Sashe 22
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baka ma damu da mutuwar É—ana ba. Kai damuwar ka shine kayi abinda ranka yake so, oh! Na manta. Abinda tsinanniyar nan ke so.
"Well let me tell you this Saifuddeen. Ba zaka tozartani ba, sannan ka tozarta mahaifina daya buɗe maka ƙofar shiga siyasa. Idan kana tunanin zaka samu zaman lafiya a kujerar ka to ka sake tunani"
Matsowa tayi daf da shi ta sa yatsarta manuniya dai-dai ƙirjinsa tace "Na rantse maka Saifuddeen sai kayi dana sanin zama Gwamna a jihar nan, na rantse sai ka ƙwammace baka taɓa amsa sunan Gwamna ba. Na rantse maka ni Bilkisu Sani Kachallah sai na maida ka ba kowa ba a wannan jaha, duk abubuwan da ka ƙwacemin tun ina ƙarama sai na ƙwace su a hannunka"
"Mi kike nufi Bilkisu?"
"Kar ka damu Mr Governor, da sannu zaka fahimci komai"
Juyawa ta yi zata bar É—akin ya kira sunanta "Bilkisu!"
A ƙasaice ta juyar da wuyanta ba tare da ta amsa ba.
" Idan kina tunanin na manta da cewa macijin ki ne ya kashe min ɗa, to ki sani ina sane da komai, kuma ba zan taɓa yafe miki ba"
"Wannan kuma kai ta shafa"
Bilkisu ta fice daga ɗakin ta bar Gwamna tsaye yana huci, ƙarshe kuma numfashinsa ya fara ƙoƙarin sarƙewa da ƙyar ya lalumo inhaler ya shaƙa.
Wannan dare ya buɗe wani sabon babi a rayuwar auren Saifuddeen da Bilkisu. Kowannensu ya kwana ne da yaƙinin ba zai taɓa bari abinda ɗanuwansa ke iƙirari ya faru ba...
***
Meeting na gaggawa Bilkisu Kachallah ta shirya a gidanta. Wannan ne zama na farko da za ta yi tun bayan rasuwan Junior. Tun da aka yi rasuwan babu wanda ta gana da shi cikin muƙarrabenta, hatta COS ma waya kawai suka yi sau biyu.
An buɗe meeting ɗin ne da maganar sauke kwamishinoni da aka yi da kuma resigning da Mr Paul yai. Duk wani muƙami da yake da daraja an cike ne da mutanen Gwamna wanda hakan bai yiwa kowa daɗi ba.
"Ina shi Mr Paul É—in?" Bilkisu ta tambaya bayan COS ya gama bayaninsa.
"Yace zai zo" M Sani ya amsa mata.
Bayan ta gama jin duk wani ƙorafi da shawarwari sannan ta fara magana, dai-dai nan ne kuma Mr Paul ya shigo falon.
Mr Paul yana zama yace " gentlemen, ban ga dalilin da zai sa a kira ni wannan zaman ba. I am no longer the commissioner of finance. Lokacin dana dage akan incompetency na Saifuddeen babu wanda ya goyi bayana, yanzu ga irinta nan"
Ya duba ilahirin falon bai ga Alhaji Sani Kachallah ba yace "yau ina Alhaji Sani da ke kukan ana so a hana É—ansa zama Gwamna shekaru biyu baya"
Ya kalli Bilkisu ido cikin ido yace " na ji ance hana shi sarautar sarki da Gwamna yai ya sa mishi ciwon damuwa. Ku yi saurin kai shi psychiatric fa, depression is real you know"
"Mr Paul! " COS ya daka tsawa
"Mafita muke nema anan ba izgili ko cin mutunci ba"
"Oh really! To ai babu amfanin zama na a nan domin na riga na nemawa kaina mafita. Zaɓe mai zuwa ina tareda Umaru Kwom, untill then na barku lafiya"
Yana miƙewa Bilkisu tace " ka cewa iyalinka su tanadi akwatin gawa kafin kwana bakwai"
Mr Paul ya juyo a firgice
"Mi hakan ke nufi?"
Wata ƙaramar dariya Bilkisu tayi sannan ta miƙe tsaye tace " duk wanda yai ƙoƙarin cin amanata ba zai wuce kwana bakwai a doron ƙasa ba. Wannan shine hukuncin mai cin amanar alƙawarin jini"
Ɗaga wata takarda da ta yi sama yasa kowa a wajen ya waro ido waje daga nan kuma aka fara kallon-kallo. Tabbas takardar yarjejeniya ce da aka rubuta kuma kowa ya sanya hannu da jininsa kusan shekara ɗaya daya wuce. A ranan da suka yi abin Bilkisu ce ta basu wata ƙaramar allura kowa ya chaki babbar yatsarsa da shi sai da jini ya fito.
"Idan kun ga dama ku chanja jam'iyya idan kun ga dama ku gudu ku bar ƙasar, amma ku sani duk wanda ya ci amanata ni Bilkisu Sani Kachallah to ya sani ya shirya sallama ne da duniya"
Tsit falon yai na kusan minti É—aya kafin Bilkisu ta kalli COS tace "ina so a kashe Project tomatonion, ya za ayi?"...
18
***
Wani shiri aka fitar daga ofishin Kwamishinan noma da raya karkara, wato PROJECT TOMATONION kamar yadda aka saka wa shirin. Kowa a cikin jahar ya baza ido don ganin yadda wannan shiri zai kawo cigaba wa jihar kamar yadda Kwamishinan da matar Gwamna Asiya Kachallah suka yi iƙirari. Ganin cewa shirin ya maida hankali kan ƙananan manoma dake ƙauyuka da karkara sai ya zamto mutane da dama na zuwa ƙauyukansu dan su yi rajista su amshi tallafi na kuɗi da taki da gwamnati ke son bayarwa. Aksarin mutane dake shirin karɓan tallafin dan aljihunsu suke yi amma ba wai dan farfaɗo da arziƙin noma ba. Sai dai daf da za a fara raba tallafin aka kawo wani tsari wanda zai tantance masu gaskiya da kuma manoman bogi.
Wasu saboda tsaurin tsarin yasa dole suka yi amanna da cewa zasu gwada sa'arsu wajen noman da gwamnati ke son ayi.
Yiyuwar wannan shiri ya rataya ne kwacokam a wuyan Asiya shiyasa ta duƙufa sosai wajen ganin cewa ba a yi magu-magu a shirin ba.
Alhamdulillahi kuma har aka gama raba tallafin kuÉ—i da taki dama iri ba a samu wata babbar matsala da zata jawo wani cikas a shirin ba.
Kusan sati uku Asiya ta ɗauka tana zirga -zirgan yawo garuruwa da ƙauyuka abin sai ya dawo kamar wani sabon kamfen. Mutane da dama sun gano manufarta amma sai suke ganin kamar ba zai yiwu ba musamman daya ke har yanzu akwai ɗan matsalolin tsaro dake kutsowa jahar kaɗan-kaɗan. Bayan duk wasu shirye-shirye Asiya ta ƙaddamar da shirin PROJECT-TOMATONION ranan wata Asabat da safiya a ranan ne kuma ta buɗe wani sabon babi a tarihinta na matar Gwamna Saifuddeen Kachallah...
***
Kwanaki biyar kenan da lauching wannan program ɗin. A yau ne kuma Asiya ta shirya zuwa manyar makarantu dake jahar dan gani da ido cewa suma ɗin sun fara wannan Project kaman yadda ya kamata. Sai data gama shiryawa zata fita taji hajijiya na neman kada ita da ƙyar ta samu ta dafa bango, duk da haka sai data kai ƙasa ta zauna kafin ta ji dai-dai. Ta kai minti uku tana riƙe da goshinta.
"Ranki shi daɗe" Badawiyya ta faɗa tareda ƙarasowa wajen da sauri. Taimaka mata tayi ta miƙe tana tambayarta ko lafiya?.
"Hajijiya ne kawai, inaga dan ban karya bane"
"Amma..."
" zan sha magani kafin mu tafi"
Basu tafin ba sai da Badawiyya ta tabbatar ta sha tea da slize biyu na bread sannan ta sha maganin ciwon kai.
Jami'a suka fara zuwa kafin suka wuce kwalejin noma da kuma polytechnic. Manufar ita ce a farfaÉ—o da harkan noma a makarantu. Taya É—alibi zai yi shekara uku zuwa huÉ—u yana karantar harkar noma amma idan ya gama aka bashi gona ba zai iya yin komai ba.
An shigo da Project Tomatonion makarantun ne dan a horar da ɗalibai kan harkan noma, ba wai a iya takarda ba har a aikace. Yawanci makarantun sun yi ƙorafin rashin kayan aiki da kuma lalacewar wasu daga cikin kayan aiki da suke da shi. Kafin a ƙaddamar da shirin duk wasu kayan aiki da suka lalace an gyara sannan akwai magana mai ƙarfi daga ofishin Gwamna kan cewa za a fidda kuɗi domin a siyo sabbin kayan aiki da babu.
"Ina so harkan noma ya samarwa manyan makarantu kuɗin shigowa ta inda zasu iya riƙe kansu koda babu tallafin Gwamnati" abinda Asiya ta gayawa kwamishinan noma da kwamishinan ilimi kenan lokacin da ta nemi sa hannunsu kan tallafawa shirin nata ya kai ga manyan makarantu.
A hanyarsu ta dawowa ne Badawiyya ta taɓo batun kama Madam Bintu da take son yi.
Asiya ta riƙo hannun Badawiyya tace "Idan muka ce zamu kama Madam Bintu yanzu, tafiyar mu ba za ta yi dai-dai ba. Na san a matse kike ki ɗau fansa but trust me Badawiyya, Madam Bintu za ta shiga hannun ki, very soon"
"Shikenan zan yi haƙuri kamar yadda kika ce"
"Nagode da kika fahimceni Badawiyya. Da yardar Allah komai zai tafi kamar yadda muka tsara "...
*
Asiya tana shiga babban falon gidan ta tarar da Bilkisu tana surfawa Mahirah masifa hannunta riƙe da wasu takardu.
"I'm very disappointed in you Mahirah. Malamar Islamiyya kike son zama?. Listen to me young lady ba a gidan nan zaki je Sudan ki karanto shirme ba. Ki gyara shirin ki da kyau yarinya you are going to Harvard ko kuma Yale"
"Mommy dan Allah ki saurareni, course É—in da nake son karantawa kenan..."
"Idan kika sake magana zan mare ki. Bari ma ki ga" ta kama takardan admission letter É—in ta yaga shi gida huÉ—u sannan ta watsar da shi. Ko kallon Mahirah bata sake yi ba ta haura sama.
A hankali Asiya ta ƙaraso gaban Mahirah ta riƙeta.
"Anty dan Allah ki saka baki, Daddy yace bazan yi karatu a ƙasar waje ba Mommy kuma tace bazan je Sudan ba dan kawai zan karanta Islamic Jurisprudence"
"Yaushe Excellency yace ba zaki tafi Sudan ba?"
"Bayan rasuwan Junior dana mishi magana akan na samu admission a Sudan shine yace wai a nan Congo zan yi karatu" ta ƙarisa maganar tana sheshsheƙan kuka.
"Ki dena kuka zan gwada yi masa magana. Sai ki dage da addu'a kinji"
Mahirah ta gyaÉ—a kai tana faman goge hawaye.
Asiya na shiga É—aki ta rage kayan jikinta ta wuce banÉ—aki ta É—auro alwala, tayi mamakin ganin har yanzu jini bai zo mata ba. Tun jiya take tsammanin ganin jini amma har yanzu shiru. Kwana biyar baya ta É—an ga spotting na jini a underwear É—inta, da farko ma tayi tunanin ko period É—in ne yazo da wuri sai daga baya kuma taji shiru ba komai.
Bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar wani tunanin ya faÉ—o mata. Ko dai ciki gareta ne?...