Sashe 40
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Idan ban yi hakan ba kashe shi zaki yi?" Asiya ta yi tambayar fiskarta a É—aure.
"Ya dangana da irin zaɓin ki"
Lokacin da Bilkisu ta miƙe zata tafi Asiya tace " shine fa Uban 'ya'yanki"
Bilkisu ta ƙara taku biyu sannan tace "ba laifi bane idan sun zama marayu, shima Ubansu a maraya ya taso"
"Subhanallah!" Asiya ta furta tana riƙe baki...
***
"Baka da ikon kai min 'yata wajen Asiya. She's my daughter and she stays here with me"
"Kin saurari kan ki kuwa? Ina kike lokacin da na kawo Nana gidan nan?. She waited for you for five hours babu ke babu dalilinki"
"Ban san yau zaka dawo ba, baka gaya min zaka dawo yau ba"
Ya girgiza kai kawai dan duk wani bayani da zai yi ɓata lokaci ne. Inama ta ɗau kiransa balle har yai mata bayani. Ko da suka je Sudan ma ƙorafin da Mahirah ta masa kenan akan Bilkisu bata kiranta, idan kuma ta kira sai ta ga dama take ɗauka.
"Ka je ka dawo min da 'yata"
"Khadijah ba 'yar goyo bace, idan kina son ganinta kin san inda zaki sameta"
Ta so yin jayayya da shi amma akwai inda za ta je yanzu.
Ko ta halin ƙaƙa sai ta siyi award ɗin nan, wannan award shine zai ƙara mata daraja a idon mutane. Mutane biyar za'a nominating kuma dole ta kasance cikinsu.
Da wannan tunani ta fita daga gidan.
*
"Mr Chairman ban gane kana son janye endorsement ɗinka ba. Wa kake da shi daya fini, kana tunanin Saifuddeen zai iya taɓuka abin kirki ne a wa'adinsa na gaba. This man is coming after us, ya bari Asiya matarsa tana yi mana ɗauki ɗai-ɗai tana kaimu kurkuku. Kar ka manta matarsa Asiya ce ta tura Sani Kachallah prison fa"
Party Chairman yai gyaran murya yana ƙara tuno alƙawurran Bilkisu Kachallah. Kaso sittin na duka kasuwancinta nasa ne, daga yanzu har ta yi shekara huɗu akan kujerar Gwamna. Shi kansa ya so sanin sirrin kasuwancin muggan ƙwayoyi da na makamai amma har yanzu bai sani ba, dan yana tsoron kar ta ɓaci.
"Mr Lamara ka ƙara bani lokaci nayi tunani, ka san jama'ar Congo ba za su so zaɓan wanda ba musul..."
"Dakata! Na gane matsayarka"
Ya miƙe tsaye rai a ɓace yace " da kai da ita ɗin dukkanku zaku rasa kujerar Congo"
"Lamara, Mr Lamara" Chairman ya bi shi da kira amma ko juyowa bai yi ba.
Bayan ya koma Congo ko hutawa bai yi ba ya nufi gidan Alhaji Umaru Kwom amma rashin sa'a ya tarar ya tafi jinya ƙasar waje.
Zai koma jam'iyyar su Umaru Kwom sannan ya fito a mataimakin Gwamna, in har komai ya tabbata suka ci zaɓe zai san yadda zai yi ya ɗauke Umaru Kwom a hanya amma kafin nan zai yi maganin Bilkisu Kachallah.
Barin gidan Alhaji Umaru Kwom keda wuya lauyansa ya kira shi. Ba maganar waya bace abinda Lauyan ya faÉ—a masa kenan.
Gidan shaƙatawarsa yace su haɗu dan asalin gidansa akwai hayaniya, 'ya'yansa sun zo hutu daga ƙasar waje.
Gaba ɗaya notinan kansa sai da suka kunce lokacin da ya karanta takardar gayyata da Lawyansa ya miƙa masa.
"Barrister mi yake faruwa?"
Gashi nan a rubuce amma bai gane inda rubutun ya dosa ba.
"Matar tsohon Gwamna tana tuhumata da kashe mijinta, HOW? Ba tana ƙasar waje ba?"
"Sir, it seems baka san miyake faruwa a gari ba. Kusan wata shida kenan da dawowar Hajiya Sha'awanatu Bacchi garin nan"
A da dai babu abinda zai shiga ko kuma ya fita daga jihar nan matuƙar yana da mahimmanci ba tareda shi Lamara Damana ya sani ba. To mi ya faru? Ko dan ya karkatar da hankalinsa kan batun samun kujerar Gwamna ne, ko kuma dai cire shi daga muƙamin Chief of Staff ne ya rage masa ƙarfi.
Ina munafukai masu kawo masa labarin abubuwan dake wanzuwa a jihar ?
"Da gaske ne Abdul Tsangaya yana da recording na maganarmu?"
"Waye Abdul Tsangaya?" Lawyer ya tambaya cikin rashin fahimta.
Ba zai karaya ba. Wannan ba komai bane, babu wanda ya isa ya gano abinda ya aikata shekaru kusan huÉ—u, kai biyar ma za ace yanzu kam.
Babu wanda ya isa ya tura shi kurkuku, zai amsa kiransu kuma zai ci nasara.
***
"Wai da gaske ne akwai recording ko kuma dai?"
"Kin ga Badawiyya ki kwantar da hankalinki ki cigaba da cin amarci, wannan case ba naki bane"
"Dole ki ce haka ai, kaman yau ne na fara shiga case É—in da ba nawa ba"
"Allah ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba. Kin san dai yanzu ke matar mutum ne"
"Ke kuma matar Aljani ko?"
Asiya ta saka dariya ta gyara zamanta sannan tace " Abdul Tsangaya yace ya naÉ—i hiransu amma gaskiya an sace wayar da daÉ—ewa kuma babu back-up"
"Kina tunanin shi kuma Lamara Damana zai saki baki ya tonawa kansa asiri saboda an masa barazana"
"Ba zai tonawa kansa asiri ba, amma yana fama da wannan case É—in Bilkisu zata bankaÉ—o dukkan sirrikansa dan damarta kenan. Idan ba a kamashi ta kisan tsohon Gwamna ba za a kama shi ta cin hanci da rashawa"
"Ita kuma Bilkisu fah?"
Asiya ta yi shiru, dan bata faÉ—awa Badawiyya kashedin da Bilkisu ta mata ba.
Duk da bata faÉ—a É—inba Badawiyya ta gano hakan daga shirun da ta yi.
"Kina tsoron kada ta yiwa Gwamna wani abu?"
"Ban san mi zan yi ba Badawiyya. Wani lokaci na kanji a raina cewa na bar wannan binciken na rufe ido kawai na bar Gwamna ya ƙare wa'adinsa mu bar musu Gwamnatin su cigaba da abinda suka ga dama"
"Kina sauraren radio kuwa?"
Asiya ta girgiza kai "A'a"
"Idan kika cire hannunki zaki katse ladan da kike samu Asiya. Lokacin dana je ƙauye bakina ba zai iya faɗa miki irin addu'o'in da na ji ana yi miki ba. This Projec Tomatonion kaɗai da kika assasa baki san yadda mutane da dama suka amfana da shi ba. Infact saboda shine ma aka nominating ɗinki for the best governor's wife award"
"Kai Badawiyya ina kika ji wannan kuma, yaushe ma aka fara bada award É—in"
"Matar Shugaban ƙasa ce da wasu tsofin matan Gwamnoni suka ƙirƙiro award ɗin, wannan ne shekara na huɗu da za a sake bayarda award ɗin. Abin alfahari ne a gareki Asiya, kuma ina addu'ar Allah yasa ki ci award ɗin nan"
"kinga bar maganan award É—in nan. Za ayi wani seminar a College of Agric Congo ina so ki wakilce ni idan Maigida ya amince"
"ChabÉ—i jam! Ban gama honeymoon ba"
"Honeymoon ko. Za ki gane kuran ki idan kika shiga labour room kina zazzare ido ai" ta ƙarisa maganar tana dariya. Sai dai shirun da ta ji daga ɓangaren Badawiyya yasa ta katse dariyar, murya a sassauce tace "Badawiyya?"
"Ba zan taɓa shiga labour room ba Asiya, Madam Bintu ta ɗauke min wannan damar" Badawiyya ta kufce da kuka. Kukan kenan Asiya ta ji kafin katse kiran da Badawiyya tayi tun kafin ta samu damar yi mata bayani.
Ta manta shaÉ—af. Ta ya zata manta da irin wannan tabo mai girma na rayuwar Badawiyya.
*"An cire mahaifar gaba É—aya, shi da kan shi ya cire mahaifar Asiya"*
Ta tuno kukan Badawiyya ranan da aka kaita É—akinta.
Ba zata manta ba, addu'ar samun ƙazantar ɗaki ta mata shine ta bata amsa da wannan ɗin.
Ta san labarinta lokacin da suke bibiyar case É—in Madam Bintu amma bata É—auka abinda Madam Bintu ta mata har ya kai wannan ba, ta É—auka kawai jaririn kawai aka kashe.
"I was only seventeen. Ban san anyi komai ba sai bayan kusan wata biyu da yin aikin, lokacin na samu lafiya har ana shirin sallamata. Ina tsaka da baƙin cikin kashe mini jariri da aka yi, then Dr Mustafah ya sake kawo min mummunan labari. Cewa yai anyi hakan ne dan a ceci rayuwata. Ko mi za a yiwa Madam Bintu yau ba zai taɓa dawo min da abinda na rasa ba"
Asiya ta riƙe baki tareda fashewa da kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Taya za ta manta da wannan abu Dan Allah. Yanzu Badawiyya sai ta ga kamar gori take mata. To wani gori? Ita dake da mahaifar ma mi ta tsinana ne, har yanzu dai ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Sai... sai...alokacin Azumi. Ta girgiza kai stress ne yasa bata ga jini ba a lokacin, kamar yadda Likita yace wancan karan wai stress na iya jirkita yanayin al'adar mace.
Sake kiran Badawiyya ta yi dan ta bata haƙuri amma sai ta ji numbar a kashe. Idanunta cike da ƙwalla ta tura mata dogon text na ban haƙuri tareda jaddada mata cewa mantuwa ce ta yi ba wai tayi maganar da wani niyya ba.
***
"Mommy, Mommy, Mom"
"What!"
Bilkisu ta juyo a fusace. Tsoro ƙarara ta gani a idon 'yarta dan haka ta ɗan sassauta murya tace "waya nake yi Nana, Please"
Ta maida wayar kunnenta ta cigaba da ihun da take wanda shine ya tada Nanan ma daga bacci.
"So, Rector na College of Agric ya bata award kuma an yi nominating É—inta a matsayin the best governor's wife. KuÉ—aÉ—ena dana baka fa?"
"I should calm down. Ok indai ba a nominating É—ina ba to lallai ba ta isa taci award É—in nan ba. Wani stupid Project ta aiwatar a jihar nan, eh?. Ni kuma da nake taimakawa marayu sannan na tura mutane Makkah da gumi na fa?. Don't tell me nonsense. Mtsw" ta katse kiran.
Zama tayi gefen kujera tana riƙe kanta da hannu biyu, yayinda dukkan jikinta ya ɗau zafi. Wannan cin mutunci ne a nominating Matar Gwamnar jihar Congo sannan a ɗaura sunan Asiya a kai. Yaushe ma ta aure shi? Three, no four years. Har ta cancanci a dangantata da Saifuddeen.
"She has no right to that award"
"Mommy" Nana ta sa hannu ta dafa kafaÉ—arta
Bilkisu ta juyo a wahalce ta fuskanci 'yarta, tunda Nana ta dawo gidan yau ne ta tsaya ta mata kallon ƙurilla.
16 year old addict daughter da ta sani ba ita ce ke durƙushe gabanta ba. Wannan kamilalliyar fuska gareta, ga maganarta nan mai sanyi.