← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 48

Sashe 1

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

01

***

"Nana ki fito mu yi breakfast da Daddy" muryan Mahirah ya doki kunnen Nana da ke zaune chan ƙuryan gado tana maƙyarƙyata. Minti biyar da suka wuce ta fito zata je dinning ta yi kiciɓis da macijin mommynsu ta koma ɗaki a guje jikinta na maƙyarƙyata. Ba yau ne hakan ya fara faruwa ba, ranan da ta fara ganin macijin a nannaɗe a hannun mommynsu sai da ta kusa shiɗewa saboda tsoro, a hakan sai Mommyn na su ta shiga yi mata faɗa wai babu abinda macijin zai mata it's just a pet snake. Pet snake kamar wanda suke zaune a daji. Tunda suka zo gidan ko kyanwa babu balle kare amma a rasa pet ɗin da za a kawo gida sai maciji.

Su uku ne zaune a wajen dinning É—in, yau ne É—aya daga cikin ranaku biyu da Gwamna ya tilastawa kansa zama yai breakfast da 'ya'yansa. A yanzu kam zama da 'ya'yansa shine kaÉ—ai ke saka masa nitsuwa.

Mahirah ta miƙe ganin har yanzu Nana ta ƙi fitowa, bayan tafiyar Mahirah Gwamna ya zubawa Junior idanu yana kallon yadda yaron ke wasa da abincin da ke gabansa, gani yai yaron ya rame masa kuma babu walwala a tattare da shi kamar da.

"Babana" Gwamna ya kira shi a hankali, amma maimakon da idan ya kirashi da hakan yake cewa shi ba Babansa bane, yau kam ko É—aga idanunsa bai yi ba balle ya tanka masa.

Gwamna ya riƙo hannun yaron yana faɗin "Sa'ad junior"
Ai kafin ya ƙarisa maganar Junior ya challah ƙara yana faɗin "Mommy no snake, please no snake"

Gwamna ya taso ya rungume Junior tsam a jikinsa yana bubbuga masa baya. Shi kansa wannan maciji da Bilkisu ta kawo gidan ya tsaya masa a rai amma ya kasa yi mata magana a kai.

Mahirah ta fi minti biyu tana buga ƙofar ɗakin Nana kafin da ƙyar Nanan ta ja jiki ta zo ta buɗe mata.

"Miyasa kika kulle ƙofa?... Nana miya sameki?... kuka kika yi?"

Shiru babu amsa sai kuka da Nanan ta sake fashewa da shi.
"Nana minene please?" Mahirah ta faÉ—a itama kaman zata yi kuka.

"Mom...Mom... Mommy's snake" ta faɗa da ƙyar.

"A ina kika ganshi, Mommy ta fita da shi É—azu"

Nana ta yi shiru ta kasa magana dan kanta ya ruÉ—e shin kafin Mommyn ta fita da shine ta ga macijin ko bayan an fita da shi?

"Kar ki damu babu abinda zai miki, ki zo muje mu karya Daddy na ƙasa kin san ba wai koyaushe muke ganinsa ba"

Da ƙyar Nana ta amince suka sauko ƙasa. A nan suka tarar Daddyn nasu na fama da lallashin Junior.

Mahirah tace "Daddy dan Allah ka ce Mommy ta dena yawo da macijin nan. Nima ba wai ina son shi bane, amma Nana da Junior always panic idan suka ganshi. Daddy dan Allah kayi wani abu akai"

"Ku kwantar da hankalinku, zan mata magana"

Safiyar ranan dai sun ci abincin ne a darare dan kowa ba wai ya ci da kwanciyar rai bane.

***

Nana da Mahirah suka shiga haɗa kayansu da sauri-sauri saboda basa so mahaifiyarsu ta dawo ta samesu a gidan. Kwana uku kenan da Daddy yai musu alƙawarin zai yiwa Mommy magana amma babu abinda ya chanja dan ko yau da safe da macijin Mommynsu ta fita. Jiya da yake Mommy ta wuni a gida Nana ko iya fitowa bata yi ba saboda tsoro dan idan Mommy na gida tana barin macijin yai ta shawagi tsakanin ɗakinta da kuma falon ƙasa.

Sai da suka gama haɗa komai sun sauko da akwatunan kawai suka ji ƙaran siren.

"Mommy" Nana ta faÉ—a a tsorace

"Inaga Daddy ne fa"

"Mommy ce Mahirah" Nana ta faÉ—a tana shirin kuka.

Mahirah tayi ƙarfin hali tace "koma Mommyn ce mu tsaya mu gaya mata matakin da muka ɗauka"

Suna tsaye riƙe da akwatuna Bilkisu Kachallah ta shigo biye da ita kuma wasu manya-manyan mata ne guda biyu da suke matsayin personal bodyguards ɗinta. Ko a ina ta samo su oho, dan kuwa basu yi kama da 'yan Nigeria ba. Sun fi kama da black Americans da suka ƙware a body building. Da za su cire rigan jikinsu babu tantama sai ka ga 6 abs kaman a jikin shaharraren ɗan damben nan The Rock. Suna sanye da baƙaƙen kaya riga da wando da kuma baƙin gilashi da suka toshe idanunsu da shi, fiskarsu a ɗaure babu alamun fara'a ko kaɗan.

"Ina zuwa?"

Nana ta É—an matsa bayan Mahirah, duk da babu macijin a hannun Bilkisu amma a karan kanta Mommyn na su yanzu tsoro take bata.

Mahiran ma tsoron ne ya É—arsu a zuciyarta lokacin da suka haÉ—a ido da Bilkisu Kachallah.

"Ehen, ina zaku je kuka tattaro kaya kaman masu shirin ƙaura?"

Mahirah ta haÉ—iye miyau tana karanto addu'a a ranta *Allahumma lah sahla illa ma ja'altahu sahla...*

"Khadijah, Mahirah, baku da baki ne?"

"Mommy.... Kachallah house zamu je. Ba zamu iya zama a nan ba, idan kina so mu zauna ki zaɓi ko mu ko macijin ki"

Bilkisu ta yi mamakin ƙarfin halin Mahirah. Yarinyar da ada bata iya buɗan baki tayi magana idan tana wajen sai gashi ita ce ke ɗaga murya a gabanta. Ita fa yanzu ta kai matsayin da babu wani mahaluki da zai ɗaga mata murya, not her parents, not her husband and especially not 'ya'yan data haifa balle bare.

Hannu ta É—agawa guards É—inta masu suna Vayentha da Mistica nan da nan suka sara mata suka bar falon da sauri.
Bayan fitan su Bilkisu ta maida dubanta ga Mahirah tace "ni kike ɗagawa murya Aisha, are you cra...zy" ta wanke Mahirah da mari sai da yarinyar ta faɗi ƙasa.

"Nobody shouts at me. Nobody gives me orders. Kai ku sawa ran ku cewa daga yanzu babu mai fita daga gidan nan sai da izinina. Kachallah house or not babu inda zaku je daya wuce makaranta, Islamiyya ma na soke shi daga yau, zan sa malami ya dinga zuwa gida yana koyar da ku. Now get out of my sight"

Kafin ta ƙarisa maganar Nana ta yi sama a ɗari. Mahirah kuma ta miƙe riƙe da fiskarta tace "Mommy dan Allah ki bari mu tafi ko ba dan ni ba, Nana zata iya suma idan ta sake ganin macijin nan, Junior ma..."

"Oh! Ba za ki dena magana ba kenan. Mahirah ni kam aiko ki aka yi ne?"

Mahirah ta juya zuciyarta cike da ƙunci tana addu'ar Allah ya shiryi mahaifiyar su.

***

*Ya Hayyu Ya Qayyum. Ya Hayyu Ya Qayyum* abinda Asiya ke maimaitawa kenan lokacin da warden Maida ta buɗe ƙofar cell ɗinta.

"Asiya Kachallah ki fito Lawya zata ganki"

Lokacin da suka ƙarisa wajen da Barr. Zaytoonah ke jiranta sai Asiya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Warden Maida ta daka mata tsawa akan ta tashi, sai dai tana ƙoƙarin tashi ta sake faɗuwa saboda jikinta da babu ƙwari. Warden ta sa kulki ta ɗan shureta hakan yasa Barr Zaytoonah ta daka mata tsawa.

Bayan fitan warden Maida Asiya ta ƙyaftawa Barr Zaytoonah ido, Zaytoonah ta ɗaga mata babbar yatsa alamar jinjina.

Ba wani magana suka yi mai tsawo ba daya wuce ta kwantar da hankalinta komai zai tafi dai dai.

"Barr Zaytoonah jaridar"

Zaytoonah ta fito da jarida daga jaka ta miƙa mata, hoton Gwamna Saifuddeen daya ke shafin farko ne ya ɗauke mata hankali. *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya riƙe albashin ma'aikata*

"Wannan watan ma bai biya albashi ba ko?" Asiya ta faÉ—a a hankali

"ya rage albashin malamai ma ki duba shafi na biyar zaki gani"

Duk da Asiya ta sani shafi na biyar shine shafin da Zaytoonah ta rubuta mata saƙo amma a yanzu ta fi damuwa da chanjawar da Gwamna yai, wai wata biyu kenan bai biya albashin ma'aikata ba.

Ta buɗo shafi na biyar ta fara karanta saƙon da Zaytoonah ta rubuta.

"Zasu kawo Timothy mutumin da BBC eye tayi hira da shi, na san an riga an biya shi akan ya nuna cewa ke ce uwar É—akinsa, amma kar ki damu na san yadda zan yi na rushe duk wani hadda da aka sa shi yai. There's hope, ki cigaba da addu'a"

Asiya ta rintse ido sai hawaye. Ba komai ke damunta ba fiye da yadda Gwamna ya koma azzalumi.

***

A zaman kotu na gaba, Barr. Zaytoonah ta gabatar da video da ta naɗa lokacin da warden Maida ke ƙoƙarin ture Asiya tana mata tsawa.
Ta yi nuni da cin zarafin client ɗinta da aka yi bayan kotu bata zartar da hukunci akanta ba. Idan Kotu ba ta bada bail ɗin Asiya ba hukumar human right zasu shigar da ƙara saboda an take haƙƙin Asiya.

Da wannan kotu ta bada bail É—in Asiya, amma zata zauna under house confinement ba me zuwa wajenta kuma ba fita sai idan zata je kotu ko kuma idan akwai emergency.

Bilkisu na jin wannan labari ta dinga ihu dan a yadda ta tsara Asiya ba zata bar kurkuku ba sai ta serving jail sentence na aƙalla shekaru goma.

"Ban gane an bada bail É—inta ba, yaushe za a gabatar da Timothy ne?"

"Sorry Boss Lady ya kamata Agent Dahlia ta zo da shi kotu wannan zama da aka yi amma bata zo da shi ba, i think... "

" Don't think Lamara, you should act" Bilkisu ta daka masa tsawa.

***

Ranan da aka maida Asiya gida haka ta dinga ƙarewa ɗakinta kallo domin ya mata faɗi, zaman sama da wata ɗaya da tayi a ɗan ƙaramin ɗakinta na kurkuku sai take ganin ɗakinta na gidan Gwamna ya zamo tamkar wani mansion.

Bata yi tunanin ganin kowa ba dan Zaytoonah ta faɗa mata cewa babu wanda zai zo wajenta aside ita da take lawyarta sai kuma masu kawo mata abinci. Ko ina Sumayya da Jummai suka shiga? bata gan su ba har aka shigo da ita cikin falonta. Kuma ya kamata ace suma sun tsaya a ƙofar gida kamar yadda Yaya Bello ya tsaya suka gaisa a tsanake.
Lokacin da ta yi sallar Isha sai ta kwanta dan ta huta amma sai ta kasa bacci, ta takure gefe guda tana maƙyarƙyata. Yadda sauro suka cizeta a kurkuku, ka ɗauka duka sauron cikin kurkukun ne suka tare a ɗakinta.
Chapter 1 · 0% Book details