← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 48

Sashe 42

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Minti biyar da zuwanta gidan kurkukun aka turo mata Alhaji Sani Kachallah, gashi cikin kayan fursuna abin tausayi.
Ta ƙura masa ido babu ko ƙyaftawa. Ya yi baƙi da shi, timbinsa ya motse ya koma ciki. Idanuwansa sun yi wani rami kamar a saka ƙwandala ya zauna a ciki. Duk wani alamu na tsufa da ada jin daɗi da kwanciyar hankali suka ɓoye yanzu sun bayyana.

Kunya ya kamata lokacin da ya ce " ni kam ko zana ni zaki yi ne?. Sai dai kuma ban gan ki da kayan zane ba"

A ladafce ta gaida shi tana tambayar shi ya jiki.

Bayan wani dogon shiru Alhaji Sani ya fara bayani " ina sane da duk abinda yake faruwa, kuma na sa a raina ko ke ko Saifuddeen É—ayan ku zai zo. Ashe kin fishi hankali ma"

"Lah Baba"

"Gaskiya ne ai, ba dan ke ba da tuni sun kashe min shi. Allah ya ƙara miki juriya"

"Amin Baba"

Kafin yai magana tari ya kufce masa, ya jima yana tarin kafin ya samu nitsuwa.

"Sannu Baba. Kana buƙatar likita ne?"

"Hmm kada ki damu Likitan da muke da shi a nan ya duba ni"

"Allah ya ƙara lafiya"
Alhaji Sani ya amsa da Amin.

"Baba maganar tsaro yafi ƙarfin mu fa. Ko dai mu nemi taimakon Gwamnatin tarayya ne?"

"Ina da shawara. Ina da yaƙinin za a iya samun mafita"

Wani tarin ne ya sake kufce masa, wannan karan bai yi dayawa ba tarin ya lafa masa.

Asiya ta dinga yi masa sannu, a lokaci guda kuma tana tuno mafarkin da ta yi...

***

"Mommy ki zo ki ga. Mommy come please"

Bilkisu da ke gaban madubi tana gyara É—aurin É—ankwalinta ta fito daga É—aki da sauri. Yau take so ta samu party Chairman batun form na takarar Gwamnan da za ta siya da zarar an sake shi ranan Monday. Ita take son riga Saifuddeen siya saboda ta samu damar hana Saifuddeen siyan nashi form É—in.

A tsaye ta samu Nana gaban TV ta riƙe baki tana kallon mutumin dake jawabi a gaban 'yan jaridu.

Tun daga kanun labaran da aka karanto Nana ta ƙwalawa mahaifiyarta kira dan sunan mahaifiyarta da ta ji an ambata.

"Minene? Mi munafukin uban naki ke faɗi?" Ta faɗa tana cire ɗankwalin kanta tunda yaƙi ɗauruwa.

"za'a bawa duk wanda ya kama taƙadarin ɗan ta'addar nan Tanko Janwuya naira miliyan ɗari. Wanda ya kawo mana gawarsa kuwa za a bashi kyautar naira miliyan ɗari da hamsin. Haƙiƙa Tanko janwuya ɗan ta'adda ne da Gwamatinmu ta bada damar a nemo shi ko a mace ko a raye.

"Hakanan muna jinjina ga ilahirin hukumomin tsaro da suke aiki dare da rana wajen ganin an kawo zaman lafiya a wannan jiha tamu mai albarka. Ina yiwa jami'an tsaro albishir da cewa duk wanda ya ji rauni ko aka rasa rai a wajen kare rayukan 'yan ƙasa Gwamnatinmu ta ware wani kaso mai tsoka na shi da iyalen shi. Akwai ƙarin alawus mai tsoka ga duk wani jami'in tsaro dake cikin jihar nan. Suma 'yan vigilante ba a barsu a baya ba a wannan alawus da Gwamnati za ta bayar"

Dogon numfashi ya ja wanda ya ratsa microphones dake gabansa ya fito ta talabijin ya daki kunnen Bilkisu kafin kuma maganganunsa na gaba su zamtowa Bilkisu tashin bam da ya tafi da jinta da ganinta na gajeran lokaci.

"Daga yau, shahuɗu ga watan July, ni Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah na sauke matata Bilkisu Sani Kachallah daga duk wani muƙami da take da kai, na ɗauke duk wani walwala da jin daɗi da take samu sakamakon kasancewarta tsohuwar first lady na jihar nan. Ni Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah na hanata fita daga cikin jihar nan har sai Kotu ta wanketa daga zargin da tsohon Chief of Staff na jiha wato Mr Lamara Damana ya jefeta da shi. Za ta zauna a gidansu ta jira sammaci daga Kotu. Daga yau, duk wani ayyuka da ya danganci ofishin Matar Gwamna zai dawo ƙarƙashin iko da kulawar matata Asya Shahidah Faruƙ Kachallah."

Ɗankwalin hannun Bilkisu ya faɗo ƙasa biyo bayan sa hannu da tayi a kai ta kwarma ihu Noooo...

"Ba ka isa ka min haka ba. Ba ka isa ba Saifuddeen, Babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan nan"

Samun waje ta yi ta zauna tana ƙara maimaitawa kanta babu wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan Gwamnati.

Ko minti talatin ba ayi ba wasu jami'ai mata suka shigo gidan biye da su kuma Asiya ce da ta sha baƙin gilashi.

Nana ta gaji da roƙon mahaifiyarta akan ta tashi ta shirya su bar gidan amma ta ƙi, dan haka ta wuce ɗaki ta shiga fidda kayanta a closet tana zuba mata su cikin akwati.

Bilkisu na ganin Asiya tayi kanta kamar za ta shaƙeta securities da suka biyo Asiya suka riƙe ta.

"I'm going to kill you, da hannuna zan kashe ki. Ku sakeni babu inda zan je. Ku sakeni na ce"

Asiya ce ta É—aga musu hannu suka sake Bilkisu. Kallon-kallo suka tsaya yi kowannensu yana kissima abubuwan da zai yi wa É—anuwanshi.
Kamar an tsikareta Bilkisu ta haura sama da gudu.

Nana na tsaka da haÉ—a kayan mahaifiyarta ta ji tsigowarta É—akin. A fusace ta shiga duban wani abu daga cikin kayan nata.

"Mommy" Nana ta faɗa a ɗimauce ganin abinda mahaifiyarta ta ɗauko cikin wani baƙin akwati.
Bilkisu na fita daga ɗakin Nana na bin bayanta tana ƙwala mata kira tareda faɗin kada ta yi abinda za ta yi nadama.

Asiya na nan tsaye a inda ta barta.

"Ba zaki taɓa cin nasara a kaina ba. Ni Bilkisu Kachallah na fi ƙarfin ki"

Ta saita bindiga dai dai goshin Asiya. Suma securities É—in suka saita mata bindiga suna faÉ—in ta ajiye nata bindigar. Wani takaici ya rufeta, waÉ—annan yaran chief securityn Gwamna ne kuma itace ta kawo su wannan gida.

Asiya kam rufe ido tayi tana jiran saukan harsashi dan ko yunƙurin guduwa bata yi ba.

Ƙaran fashewar glass yasa Asiya ta buɗe ido dan ƙaran da ta ji bai yi kama da ta bindiga ba.

Nana ta riƙe kai ta fashe da kuka ganin mahaifiyarta ta faɗi ƙasa jini na zuba.
Wani verse ta É—auka ta rutsawa Bilkisu a ka lokacin da suke sa'insa da securities akan ta ajiye bindigarta.

***

"Yanzu laifina kake gani kenan?"

"I just said it was unnecessary. Kin riga kin san halinta miyasa zaki je inda take a lokacin da take cikin ɓacin rai"

Asiya ta buɗe baki ta rufe dan gaba ɗaya maganarta ya toƙare ne a maƙoshi. Yau da mutuwa Bilkisu ta yi kenan cewa zai yi ita ta kasheta.

"Allah ya baka haƙuri"

Ta faɗa da ɗan ƙarfin daya rage mata.
Bai ce komai ba ya wuce ya barta tsaye cike da tunani...

Kwana ɗaya Bilkisu tayi a asibiti aka sallamota ko kuma ace ta sallami kanta. Duk yadda ta yi dan ta koma gidan Gwamnati hakan bai yiwu ba dan Mahaifiyarta sam ta ƙi yarje mata, dole ta huci zuciyarta suka koma Kachallah house wanda shima gidan ya rasa fasalinsa tun lokacin da aka kama Alhaji Sani.

Ta ci duk wani buri na ɗaukan fansa da kuma lalata lamurran Gwamnatin Saifuddeen sai dai kash, ta kasa samun wayar Tanko Janwuya, shima yanzu ta kansa yake dan jami'an tsaro sun tasanmai haiƙan, kutsa kai kawai suke yi cikin ƙauyukan daya mamaye suna kashe muƙarrabansa.

Party Chairman ma ya dena ɗaukar wayarta tayi kiran, tayi text amma duka babu amsa. Duk lokacin da ta yi yunƙurin fita daga gidansu sai jami'an tsaro dake tsare da gidan su hanata.
FaÉ—a take da kowa a gidan, ta zama tamkar wata zararriya sabon kamu. Mahaifiyarta kaÉ—ai ke iya yi mata magana wani lokaci ta ji wani lokaci kuwa ta daka mata tsawa.

Duk wasu sources É—inta ta kira amma kowannensu ta kansa yake. Babu wanda zai so a haÉ—a shi da tuhumar da ake mata.

*

A yau Asabat ne kuma aka wayi gari da labarin heart attack da Alhaji Sani ya samu a gidan yari. Daga Asibitin gidan kurkuku aka wuce da shi Teaching Hospital.

Kan Gwamna Saifuddeen ya É—au zafi, musamman daya je ya ga halinda Baban nasa ya shiga.
Tabbas yana buƙatar kulawa ta musamman kuma indai za a sake mayar da shi gidan kurkuku ne to bare taɓa samun sauƙi ba.

Matsawa masu kula da shari'ar ɗaukaka ƙarar Alhaji Sani yai dan shi hankalinsa ya bar kan maganar Bilkisu ya koma ta samun lafiya da kuma 'yancin Baban sa.
Ba zai yafewa kansa ba idan Alhaji Sani ya mutu a kurkuku. Idan har shari'ar ba za tayi daÉ—i ba gara kawai yai amfani da damarsa yai wa Alhaji Sani afuwa ya granting na shi state pardon.

A wani zuwa da ya yi gaishe da Alhaji Sani sai da ya zubda hawaye, ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.

"Ka yafe min Saifu. Duk abinda ya faru, duk abinda Bilkisu ta aikata akwai hannuna a ciki. Na gagara yi mata tarbiyyan da ya dace, sannan nayi sakaci da lamurranta har suka lalace haka. Ka yafe min Saifu domin a lokacin dana haɗa ku na sani biyayya ka min ba wai kana sonta ba. Ba dan arziƙin 'ya'ya ba da sai nace nayi dana sanin haɗa ku aure da na yi"

"Baba please"

"Ka bari na faÉ—i abinda ke zuciyata domin ba lallai nayi nisan kwana ba"

"Insha Allahu zaka samu lafiya, sannan za ka samu 'yancinka"

"Na roƙe ka kada ka riƙe auren Bilkisu saboda ni. Idan har ka ji a ranka rabuwarku yafi alkhairi Dan Allah ka sawwaƙa mata. Zan so kayi hakan tun yanzu amma ba zan tursasa maka ba. Ina fata ko bayan raina zaka samu damar yafe mini. Ba zan yiwa Bilkisu baki ba, Ina mata addu'ar shiriya kafin lokaci ya ƙure mata"

Daga haka yai shiru. Sai da Saifuddeen ya miƙe zai tafi sannan yace " ka turo min Asiya"

31
Chapter 42 · 0% Book details