← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 48

Sashe 34

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ta bar falon bai iya rufe bakinsa ba. Wancan karan da ta gaggaya masa maganganu bai ji zafin su ba kamar yadda maganganunta na yau suka dake shi.
Ba abinda ya ƙara rikita shi irin kalamanta na ƙarshe.
Shi bai ma san mi zai yadda da shi ba. Ga jarida nan Bilkisu ta bashi amma maganganun Asiya sun sake dulmiyar da shi kan sanin gaskiya. Shin waye ya sa aka buga jaridar nan wanda tabbas ita ake shirin fitarwa kafin Alhaji Sani yai bayani a gidan talabijin.

***

Asiya Shahidah na É—aukan sabon zango a shirinta na Asiya's Garden Badawiyya ta katse camerar lokacin da suka ji shigowar motoci cikin gidan.

Badawiyya tace "Ina ga kamar first lady ce ta shigo, da fatan kin tanadi bayani"

"Bismillah, tazo ina jiranta. Maganar ƙawarta Bintu zata yi ko kuma na ɗan yayarta ko ta mahaifinta?"

Ko minti uku bai cika ba sai ga Bilkisu ta doso inda suke, dake an kewaye wajen dole sai ta ƙofa ɗaya zaka shigo. Tana cikin tafiya takalminta mai tsini ya maƙale cikin ƙasa.

"Welcome to Asiya's garden, ki tsaya daga wajen a kawo miki takalmin gona" Asiya ta faɗa da ƙarfi muryarta cike da dariyar shaƙiyanci.

Bilkisu ta turo baki ta cigaba da tafiya tana yi tana tattaka albasar da Asiya ta shuka wanda sun fara fitowa sun yi tsayi.

Tana zuwa gaban Asiya ta ɗaga hannu zata kwaɗa mata mari Asiya ta riƙe hannun.

"Kar ki kuskura"

"Dani kike faÉ—a Asiya, leave my father out of this"

"Ni kuma? Mi ya ke faruwa? Ko dai dama da gaske ne Alhaji Sani ya sace miliyoyin kuÉ—aÉ—e?"

"How dare you say that! "

Bilkisu ta nuna ta da yatsa tace "wannan ce dama ta ƙarshe da zan baki Asiya, abinda zai biyo bayan wannan rana ba zai miki daɗi ba domin wutar da kika kunna a gida zai ƙona gari"

"I know how the game works Bilkisu Kachallah"

"Then be ready for a deadly game Asiya"

Daga faÉ—in haka Bilkisu ta juya ta tafi.

Badawiyya dake gefe ta riƙe baki tana faɗin "amma wannan mata akwai ƙarfin gwiwa, yanzu ko tsoron nata asirin ya tonu bata yi"

"Ƙyaleta. Ta ɗauka har yanzu ni Asiyar data tura kurkuku ce"

Badawiyya ta amsa da cewa " duk da haka ki bi a hankali bata da imani zata iya yin komai"

Da wannan suka cigaba da É—aukan shirin nasu...

***

Koda Bilkisu ta koma gida kiran Tanko Janwuya tayi ta bashi wani sabon Umarni duk da de yanzu a hannun Alhaji Umaru Kwom yake karɓan kwangila amma ai ba zai manta da Uwarɗakinsa ba.
Bayan ta gama bashi umurni ya kece da dariya yace mata a shirye yake yai duk abinda take so matuƙar zai samu kayan aiki da kuma alkhairin da ta saba yi masa.

Bata da lokaci, yanzu ne dai-dai lokacin daya dace ta yi amfani da damarta kafin ya suɓuce mata.
Saura kwana biyar saƙonta ya iso. Ance mata wannan sinadarin is untraceable, ba za a taɓa iya gano asalin sa ba. Duk wani likita duk wani bincike da za ayi zai tsaya ne akan cewa damuwa da gajiya su suka haifar da shanyewar jikin Gwamna Saifuddeen.

Wani abu ya tsartu mata a zuciya mai kama da soyayya.
A hankali rana ta farko da zata iya alaƙantawa da ranan ne ta fara yiwa Saifuddeen soyayya data wuce ta 'yanuwantaka ya dawo mata.
Duk da tana shekarun da za a iya cewa bata mallaki hankalin kanta ba amma har wa yau ta sani ranan birthday É—inta na cika shekara shabiyu a duniya da Saifuddeen ya bata kyautar rose flower ta ji a ranta idan ba Saifuddeen ba baza ta iya rayuwa da kowa ba har abada.
Zata iya rantsewa cewa har yanzu furen nan na cikin wani box da take saka jewelries É—inta a chan gidan Saifuddeen.

A hankali kuma ShaiÉ—an ya ingizo mata wani tunani wanda akoda yaushe shi ke rinjayanta take aikata duk abinda ta sa a gaba.
Ta miƙe tsaye tana jaddadawa kanta ba zata bari wani abu wai shi SO ya rufe mata ido ba.

"Soyayyata gare ka Saifuddeen ya ƙare ranan da ka shigo da waccar matsiyaciyar rayuwar ka. Na tsani zama a ƙarƙashin ikon ka, ba dan kai ba da Baba ya bani dama na zauna a kujerar da kake zaune. I should be the Governor. I am the Governor"

Kamar kullum da wannan sunbatun ShaiÉ—an ya ribaci zuciyarta, ko kaÉ—an bata birkita da umurnin data bawa Tanko Janwuya ba.

**

Zuwa yanzu Gwamna ya fara fiskantar matsin lamba daga 'ya'yan jam'iyya dama shugaban jam'iyya na jiha wanda ke barazanar kai ƙaran sa zuwa ga shugaban Jam'iyya ta ƙasa.

Idan har aka kama Alhaji Sani Kachallah ba ƙaramin tozarci bane ga jam'iyyar su, Alhaji Sani Uba ne a cikin jam'iyya, Uba ne ma a ƙasar gaba ɗaya.

So ake yai duk abinda zai yi domin kashe wannan gobara data kunno kai. Hakan na nufin bayarda cin hanci dama yin abubuwan da suka kasance abin ƙyama a tsarin mulkinsa.

Bai san inda zai sa kansa ba, idan ya tsoma hannunsa cikin wannan shari'a duniya zata zarge shi sannan idan ya bari aka tura Alhaji Sani kurkuku to kamar ya tozarta mahaifinsa ne da hannunsa.

A wani ɓangaren kuma dukka matan nasa biyu babu wanda zai iya tunkara da neman shawara dan dukkansu ya san manufarsu daban ne.

**

A wani makeken falo kuwa Chief of staff na Gwamna wato Mr Lamara Damana ke zaune da wasu mutane guda huÉ—u. Dukkan su kuwa ana damawa da su a cikin gwamnati.

Cikon na biyar É—in su ya zo ne minti goma shabiyu da fara tattaunawar su.

Mr Lamara yana ganinsa ya sake fiska domin shine mutum na ƙarshe da yake buƙata idan har kuwa ya zo tabbas ya nuna yana tare da shi kenan.

"Barka da zuwa Mr chairman Sir" Mr Lamara ya faÉ—a yana faÉ—aÉ—a murmushinsa.

"Just get straight to the point ka san akwai meeting gobe da safe"

Chairman ya faÉ—a yana duba agogonsa

Mr Lamara ya miƙe tsaye hannunsa ɗauke da wine glass dake ɗauke da wani sabon samfurin giya da aka kawo masa daga ƙasar Faransa.

"Mr Chairman na nemi kazo nan ne saboda mu nuna maka manufar mu akan wannan batu daya tada hankalin kowa"
Ya ɗan kurɓi giyan kaɗan sannan ya cigaba.

"kowa a nan ya sani Gwamna Saifuddeen Kachallah ba shi da ra'ayi irin namu kuma iya tsawon wannan lokaci Alhaji Sani da matarsa Bilkisu ke sa shi yin wasu ayyuka da mu 'ya'yan jam'iyya ke buƙata. To yanzu zance ya chanja, abubuwa da dama sun faru wanda yasa ahalin Gwamna Kachallah ke gab da rushewa."

Dukkan su suka bishi da kallo mai alamar tambaya idan ka cire Mr Paul wanda ya san kaso hamsin cikin tsare-tsaren da Mr Lamara yake yi.

"Mr Chairman ina so ka É—auke ido akan maganar Alhaji Sani Kachallah"

Chairman ya bishi da kallon tuhuma

"Ina nufin ka bari a karya ƙashin bayan Gwamna Saifuddeen"

Kallon-kallon aka fara yi wasu kuma na magana ƙasa-ƙasa, har lokacin kuma Chairman ɗin bai yi magana ba.

Wannan ya bawa Mr Lamara damar jefowa Chairman É—in wata maganar

"Mr Chairman Sir, ka dafa hannuna na zama Gwamnan jihar Congo"

Kowa a wajen ya zubawa Chairman ido ana sauraron mi zai faÉ—a.

Chairman dai bai bada gamsashshiyar amsa ba dan cewa yai amsar sa zata fito a meeting É—in da za a yi gobe.

***

Bacci take amma bai yi nisa ba dan har lokacin tana iya jiyo karatun suratul baƙara ƙasa-ƙasa da ta kunna kafin ta yi bacci.
Wayarta ya ɗau ƙara bayan karatun ya tsaya chak. Ta sa hannu ta laluma wayartata dake kan side drawer ta manna wayar a kunne ba tareda ta buɗe ido ba saboda bacci dake cinta.

"Hello Adda, Adda Shahidah Mansur ne, an sace Ale, Wallahi É—azu-É—azun nan aka shigo gida aka sace Ale"

Zumɓur ta miƙe dan kalaman da take ji sun mata wani iri a kunne. Tukunna ma waye Mansur?

"Hello waye wannan? Ka san mi kake faÉ—a kuwa?"

"Adda Mansur ne, Mansur ƙanin Ɗahiru da Asabe ya kira mata sunayen 'yan ɗakinsu. Ɗazu ɗazun nan wasu 'yan bindiga suka shigo suka sace Ale..." bai ƙarisa maganar ba taji ana faɗin
"Kai Mansur wa kake kira, ba ance kar ku kira kowa ba..."
Sai kuma wayar ta yanke.

Cikin kaɗuwa Asiya ta shiga kiran numbar amma bai shiga ba, nan ta shiga kiran nambobin matan Ale amma duka babu wacce ta ɗauka hakan ya ƙara tada mata hankali ta shiga neman nambobin ƙannen mahaifinta dan numbar Ale kam a kashe take tun gwadawar farko.

Sai bayan kusan minti takwas da jin mummunan labarin daga wajen Mansur sannan Baffa Malam ya ɗaga kiranta ya sanar da ita abinda ya faru. Da gaske ne 'yan bindiga sun zo garin na su kuma sun ɗauke Ale da wani maƙocinsa.

Batun birkicewa kam ba a magana dan a ruÉ—e Asiya ta kira numbar Commissioner of Police tana masa tsawa akan a nemo mata mahaifi. Bayan ta yi wayar ne kuma hankalinta ya dawo akan ko Gwamna bata gayawa ba. Haka ta fito daga É—akinta ta nufi É—akin Gwamna waya a hannu tana zubda hawaye.

Duk wani fushi dake tsakaninsu ya gushe a zuciyar Gwamna lokacin da Asiya ta kwanta jikinsa ta fashe da kuka.

Ƙoƙarin rarrashinta ya fara duk da bai san mi ya faru ba, kukanta na raunata masa zuciya. Sai da ta samu ta ɗan nitsu kafin ta sanar da shi abinda ya faru.

Bacci ranan gaba ɗaya ƙaurace musu yai ba dan ya hanata fita waje bama da bazata kwana a gidan ba. Duk wani bayani na kwantar da hankali ya mata amma taƙi sauraronsa musamman ma data dinga masa izgili da cewa a Gwamnatinsa ne mutum yana kwance da iyalinsa za a shiga gida a sace shi.
Babu abinda zai iya yi mata, duk wasu jami'an tsaro da zai kira ya kira ya sanar da su halin da ake ciki amma a haka gani take bai yi komai ba.
Chapter 34 · 0% Book details