Sashe 28
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan rana Asiya ta kasance cikin fargaba da tsoro. Bayan tafiyar Gwamna ta jima tsaye tana hawaye kafin daga baya ta koma É—aki ta kwanta.
Haka ta wuni bata ci komai ba.
Kusan ƙarfe bakwai na dare Agent Dahlia ta kirata tana yi mata albishir akan an samu nasarar cafke Madam Bintu a filin jirgin ƙasa tana shirin barin gari bayan tayi shigar tsohuwa. Ko kaɗan labarin bai faranta mata rai ba ta dai amsa da to sannan ta kashe wayoyinta gaba ɗaya.
Har dare Gwamna bai dawo ba kuma alamu sun nuna bashi da niyyar dawowan domin agogon ɗakin Asiya ya doka ƙarfe shabiyun dare kusan mintuna takwas da suka wuce.
Kusan ƙarfe ɗaya saura motocinsa suka shigo gidan, bata yi wani harama dan ta tarbeshi ba dan tasan ɗayan biyu ne. Ko dai ya zo ya sameta a ɗakinta ko kuma ya wuce nashi ɗakin.
Duk da bata saka ran cewa ɗakinta zai zo ba sai ga shi yana ƙwanƙwasa mata ƙofar ɗaki.
A matse take taji mi zai zo da shi dan haka a bugu na uku ta buɗe masa ƙofar ta matsa masa ya shigo ba tareda ta iya kallon fuskarsa ba.
"Na zo ne na faÉ—a miki hukuncin dana yanke"
Da sauri ta É—ago ido ta kalleshi, duk da faÉ—uwar gaba da take ji hakan bai hanata tunowa da tarayyarsu É—azu da rana ba.
"Za ki ajiye duk wani abu da kike da shi akan Baba. Idan kika yi haka zan yi resigning a kan kujerar Gwamna.
"Asirin Baba ba zai tonu akan idona ba Asya"
Wata dariyar rainin hankali ta yi sannan ta zauna bakin gado tana kallonsa ido cikin ido.
"Wannan umurni ne a matsayina na Miji ba a matsayina na Gwamna ba"
"Idan na ƙi fa?" Ta faɗa kai tsaye dan yanzu haushi ya fara bata daya fito da tsantsan son ransa a fili.
Ƙarisowa yai ya zauna kusa da ita tareda kamo hannunta biyu ya riƙe su gam sannan ya fara magana
" kina tunanin na faɗi wannan ne saboda son zuciya? Asya idan aka fitar da waɗannan takardu ba Baba kawai maganar zai shafa ba. Zai shafi wasu makusantan Baba kuma hakan zai iya jawo asarar rayuka. Ban shirya rasa ki ba, ban shirya rasa wani nawa ba. Zan yi resigning, zan ajiye kujerar nan, we can forget about all this. Na yiwa Baba magana kuma na san zai ƙarisa ayyukan kwangilar da aka bashi sannan zai dinga maida kuɗin a hankali har ya gama maida duka kuɗaɗen"
Tayi saurin katse shi da cewa
"Na yadda ba zan miƙa takardun ba. Amma kada ka manta alƙawarin da ka ɗauka ranan da aka rantsar da kai. Ka tuna cewa duk abinda ka aikata zaka yi bayani a gaban Allah"
Maganarta ta shige shi sosai dan har hannunsa ya fara rawa.
Ta zare hannunta daga nashi ta É—ago kumburarrun idanunta ta kalli cikin idanunsa tace " zaka yi resigning saboda tsoron Allah ko dan gudun maganar mutane?.
"Hmmm! kana tunanin ni kaÉ—ai ce ke son ganin bayan Alhaji Sani Kachallah?. Akwai abubuwa dayawa da baka sani ba your Excellency ko kuma nace kake tsoron sani"
"Asya..."
"Zan cire hannuna akan case ɗin Madam Bintu Chadi amma ka sani dole ne Badawiyya ta ƙwaci haƙƙinta.
Zan cire hannuna a duk wani abu daya shafi ahalin Kachallah. Sai dai akwai ɗaya wanda na riga na miƙa shi hannun Human Rights kuma kwanan nan za a shigar da ƙara"
Da sauri ya zaro ido waje dan a gurguwar tunaninsa ya É—auka maganar mutuwar Junior ta kai Human Rights.
Miƙewa ta yi ta je ta ɗauko wani file cikin drawer dake gefen gado ta kawo masa.
"Ka buÉ—e" ta faÉ—a tana masa wani irin kallo mai É—auke da tuhuma.
Yana buÉ—e file É—in yaci karo da wani hoto. Abinda ya gani a hoton ne ya sa shi kallonta a firgice.
"Ka karanta takardun ciki zaka fahimci abinda hoton ke nufi"
"Dan Allah ki gaya min abinda ke ciki Asya"
Murmushin gefen baki tayi sannan tace " Sa'idu Musa ɗan shekara shahuɗu kenan, wanda aka yiwa fyaɗe. Ko ince anyi wata biyar ana luwaɗi da shi. Kamar yadda ka gani a hoton aiki ake masa a bayansa saboda infection daya ruɓar da takashinsa"
Hawayen da suka zubo mata tayi saurin gogewa sannan tace "Sa'idu Almajiri ne da ya gudu daga makarantar su a chan wani ƙauye wai Kantu. Aikin wanki da guga aka ɗauke shi amma aka dinga luwaɗi da shi, da aka ga ya fara ciwo aka bashi dubu hamsin aka kore shi tareda gargaɗi mai tsanani. An samu yaron ne dai-dai yana ƙoƙarin rataye kansa"
Baki na rawa Gwamna yace "wa?... waye ya aikata haka? Waye wannan? "
"Ka duba sauran hotunan"
Gwamna ya maida dubansa ga file ɗin sannan kaman wanda aka zarewa laka haka ya buɗe file ɗin a hankali ya fara duba hotuna da kuma takardun dake ciki, sunan daya gani bai firgita shi ba domin suna ne gama gari sai dai cak ya tsaya lokacin daya ci karo da wani hoto daya sa numfashinsa ɗaukewa na 'yan daƙiƙai.
"ÆŠan...É—an Rufaidah!" ya faÉ—a yana kallon Asiya kamar dai yana jira ta tabbatar masa abinda ya gani.
"Ya Subahannallah!" Yai saurin riƙe goshin sa dake wani mugun sara masa.
"shima a dakatar da shari'ar ne har sai ka sauka daga kujerar Gwamna?"
Shiru yai yana jin wani raɗaɗi na mamaye ilahirin jikinsa, lokaci guda kuma numfashinsa ya fara sarƙewa.
"Your Excellency" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Da ƙyar ta iya zaro inhaler daga aljihunsa ta bashi ya shaƙa sannan ta tallafa masa ya kwanta akan gado.
Kusan minti goma yana kwance abubuwa da dama na yi masa yawo a ka . Chan kuma kamar wanda aka tsikare shi ya miƙe ya ɗau file ɗin ya fice daga ɗaki ko sauraron Asiya dake masa magana bai yi ba.
Tunda ta ji ƙaran fitan mota ta san ba zai kwana gida ba. Addu'arta ɗaya Allah ya tsare shi.
***
Washegari labarin kama Madam Bintu ya baza gari. Duk wanɗanda ke da alaƙa da harkokinta sun fara barin gari, wasu kuwa duk sun ƙona takardun da suke ganin zai iya zama shaidar harkokin kasuwancin su.
Bilkisu Kachallah ta shiga wani hali tun jiya da dare zuwa yau da safen nan da take ganin yadda ake tisa ƙeyar Madam Bintu cikin motar 'yan sanda. Kwanaki kusan takwas da Madam Bintu tayi a ɓoye sun bayyanar da ainihin tsufarta wanda zallar mai da kwalliya ke ɓoyewa a baya. Yadda cinyayyen gashinta yai buzu-buzu kace mahaukaciya ce sabuwar kamu.
Ta kira duk wani contact nata cikin kwanakin nan amma duk abu É—aya ake gaya mata abinda aka samu game da Madam Bintu zai iya shafarta madamar Madam Bintu ta buÉ—i baki ta ambaceta cikin shari'ar da za a fara.
Ba wannan bama bata gama gane mi Gwamna ke nufi da hotunan daya nuna mata jiya ba. Duk da kuwa ta ƙaryata komai amma kuma yanzu da komai ke dawo mata dalla-dalla sai ta fara tunanin matsalar da zata shiga idan maganar nan ta fito waje. Ita ce ke ƙoƙarin maye gurbin Saifuddeen kuma tabbas idan aka jonata da Bintu ko M Sani mutane zasu zargeta su yi kokonto akan shugabancinta.
Wai taya ma M Sani zai mata haka ne?
Mi ya rasa a rayuwar nan da zai fara bin maza. Ƙarin abin takaicin ma wai ya auri namiji a US shekaru biyu da suka wuce kuma wai har sun rabu bayan matar (namiji) tayi ƙaransa bisa cin zarafinsa daya ke yi.
Takardun saki da Saifuddeen ya nuna mata jiya ya tabbatar mata da cewa M Sani ya dawo Nigeria ne bayan ya rasa fiye da rabin dukiyarsa ga matarsa mai suna Scott Green.
Bilkisu ta zauna akan kujera tana ƙara gwada numbar M Sani wanda tun jiya take a kashe.
Tana cikin juyayin wannan abu wayar COS ta shigo, da sauri ta amsa dan kuwa dama tana son magana da shi.
"Mr Lamara mi yake faruwa?"
"As you suspect Asiya ce ta bada lead aka kama Bintu. Har yanzu ban samu damar ganawa da ita ko lauyanta ba amma..."
"Ina so shari'ar ta tsaya iya kanta, kayi duk abinda zaka yi ganin bata ambaci sunana ba" Bilkisu ta katse shi
"Matsalar shine bamu san mi Asiya ke da shi game da ke ba, in dai Bintu ce na tabbata zata riƙe amanar ki"
"I'm counting on you Mr Lamara akwai wani abu a ƙasa bayan na Madam Bintu"
"Your Excellency mi kenan?"
Shiru tayi na 'yan daƙiƙai tana nazari kafin tace "ina ga zamu matso da plans namu gaba"
"Ba kya ganin ya kamata ki bari abubuwa su lafa tukunna"
"Yanzu ne nake da dama, this is the best chance i've got. Idan Gwamna ya kwanta ciwo zan samu soyayya da tausayi daga wajen mutane"
Daga inda COS ke zaune ya É—an sassauta murya yace "ba kya ganin mutane zasu fi tausaya wa Asiya, ba kya ganin ita kanta Asiya zata so kujerar da kike so?"
Maganar da yai ta dake ta, dan take taji tana tunanin yiwuwar abinda ya faÉ—a. Fiye da rabin cabinet na Gwamna mutanen Asiya ne yanzu sannan sunanta ya kama bakin mutane tunda ta fara program É—inta.
Mr Lamara yayi gaskiya, ko dan ta cigaba da legacy na Saifuddeen zata so kujerar sa.
"Hakan ba zai yiwu ba" ta ɗan shaƙi numfashi sannan ta cigaba
"Domin mutuwar ta shine dalilin rashin lafiyar Saifuddeen"
Ajiye wayar tayi sannan ta miƙe ta wuce ɗakinta da sauri...
Daga ɓangaren Mr Lamara kuwa murmushin farin ciki yai domin yana jiyo ƙamshin nasara a kusa da shi.
Har ma Bilkisu zata ambaci wannan lokaci da damar ta. Wannan damar sa ce, kuma tsaf zai yi amfani da ita yadda ya kamata.
Ya fara yiwa Bilkisu saran ɓoye ne tun lokacin da ta fara fifita M Sani akan sa.
Tuni ya baza mutanensa dan ganin an nemo masa tarihin M Sani na baya da kuma a yanzu. Ya sani saurayi kaman M Sani ba zai taɓa rasa dirty past ba.