Sashe 44
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga ɓangaren Gwamna ya fara samun matsin lamba daga jam'iyya akan indai ba zai sayi form ɗin takara ba to ya bari mataimakinsa ya siya. Duk da akwai mutane uku da suka sayi form ɗin amma shine candidate ɗin da idan ya fito takara babu makawa mutane zasu zaɓe shi.
Idan ya dawo gida sai ya ga gidan ya masa faɗi. Asiya ta ƙi zama a gidan Gwamnati. Ya sani fushi take da shi saboda maganar da yai ranan da securities suka je fitar da Bilkisu daga gidan. Ga Nana nan kullum cikin roƙonsa take akan yasa a sako mommynsu.
Yana jin kunyar haɗuwa da Asiya dan ya sani bashi da bakin da zai mata bayani kan dalilinsa na rashin miƙa shaidun da za su sa a hukunta Bilkisu ga kotu.
Cikin kwanakin nan yana tunani da kuma dana sani. Inama ace bai amince yayi takara ba bayan ya cinye wa'adin Gwamna mai rasuwa.
Ba wai baya son a hukunta Bilkisu bane sai dai ya kasa gaskata abubuwan daya gani. Ya kasa yarda cewa Bilkisu ce ta aiwatar da dukkan abubuwan da ake tuhumarta da su.
A wani ɓangare kuma yana ɗaura laifin abinda ya faru a kansa. Kamar yadda Bilkisu ta faɗa masa shine silar komai, shine silar maida ita abinda ta zamo yau. Sau tari idan ya zauna yana tunani sai yaga ai Bilkisu gaskiya ta faɗa. Saboda shi duk waɗannan abubuwan suka faru.
To bari zai yi a hukunta Bilkisu bayan shine sanadin lalacewarta haka. To da wani ido zai dinga kallon Nana da Mahirah idan har aka yankewa mahaifiyarsu hukuncin kisa?...
***
"Har yanzu Gwamna bai ce miki komai ba?"
"Ni dai na zuba masa ido ne naga iya gudun ruwansa"
"Abin kam ba daÉ—i. Zai dinga gani kamar ya ci amanar mahaifinta ne"
"Amanar banza. Duk tarin laifuffukan da ta yi ace har akwai wata amana da zata hana ai mata hukunci"
"Calm down ba ni ne Gwamna Saifuddeen ba"
Badawiyya ta ɗauki kofi ta tsiyayawa kanta 5alive Berryblast mai sanyi ta kurɓa a hankali.
"Kin ga kar ki sa wata damuwa a ran ki. Ke kin yi naki kin gama. Ki bari shima yai nashi, na tabbata zai yi abinda ya dace. Give him some time"
Asiya ta girgiza kai itama ta tsiyayi juice É—in ta fara sha.
Ta kalli Badawiyya ta yi murmushi a ranta. Gaskiya aure ni'ima ne idan kayi dacen miji. Tana yiwa ƙawartata addu'ar samun zaman lafiya mai ɗaurewa dan farin ciki da nitsuwa duk sun bayyana a tattare da ita...
Yau safiyar Monday Asiya tana gyara gadonta ta ji wayarta na ringing. Kan dresser ta ɗauko wayar ta ƙara a kunne.
"Madam Bintu ta mutu"
Asiya ta yi saurin duba wayar dan ta tabbatar Badawiyyar ce ke magana
"An ce jiya da daddare ta dinga bubbuga kanta a jikin bango, kafin a zo a dubata ta jikata kuma ta zubar da jini sosai. Ba za ki so ganin gawarta ba Asiya, ni da na gani har yanzu na kasa samun nitsuwa. Allah ka sa mu yi ƙarshe mai kyau, Allah mun tuba"
Asiya ta yi shiru tana jin sheshsheƙar kukan Badawiyya bata san mi zata ce ba, bata san wani addu'a ya kamata ta yi ba. Ba ta san irin lallashin da zata mata ba.
*
Ƙaton dogon gate ɗin gidan kurkukun Congo ya buɗe lokacin da wata baƙar mota mai lambar Gwamnati ta yi horn yayinda wasu motoci biyu duka baƙaƙe suke biye da ita.
Security ya fito da sauri ya buɗe ƙofar motan dake tsakiya. Wata ƙasaitacciyar mace ta fito fiskarta ɗauke da murmushi, sai dai murmushin yafi kama da ta 'yan wasan kwaikwayo dan kuwa bai kai zuci ba.
Duk inda ta wuce gaisheta ake yi hakan ya tabbatar da cewa ita É—in macece mai daraja a idon mutane. Macece mai lamba ta É—aya a duk cikin matan dake faÉ—in jihar Congo.
Rayuwa juyi-juyi. Yau ga Asiya zaune da 'yancinta ita kuma Bilkisu Kachallah zaune da kayan firsina tana jiran hukunci.
"Kin zo dan ki min dariya ne?"
Kaico mutum yai rayuwan zalunci da rashin imani. Mutum ba komai bane.
Yau gashi duniya ta juyawa Bilkisu Kachallah. Fiskarta yanƙwane kamar wata tsohuwa ga wasu ƙananan ƙuraje da suka feso mata suka ƙarawa fiskarta muni.
"Kin san dai har yanzu ina da damar da zan iya sanyawa a hallakaki a hallaka banza"
Ta katse shirun Asiya.
"Hmmm. Duniya kenan. Ni ban zo dan na miki dariya ba domin ke abar tausayi ce ba abar dariya ba"
"Allah ya tsinewa tausayi. Na fi ƙarfin ki ji tausayina, zan fito nan bada jimawa ba kuma Alkali ne zai wanke sunana. All of you will pay for what you did to me. Idan na zama Gwamna kan ki zan sa a fara fillewa"
"Ke mahaukaciya ce Bilkisu. Ki tuba ga Allah ko zaki samu sauƙi"
Bilkisu ta kwashe da dariya sai da ofishin da suke ciki ya amsa.
"Kin san dana sani É—aya nayi a rayuwata"
"Na yi dana sanin kashe ki da banyi ba da hannuna"
"Na zo in miki nasiha ne Bilkisu. Ki tuba ga Allah sannan ki amsa laifukan ki, idan baki yi dan kowa ba kiyi dan yaran ki. Kin sani su mata ne kuma duk abinda kika aikata zai iya shafar rayuwarsu nan gaba. Wai shin ma ba kya tunanin mutuwar ki ne?"
Wata dariyar Bilkisu ta sake yi. Asiya ta shiga girgiza kai. Duk yadda ta tsani matar nan, chan cikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya shiryar da ita. Tana matuƙar tausayin mutuwarta a haka. Ko jiya sai da Nana ta zo roƙonta wai Dan Allah ta sa baki a sako mahaifiyarsu. Nana bata san girman laifukan mahaifiyarta ba, dan da ta sani da ba za ta nemi a sake ta ba.
Babu É—a na gari da zai so ganin uwarsa a irin wannan hali.
Ganin ɓata lokaci kawai take akan Bilkisu yasa ta miƙe tsaye.
"Ki yi tunani Bilkisu, abinda kike ba zai fishshe ki ba"
Bilkisu ta miƙe tsaye itama duk da Asiyar ta fita tsayi, ta ɗaga kai ta kalleta ido cikin ido tace "baki isa ki ga bayana ba Asiya. I will always rule this state. Wannan da kike gani temporary ne, zan fito, kuma zan shiga takara kuma zan ci zaɓe. Duk wannan da kike taƙama da shi"
Ta nunata sama da ƙasa, idonta ya sauka kan cikin Asiya
"Jiƙar mai ƙusumbi sai sun dawo tsumma a jikin ki"
Idanunta suka kasa motsawa daga cikin Asiya. Doguwar rigar Atamfa ta saka tareda babban mayafi daya tafi dai dai da kalar Atamfar wanda yafi kama da kalar ruwan goro
"Wani cikin kika sake samu?"
Asiya ta kalleta cikin rashin fahimta. "Ban gane ba?"
"Well, ki yi ta ɗaukan ciki kina wahalar da kan ki dan kuwa yadda wancan ya tafi wannan ma binsa zai yi. Ba za ki taɓa haihuwa da Saifuddeen ba. NEVER" ta faɗa da wani irin tsawa wanda ya sa Asiya ta firgita, kalamanta suka fi tsawan firgitata.
Dariya ne ya biyo bayan haka dan har aka zo aka tafi da ita bata bar dariya ba.
Mamaki ne da tambayoyi suka cikawa Asiya kwanya.
Mi Bilkisu ke nufi? Ko dai haukan kanta ne ke saka ta maganar shirme.
Shugaban kurkukun ne ta shigo ofishin tana yiwa Asiya sannu tareda fatan Bilkisu bata ba ta wata matsala ba. Da kyar Asiya ta iya amsa mata sama-sama kafin ta fice daga office É—in.
Waje É—aya ne za ta samu amsa, kuma nan ta nufa
32
***
Matar Gwamna tana da damar zuwa ofishin Gwamna a kowanni lokaci. Asiya za ta iya irga sau nawa ta taka taje ofishin Gwamna tun lokacin tana ƙaramar 'yar jarida zuwa yanzu da matsayinta ya kasance daraja ta ɗaya a wannan jiha.
Ofishin Gwamna bai taɓa mata nisa ba irin na yau, dan tunda ta fito daga mota take ganin ga kowanni taku ɗaya da ta yi ofishin na ƙara nisan taku goma.
Ta ko'ina gaishe ta ake amma damuwar dake tattare da ita ya hanata sakewa ta gaisa da mutane. Ba za ta iya cewa ga amsar da take basu ba amma abu É—aya ta iya daurewa a kai shine murmushi. Murmushin nata da ya tsaya iya fatar baki.
Ba bu wani shamaki daya hanata shiga ofishin Gwamna kai tsaye dan kowa buÉ—a mata hanya yake domin ita da mai ofishin sun zamo É—aya.
Shi kaɗai ne a office ɗin kuma rubutu yake, zaka gane rubutun na da mahimmanci a gareshi dan hatta eye glass ɗinsa da bai cika amfani da shi ba sai dare yana manne a fiskarsa ya duƙufa yana rubutu.
Sai da ta iso gabansa sannan ya iya ɗaga kai ya kalleta. Wani murmushi ne ya suɓuce masa. Ko dan bai yi tunanin ganinta a ofishinsa ba, ko kuma dan kewanta da yake yi, ko kuma duka
"Akwai abinda kake ɓoye min ne?"
Ta yi maganar cike da fatan babu gaskiya cikin abinda Bilkisu ta faÉ—a.
A cikin mota ta gama tunanin yiwuwar maganar Bilkisu kuma abu biyu ta iya hangowa. Tabbas ba ta ga jininta ba lokacin Azumi sannan komai zai iya faruwa a hatsarin da suka yi a hanyar su ta zuwa Congo bayan sallah.
Bai san inda maganarta ya dosa ba dan haka ya ajiye biron hannunsa ya haɗa hannunsa biyu ya ɗaura haɓarsa a kansu ya zuba mata ido yana jiran ƙarin bayani.
"Lokacin da muka yi hatsari" ta tsaya da maganar dan bata san wasu kalmomi za ta yi amfani da su ba.
Ta ɗan ja numfashi a hankali " akwai abinda na rasa lokacin da na yi hatsari ne? Akwai abinda Likita ya faɗa maka ka ɓoye min?"
"Asya" ya miƙe daga kujerarsa ya zagayo inda take tsaye. Hannunta biyu ya kamo ya haɗasu ya manna musu kiss murya a sanyaye yace "mi kike nufi? Abinda ya faru lokacin ba abune daya kamata ace kina tunawa da shi ba tunda Alhamdulillahi dukkanku uku kuna nan lafiya"
"Har É—an cikin nawa ma sai an siyasantar da shi"
"Asya"
Ta kwace hannunta daga cikin nasa. Yanayin yadda ya kira sunanta, yadda idanunsa suka rikiɗa zuwa roƙo su suka fahimtar da ita cewa gaskiya ne abinda Bilkisu ta faɗa.