← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 48

Sashe 37

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Gwamna ya zo gaishe da Ale FaruÆ™ tareda yi masa jaje. Bai samu ganin Asiyar ba sai da zai tafi ita kuma ta shigo É—akin Ale da alama bata san har lokacin yana nan ba ko kuma dai ta shigo É—in ne dan su haÉ—u.

Kallon-kallon suke domin ta ido suke aikawa junansu saƙonni

"I'm sorry Asya" ya furta a hankali lokacin da ya matso kusa da ita.

Yana shirin taɓata ta wafce hannun tareda watsa masa harara.

"Baba ya ce in miki gaisuwa"

Tana da labarin shi ne ya matsawa Lawyoyin Alhaji Sani Kachallah dan a ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke masa.

Sun jima suna aikawa junansu kallon tuhuma kafin Gwamna ya samu ƙarfin ficewa daga ɗakin.
Abin baƙin ciki abinda masoyan suka zamo kenan. Har ya fice daga ɗakin ba ta iya yin kyakykyawan numfashi ba saboda yadda ƙanshinsa ya gauraye ɗakin Ale. Wani ɓangare nata yana kewar kasancewa a ƙirjin shi tana jin bugawar zuciyar shi. Wani ɓangare nata yana kewar dogayen hannunsa da idan ya zagayeta da su take ganin tana cikin ni'ima da kwanciyar hankali.
Ba irin wannan rayuwar ta hasaso ba lokacin da suke chan America. This is not the return she planned for.

"Asiya kina ina?" Muryan Ale ya katseta

"Gani Baba"

Sai da ta zauna gefensa ya riƙo hannunta yace "Mijin ki ya fita ko?"
GyaÉ—a kai ta yi kamar yana iya kallonta.
"Ki yi masa haƙuri kin ji, koma minene ya faru ba laifinsa bane. Gwamna yana iya ƙoƙarinsa Abin ne yafi ƙarfinsa. Na sani kina ɗaura masa laifin abinda ya same ni, amma idan kika duba da kyau zaki ga abinda ya faru yana daga cikin ƙaddarata babu yadda za ai na iya tsallakewa"

"Baba ƙaddara ne amma da sakaci. Akwai sakacin shugaba Baba, Gwamna mijina ne, ni na san baya ƙoƙartawa yadda ya kamata. He's a coward, he's just a coward" ta ƙarisa maganar kaman zata yi kuka.

"To ki yi ta masa addu'a mana, sannan ki taimaka masa da shawarwari ki kuma dinga tunasar da shi kowanni lokaci, kada ki taɓa gajiya da hakan kin ji shalelelen Gwani"

Ba dan abinda ya faru ba da sai tace ta yi mamakin kalaman Ale, wai shine ke yi mata nasiha mai taɓa zuciya haka...

***

Har aka ƙare Azumi aka yi sallah Asiya ba ta saka ranan komawa gidan ta ba. Ta bada mahimmanci wajen kula da mahaifinta. Ba dan ma albishir da Badawiyya ta mata ba na cewa Dr Mustafah ya kai kuɗin aurenta da ba za ta saka ranan komawa garin Congo ba.

Badawiyya tamkar 'yaruwa ce a gareta dan haka dole ta je ta tsaya a kan maganar bikinta.

Sallah da kwana takwas Asiya ta shirya komawa Congo.

*
Gwamna Saifuddeen Kachallah yana office ɗinsa wayoyinsa biyu suka hau ringing lokaci guda. Wayar farko numbar Asiya ke kira ɗayan kuma baƙon numba ne, truecaller ya kawo masa sunan Bashir Faruƙ Baba. Yayi mamakin ganin kiranta dan a lokuta biyu daya gwada kiran numbarta a lokacin Sallah da kuma bayan Sallah bata amsa kiran ba.

Har É—an sandan ya gama bayani Gwamna Saifuddeen bai san inda kansa yake ba. Cikin gaggawa ya fice daga office É—insa yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun a bayyane.

Zama yai a kujeran dake gefen gadonta ya ƙura mata idanu. Ta yi fayau da ita abin har ya bashi tsoro, ko dan ya jima bai mata kyakykyawan gani bane.
A hankali ya fara bin zanen lallen da ke yatsunta wanda yadda suka yi ja zur da su suka ƙarawa yatsunta kyau.

Jini leda uku za a ƙara mata dan tana buƙatar jini sosai. Wanda aka saka mata na ƙaninta ne Bashir wanda yake aiki a Asibitin, shine kuma ya kira Gwamna lokacin da aka kawo Asiya jina-jina. Allah ma ya taimaka inda hatsarin ya faru kusa da gari ne da a haka jinin Asiya zai ƙare har ta mace babu taimakon gaggawa.
Ita da dreban ne kawai suka samu rauni mai tsanani amma Jummai dake bayan motar tareda Asiya ba ta wani ji ciwo na a zo a gani ba dan cikin hayyacinta polisawa suka kawo su Asibitin. Ita ne ma ta ƙwalawa Bashir kira lokacin da suka shigo Asibitin ta ganshi yana gaisawa da wani likita.

Asibitin General Hospital dake ƙaramar hukumar Giwo na ɗaya daga cikin Asibitocin ƙananan hukumomi da Gwamna ya gyara kwanan nan. Dan haka kusan duk wasu kayan aiki da ake buƙata akwaisu a Asibitin.

"Your Excellency gaskiya ba zamu iya cewa akwai abinda ya taɓa kanta ba har sai anyi CT scan" babban Likitan Asibitin Dr Muhammad ya bayyanawa Gwamna.

"Akwai abinda ya kamata ka sani Ranka shi daÉ—e"
Sai daya ja numfashi sannan ya cigaba "Hajiya Asiya ta yi ɓari, inaga ba zai wuce sati biyar zuwa shida ba, wannan nema ya sa ta zubar da jini sosai"
Har ya gama maganar sa Gwamna Saifuddeen bai ko ƙyafta ba daga irin kallon daya ke masa na rashin fahimta.

"Ban gane ba?" yai tambayar cike da fatan abinda Likitan ya faÉ—a kuskurene.

"I'm sorry your Excellency. Cikin dake jikinta ya zube" yai maganar da yaƙinin cewa Gwamna ya san da zaman cikin a jikin Asiya.

Gwamna ya sa hannu biyu ya riƙe kansa yayinda idanunsa suka ciko da hawaye...

*
Farkawar Asiya na farko a cikin motar ambulance ne, dishi-dishi ta dinga ganin mutanen ciki, ba ta iya ganin fuskar mutumin daya riƙe mata hannu ba dan ya mata tsayi dayawa kusan sakan biyar ta ɗauka kafin ta sake rufe idonta, tana jin wani murya sama-sama yana faɗin "I love you Asya, i really..." shikenan bacci ya sake ɗauketa.

Lokacin da Asiya ta farka na biyu da ƙarfin jikinta ta buɗe ido dan alluran da aka mata ya fara saketa. Babu kowa a ɗakin sai ƙaran na'orori da kuma ƙaramin fridge dake ɗakin.
Sai da ta kusa minti biyar a farke kafin aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.

Kallo É—aya ta masa ta gane cewa Likitan Gwamna ne.

"Your Excellency kin tashi, akwai inda ke miki ciwo?"

Asiya ta nuna kanta wanda har yanzu yana naÉ—e da bandeji.

"Bayan kan babu inda yake miki ciwo?"

Likitan ya sake tambaya. Asiya ta girgiza masa kai.

"Jummai, Jummai da Direba fa?"

"Suna nan"

"Babu abinda ya same su?"

"Ba sosai ba. Akwai allurar da zan miki yanzu"

Ta ɗan gyaɗa kai amma chan cikin ranta tana ganin kamar akwai wani abinda Likitan yake ɓoye mata.

Gwamna ne ya shigo É—akin bayan fitan likita, suna haÉ—a ido ta kauda kai gefe.
Hannunta ɗaya ya riƙe ya kissing yatsunta.
"Yaya jikin ki?" Ya tambaya yana kissing tafin hannunta.

Akwai abubuwan da take son faɗa masa amma bata da ƙarfin dogon magana da shi. Ƙoƙarin janye hannunta tayi yai saurin riƙe hannun gam, ta bi hannunsu da kallo ba tareda tayi magana ba.

"Asya ki yi haƙuri dan Allah. Na sani ban kasance dake ba a lokacin da kika fi buƙatana, i'm sorry. Ki manta da komai mu dawo da farin cikin dake aurenmu"

BuÉ—e baki tayi kamar za ta yi doguwar magana amma abinda ya fito daga bakinta shine " ka sake min hannu"

"Shahidah please"

Ta so ace abinda ya faɗa mai sauƙi ne amma babu sauƙi ko kaɗan. Matuƙar yana Gwamna ba za ta iya rufe ido ta ɗauke shi matsayin mijinta ba, yes mijinta ne babu shakka amma a lokaci guda kuma shi ɗin shugaba ne wannan kuma yafi komai mahimmanci. Idan har zai zame mata miji nagari a cikin gida amma a wajen talakawa zai zamo azzalumin shugaba, minene ribarta.

Babu ta yadda zata manta da abubuwan da suka faru domin ko ta manta irin haka ba zai daina maimaituwa a rayuwarsu ba matuƙar dukkansu biyun basu fiskanci alƙibla ɗaya ba.

Ganin ta ƙi kula shi sai ya miƙe tsaye ya kissing kumatunta yana mata addu'ar samun lafiya.
Bayan fitansa ta maida dubanta ga ƙofar tana jiran ya sake buɗe ƙofar ya shigo wannan karan ya rungumeta jikinsa yace ya yadda da ita ɗari bisa ɗari ba zai sake zarginta ba.

***

Bilkisu Kachallah ta kasa zaune ta kasa tsaye. Agogon office ɗinta ya nuna ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Tunda aka gaya mata Asiya na nan da rai hankalinta ya tashi, ƙarin baƙin cikin shine babu wani ciwo da ta ji na a zo a gani . Labarin daya ɗan daɗaɗa mata rai shine ce mata da aka yi Asiya ta yi ɓari. Wato dama ashe ciki gareta, cikin Saifuddeen.
Ta riga ta ɗau alƙawari a wajen meeting ɗinsu kan cewa za ta kawo ƙarshen matsalar Asiya. Waɗannan mutane suna tsoron hukumar EFCC kamar yadda su ke tsoron mutuwarsu. Ita kam ba damuwarta ba kenan, ta fi damuwa da ƙuri'un da talakawa zasu jefa mata idan lokaci ya zo, hukumar EFCC ba za su iya taɓata ba.

Dole ta yi wani yunƙuri akan Asiya amma kafin nan bari ta samu ganawa da mataimakin Gwamna tukunna.

***

"Your Excellency shugaban gidan jaridar The Daily Breeze yana jiranka"

Gwamna Saifuddeen ya amshi takarda daga wajen Sakatarensa sannan yace "kace ya shigo"

Bayan ya saka hannu a takardun ya miƙa wa Sakatare su dan a miƙa su ofishin da suka dace.

"Your Excellency"

"Mr Odu"
Gwamna ya kira sunan mutumin yana faÉ—aÉ—a murmushinsa.

Sai da Gwamna ya mai nuni da kujera sannan Mr Odu ya zauna har lokacin bai bar yin murmushi ba.

Gwamna ya buÉ—e drawer dake manne da table É—insa ya É—auko wani jarida ya ajiye gaban Mr Odu.

Ko da Gwamna bai ce komai ba, Mr Odu ya riga ya san mi Gwamnan ke nufi da jaridar. Cikin biyu ne yai ɗaya, ko ya faɗi gaskiya ya samu dama a wajen Gwamna ko kuma yai ƙarya ya sake matse Mr Lamara Damana akan ya ƙara wasu maƙudan kuɗaɗe dan ya rufa masa asiri...

***
Chapter 37 · 0% Book details