← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 48

Sashe 16

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya ta shiga banɗaki ta fito masa da buta da kuma empty bucket. Ta gyara masa zama dan ya samu yai alwala da kyau. Yana cikin yin alwalar Bilkisu ta shigo ɗakin. Ta zauna gefen Gwamna tana tattaɓa jikinsa tareda tambayarsa inda ke masa ciwo yanzu.

Asiya ta miƙe ta shumfiɗa sallaya ta ƙariso wajen Gwamna ta fara ƙoƙarin cire masa drip.

"Are you mad! Kina son kashe shi ne?" Bilkisu ta daka mata tsawa

"Ruwa na biyu kenan da aka sa masa, tunda ya samu ƙarfin jiki inaga sallah ya dace yai"

"You must be very stupid. Waye ya baki izinin zaɓa masa abinda ya dace da shi"

Asiya ta harzuƙa amma sai ta tuno karatunta nan da nan ta karya harshe ta ce "Mrs First Lady Gwamna da kansa ya buƙaci na cire masa ruwan zai yi sallah"

Bilkisu ta kalli Gwamna sannan ta kalli Asiya.

"Idan kina ganin ba shi da ƙarfi har yanzu, musulunci ya bashi damar yin sallah a zaune"

A zaunen yai sallah yayinda duka mata biyun suka bishi da ido kowa na kitsa abubuwa a ranta.
A ɓangaren Asiya tana tunanin fitar da Gwamna waje dan a duba lafiyarsa. Ita kuma Bilkisu tana kitsa yadda za ta takawa Asiya birki ta ke.

Wunin ranan Asiya tayi shi ne tareda Gwamna tana nuna masa kulawa da soyayya. Da yamma Bilkisu ta zo wai zata tafi da shi chan gidan Gwamnati. Asiya tace bata san zance ba, Likita yace Gwamna yana buƙatar hutu.

"Kar ki ga kin je National Institute ki nemi nuna min iko a gidana. Only Bilkisu rules here, kuma na ce ba zai zauna a nan ba"

Asiya ta yi murmushi ta ce " na san Likita ya miki bayanin halin da Gwamna yake ciki idan kina son lafiyarsa, the best thing shine ki bar shi a nan ya samu hutu"

"The Governor stays with me" daga haka ta juya ta tafi.

Washegari kuma Asiya ta bita chan gidan Gwamnati dan ta duba lafiyar Gwamna tareda yiwa Bilkisu maganar fita da shi ƙasar waje. Bilkisu ta ƙeƙasa ƙasa tace bata san zance ba infact cewa ta yi bata yarda Asiya ta sake takowa Government house ba ta tsaya a ɗaya gidan. Asiya za ta yi magana Bilkisu ta kira bodyguards ɗinta Vayentha da Mistika ta ce su raka Asiya waje.

"Kada ki taɓa bari maƙiyinki ya san fiskarki balle har ya gane manufar ki a kansa" maganar Madam Chess da ta tuna ya sa ta haƙura ta fice daga gidan ba tareda ta yi gardama ba...

13

"Kina ganin abinda kika shirya shine dai dai?"

"Tabbas kuwa ba zan bari ta tafi da Gwamna ba. She's planning something"

"Amma ba kya ganin Gwamna yana buƙatar ganin Likita"

"Zai ga Likita a nan Nigeria, za mu shigo da ƙwararren Likita idan akwai buƙatar hakan"

"Shikenan Boss, duk abinda kika ce ahi shi za a yi"

Bayan tafiyar M Sani, Bilkisu ta zauna tana juyayin abinda Asiya ta faÉ—a. Wato so ta ke ta tafi da shi ta nema masa magani. Babu wanda ya isa ya É—auke mata Saifuddeen, ita kaÉ—ai za ta juya shi, ita kaÉ—ai.

Da wannan ta rufe batun a ranta.

***

A bangaren Asiya kuwa ta fara gabatar da duk wani shiri na tafiyar su, idan yaƙi ma za a yi to sai dai a yi amma dole ne ta je a duba lafiyar Gwamna. Ba asiri ne kawai ke cin sa ba har da damuwar ƙwaƙwalwa, yana buƙatar ganin ƙwararren Likita.

Ta fito kenan daga ɗaki ta samu saƙon Chief of Staff a wayarta.
Dan haka kafin ta fara zuwa chan Kachallah house sai ta wuce inda ya ce su haÉ—u.
Tana zuwa gidan aka wangale mata gate ta shiga. Bayan ta fito daga motarta wani bodyguard ya mata jagora zuwa inda Lamara Damana ke zaune a wajen gazebo yana hutawa.

"Your excellency" ya faɗa fiskarsa ɗauke da murmushi yana miƙewa tareda nuna mata wajen zama.

Asiya ta zauna ta kalmashe ƙafarta ta haɗe rai ta ce " a wani dalilin kake son mu haɗu?"

"Haba Excellency ko ruwa kya sha ai"

"Ban zo nan dan na sha ruwa ba, ka faɗi maganar ka bana son ɓoye-ɓoye"

COS ya kurɓi giya kaɗan sannan ya ce
"Idan kina son ganin bayan Bilkisu Kachallah za ki buƙaci taimakona"

Asiya ta fashe da dariya mai kama da ta renin hankali.

"Waya gaya maka ina son ganin bayan Bilkisu Kachallah? Gaskiya ka chanja tunani"

"Hajiya Asiya ke kan ki kin san na san mi ya kai ki Kuru"
Ya É—an yi shiru yana nazarinta sannan ya cigaba "REVENGE, kin tafi chan ne saboda kina son É—aukan fansa. Wannan ne dalilin da ya sa ban faÉ—awa Bilkisu ainihin inda kika je ba don na san daga airport na Congo jirgin Jos kika shiga ba ta zuwa Abuja ba balle ki shiga ta tafiya New York"

"You are getting it wrong Mr Lamara, Revenge sai ka ce a film. Abinda ya kaini Kuru shine KARATU"

Ya gane sarai ta fahimce shi, rainin hankali ne kawai da dabara kuma indai wannan za ta nuna masa to shi ya taka ta a irin hakan

"Ina da evidence da za ki yi amfani da shi wajen tura Bilkisu Kachallah kurkuku cikin sauƙi"

Asiya ta juya maganar da cewa " na É—auka za ka taimaka min ne wajen samun lafiyar Gwamna amma tunda wani tatsuniya kake faÉ—a gara na tafi dan ina da abinyi"

"Kina so ki ce kin damu da samun lafiyar Gwamna amma ba ki damu da ganin ƙarshen Bilkisu Kachallah ba?"

Asiya ta saka baƙin glass a idonta sannan ta ce " ba abinda zan yi da ƙarshen Bilkisu Kachallah. Abu ɗaya ke dictionary ɗina, samun lafiyar mijina"

Bayan tafiyar Asiya Chief of Staff Lamara Damana ya ɗau champagne cup ya kwankwaɗi sauran giyan da ke cikinsa sannan ya fito da tabar sigari mai kauri irin wanda manyan mutane ke sha ya sa a baki sannan ya saka mata wuta ya shaƙi hayaƙinta ya furzar ta gefen baki. A fili ya furta "so you are playing hard to get huh"

***

A chan Kachallah house kuwa Asiya da Halimah Kachallah ne suka baza koli a É—akin Haliman. Kayayyaki ne A barbaje akan gado Halima na nunawa Asiya.

"In-law cikin peach gown da pink É—in nan wanne zai tafi da kalar fatata?"

"Anty Halimah duk biyu babu wanda ba zai je ba"

"Kai In-law ba dan ki tayani zaɓe na kira ki ba. Tun ɗazu sai rawar ido na ke kin ƙi ki sa min baki. Anty Asiya kefa fashion diva ce "

"Kiyi haƙuri Anty Halimah. Gaba ɗaya raina ne a dagule. Bilkisu tana son hana ni fita da Gwamna"

"Ba dole ta hana ba, tana tunanin honeymoon za ku je"

"Kai! Anty Halimah"

Halima ta sa dariya. Itama Asiyar ta yi ƙoƙarin danne damuwarta ta shiga yin dariyar.

Duk da tata matsalar da take ciki hakan bai hanata jin tausayin Halimah Kachallah ba. Finally ta kusa shiga gidan miji. Tunda Asiya ta saita tsakaninsu da Yaya Bello lokacin da aka sakota daga kurkuku Halimah ta saka buri a ranta cewa kafin ta clocking thirty six zata shiga gidan miji to yanzu saura wata huÉ—u kuma an saka auren na su zuwa wata biyu masu zuwa. Duk bidirin da ake yi Bilkisu bata da sani a kai domin tunda Halimah ta yiwa Alhaji
Sani maganar saurayinta zai turo ya haÉ—ata da Kawunsa akan ta tura su wajensa dan bashi da lokaci. Ta ji zafin abinda ya mata amma ta share dan farin cikinta ya mamaye duk wani kayan haushi da za a yi a gidan, balle ta riga ta kwana da sanin Mahaifinsu ya koma sai abinda mai girma Bilkisu ta faÉ—a...

Kwana biyu ya rage su tafi Gwamna ya kira Asiya yace mata ta dakatar da duk wani shiri da take don babu inda zai je ya riga ya samu lafiya. Maganarsa ya matuƙar kaɗata dan a iya maganar da su ka yi da shi ba shi da matsala da tafiyar da take shirya musu.

Ta ji a ranta ta je ta samu Bilkisu ta nuna mata ta san mi yake faruwa amma sai wata zuciyar ta gargaÉ—eta akan hakan domin akwai sauran rina a kaba, sai kawai ta fara tsara yadda za a sato mata Gwamna ranan da za su yi tafiyar.

Ana gobe ne tafiyar da Asiya ta shirya Gwamna da First Lady suka karɓi baƙuncin party chairman wanda ya zo ne takanas saboda abinda ya faru kwanan baya. Jam'iyyarsu tana fushi da ayyukan Gwamna a jihar, kuma sun yi Allah wadarai da abinda ya faru da shi a ƙaramar hukumar Boyo.

Da ke zuwan na bazata ne a tsanake Bilkisu ta shiga ƙoƙarin shiryawa party Chairman liyafar girmamawa.
A wajen liyafar Chairman Alhaji Ado Lawali ya taɓo batun abinda ya faru a Boyo tareda kawo suggestion na yadda za a yi maganin abin musamman saboda an fara zagin jam'iyyarsu gaba ɗaya har matasa suna iƙirarin zaɓe na gaba ba za su dangwalawa duk wani ɗan takara daya fito daga jam'iyyar ba.

Maganar Boyo ya saka Gwamna cikin damuwa, ƙwaƙwalwarsa ta ɗau chaji tana tuno masa duk abinda ya faru a wannan rana. Yana tsaye a wajen suka ga ya dafe kansa yana ƙoƙarin jan numfashi da ƙyar kafin chairman ya ankara Gwamna ya sake jiki ya faɗi ƙasa. Hankalin Bilkisu yai ƙololuwar tashi ta yi kansa da gudu tana kiran sunansa a birkice. Ƙoƙarin neman inhaler ta ke a jikinsa ta rasa lokacin da ta samu kuwa ta kama matsawa da ƙarfi amma inaaa tuni Gwamna ya suma.

"Saifuddeen ka tashi kar ka mutu. Ka tashi please. Look at me, ka tashi, ka tashi na ce"

Da ƙyar aka janyeta daga jikinsa aka fice da shi ruwa ruwa daga ɗakin taro.
Kafin kace me gaba ɗaya gari ya ɗauka cewa Gwamna Saifuddeen yana asibiti rai a hannun Allah. Wasu na yi masa addu'a, wasu na Allah shi ƙara, wasu sun yi shiru suna tunanin mi zai faru idan Gwamna ya mutu.
Chapter 16 · 0% Book details