Sashe 39
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi saurin kauda idonta daga yadda ya riƙe mata su da nashi idanun. Kallon tuhuma yake mata ta sani. Ko dai ya ga tabo a jikinta ne wanda ya nuna masa irin yadda Party Chairman ya dinga shigarta kamar wata karya.
So take ta tambayeshi mi yake a falonta ƙarfe goma shaɗaya na dare amma tambayar da ya fito daga bakinta daban.
"Mi kake yi baka yi bacci ba?"
Shima É—in so yake ya tambayeta ina ta je amma ya musanya tambayar da cewa "Gobe za'a sallami Nana daga Rehab ina so na je na É—aukota, zamu biya Sudan wajen Mahira daga nan sai na kawota gida"
Nana, Mahira. 'Ya'yanta fa kenan. Ita É—in fa uwa ce.
*"I Bilkisu Sani Kachallah. Do solemnly swear"*
Ta hango kanta a gaban Alkali ana rantsar da ita.
"Sai da safe" ya faɗa tareda wucewa ta gefenta ya buɗe ƙofa ya fice daga falon. So take ta riƙe shi, tace masa yai haƙuri ta ci amanarsa, amma ta kasa yunƙurin yin komai har ya fita.
Ko jakarta bata ɗauka ba daga inda ta ajiye shi bakin ƙofa haka ta wuce cikin bedroom ɗinta dan ta kwanta ko hakan zai sa ta samu nitsuwa...
Ƙarfe tara na safe ta tashi da bugun ƙofar mai aikinta.
"Waye?" Ta faÉ—a da muryan bacci.
"Safiyya ce Your Excellency"
"Minene?"
"Akwai wasu manyan baƙi suna jiran ki a babban falo"
Bata amsa mata ba ta dafe kanta dake mata ciwo.
Kusan minti arba'in ta ɗauka sannan ta fito shirye cikin wata rantsatstsiyar leshi ja mai duwatsu baƙaƙe.
Ba ta ɗauka baƙin zasu jirata ba amma sai gashi sun zauna jiranta kamar wasu 'yan maula.
" wannan walaƙanci ne Boss, kin san tun yaushe muke jira kuwa" mutumin da ta shaida shi da Alhaji Baffale ya faɗa cikin ɓacin rai.
Da a da ne ko kusa ba zai iya É—aga mata murya ba balle har ya mata tsawa.
Ta samu kujera opposite da su ta zauna.
"Dole ne ku fito mana da matsaya ɗaya, mun gaji da raba mana alƙibla da kuke yi"
"Alhaji Baffale calm down. Idan baka yi magana a nitse ba taya zan fahimce ka"
Sai a sannan É—ayan wanda shima tsohon Kwamishina ne ya fara magana.
"Jiya ba kya gari Lamara Damana yai meeting yana neman mu mara masa baya a zaɓe mai zuwa, yana so jam'iyya ta bashi tiketin zama ɗan takara a Primary election da za a yi nan bada daɗewa ba. Kema kin yi irin wannan magana a ranan da kika yi alƙawarin zaki yi maganin Asiya Kachallah. Wai wanne a cikin ku zamu bi ne?"
Dariya mai ƙarfi Bilkisu ta sake tareda tafa hannu. Lallai kam! dama ance makashinka yana tareda kai.
Lamara Damana yana so ya ci amanarta, ko kuma ma ya riga ya ci amanarta. Sai kuma ta tuna cewa yasan kusan duk wani sirri nata, hakan yasa ta daka tsalle kamar wata zararriya ta wuce cikin É—aki da sauri.
Ko mi ta ɗauko oho, dan bata yiwa baƙin nata magana ba ta fice daga falon. Masu tsaronta dake bakin ƙofa suka bi bayanta cikin sauri.
Kai tsaye gidansa ta wuce dan tanada labari daga wajen Party Chairman cewa mijinta ya sauke chief of staff É—insa.
Kusan babu shamaki tsakaninsu dan haka har ta kai falonsa babu wanda ya hanata shiga. Tana shiga falon ta same shi yana sipping giya a hankali yayinda yake duba wasu takardu.
Wata ƙaramar bindiga ta fito dashi daga cikin jakarta, ta nuna shi da bindigar, zuciyarta cike yake da tsanar Baƙin guntun mutumin dake zaune gabanta.
"Yau zan kashe ka na kashe banza"
"Shin za ki so ki ji batun sirrikanki dana sanar da Asiya ko?"
"Kai baƙin Arne!" ta daka masa tsawa tareda saka hannu biyu ta riƙe bindigar da kyau tana daf da sake harsashin.
Wata mahaukaciyar dariya Lamara Damana ya fara.
"Na yarda ni baƙin Arne ne, ke kuma fah?"
Ya sake fashewa da dariya yace " gara ni mahaifina Bamaguje ne, mahaifiyata kuma a sama ta tsinci addinin Kiristanci, ban taɓa iƙirarin ina bin wani addini ba dan haka abinda kika faɗa yana kan dai-dai"
"Shut up! ko na bindige mummunan bakinka"
"Idan kina so zamu iya haÉ—a hannu ki zama mataimakiyata, at least idan ba ki yi amfani a office ba za ki min amfani a cikin É—aki"
Yawu ta furza masa har lokacin bata sauke bindigar ba, tace " Allah ya kiyaye na zauna a ƙarƙashinka. Ba zaka taɓa samun abinda kake so ba, ni da kaina zan kashe ka"
"Bilkisu kenan, na jima da sanin cewa maganinki ya karye dan haka babu abinda zai sa naji tsoron ki. Ko da yake ya kamata na ji tsoron matar da take ƙoƙarin kashe mijinta saboda kujerarsa"
"Ba kashe Saifuddeen zan yi ba, i will never kill him"
Mr Lamara Damana ya sake bushewa da dariya harda buga ƙafa.
"Hakane. Ba kashe shi zaki yi ba, so kike ya ƙarisa rayuwarsa a kwance. Wannan ma abin dubawa ne"
"Mi ka gayawa Asiya?, mi ka bata?"
"Kiyi tunanin matakin da zata ɗauka idan ta san kina ƙoƙarin kashe mata miji. Af. Na manta ita ɗinma kin yi yunƙurin kasheta ai"
Hannunta ne ya shiga rawa dan lokaci guda wani tsoron Asiya ya shigeta.
Lamara Damana ya cigaba da dariya ko ba komai yau É—aya yaga tsananin tsoro da damuwa a tattare da Bilkisu Kachallah.
29
Tunda Asiya ta ji bayanan Mr Lamara Damana a waya ta rasa sukuni. Duk da ta sani Saifuddeen ya tafi ƙasar America ɗauko 'yarsa amma hakan bai hanata tsorata ba.
Ashe Bilkisu za ta iya tunanin kashe Saifuddeen balle ma har ta yi yunƙurin yin hakan? Lallai kam ta raina hatsabibancin matar nan. Ce mata da ya yi wai hatsarin da ta yi Bilkisu ce ta sa a kasheta bai ɗaga mata hankali ba, amma Saifuddeen. Mijinta ne fa, uban 'ya'yanta. Kai Bilkisu hatsabibiyace.
Sai da ta yi waya da Gwamna kafin hankalinta ya É—an kwanta ta samu damar cigaba da shiga shagalin bikin Badawiyya.
Wani abu daya mata daɗi shine tunda Mr Lamara ya iya gaya mata waɗannan sirrikan kenan abubuwa sun ɓaci tsakaninsu. Dama kuma hakan take so.
Idan Gwamna ya dawo zata gwada masa maganar Bilkisu ko zai amince yai takatsantsan da lamurranta.
***
A ɓangaren Bilkisu kuwa ta rasa ina zata saka ranta ya mata daɗi, duk wasu abubuwanta na shirin kwaɓewa lokaci guda. Idan ta bari aka tsige Saifuddeen kamar yadda ta gayawa Party Chairman, Mr Lamara zai yi amfani da wannan damar ya hanata samun damar zama mataimakiyar Gwamna.
"Ke wawiya ce Bilkisu. Ba kya ganin mi yake son yi ne. So yake a tsige Gwamna shi kuma ya kayar da mataimakin Gwamna a lokacin zaɓen Primary elections sai ya zama shi kaɗai ne ɗan takara mai ƙarfi a jam'iyya"
Ta riƙe kai tana furzar da iska lokaci guda kuma jikinta ya shiga ɓari. Tayi saurin jawo wasu ƙwayoyi dake cikin purse ɗinta ta watsa bakinta.
Duk wani namiji ta tsane shi. Su maza basu da amana ko kaÉ—an. "Mi zan yi? mi zan yi?" Ta fara tambayar kanta kamar wata zararriya.
"Ki zama Asiya" wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsa.
Ta miƙe daga kan gado tana neman abinda Asiya zata yi idan ta shiga irin wannan yanayi.
Gaba É—aya wunin ranan ya tafi ne wajen tunani. Sai da ta fidda rai da samun mafita sannan wani shawara ya faÉ—o mata wanda take tunanin da shi zata yi maganin Mr Lamara da kuma Asiya.
***
Asiya tana karatun Qur'ani bayan ta idar da sallar Magariba ta ji sallama.
Maimuna ce sabuwar ma'aikaciyarta da ta É—auko daga garinsu.
"Anty kina da baƙuwa"
Sai da Asiya ta kai ayar da take karantawa sannan ta amsa mata
"Kice ina zuwa"
Bayan ta ƙare shafin da ta ke ciki sannan ta rufe Qur'anin ta fito ko hijabin da tai sallah da shi bata cire ba.
Wa za ta gani a falon banda matar da basa ga maciji da ita.
"Labule kika chanja a falon?. Wannan painting ma baya falon nan da" ta yi maganar tana nuna wani wall paint na furanni dake manne jikin bango.
"Na san ba maganar chanja labule ne ya kawo ki ba"
"Tabbas" idanunta ya sauka akan na Asiya dai-dai ta zauna kujerar dake kallon nata. Wani kishi ne ya motso mata yadda 'yar wannan yarinyar ta shigo gidanta ta mamaye komai. Hankalinta kwance babu wani alamun damuwa a tareda ita.
Wai 'yar wannan yarinyar, jikar maiƙusumbi ta fi ta gata da kwanciyar hankali a jihar nan.
Asiya ta maida kallonta ga tasbahar da take ja dan wannan ya fi mata mahimmanci akan shirun da suka yi dukkannsu biyu.
"Idan kika tona min asiri, asirin Saifuddeen zaki tona"
Asiya ta É—ago ido ta kalleta a fusace.
"Mi kike nufi?"
Bilkisu ta tura mata wasu takardu kan wani glass table dake tsakiyarsu.
Asiya ta É—auki takardun ta fara karantawa.
Tana gamawa ta kalli Bilkisu cike da ɓacin rai
"Shi kansa Saifuddeen ba zai iya tuna lokacin daya cire waÉ—annan kuÉ—aÉ—en ba amma saboda shi ya cire su inaga hukumar EFCC ba za su zurfafa bincike ba idan suka samu waÉ—annan takardu"
Ta ɗan matso da kanta ta ce " na sani ba a kama Gwamna idan yana kan kujerarsa amma kinaga 'yan majalisa zasu yi shiru idan suka ga wannan? To ace ma ba a tsige shi ba kina ga bayan ya ajiye mulki ba zai ƙarisa rayuwarsa a kurkuku ba? Bana tunanin da ƙuruciyarki za ki zauna zaman jiran mijin da zai yi zaman shekaru shabiyar ko ashirin a kurkuku"
Ta sani wannan kuɗin an cinyesu ne a lokacin da Gwamna yake ƙarƙashin ikon Bilkisu, a lokacin da baya cikin hayyacinsa.
Sai dai gaskiyar Bilkisu ne da ta ce babu wanda zai damu ya zurfafa bincike, abinda za a É—auka shine Gwamna Saifuddeen Kachallah ya lashe Biliyan goma shabiyu cikin kuÉ—in asusun jiha.
Ta cize leɓe tana neman mafita duk da za ta iya rantsewa ko naira ɗaya Saifuddeen bai yi amfani da shi a kuɗin nan ba.
"Idan har kina son mijinki na tabbata duk abinda kike da shi a kaina zaki yi gaggawar ƙona su"