Sashe 2
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe kamar Barr. Zaytoonah ta san bata da lafiya, lokacin da ta zo sai ta taho da wata likita mai suna Dr Hoodah. Ko dama zazzaɓin jira yake ta sha magani, tana shan magani ko minti shabiyar bai kai ba ta fara kela amai. Ƙarshe dai allura aka mata aka saka mata ledar ruwa saboda ta samu ƙarfin jiki.
Kwananta na biyu a gidan da ta samu ta ci abinci sai gashi ta ɓarke da gudawa saboda system ɗinta ya fara sabawa da abincin prison.
***
A yau ma Gwamna ya sake yunƙurin zare jiki dan yaje ya duba Asiya amma yana buɗe ƙofar ɗakinsa yai kiciɓis da macijin Bilkisu ya fasa kai yana zaro harshensa. Ƙirjinsa ya buga dam yai saurin rufo ƙofan ya koma ya kwanta.
Tunda aka bada bail É—in Asiya Bilkisu ta tare a É—akinsa da kwana, rabon da ta kwana a É—akin har ya manta, amma tunda aka sako Asiya ta dawo kwana É—akinsa. Ta riga ta masa kashedin akan bata yarda ya je ya ga Asiya ba amma duk da haka idan ya kwanta sai wani sashe na zuciyarsa ya dinga ingiza shi akan yaje ya dubata musamman da yaga videon da ya watsu a media na yadda ake maltreating matar gwamna a kurkuku.
Gwamna ya dinga juyi ya kasa bacci, Asiya ce a ransa, Asiya yake son gani. Ƙarshe ya miƙe ya je ya ɗauko maganinsa ya sha guda huɗu maimakon ɗaya, duk da haka ya jima kafin bacci ya ɗauke shi...
***
Nana ta shige banɗaki a sulale dan bata so ta tayarda Mahirah. Tunda ta fara shan ƙwaya saboda ta dena jin tsoron macijin Mommy sai kuma muguwar sha'awar shan ƙwayar ya dawo mata fiye ma da da, sai abinma ya zamo kaman bata taɓa dena sha ba.
Ta buɗe wata baƙar leda da Kabir ya bata a school bayan ta bashi dubu goma cash. Jikinta har rawa yake lokacin data fito da ƙaramar takarda da aka nannaɗa ƙwayar a ciki, ta zuba rabin garin da ke cikin takardar akan cover na toilet sit, ta ja layi guda uku da garin cocaine da ta zuba sannan ta toshe hancinta ɗaya ta zuƙi garin da ɗaya hancin, ta girgiza kai sannan ta sake zuƙan sauran layuka biyu data zana sai a sannan ta fara jin kanta dai dai. Ta maida sauran ƙullin garin cikin leda ta cusashi cikin aljihun pyajamas ɗinta sannan ta koma ɗaki ta kwanta, wannan data shaƙa zai kaita har rana sauran na ledan zai kai mata zuwa dare, gobe Kabir zai kawo mata na dubu hamsin.
Bata jima da kwantawa ba Mahirah ta tashi sallar Asuba. Bayan ta yi alwala ta zo ta tashi Nana sallah.
Da alwalan da sallar duka babu wanda Nana tayi cikin nitsuwa dan dai tayi sallah ne amma bata san ma takamaimai mi take faÉ—a ba a cikin sallar. Tayi sujjada ya yi sau biyar kafin ta sallame. Hankalin Mahirah na kan Qur'ani da ta ke karantawa bata lura da irin shirmen da 'yar uwarta ta dinga yi a sallah ba.
***
Yau aka gurfanar da Timothy Igwe a gaban kotu, mutumin da yai iƙirarin matar Gwamnar jihar Congo yake wa aiki.
Bayan alƙalin Gwamnati yai masa tambayoyi. Tamkar wanda yai hadda haka Timothy ya dinga jero amsoshin tambayoyin babu ko fargaba ko wani gargada.
Bayan an ba wa Barr. Zaytoonah damar yi masa tambaya abinda ta fara yi shine tace a kira mata Asiya Kachallah. Gaba É—aya sai aka fara kallon kallo saboda ga Asiyar da kowa ya sani tsaye a witness box.
Bayan matar da aka kira ta zo ta tsaya sannan Barr. Zaytoonah ta mayar da dubanta ga alƙali tace " wannan mata da kuke gani sunanta Asiya Kachallah, shekarunta hamsin da biyu a duniya kuma ta kasance cousin ga Alhaji Sani Kachallah"
"Objection my Lord Barr Zaytoonah ta sake layi daga abinda ake magana a kai"
Alƙali yace Barr Zaytoonah ta fito fili ta bayyanawa kotu mi take nufi.
"Ina so kotu ta tuna da bayanin Timothy Igwe a wannan video inda yace matar Gwamnar jahar Congo yake yiwa aiki, sannan ina so kotu ta tuna cewa yanzu kuma Timothy ya bayyanawa kotu cewa Asiya Kachallah yake yiwa aiki. A lokacin da yace matar Gwamnar jahar Congo yake yiwa aiki matan Gwamnan Congo su biyu ne, so Bilkisu Kachallah is also a suspect. Sannan yanzu da ya ce Asiya Kachallah yake yiwa aiki wannan mata mai suna Asiya Kachallah zata iya zama suspect saboda sunan client ɗina *Asiya Shahidah Faruƙ Baba* kafin aure da kuma bayan aurenta. So a nan, ya nuna cewa Timothy ya chanja magana kuma ƙarya yake yi"
"Objection my lord" Lawyan Gwamnati ya faɗa da ƙarfi.
"Objection sustained"
Barr. Zaytoonah ta girgiza kai dan ta san an siye alƙalin, idan ba haka ba abinda take faɗa yana kan hanya bai kamata a dakatar da ita ba.
"My Lord, Mr Timothy ya ƙi bayyana suna ne saboda yarjejeniyar da akayi da BBC eye kenan kafin a saka shi a documentary da aka yi akan safarar miyagun ƙwayoyi. Ina so kotu ta tuna da irin muggan ƙwayoyin da aka samu a ɗakin Asiya Kach... Asiya Faruq Baba"
"Objection my Lord" Barr Zaytoonah ta faÉ—a a fusace...
***
"Shikenan Mommyn Alinah. Nagode da ƙoƙarin ki akaina"
Abinda Asiya ta faÉ—a kenan a hankali dai-dai za a fita da ita.
"Asiya, bai ƙare ba, we will appeal, sai mun je har supreme akan gaskiyar mu" Barr. Zaytoonah ta faɗa kamar zata yi kuka.
Lokacin da aka fito da Asiya idan kaga ruwan jama'a a bakin kotun ka É—auka sarauniyar ingila ce zata fito.
Da ƙyar aka samu aka shigar da ita mota dan mutane dayawa kowa na son ganin Asiya...
Bilkisu Kachallah tayi murmushi ganin yadda ake tura Asiya cikin mota duk dama an rufe fiskarta da gyale amma ba ƙaramin nishaɗi ta ji ba ganin maƙiyiyarta a hanyar zuwa kurkuku.
"Ten years imprisonment, na tabbata wannan lawyar zata ɗaukaka ƙara"
"Sai me idan ta ɗaukaka ƙara, we'll keep bribing the judges, wanda ya ƙi yi mana abunda muke so mu kau da shi"
COS ya É—an yi shiru sannan yace "what's next? Boss lady"
Bilkisu ta yi murmushi tace "ka aikawa mai martaba da takardar kira"
COS ya kalleta cikin rashin fahimta. Maimakon ta bashi amsa sai tace yai abinda tace kawai...
2
*Congo Prison Female Ward*
Æangaren mata na kurkukun yana da hawa har guda huÉ—u. Wannan hawa-hawa kuwa shi ake kira da iya kuÉ—inka iya shagalinka. Tun daga lokacin da aka kawo firsuna to ma'aikatan kurkukun za su tsarge maka wannan mataki-mataki da aka tsara wanda kuwa duk dan saboda neman kuÉ—i, son zuciya da kuma rashin gaskiya ne aka Æ™irÆ™iri hakan.
Idan kai faƙiri ne, yaku bayi, marar gata to chan general cell za a kaika inda zaka zauna da inmates sama da hamsin. A dake ka, a ci zarafin ka babu wanda ya damu da kai, ƙarfin ka da wayonka ya ƙwace ka. General cell wato A-ward ake kira da Ghetto cell.
Idan kana da 'yan chanjin ka za a kaika B- ward inda ake kira Grade-3 a nan kowanni firsina yana biyan dubu biyar a wata, a shekara dubu sittin kenan. Firsina biyar zuwa shida ake zubawa a ciki idan kun yi rabo ku zama ku huɗu amma ba a saka ƙasa da haka. Banbancinsa da Ghetto shine akwai banɗaki da iya 'yan ɗakin zasu dinga amfani da shi sannan akwai fanka a ɗakin.
Hawa na uku shine C-ward da ake kira Sarauniya-Hall, a nan mutum biyu ake sawa a ɗaki, kowannensu yana biyan dubu shabiyu a wata. Banbancinsa da Grade-3 shine banɗakinku standard ne akwai ruwa a famfo, akwai shower, akwai fanka, sannnan idan babu wuta idan aka kunna generator zaku samu wuta. A da Sarauniya Hall shine jin daɗin ƙarshe a kurkukun kafin kuma shekaru kusan bakwai da suka wuce aka gina D-ward..
D-ward shine mataki na ƙarshe wanda shine ƙololuwa, nan ne gidan ajebos wato yaran 'yan siyasa da attajirai dama manyan 'yan kasuwa mata da aka kama da laifi. Yawancin waɗanda ake sawa a ciki ma ba su cika jimawa ba, dan da an kawo mutum yayi ɗan watanni zuwa shekara zaka ga an sake mutum saboda anbi ta ƙarƙashin ƙasa an gyara shari'ar da aka yanke da farko.
Aso rock kaman yadda ake kiran wajen, waje ne na hutu, dan idan kana wajen ba za ma ka É—auka kana cikin prison ba saboda abubuwan more rayuwa da suke wajen kaman kana gida ne. A wannan waje kowanni É—aki mutum É—aya ne a ciki sai wanda ya É—auko guard daga Ghetto cell wanda duk wannan na cikin kuÉ—in da zaka biya. Guard firsina ne da zaka É—auka kana bashi 'yan chanji wani zubin ma baka bada komai just saboda samun wajen kwanciya mai kyau da rashin takura shikesa wasu ke rububin 'yan Aso rock su É—aukesu a matsayin guard. Guard kaman mai aiki ne, gyara É—akin VIP dake Aso rock, wanki, wanke-wanke da duk wani aikatau. Saboda yawanci 'yan Aso rock basa cin abincin gidan kurkukun, guard shine zai dinga yin girki.
'Yan Aso rock har alfarmar amfani da waya suke da shi duk da dai ba wai an yarda bane amma iya kuÉ—inka iya shagalinka dan haka kuÉ—in da ake biya yana covering duk wani rules da zaka breaking a prison É—in.