← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 48

Sashe 11

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma Muhammad ka min laifi, kana garin nan tun last month amma ba za ka zo ka gaishe ni ba"

"Your Excellency ai yanzu ganin ki ya fi ganin Gwamna. Kin san sau nawa ina zuwa government house ba kya nan"

"Sorry son, na manta ranan Mahirah ta gaya min ka zo"

"Kin yarda kin fi Gwamna kenan" M Sani yai maganar yana murmushi.

"Duk abunda mu ke ai don Gwamna É—in ne"

"I see"

Shiru ne ya biyu bayan haka sai takardu da Bilkisu ke ta flipping cikin sauri da alama ba ta ga abinda ta ke nema ba.

"Excellency I want to join politics"

Bilkisu ta dakatar da abin da ta ke ta zuba masa ido.

"Tun Baba na da rai na ke son miki magana amma Mommy ta hana shiyasa na yi shiru da zancen"

"Yanzu Rufaidan ta yarda kenan?"

M Sani ya girgiza kai

"Then?"

"Na riga na deciding zan shiga ko tana so ko bata so"

Bilkisu ta yi murmushi har sai da haƙoranta su ka bayyana. Ta hango dogon buri a idon ɗan 'yaruwarta, kuma lallai idan ta tallafa masa akan burinsa za ta samu mataimaki na jini.

"Babana ka je ka yi tunani ka san ba a jayayya da iyaye"

"Haba Excellency, i'm an adult ina da damar da zan yi duk abinda na ga dama ko iyaye na suna so ko basa so"

"Babana lallai ka girma"

"commisioner M Sani at your service Boss"

Bilkisu Kachallah ta bushe da dariya harda buga table. Tabbas dole ta jawo M Sani jikinta domin irin dakakkiyar zuciyar da ta ke so kenan.

***

Lokacin da Asiya ta shirya tafiya Umurah Bilkisu ba ta ji wani É—ar ba dan ta riga ta sa an mata bincike kuma tabbas babu hannun Gwamna a tafiyar da kuÉ—inta ta biya kuÉ—in jirgi.
Abu É—aya ne ya ke damunta shine shirun da Asiya ta yi ta bibiyi komai na ta amma bata ga alamar tana yin wani abu akan abinda ya faru ba tunda dai yanzu kam kowa ya san kowa.

Lokacin da Asiya ta wuce Saudiyya kuwa sai Bilkisu ta tarkata hankalinta ta maida shi kan batun tsige Mai martaba Sarki sai dai kuma har yanzu dai abun bai yiwu ba. Ta rasa gane kan al'amarin Gwamna, a wasu abubuwan baya mata gardama, amma wani batun idan ta masa sai ta ga ya yi shiru ya ƙi aiwatar da abinda ta ce. Ta sa a ranta da ta samu sarari za ta je India a bibiyi ƙarfin aikin da aka mata.

Ranan da Asiya ta dawo Nigeria ba ta wuce jihar Congo ba sai ta wuce NIPSS da ke Jos. Tun kafin ta tafi Saudiyya CY yai mata maganar makarantar tareda kwaɗaita mata samun nasara akan burinta na yaƙar Bilkisu matuƙar ta samu shiga wannan makaranta. Lokacin da ta yi bincike akan makarantar sai ta ga ba ta da ko ɗaya daga cikin requirement na su, asali ma ita ɗin bata chanchanci ta shiga makarantar ba saboda tsaurinsa. Babu yadda za ayi a nominating ɗinta bata kai shekara arba'in ba sannan bata taka wani matsayi ba a rayuwarta.

Sai dai bata san ya aka yi CY ya samu shigar da ita wannan makaranta ba har ta kai board of governors sun nominating É—in ta.

Lokacin da ta je gaban board of directors ta sha mamakin ganin mutumin da ba ta taɓa tsammani za ta gani a wajen ba.
Ta tambayi CY kafin ta zo kuma ya tabbatar mata da cewa babu sunan Gwamna Saifuddeen a cikin board of directors na makarantan amma kuma sai ga shi zaune cikin su.

Da ƙyar ta iya saita nitsuwarta lokacin da ta tsaya gaban su tana amsa tambayoyi. Kusan kowa ya mata tambaya a wajen amma banda shi, asalima bai maida hankalinsa kan ta ba sai kawai ya duƙar da kai yana ta rubuce-rubuce.

Minti talatin da takwas ta yi a wajen ta fito daga hall É—in a ruÉ—e. Ba dai Gwamna zai hana a bata admission ba.

Bayan ta samu waje ta zauna ta kira CY yana É—auka ta ce " CY kana son kashe min aure ne?"

Daga ɓangarensa yai shiru saboda maganar ta masa dirar mikiya.
Yana son Asiya, zai iya rantsewa ya fi Gwamna son Asiya. Tsananin soyayyar da ya ke mata ya sa shi nema mata wannan makaranta ta hanyar mahaifiyarsa, don ya tabbata idan Asiya ta yi National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) za ta samu makamin ya ƙi da Bilkisu Kachallah. Asiya is far from an eligible candidate a makarantar. Makarantar da sai manyan 'yan siyasa ko 'yan kasuwa ke shigarta, makarantar da ko malami sai ya kai matsayin professor ko associate professor kafin a iya bashi admission. Makarantar da idan ba ka kai shekaru arba'in bama ba za a kalleka ba balle a saurareka. But he boycott all this for her.

"CY kana jina? Ka ce babu sunansa a cikinsu kuma gashi nan na gan shi a wajen"

A ruÉ—e CY ya shiga ba ta amsa " i'm sorry Asiya. Babu sunansa a cikin sunayen da Mommy ta turo min shiyasa na gaya miki baya ciki"

"Shikenan, inaga tunda ya ganni ba zai yarda ma su bani admission ba"

"I'm truly sorry Asiya"

"Shikenan ya wuce CY"

Asiya ta katse wayar tana sauke ajiyar zuciya.

***

Sati biyu bayan dawowarta daga Saudiyya aka turo mata admission letter ta email. Ta yi murna sosai dan kuwa ta cire rai da samun gurbin karatu saboda Gwamna ya ƙi mata maganar zuwanta Kuru a Jos.

Lokacin da ta fitar da admission letter É—in har É—akinsa ta same shi ta masa maganar tafiya makarantar...

Ba su rabu ta daÉ—i ba shiyasa ko sallama ba ta masa ba ranan da ta tattara kayanta ta tafi.
Shiri ne na musamman ta yi dan haka ta samu Bilkisu a falo ta sanar da ita cewa za ta tafi yin masters É—inta a Stanford University tana mata albishir da ta ci karanta ba babbaka dan ita kam karatu ne a gabanta.

Bilkisu ta mata fatan nasara. Ta riga ta samu tabbaci daga COS akan da gaske ne Asiya ta samu gurbin karatu a Stanford dan har kwafin admission letter É—in ya kawo mata. Abinda bata sani ba shine takardar na bogi ne da CY yai ya bawa Asiya a matsayin shaidar tafiyarta Stanford.

Wannan rabuwa yai wa Asiya ciwo domin tafiya ce za ta yi ba tareda ta waiwayi gida ba har na wata goma ba wai dan babu hali ba sai don tana son ta samu nitsuwa wajen yin abinda ya kaita da kuma sauran bincike da ta ke yi ta ƙarƙashin ƙasa.

Ta damƙa amanar ƙannenta a hannun Abba wanda tun dawowarta daga prison ma ba su koma da zama wajenta ba, sun dai zo mata hutu na kusan sati ɗaya daga nan suka koma gidan Abba da zama.

Wani abu daya tsayawa Asiya a rai har ta tafi shine furucin Gwamna a kanta. Zarginta da ya ke da CY kwata-kwata bai kama hankali ba...

09

***

Idan akwai ƙuncin rayuwa, to kuwa ƙofofin ta'addanci da fitintinu suna buɗuwa. Watanni shida kenan da fara shugabancin Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah bayan ya lashe zaɓen jihar Congo. Abubuwan da ake gani za su yi sauƙi sai kuma komai ya fara taɓarɓarewa. Wata uku babu albashi ga shi babu wani major aiki da aka fara. Ba a ɗauki aiki ba sai ma dakatar da ma'aikata da aka dinga yi saboda verification na ma'aikata da Gwamna ya ƙirƙiro .
Da za ayi Verification ɗin tsakani da Allah to akwai macuta dayawa da za a zaƙulo waje, amma su masu cutan sai ka ga an clearing na su, amma masu gaskiyan sai abin yake ta shafansu fiye da ainihin macutan.

Cikin 'yan kwanakin nan anyi fashi a babbar hanyar da ta sada jihar Congo da jihohin Kano da Bauchi kusan sau biyar, kuma duk fashin da aka yi sai an samu salwantar rayuwa. A cikin jaha kuwa yara 'yan shaye-shaye sun addabi mutane da sace-sace na cikin gida. Kowa yanzu yana taka tsantsan ne da gidan sa, wasu har karnuka suka dinga siya suna ajiyewa a gida saboda gadi, dan abin ya kai halin ha'ula'i.
Kaza nan nan bata isa ta yi nisa da ƙofar gida ba, dan tana shiga lungu to babu fitowa kenan.

Ana cikin wannan matsi kuma aka sake shigo da harkan kidnapping. An fara da É—aukan wani tsohon Kansila ne, wanda bayan an biya kuÉ—in fansa sai gawar sa aka sako musu.
Cikin watanni biyu an sace magidanta da ma matasa sama da arba'in, wannan abu ya sake tunzura mutane, aka shiga Allah wadai da mulkin SSK. Abinda a ke ji yana faruwa a wasu jahahohi nesa da su sai ga shi an fara a kusa da su.

A 'yan kwanakin nan kuma maganar tsige Sarki da ake son yi ne ya saka wasu mutane yin zanga-zanga a cikin jahar. Maganar bata gama tabbata ba, amma ƙishin-ƙishin da ake ji shine an fara maganar a state house of assembly. Babu makawa idan aka tsige Sarki kowa ya sani cewa Alhaji Sani Kachallah za a ɗaura a kujerar mulki tunda shima sarautar gidan su ce. Wannan son zuciya da ake son yi ya sake ɗarsawa mutane ƙiyayyar Gwamna Saifuddeen.

***

*National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru*

A wani ɗakin karatu kuwa wata mace ce data amsa suna wayayyiyar mace ta ke dudduba wani littafi da ke gabanta, matar sanye ta ke da baƙar jacket da ya kai mata gwiwa, tana sanye da pencil jeans, sai rigar ciki da ta saka kalar ruwan goro, ta yi rolling da gyale shima ruwan goro. Akwai manya manyan bangles a hannunta ruwan ƙasa sai kuma zobben azurfa guda biyu da ke yatsarta na uku dana huɗu a hannunta na dama . Minti biyar kenan da gama lectures da aka yi mu su yau, kuma Alhamdulillah ta ƙaru da abubuwa sosai a wannan lecture da aka yi akan maudu'i mai taken Shugabanci.
Chapter 11 · 0% Book details