← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Seriously Excellency, this is a bad time, idan har aka yi wani abu na taro a critical moment haka duniya za ta zage mu. Already ana kukan babu a jihar nan, ga É—aliban da aka sace sun doshi wata É—aya babu labarinsu. Ko da za ayi celebration Boss sai dai ayi shi low key. Kamar a kira taron addu'a haka kin gane ai"

Bilkisu ta yi shiru tana nazarin kalamansa. Tunda Muhammad Sani yai nasaran ture Lamara Damana daga jikinta shine ya zamo na hannun damanta mai bata shawara a kan komai.

"Inaga ki ƙara sunan mutanen da za ki tura Hajji wannan shekaran, saboda a rufe bakin malamai"

"Yawwa M Sani, shi wannan Malam Idris Tukur É—in ya za ayi da shi ne?"

M Sani ya kwashe da dariya. Sai da ya yi mai isar sa kafin ya kalleta ya ce " Boss kin san bana wasa da assignment É—ina"
Ya ɗauko wasu takardu a cikin folder ya miƙa mata ya ce " Malam Tukur ba zai ba mu matsala ba daga yanzu, he has received 50M fisabilillah. Masallaci da Makarantansa duk za a kammala masa ginin su nan da watanni uku, duka Fisabililahi daga ƙarƙashin jagorancin Hajiya Bilkisu Kachallah"

Bilkisu ta tintsire da dariya tana faÉ—in "Malam zai ci kaji yai naman wuya kenan"

"Ofcourse My Boss, sauran ƙananun ƙwarin kam miliyan biyar-biyar da kujeran Makkah zai miki maganinsu"

"Amma wannan bagidajen Malamin fa? Tuna min sunan sa"

"Malam Hussaini Zango"

"Yes shi. Na ji labarin shima yana ranting acikin gari"

"Kar ki damu da shi. Na karance shi, gaskiya ba zai sayu da kuɗi ba, amma kuma mabiyansa ai mayunwata ne, da sannu za su tattara su koma ƙarƙasin Malam Tukur" M Sani ya faɗa yana murmushin mugunta.

Bilkisu Kachallah ta ce "weldone my boy"

***

A ofishin Chief of Staff kuwa. Lamara Damana ne ke zaune akan kujera yana jujjuya biro a hannunsa. A koda yaushe shi yana tare ne da mai nasara, yana goyon bayan inda zai samu daraja da kima ne, yana goyon bayan wanda zumar mulki ke hannunsa.

Ba haka ya hango ba lokacin da ya goyawa Bilkisu Kachallah baya. Tunda yaron nan ya zo ta fara rena masa wayo. Ta ya za ta yi amfani da shawaran yaro ƙarami ɗan shekara ashirin da bakwai ta yi watsi da nasa shawaran. Yaushe Muhammad Sani ya zo duniya? Yaushe ma ya shiga harkar siyasa?.

Yai murmushin gefen baki ya ce " idan ƙabilanci da 'yanuwantaka za ki nuna min Bilkisu, ni kuma zan nuna miki cewa ni Lamara Damana ba kanwan lasa ba ne"

Hoton poster na Asiya ya ɗauko daga cikin wani file. Yana sane da cewa Asiya ta je institute ne saboda ta ɗau fansar abinda Bilkisu Kachallah ta mata. Shiyasa ma da Bilkisu ta sa shi bincike a kan makarantar da Asiya ta tafi ya mata ƙarya cewa fa gaske ɗin ta je America yin masters ɗinta ne.
COS yai murmushi ya ce idan kuwa Asiya na son revenge ni kuma zan taimaka mata da duk abinda za ta buƙata. Ya ɗau red marker ya zana ƙaton × akan hoton Bilkisu Kachallah. Sai kuma ya ɗauko green marker ya zana ƙaton good mark a hoton Asiya. Yana ajiye marker ya ce "let the battle begin"

A zuciyarsa ya fara tsara yadda zai koma gefe ya kalli yadda waɗannan mata biyu za su yi yaƙi tsakaninsu. Yayi alƙawarin tsayawa a gefen kowacce ya bata gudummawa gwargwadon ƙoƙarinta. Daga ƙarshe idan ya hango mai nasara a ciki sai yai maza ya koma wajenta gaba ɗaya. Duk da zuciyarsa na riya masa Asiya ce za ta yi nasara amma for now ba zai bar jikin Bilkisu Kachallah ba.

***

Yayinda lamurra su ke ta sake taɓarɓarewa a jahar Congo. Kan Malaman addini ya rabu ne kashi uku. Akwai masu kallo, waɗannan sun zuba ido ne suna kallon yadda ake shugabanci a jihar amma ba su saka baki a kai ba balle har su yiwa Gwamna da muƙarrabansa wa'azi.

Kashi na biyu kuwa su ne su ke ta sukan Gwamna da matarsa wacce yawo da ta ke da maciji a cikin gari yasa su ke kafurtata wasu kuma su ke kiranta da 'yar ƙungiyar asiri. Waɗannan su ne ire-iren tawagar Malam Tukur wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai da ake ji da su a jihar. Lokacin da Malam Tukur ya ga miliyoyi a account ɗinsa ya kuma ga an kama aikin masallacinsa gadan-gadan sai kawai ya fara reversing wa'azinsa yana gayawa Mutane kada a tsinewa shuwagabanni, addu'a za a dinga musu a kuma ci gaba da haƙuri har Allah ya kawo ɗauki, domin Allah Sami'un Basirun ne yana ji kuma yana gani. Da sannu maganganun Malam ya fara shiga zuciyar mutane.

Kashi na uku su ne ire-iren Malam Zango, waɗannan su ke ƙoƙarin yiwa Gwamnati wa'azi, tareda ƙoƙarin kawo kukan talakawa ga kunnunwan gwamnati. Sai dai irin su Malam Zango ba su da Mabiya dayawa, yawancin ma su zuwa ma yunwa da talauci ne ya sa su komawa ga masallaci suna bibiyar wa'azi da karatuttukan sunnah, da zaran an samu sauƙi za su watse...

***
Gwamna SSK ya fara duba visar da ke gabansa. Bai san ya aka yi ya ce a booking masa tafiya wannan ƙasar ba. Yaushe ya bada wannan umurni?

Lokacin da Sakatare ya kawo masa file É—in ya gani tsoron tambayar sa yai kada yai tunanin ko ya fara zaucewa ne.

Mi zai yi a Gambia?. Ya sake tambayar kansa.

Ya latsa computer da ke gabansa ya duba duka schedules ɗinsa na wannan sati amma bai ga inda aka tsara tafiyarsa wannan ƙasa ba. To ya aka yi aka booking masa tafiya ƙasar Gambia shi ɗaya, kumama tafiyar yau da yamma ne.

Chan dai da ya rasa amsoshin tambayoyinsa sai ya É—au waya ya kira COS. Ba a jima ba sai ga shi ya shigo office É—insa.

Lamara Damana na zama Gwamna ya tura masa visar da ticket na tafiyar.

"Na minene wannan?"

Lamara ya kalli takardun sannan ya dubi Gwamna ya ce "umurnin da ka bani jiya kenan Excellency"

Cikin rashin fahimta yace "umurni? Da yaushe kenan?"

"Your Excellency Sir ba ka tuna ba? Jiya ƙarfe biyun dare ka kirani kace na booking maka jirgi zuwa Gambia za ka je ka duba mahaifiyar ka"

Gwamna ya zaro ido waje lokacin da ya tuno abinda ya faru jiya da dare. Tabbas shi ya kira Lamara, ba ma haka ba har kuka ya fara yi masa lokacin da ya ce masa ba zai iya booking masa yau ba saboda akwai meeting da za su yi da wasu manya.

"Excellency sorry to say, amma mahaifiyarka ta rasu Sir. Ko dai wajen wata 'yar uwarta za ka je?"

Maganan da Lamara ya masa kenan jiya, kuma maimakon ya nitsu ya saurare shi, sai ya daka masa tsawa akan ya nema masa jirgi shi zai tafi ƙasar Gambia wajen mahaifiyarsa.

Gwamna da COS suka fara kallon-kallo. Idan wannan magana ta fita akwai matsala babba. Gwamna ya fara zaucewa.

Gwamna ya buÉ—e baki a hankali yace " maganar nan ta tsaya a nan"

COS ya ce " an gama Excellency"

Bayan tafiyar Lamara Damana, Gwamna ya dafe kansa da ke mugun sara masa ya fara tunanin taya zai ɓullowa wannan lamari. Anya bai fara zaucewa ba kuwa? Domin ba wannan ne karo na farko da ya ke yin abu kuma ya manta da cewa yayi ba.
Jiya mafarkin mahaifiyarsa ya farkar da shi daga bacci, kewarta ya ke. Yanayin daya ganta a mafarki ya masa kamar tana nan raye kuma tana fushi da shi. Lokacin da ya farka nan da nan ya shiga kiran numbar Sakatarensa amma numbar bata shiga ba shiyasa ma ya kira Chief of Staff É—insa...

***

A yau ma Gwamna Saifuddeen Kachallah bai iya rintsawa ba, duk da kuwa cikin dare an yi ta tsala ruwan sama kaman da bakin ƙwarya, ni'ima ta sauka a wannan dare.
Washegari tun kafin Gwamna ya fita office aka kawo mishi labari cewa an samu ambaliyar ruwa a ƙaramar hukumar Boyo da kuma wa su ƙauyuka kusan guda huɗu wannan ya jawo asarar rayuka da dukiya. Saboda ƙarfin ruwan sai da ta yanke Gadar da zai kai ka Boyo daga garin Saje, wannan ya haifar da hatsari har aka rasa rayuka da dama.

Gwamna yana ajiye waya Bilkisu ta kalleshi ta ce "yanzu ya za ayi kenan?"

A handsfree ya saka kiran dan haka ta ji komai, bai san mi zai ce ba dan a mafiya lokuta ya kan rasa abun faÉ—a idan yana tareda ita.

"Inaga ka je ka sympathising da su,wannan zai ɗaga darajar ka a idon su. Ƙila ma ya kawo ƙarshen ƙananun maganganu da ake yi a kanka a yankin"
Gwamna ya amsa da toh...

11

Gwamna Saifuddeen Kachallah ya miƙe daga kujerarsa ya nufi banɗaki dake cikin makeken ofishinsa. Ya buɗe tap ya wanke hannunsa sannan ya sa hannu ɗaya ya tari ruwa ya wanke fiskarsa da shi, sai da yai haka sau uku kafin ya rufe tap ɗin ya ƙurawa fiskarsa ido ta jikin madubi. Wannan fuska da ya ke gani a jikin madubi ba shine Saifuddeen da ya sani watanni goma shaɗaya da suka wuce ba.
Ba zai iya tuna abinda ya banbanta wancan Saifuddeen da wannan Saifuddeen É—in ba amma tabbas akwai banbanci mai faÉ—i tsakaninsu.

Ya kai kusan minti biyar yana kallon kansa a madubi kafin yai saurin É—auke kai saboda mummunan abinda zuciyarsa ta ayyano masa.

Lokacin daya fito daga banÉ—akin ya saita kansa kamar babu abinda ke damunsa dan kuwa a kullum abinda ke bayyane wa jama'a kenan wato Gwamna yana nan cikin kwanciyar hankali duk da kuwa ana fama da talauci, tsadar rayuwa, kidnapping dama fashi da makami a Jihar.

Minti biyu yai a office É—in sannan ya fito inda tawagarsa suka mara masa baya dan kai ziyarar ganin ido garuruwan da ambaliyar ruwa yai wa ta'adi.

***

Yau ta tashi ne da kewar mijinta. Mafarkin da ta yi ya bata tsoro hakan ya sa ta ke kwaɗayin kasancewa da shi ta nuna masa komai ya kusa zuwa ƙarshe.
Saura ƙiris ta dawo gare shi, ta dawo don ta taimaka masa cikin mulkinsa.
Chapter 13 · 0% Book details