haƙuri yai ya fita ya ɗau motar Asiya sai Kachallah house.
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ake yasa Halima ta sassauta sheshsheƙar kukanta.
"Anty Halima wai Bello na nemanki a waje. Anty Halima kin yi bacci ne?"
Mai aikin nasu Indo ba dai shirme ba kam.
Halima ta goge fiskarta tace "Indo kice masa na yi bacci"
"Anty kika ce me?"
Halima ta É—an É—aga murya tace "Kice masa" sai kuma ta chanja tace "ina fitowa"
Minti goma sai gata gaban Yaya Bello da ke tsaye gaban mota.
"Yayanmu zuwan dare haka"
"Yo ai kin tsorata ni, babbar mace da kuka ai akwai damuwa"
"Dama kuka na yara ne kawai?"
"A'a. Sai dai ina tsoron kada ki rataye kan ki irinna Isuhu. Shima lokacin da ya ke kuka kowa ya É—auka Aljanu suka buge shi"
Halima tayi murmushi mai ciwo sannan tace "ba zan rataye kaina ba Yayanmu"
"Sai yanzu na ji hankalina ya kwanta. To sai da safenmu"
Juyawa yai zai buÉ—e mota ya ji ta ce "Yayanmu ka aureni dan Allah"
Yaya Bello ya juya kai gefe da gefe dan ya tabbatar da wani tayi maganar ba shi ba, sai ya ga babu kowa su biyu ne kawai a wajen.
"Ko ba ka sona ka aureni, ni ina son ka"...
***
Asiya da Madam Chess sun ɗinke sosai cikin kwanakin nan. Madam Chess ta mata alƙawarin matuƙar ta cita a wasan Chess da suke bugawa zata bata tarihinta da dalilin zamanta a wannan kurkuku. Har yanzu Asiya bata gama gane wasan ba shiyasa ko minti goma ba ayi Madam Chess ke cinta.
Lauratu da JP sun zama 'yan kallo a ɗakin dan walwalar da basu taɓa gani a wajen Madam Chess ba suke gani yanzu tun da Asiya ta zo ɗakinsu.
"Mommy dan Allah ki faÉ—a min. Ina zan iya karawa da ke bayan kin É—au shekaru kina bugawa"
Madam Chess ta yi murmushinta na manya tace " ba ki da haƙuri kuma kina da gaggawa. Wannan su suke sawa na cinye ki tun a tashin farko"
Asiya ta zumɓura baki tana jujjuya knight ɗin dake hannunta, ta sake ganin board ɗin da kyau sannan ta maida knight ɗin data ɗauka ta ɗauki queen.
Madam Chess tace "Good move"
Tarayya da wannan mata yasa Asiya ta rage saka damuwa a ranta. Infact itama karatu ta ke yi a duk free time É—inta tunda ba laifi ba a sakata aiki.
Ranan kwatsam sai aka kirata wai tanada baƙi. Jiya Barr. zaytoonah ta zo mata da albishir akan za a fara sauraron ƙara a court of appeal nan da kwanaki tara masu zuwa. To suwaye kuma suka zo? Ban da Lawyarta babu wanda ya taɓa zuwa dubata.
Lokacin data fita sai ga Halima Kachallah, Sumayya da kuma Jummai. Suka dinga ihun murna lokacin da suka ganta kamar wasu yara ƙanana.
Abinci mai rai da lafiya suka kawo aka haÉ—u aka ci. Duk yadda Asiya ta daure sai da ta yi hawayen farin ciki ba dan komai ba sai dan 'yanuwa rahama ne.
Labarin 'yan gidan su da ta samu da kuma dawowar Abba da Ale daga Makkah ba ƙaramin daɗi ya sata ba.
"Anty Asiya kar ki damu yanzu kam duk sati sai mun zo miki. Gwamna ya bamu permit babu wanda ya isa ya hanamu ganinki"
Asiya tace " nagode Anty Halima"
"Kiyi haƙuri. Na san kina tunanin bai damu dake ba amma wallahi ya damu. Ban san dai ya zan faɗa miki bane amma kamar Yaya Saif baya hayyacinsa, kowa complain yake"
"Nagode sosai Antyna ta kaina. Ya maganar Albino kuma?"
Asiya ta chanja maganar dan bata son maganar Gwamna dan yana taɓa mata zuciya.
Halima ta yi murmushi ta ce " ni yanzu nema nake a wajen Yayanmu amma na rasa gane kansa. Wai ce min yai nayi haƙuri ba zai iya da ni ba"
"Wani Yayanmun?"
Halima ta É—an rufe fiskarta tana dariya.
"Dan Allah Yaya Bello kike so?" Sai kuma tayi saurin chanja maganar da cewa "kai nayi murna. Allah ya sanya alkhairi"
"Idan ya amince ba, kin san Yayan naki kaman mai matsa-matsai, inji ki da faÉ—a"
Asiya ta saka dariya harda tafa hannu. Rabonta da genuine dariya haka har ta manta...
***
Bilkisu Kachallah ta gama tsare-tsarenta, ta je Fada da macijiyarta amma lokacin data yiwa Mai Martaba maganar sarauta sai yai biris da zancen. Duk da ta lallami yai maganar amma hakan ya fusata ta matuƙa. Har take yi masa iƙirarin itama jinin sarauta ce. Mai Martaba tsoho mai dattaku ya maida martani da cewa Uba yake gareta idan har tana tinƙaho da jinin sarauta to dole ne ta yiwa magabatanta biyayya.
Bacci ranan ƙauracewa Bilkisu yai dan kota kwanta maganganun mai martaba ke yawo a kwanyarta. Sarautan Gimbiyar Congo take so kuma ko ana so ko ba a so sai an bata wannan sarauta.
Zuwa safiya wani tunani ya faÉ—o mata. Idan ta sa aka tsige sarki aka kuma É—aura mahaifinta babu tantama sarautan da take so automatically ya zama nata. Da wannan tunani ta tunkari É—akin Gwamna Saifuddeen Kachallah...
4
Lokacin da Bilkisu Kachallah ta shiga É—akin Gwamna baya nan ya shiga banÉ—aki. Joter da ta gani akan gadonsa ta É—auka.
*And then i kissed her* shine taken waƙar da yake rubutawa. Ba sai ta karanta ba ta san waƙar dan wa aka yita. Wani kibiyar kishi ne ya soki zuciyarta lokaci guda ta kama joter ta fara yagawa.
Gaskiyane she wants to outshine him, amma kuma soyayyar da take masa gaskiya ce. Shine namijin da ta fara so kuma take so har yau.
"Bilkisu" ta jiyo muryansa a bayanta. Ta juyo da rinannun idanunta da suka ciko da hawaye ta ce " baka taɓa rubuta waƙa danni ba. But, her"
"Ba abinda kike tunani bane, it's just a poem."
Watsa masa takardun hannunta ta yi tana faÉ—in " it's just a poem. Ni ba mahaukaciya bace Saifuddeen. Na san komai, na san ita ka ke wa rubutu, na san..."
"Assalamu Alaikum Daddy" muryan Mahirah ya katse ta.
Suna haɗa ido da Bilkisu annurin fiskar Mahirah ya ɓace.
"Ehen, miya kawo ki?"
"Dama...dama za mu je Kachallah house ne da su Nana"
"Ba inda zaku je"
Mahirah ta juya jiki a sanyaye dama ba wai Kachallah house ɗin za su je ba. Sun yi waya ne da Anty Halimah ta ke faɗa mata sun je prison jiya sun dubo Asiya. Shine ta zo tambayar Daddynsu suma ya basu izinin zuwa prison su je su ga Asiya dan ba ƙaramin kewarta suka yi ba.
Bayan fitan Mahirah daga ɗakin Bilkisu kasa ƙarisa maganar ta yi ta watsawa Gwamna mugun kallo sannan ta fice daga ɗakin.
Bayan ta samu zama da Chief of staff ta ke gaya masa buƙatarta na son a tsige Mai martaba. Maganar ta zamo masa banbaraƙwai. A wani dalilin za a tsige mutumin da yai kusan shekaru talatin da bakwai akan kujerar mulki.
"Boss lady idan ban katse miki hanzari ba. Bana tunanin abinda kike nema zai yiwu, babu dalilin da zai sa a É—aga Mai martaba akan kujerarsa, mutane za su yi magana"
"I don't care!" Ta faÉ—a tana buga desk É—inta.
"Ki sake duba maganar nan"
"Lamara Damana ina so ka nemo min dalilin da zai sa a tsige sarki"
Wannan karan COS bai yi magana ba sai miƙewa yai ya bar office ɗin. Bayan tafiyarsa Bilkisu ta kalmashe ƙafa ta sa hannu tana mammatsa kakkauran wuyanta. Yadda take jin kanta a gajiye ma ya kamata ta je spa ne a mata massage. Kiran sakatariyarta tayi ta ce ta haɗa mata appointment da wajen salon da kuma wajen spa treatment.
"Excellency Ma, Halal salon za a booking ko Prime beauty parlour?"
Har ta ce mata Halal salon sai kuma ta tuno cewa Asiya co-owner ce na Halal salon.
"Ki booking prime beauty"
Tana ajiye wayarta ta rufe idonta tana juyi akan kujerar. Ba zata taɓa bari Asiya ta fito a prison ba, duk abinda za ayi sai court appeal ma ta tabbatar da hukuncin farko.
Washegari aka shirya taro a gidan Bilkisu. Bayan kowa ya hallara a wajen sannan ta fito still É—auke da macijinta. Bayan ta zauna a kujerarta na zinari sannan ta bada damar a fara meeting. Bayan an gama tattauna abinda ya dace sai kuma Bilkisu ta kawo maganar tsige Mai Martaba.
Dukkansu sai suka fara kallon-kallo.
Alhaji Sani Kachallah yace " babu fa'ida a cikin tsige Sarki"
"Exactly" Alhaji MacciÉ—o ya goyi bayan Alhaji Sani.
Bilkisu ta saukar da macijinta ƙasa ya fara yawo a ƙasa. Tuni Mr Paul ya ɗaga ƙafafuwansa ya aza bisa kujera yana rarraba idanu.
Suma sauran da basu É—aga ba kowa yana shakkar wannan maciji da ke yawo a tsakaninsu.