Sashe 26
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mutane da dama musamman mata a cikin gida sun yi ƙoƙarin gwada abinda tace amma basu ɗauke shi da wani mahimmanci ba sai dai bayan wasu kwanaki abinda suka shuka ya fara fitowa wannan ya basu ƙwarin gwiwar cigaba da kula da shukokinsu.
A ɓangare guda kuma kasancewar Project Tomatonion ya bi ruwa sai ya zamana jikin mutane yayi laƙwas da harkar noma. Sai dai kuma ba a jima ba aka fitar da wani tsari daga gidauniyar LIGHT FOUNDATION, gidauniya ce ta wani tsohon Reverend mai retire mai suna Reverend Buba John. Gidauniyar ta haɗa hannu da wasu NGO daga ƙasashen turai tareda amincewar Gwamnatin jiha wajen kawowa manoma wani tsari da zai basu damar samun bashin gona, taki, iri, dabbobi, da ma wasu kayan aiki da ake buƙata a harkar noma.
Da farko wannan shiri bai samu karɓuwa ba saboda wasu malamai masu tsatstsauran ra'ayi dama bagidadan mutane dake iƙirarin wannan shiri da gidauniyar ta kawo ba komai bane sai wata hanya ce ta yaɗa ɓoyayyiyar manufar Reverend Buba John. Maganganu dai kala-kala dake kushe ainihin manufa da alfanun shirin...
*
"Ranki shi daɗe haɗa hannu da Light Foundation ba zai ba da abinda ake buƙata ba. Mutanen da suka bada sunan su basu kai 5% na manoma ba fa."
Badawiyya ta faɗa tana nunawa Asiya Laptop da ta riƙe
"Relax, na san za ayi hakan"
"Kin sani kuma kika yi shiru"
"Reverend Buba ne kaÉ—ai a faÉ—in jihar nan a binciken da nayi na gano cewa gidauniyarsa akwai gaskiya da amana. Ke da kan ki kika ce min gidauniyar Senator Mubarak ta kamfen ce ba dan al'umma aka kafata ba"
"To yanzu ya za ayi kenan tunda mutane sun ƙi ƙarɓan abin?"
"Na gaya miki zamu je fada gaisuwa ko?"
"Za ki yi amfani da Mai Martaba?"
Asiya tayi murmushi tace "Gaisuwa kawai zamu yi Badawiyya"...
**
"Something is fishy Mr Lamara, taya za ayi ace kwana biyu da zuwanta fada Sarki ya fito ya ƙaddamar da shirin Reverend Buba"
Mr Lamara ya ƙara duba jaridan hannunsa da kyau inda Mai Martaba Sarkin Congo da Reverend Buba suka haɗa hannu suna murmushi.
"Ba zan ce akwai hannun Asiya a ciki ba dan babu ta inda zata samu kuÉ—in da za ta sayi abubuwan nan"
"To ina Reverend ya samu uban kuÉ—in nan?"
"NGO mana"
"Oh please! Kai kan ka kasan ba duka kuÉ—aÉ—en da ake turowa ke shiga hannun Reverend ba.
"Wai ko dai Saifuddeen yabi ta baya ya bata kuÉ—aÉ—en nan ne?"
"No, da an fitar da kuÉ—in dole zan sani, beside kuÉ—in dayawa sosai Gwamna ba zai iya biya lokaci guda ba"
Bilkisu ta tura jaridar gefe tace " koma minene dai babu yadda za ayi shirin nan ya karɓu a wajen mutane"
"Mi kike so ayi?"
"Ka ɓatawa Mai martaba suna, ka chanja labarin..."
Sakatariyar Bilkisu ta banko ƙofar office da ƙarfi tana faɗin " sorry your excellency amma ban sani ba ko kin kalli news da ake yi yanzu?"
Bata jira Bilkisun ta amsa mata ba ta É—au remote na tv ta chanja zuwa tashar Hill TV.
"Bayan wannan video ya fito hukumar NDLEA ta bayyana Madam Bintu Chadi a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da take nema ido rufe. Yanzu haka bincike da ake yi a cikin gidan Madam Bintu ya daɗa tabbatar da cewa ita ɗin ficacciyar mai fataucin miyagun ƙwayoyi ce"
Bilkisu Kachallah ta miƙe zumbur ganin an nuno gidan Madam Bintu inda ake fito da tsagoron bandir-bandir na kuɗi kama daga kuɗaɗen Nigeria har na ƙasashen waje.
Mai karanto labarin ya cigaba " ba iya nan ya tsaya ba. 'Yar sanda mai retire wato Rabi'atul Badawiyya Kabir tana iƙirarin Madam Bintu da kashe mata jariri da yunƙurin kasheta shekaru kusan goma shabakwai da suka wuce, sannan ta sake tuhumarta da cinye dukiyar mijinsu wato marigayi Alhaji Rufa'i"
"Oh my God!" Bilkisu ta faɗa tana dafe ƙirji...
21
***
Kwana biyu ana neman Madam Bintu amma babu dalilinta. Ita kanta Bilkisu Kachallah bata san ina matar ta shiga ba balle ta san yadda za ayi ta taimaketa. Ta dai baza mutane ko'ina akan a nemo mata Madam Bintu kota halin ƙaƙa.
A ɓangaren Asiya kuwa ta samu labarin Madam Bintu shigar maza tayi ta bi motar akori-kura aka fice da ita daga cikin gari. Bata san takamaimai wani ƙauye ta ɓoye ba amma tasa a binciko maɓoyarta kafin Bilkisu ta gano inda take...
***
Sumayya da Jummai suna zaune a falo suna faÉ—a akan remote É—in TV Badawiyya ta shigo falon da sallama.
"Anty Badawiyya" suka faÉ—a a tare suna rige-rigen rungumarta.
"Duk ranan dana shigo gidan nan na same ku a nutse zan muku kyauta"
"Anty Wallahi ita ce ta raina ni"
Sumayya ta faÉ—a tana hararan Jummai
Jummai tayi caraf ta amsa "Wallahi Anty ni nayi resfek É—inta sosai, ita ce take da kishin tsiya"
Badawiyya tayi murmushi tace " to ki cigaba da resfek É—inta dan ta girmeki kin ji"
Sumayya ta tintsire da dariya ganin Badawiyya ta biyema Jummai.
Tunda Jummai taji kalmar (respect) a bakin Asiya watarana da take musu faÉ—a shikenan ta kama, magana É—aya biyu sai ta nemi dalilin da zata jefa kalmar ciki.
Ita Sumayya tunda ta nemi gyara mata kalmar akan ba dai-dai take faɗa ba Jummai ta hayayyyaƙo mata sai ta haƙura ta barta.
A kitchen Badawiyya ta samu Asiya tana sauke wannan É—aura wannan. Dan abin ya bada armashi ma har apron ta saka da doguwar hular nan irin ta masu dafa abinci.
"Gaskiya ne tawan, girki sai kace ana competition"
"Dan Allah duba min oven ina jin kazar nan ta gasu" Asiya ta faÉ—a tana kwashe dankali daga cikin mai.
Bayan Badawiyya ta fito da kazar ta kalli Asiya cikin zolaya tace " Excellency kaza kam ta ƙone fa"
"Haba" Asiya ta juyo a firgice
Ganin yadda Asiya ta ƙwalalo ido waje sai Badawiyya ta sa dariya tana turo mata tray ɗin gabanta.
"Amma Rabi'atu zan..."
Badawiyya ta haÉ—a hannu biyu tana faÉ—in " sorry ma"
Tare suka ƙarisa girkin suka kai falon Gwamna suka jera. sai da suka gama komai sannan Asiya ta samu daman sauraron abinda ke tafe da Badawiyya.
"Mun samu abinda muke nema akan Alhaji Sani Kachallah. Har abinda bamu yi tunani ba mun samu"
"Mi kike nufi?"
Badawiyya ta miƙa mata wasu takardu tace " Alhaji Sani Kachallah ya jima yana badaƙala da dukiyar jama'a. Wannan da kike gani list ne na duk wasu kwangila da aka karɓa a hannun Gwamnati amma ba a ƙarasa ba wasu kuma ba a ma fara ba kuma an cinye kuɗin"
"A ina aka samu waÉ—annan takardu haka. WaÉ—annan kwangilar ai akwai na shekaru ishirin baya ma, tun 90's fa. Wa yake bamu waÉ—annan confidential information haka?"
"Wanda ya bamu shaida akan M Sani shine ya bada wannan" Badawiyya ta amsa mata
Asiya ta zaro ido waje dan mutum É—aya take tunanin ya aiko musu da Shaidar da zai tarwatsa M Sani, kuma yanzun ma shi take tunanin ya aiko wannan to amma miyasa zai yi hakan?
Badawiyya ta ce "yes shi É—in ne dai da kike zargi tun tuni. Na sa an bincika min numbar motar mutumin da ya kawo takardun nan kuma an faÉ—a min sunan sa ne akan rajistar motar"
"Akwai wani abu a ƙasa Badawiyya, ba yadda za ayi ya bamu evidence irin wannan sai dai idan wani abu yake nema"
"Nima abinda nake tunani kenan, ni a tunanina ina ga so yake yai amfani dake ya kawar da Bilkisu"
"He's dangerous Badawiyya, ba wannnan kaÉ—ai ne a ransa ba, ni nafi tunanin so yake ya kawar da Gwamna dan ya cimma burinsa"
"Kina nufin irin abinda aka yiwa Saminu Bacchi?"
"Eh mana" Asiya ta amsa cike da damuwa a ranta.
Itama Badawiyyan shiru tayi tana nazarin wannan batu tabbas biri yai kama da mutum, idan ba haka ba taya Mr Lamara Damana zai so taimaka musu ba tareda sun buƙaci taimakonsa ba...
***
Mr Lamara Damana yana zaune a office ɗinsa aka kira shi aka sanar dashi Gwamna ya shigo gari wani ƙayataccen murmushi yai domin ya hango nasara a tarkon daya haɗa.
A hankali ya fara juyi da kujerarsa, tabbas nan bada jimawa ba wannan kujera da ya ke kai zata koma kujerar Gwamna.
Kalaman Yallaɓai ya tuna lokacin daya je masa da buƙatar Bilkisu Kachallah.
"Lamara Damana na jima ina karantar ka, na san mi kake so, na san kuma minene burin ka. Shawara É—aya zan baka kuma ko bana nan ita ce zata taimaka maka"
A lokacin da Yallaɓai yai wannan magana ko kaɗan bai ɗauki maganar da mahimmanci ba amma kuma bai manta da maganar ba tana nan a ƙasan zuciyarsa.
"Dama ta kan zo wa mutum lokaci guda ne a rayuwa, idan ta wuce ta tafi kenan har abada, abinda ya rage shine mutum ya cigaba da bincike yana neman wata damar daban amma ba wancan data wuce ba. Wannan kuma ya rage ga ƙaddararsa, walau ya samo wata damar mai kamar waccan ko wadda bata kaita ba, walau kuma ya cigaba da nema har ƙarshen rayuwarsa ba tareda ya samu ba.
"Mr Damana kana da dama ɗaya na zama Gwamna a jihar nan, idan ka bari ta suɓuce maka zaka ƙare rayuwar ka cikin nemar wata damar amma kuma ba zaka taɓa samu ba"
Kusan shekaru uku kenan da Yallaɓai ya masa wannan magana amma kuma sai yanzu ne ya fahimceta da kyau.
Yanzu ne yake da damar zama Gwamnan jihar Congo kuma ba zai taɓa bari wannan dama ta kufce masa ba.
DaÉ—in abinma yana zaune ba tare da wahala ba dukkan wani shiri da ya tsara zai cimma nasara.
Bilkisu tana son ture Gwamna daga kujerarsa. Ita kuma Asiya tana son ture Bilkisu daga jikin Gwamna.
Babu abinda zai yi illah yai amfani da Asiya ya kawar da duk wani wanda zai kawo masa cikas wajen cikar burinsa.
Asiya ita ce maganin matsalarsa
Da wannan tunani ya yai amfani wajen tsara duk wani tarko daya É—ana, kuma yau É—in nan É—aya daga cikin tarkon daya kafa zai kama zomo.
Mr Lamara Damana yai murmushin gefen baki haÉ—e da jijjiga kansa a hankali cike da farin ciki...