← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 48

Sashe 46

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya gama da ayyukan office ya wuce gida, yai ɓadda kama ya fita daga gida daga shi sai Direba.
An san da zuwansu dan haka babu ɓata lokaci aka buɗe musu dogon gidan.

Ta ƙara lalacewa fiye da farkon kawota gidan. Zuciyarsa ya motsa da tausayinta. Yau kwana uku kenan da cikan aurensu shekara ishirin, sai da zai taho ne lissafin anniversary ɗinsu ya faɗo masa. Ya tuna buri da Bilkisu ta sha lokacin anniversary na cikar aurensu shekara goma. Idan suka cika shekara ishirin da aure za ta yi bikin da ba a taɓa yi ba a ƙasar nan. Yau gashi ranan ya zo har ya wuce, auren na su kuma yana lilo igiyar na gab da tsinkewa.

Ya dubi fiskarta dai dai zata zauna. Lokacin da ya aureta fara ce amma ba sosai ba. A gidansa ta fara shafa mai ta mayar da kanta farar balarabiya ƙarfi da yaji. Ba zai iya tuna ya ainihin gashin kanta yake ba saboda sun rayu ne da gashin da take chanjawa akai-akai wanda ya mantar da shi kala ko kuma tsayin ainihin gashinta.

"Mr Governor da kansa. Na ji ance har yanzu ba ka sayi form É—in takara ba, good for you, dan ko ka siya asara za ka yi"

"Ki zauna Bilkisu, we need to talk"

"Ka fara dana sanin abinda ka min ne?"

Tambaya É—aya ya zo yi mata, tambayar da ta tsaya masa a rai watanni da dama da suka wuce.

"My son, Sa'ad Junior, ke kika kashe shi?"

"How dare you!" Ta miƙe a fusace.

"Shima kin kashe shi ne saboda kujerar Gwamna?"

"Kar ka gaya min maganar banza. Ni ba muguwar uwa bace. I love him, I love my son. Taya zan kashe É—ana, "

Hawaye suka fara zubo mata tunowa da ta yi da yadda ta ga gawar Junior.
Shri Malaminta na India ya faÉ—a mata É—aukan fansa macijiya tayi akan É—anta saboda ta sabunta alkawari. Amma duk da haka bata ganin laifinta a cikin wannan lamari sai laifin Saifuddeen.

Shima É—in idanunsa ne suka ciko da hawaye saboda abinda yake shirin faÉ—a mata na cinsa

"Bilkisu" ya kira sunanta da sigar jan hankali
Ta tattaro nitsuwarta ta bashi.

"Na sake ki saki É—aya"

Zuba masa ido tayi kamar ba ta ji mai yace ba.

"Gobe za a gabatar da shaidu a kan ki, ban san wani hukunci za a yanke miki ba. Amma Dan Allah kafin nan ki tuba wa Allah, laifukan ki suna da girma Bilkisu"

Dariya ta ƙwace mata. Tana yi tana nuna shi da yatsa.

"Ba ka isa ba. Ba ka isa ba Saifuddeen. Baka isa ka min haka ba"

Ta miƙe ta cakumo shi " Ba zan yarda ba. Ba zan yarda ba Saifuddeen"

A lokacin ya rasa wanne ne ya fi daminta sakin da yai mata ko kuma asirinta dake daf da tonuwa.

Ranan daya koma gida zama yai a ƙasan ɗaki yai ta kuka kamar ƙaramin yaro, jikinsa har ɓari yake saboda har yanzu yana gani kamar shine dalilin da ya sa Bilkisu ta zamo haka.

Washegari kamar yadda ya tsara ya miƙa takardun da Asiya ta bashi ga hukuma.

Tun bai bar office ba Nana ta kira shi tana kuka. Bai san mi zai ce mata ba kawai ya kashe wayar ya kwantar da kansa a kan kujera. Inama Asiya tana kusa da shi da zai ji sauƙi koda kaɗan ne a ransa.

Da sauran ƙarfi daya rage masa ya rubuta mata text ya tura, nan kuma ya kwanta yana numfashi sama sama har kuma numfashin ya tsaya...

33

Yau ne ukun rasuwan Tabawa dan haka har yanzu gidan su akwai mutane. Mutanen ne ma yasa ta koma gidan Baffa Malam dan bata jin daÉ—in jikinta tun kafin rasuwan.
Tana kwance Mama ta zo ta tasheta hannunta É—auke da wayarta.

"Tun É—azu aketa kira inaga an kira ya fi sau ishirin. Ki duba dai ko lafiya"

Asiya ta amshi wayar tana yin hamma dan baccin bai isheta ba.

Nambobin da suka yi ta kiranta ne yasa hankalinta ya tashi baccin da ke idonta ya washe. Nana, Badawiyya, Likitan Gwamna, Hajiya Umma, Halima Kachallah.

To miyake faruwa?

Ta ma rasa wa zata kira. Ganin text da aka turo guda huÉ—u yasa ta shiga wajen message da sauri.

*kina ina ne Asiya?. Wallahi idan baki zo ba wani abu ya same shi zaki yi dana sanin taurin kan ki.....* Badawiyya

*Direba yana hanya zai É—auko ki, ki bar komai ki taho tareda shi....* Haj. Umma

*Daddy ba lafiya please ki zo Asibiti...* Nana

*"I need you....* Saifuddeen

Likita ta fara kira dan gaba É—aya zuciyarta ya bata wani mummunan abu ya samu Saifuddeen.

Jin ba a amsa wayar ba ta sake shiga tashin hankali.

"Badawiyya ya mutu ko?" Ta faÉ—a cikin muryan kuka.

"Idan ya mutu ke kika kashe ai"

"Na shiga uku"

"Kwantar da hankalinki yana da rai amma gaskiya a yadda Abban Fadilah ya gaya min yana jin jiki. Asiya ki je Asibiti ki duba shi"

Ko wanka bata yi ba ta chanja kaya ta saka dogon hijabi. Tana shirin neman wanda zai zo ya kaita ne ma sai ga Direban da aka turo ya iso...

Likita yace suma yake yana farfaÉ—owa, kusan sau uku yana haka kuma a duk farfaÉ—owan da zai yi sai ya kira sunan Asya wannan yasa suke ta kiran numbarta

"Yana coma yanzu haka, zamu bashi awa ashirin da huÉ—u zuwa awa saba'in da biyu idan bai farfaÉ—o ba zamu É—au wani mataki"

Ta rufe baki da hijabinta ta fara kuka. Idan Saifuddeen bai farfaɗo ba ba zata taɓa yafewa kanta ba.

*

Kwana biyu suna jira ya farfaÉ—o amma shiru. Gaba É—aya sun tsorata da lamarin, Asiya har ta fara maganar ko waje za a fita da shi Likita yace a'a ba za a iya fita dashi a haka ba.

Allah da ikonsa a rana ta uku sai gashi ya farfaɗo. Asiya tana ɗakin itada Nana suna karatun ƙur'ani suka ji kaman gadonsa ya motsa.
Asiya tayi saurin juyawa aikuwa suka yi ido huÉ—u da shi.
Ita da Nana suka shiga rige-rigen ƙarisawa gadonsa.

Idan Allah bai rubuta lokacinka ya ƙare ba duk abinda zai sameka ba za ka mutu ba.

Gwamna yana jinya a Asibiti aka siya masa form ɗin takara a karo na biyu. Kasancewar Asiya na kusa da shi tana bashi kulawa ya sa yake samun sauƙi da sauri.

Kwanansa biyar da sallamoshi daga Asibiti aka yi zaɓen primary aka fidda sunan shi a matsayin wadda zai yi takara a jam'iyyarsu. Babban abokin adawarsa wannan karan ma Alhaji Umaru Kwom ne wanda yake ganin zai yi kamfen da abubuwan da Bilkisu ta yi ya yaƙi kamfen ɗin Saifuddeen.

A ɗaukaka ƙara da aka yi, an yankewa Mr Lamara Damana hukuncin zaman gidan yari har ƙarshen rayuwarsa. Sauran muƙarrabansa da aka rafka kuwa wasun su sun samu shekaru bakwai wasu kuma shekaru sha huɗu a gidan yari. Mr Paul kaɗai ne ya samu hukuncin shekaru ashirin a kurkuku...

Kafin ayi shari'ar Bilkisu Asiya ta baiwa Gwamna shawara dan haka shi da iyalinsa har ma da Mahirah dake Sudan suka tattara suka tafi ƙasar Gambia ganin 'yanuwan Mahaifinsu na wajen uwa.

Wannan tafiyar ta É—an sanyayawa yaran rai musamman Nana da tafi kowa damuwa da halin da mahaifiyarsu ke ciki. Mahirah kam kullum addu'arta shine Allah ya shiryar da mahaifiyarsu kada ta mutu da tarin laifuffukanta.

Sati biyu suka yi a Gambia kafin nan suka dawo gida. Duk da Asiya tana da labarin hukuncin da aka yankewa Bilkisu da kuma abinda ya biyo bayan hakan bata faÉ—awa Gwamna ba sai da suka dawo.

Sai da suka kwana biyu da dawowa kafin Asiya ta faÉ—a masa. Suma yaran shiru suka yi amma sun riga sun gani a social media tun ranar da suka dawo.

Asiya ce ta musu nasiha akan su kwantar da hankalinsu sannan su dinga yi mata addu'a.

Hukuncin kisa a kaiwa Bilkisu Kachallah amma a gaban Alkalin ta ɓingire da haukar ƙarya wanda yasa aka tsaida hukuncin har sai ta samu lafiya.

Wannan samun lafiyar yaƙi ci ya ƙi cinyewa kuwa dan Bilkisu gwana ce a irin haukar da take yi.

Lokacin da Mahirah zata koma makaranta ita da Nana suka tafi gidan mahaukata inda aka kai mahaifiyarsu. Ba tareda sanin kowa ba suka je. Sun je ne su mata nasiha amma kalaman da suka dinga fitowa daga bakin mahaifiyar su ya kashe musu jiki. Ko dai da gaske mahaifiyar su ta haukace ko kuma dai mahaifiyarsu tayi nisan da ba zata ji kira ba.
Nana ta sha kuka amma Mahirah gagara kukan ta yi, ta dinga lallashin yayarta akan su cigaba da yiwa mahaifiyarsu addu'a kawai.

"Na kusa fita daga wannan gida. Kar ku damu a zaɓen bana ni zan lashe zaɓe. Mommynku zata zamo Gwamna mace ta farko a jihar nan. Zaku gani. Amma kafin nan ku gayawa party Chairman idan ya fitar dani daga nan zan bashi 99% na dukkan abinda na tara"

"Nana, ki gaya masa kin ji?" Ta faɗa lokacin da yaran suka miƙe suna shirin tafiya.

Har suka fito daga gidan Nana bata bar kuka ba. Itama Mahiran sai da suka fito ta fara hawaye.

***

"Asya miƙo min hula" Gwamna Saifuddeen Kachallah kenan daya fito daga ɗakinsa yana ƙoƙarin gyara babbar rigansa.

Asiya ta fito daga É—aki hannunta É—auke da hula tabi bayansa. A tsakiyar falo ta same shi ta saka masa hular.

"Kayi kyau"

Ya É—an ja hannunta ya manna mata kiss a goshi yace " Ki min addu'a"

Ta riƙe goshinsa ta fara karanto masa addu'o'in tsari. Da ta gama ya ɗan sunkuyar da kansa dai dai cikinta ya manna mata kiss a wajen, ya shafa cikin yace " Daddy zai je taron rufe kamfen ka masa addu'a"

"Macece fa" Asiya ta faÉ—a tana murmushi.

"Ni na san Sa'ad Junior zai dawo Insha Allah"
Chapter 46 · 0% Book details