Sashe 24
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abba ya kamata mu je asibiti a tabbatar da sanadin mutuwar nan" babban É—an Alhaji Abdullahin ya faÉ—a yana dafa hannun mahaifinshi.
"Yaushe har Abida ta yi wayon da za ta kashe kanta. This is murder" yai maganar ƙarshen cike da tsananin ɓacin rai.
Alhaji Abdullahi ya sake ƙanƙame gawar tareda faɗin "i'm sorry Abida, ki yafe min, ki yafe min kin ji". Haka ya cigaba da sunbatu yana rungume da gawar yaƙi sakewa.
Da ƙyar aka ɓanɓare Alhaji daga jikin gawar lokacin da ƙannensa da 'yanuwansa suka shigo.
Wannan abu ya faru ne lokacin 'yan gidan sun je biki a Lagos. Da alama yarinyar ta zaɓi kashe kanta ne a dai-dai lokacin da gidan yake babu kowa sai ma'aikata da kuma yayyunta maza biyu. Ita ɗin ma da ƙyar ta sha kafin mahaifiyarta ta yarda akan ba za ta je bikin ba. Kasancewar kusan wata guda kafin mutuwar yarinyar ta chanja gaba ɗaya ,shiyasa babu wanda ya kawo komai lokacin da ta nace akan ba za ta je biki ba duk da kuwa bikin na gida ne.
Alhaji Abdullahi bai tsananta bincike ba dan ya riga ya samu suicide note ɗin da Abidar ta bari kafin mutuwarta. Abinda ya ƙara gigita shi kenan saboda sanadin mutuwartata yai kama da abinda ya aikata kusan shekaru ashirin da takwas da suka wuce. Bai taɓa dana sanin abinda yaiwa Halima Kachallah ba sai yau. Ashe da ciwo aiwa 'yar cikin ka fyaɗe. Ashe da ciwo na kusa da kai yai wa 'yar cikin ka fyaɗe.
Mu'azu tamkar ɗan cikinsa yake, tun yaron yana rarrafe aka bashi riƙonsa. Har iyau kuwa yaron bashi da uban daya fi shi, amma...
**
Gwamna yana tareda Asiya suna tattauna batu mai mahimmanci kiran Alhaji Sani Kachallah ya shigo wayar sa. A rikice ya miƙe tsaye jin batun da Alhajin ke masa.
A take ya buga wayar Alhaji Abdullahi dan gaba ɗaya kan sa ya kulle da maganar da aka faɗa masa. Sai yau yake jin maganar fyaɗe da abokinsa yai wa Halima tun tana ƙarama, kafin nan ko a taɗi bai taɓa jin zance makamancin hakan ba.
"Excellency lafiya kuwa?" Asiya ta faÉ—a a ruÉ—e
Ba tareda Gwamna ya ajiye wayar ba ya fara gaya mata abinda Alhaji Sani ya faɗa masa. "Abida 'yar Alhaji Abdullahi ce ta kashe kanta yau da safe, suicide note data bari ya nuna cousin ɗinta ne yai mata fyaɗe har sau uku kafin tafiyarsa ƙasar waje. Wai kuma shigen abinda Abdullahin ya aikata kenan shekarun baya lokacin yana zaune a Kachallah House"
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun! sakayya fa kenan tun daga duniya"
Da mamaki Gwamna ya kalli Asiya yace "kema kin san abinda ya faru da Halima ne?"
"Kwana biyu kafin aurenta take faɗa min, abin ya girgiza ni matuƙa. Na so na faɗa maka amma abubuwan da suka yi ta faruwa bayan bikin shi yasa na manta"
"Ban san mi zan ce ba Asya. Wannan abu da me yai kama"
"Allah dai ya raba mu da sharrin shaiÉ—an"
Gwamna ya amsa da Amin sannan ya É—au wayoyinsa ya fice daga falon...
Ko minti uku ba ai ba da ficewar Gwamna kiran Halima Kachallah ya shigo wayar Asiya.
"Anty Asiya na shiga uku, na shiga uku ni Halima" tayi maganar cikin kuka.
"Ki dena faÉ—in haka, miya faru?"
" nina masa baki, nina sa Abida ta kashe kanta" ta ƙarisa maganar tana sake fashewa da kuka
"Innalillahi! wani irin magana ne wannan, dan Allah ki dena kuka. Ki dena irin wannan mugun tunani, abinda ya faru na daga cikin ƙaddarar yarinyar shiyasa hakan ya faru"
"Na sha yiwa Yaya Abdullahi muguwar addu'a da mummunan fata amma ba irin wannan ba. She's so innocent"
"Ya Allah! Ba laifin ki bane Anty Halimah"
Yadda Haliman ta dage tana kuka sai ga hawaye suna shirin wankewa Asiya fiska. Ƙarshe kashe wayar tayi ta dafe kanta tana jimamin wannan al'amari. Sai data samu nitsuwa sannan ta kira numbar Yaya Bello tace dan Allah yaje gida ya lallashi matarsa. Bata gaya masa dalili ba amma tasan idan yaje chan zai ji da bakinsa.
**
Lokacin da Gwamna ya dawo gida kusan ƙarfe shaɗaya na dare gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. Abubuwa sun taru sun masa yawa. Batun mutuwar Abida dama bayyanar ainihin halin abokin nasa ya firgita shi sosai. Bai taɓa kawo cewa son matan Abdullahi har ya kai yai wa yarinya 'yar shekara tara fyaɗe ba. Eh aje lokacin yana saurayi ne, to amma ko a lokacin ai ya bawa Halima shekara kusan goma koma fiye da haka.
Bayan wannan kuma yanayin kallon da Alhaji Sani yai masa ya birkita shi matuƙa, kallone da babu ƙyallin soyayya ko farin ciki a cikinsa. Dama ya fara zargin ja baya da Alhajin ke yi dashi 'yan kwanan nan amma kuma yau ya tabbatar.
Ko dai da gaskene maganar da M Sani ya faÉ—a masa ranan a office cewa ya tozarta Baban sa.
"Uncle Saifuddeen yau na tabbatar cewa akwai ayar tambaya a kasancewarka jinin Kachallah. Ta ya za ka tozarta Grandpa a idon duniya. Baka ma É—aura wanda darajarsa yazo kusan É—aya da tashi ba sai ka É—aura É—an cikinsa, É—an cikinsa fah. Wato don yaje fada ya tsugunna yana yiwa yaron bayansa ranka shi daÉ—e ko."
"Get out!" Gwamna ya daka masa tsawa. Sai dai hakan bai hana M Sani cigaba da magana ba.
"Uncle Sakayyar da zaka yiwa Uban daya raineka kenan, Uban daya sadaukar da komai dan ya É—aura ka a wannan kujera. Inaga ka koma Gambia ka nemo iyayenka amma kai kam ba jinin Kachallah bane"...
Shigowar Asiya É—akin ya sa shi yin firgigit daga tunanin daya ke yi.
"My love ya haƙuri" ta faɗa tana rungumeshi ta baya.
"Baba yana fushi dani Asya. I can feel it"
"Ka dena irin wannan magana, kai kan ka kasan yadda Baba ke son ka ko 'ya'yan daya haifa albarka"
"Da kenan Asya, a da kenan"
Bai sake magana ba sai ya miƙe zai wuce banɗaki, bin shi ta yi dan ta taimaka masa yai wanka amma sai ya dakatar da ita...
***
Hare-hare da ake kaiwa a ƙauyuka ya fara yin yawa domin mutane da dama sun sadaukar da gonakin su sun fara baro ƙauyukansu suna neman mafaka a cikin gari. Wannan dalili yasa Gwamna ya dakatar da shirin Project Tomatonion ba tareda shawara da kowa ba.
Asiya na gida itada Badawiyya suna bibiyar wani report da aka basu kiran Kwamishinan noma ya shigo wayarta.
Tana É—aga wayar Kwamishinan ya sanar da ita hukuncin da Gwamna ya zartar.
"Mr Comissioner Sir, ban gane Gwamna ya ƙi saka hannu a kuɗin da muka nema ba"
Miƙewa tayi zumbur har sai da laptop dake kan cinyarta ya faɗo Badawiyya tayi ƙoƙarin tarewa amma sai daya kai ƙasa.
"Ban gane an terminating project ɗin ba, ban gane komai ba Sir. Ina zuwa zan zo office ɗin" ta ƙarisa maganar muryarta na rawa kaman za tayi kuka.
"Ranki shi daÉ—e miya faru?"
"Ki kira direba yanzu zamu je ofishin Gwamna"
Daga haka ta wuce wajen closet dan ta chanja kayan jikinta.
*
Lokacin da Asiya ta iso office É—in Gwamna baya nan ya shiga wani meeting dan haka ta zauna jiransa.
Tana zaune hankalinta ya kai ga wani hoto dake kan table ɗinsa. Hoto ne na Gwamna da iyalinsa. Lokacin kamfen aka ɗauki hoton, sun yi matuƙar kyau sosai kowanne a cikinsu murmushi ne shimfiɗe a fiskarsa. Ta ƙurawa fiskar Junior ido chan sai ta fara ganin yaron a idonta dai-dai lokacin da ta zo ta tarar da gawansa. Hannunta ne ya ɗau rawa hakan yasa hoton ya faɗo daga hannunta kafin ta ankara har ya kai ƙasa glass frame ɗin ya tarwatse.
"Ya Subhanallah!" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin ɗauko hoton sai dai kafin hannunta ya kai an riga anyi sama da hoton. Bata ji shigowarsa ba, ko dan tayi nisa cikin tunani.
"Your Excellency yaushe ka shigo?"
Maimakon ya amsa mata sai yace " miya kawo ki Asya?, i'm very busy today"
BuÉ—e baki tayi zata yi magana sai ta kasa dan bata san taya zata fara ba.
Kusan sakan biyar kafin ta saita nitsuwarta sannan tace "maganar project tomatonion ne. Kwamishina yace ka ƙi saka hannu akan kuɗaɗen da aka buƙata"
"Ba wai naƙi saka hannu bane, na kashe project ɗin ne gaba ɗaya"
"You can't do this Excellency"
Hannunta ɗaya ya riƙo yace "duk abinda kika ga nayi to nayi ne dan al'ummar jahar nan. Hare-haren da ake kaiwa manoma yayi yawa..."
"Bilkisu ce ta gaya maka haka? ko kuma Chief of staff É—inka?"
"Asya kina ganin jaridun da ake bugawa kullum kuwa? Kin ma ji hiran da Umaru Kwom yai jiya kuwa?"
"Your excellency na ƙaurace maka na kusan shekara guda duk dan na samawa gwamnatinka mafita amma abinda ke gabanka shine rubutun 'yan jarida!"
"Mutane biyu aka kashe jiya, rayuka biyu Asya, and many more will die idan aka cigaba da wannan project"
"Abinda suka faÉ—a maka kenan, abinda suka ce kayi kenan?" Asiya ta faÉ—a jikinta na rawa
"Asya na san yadda wannan shiri yake da mahimmanci a wajenki but you have to know that ina da hakkin kare kowanni mutum da dukiyarsa a jihar nan. Wannan shine sama da komai"
Hawaye ne ya taru a idanun Asiya, ƙoƙarin tare su take sai gashi sun fara zubowa.
"I'm sorry Asiya, i'm really sorry" ya faɗa yana ƙoƙarin rungumeta
Ɗago rinannun idanunta tayi ta kalleshi da kyau. So take tace masa shi rago ne kuma matsoraci amma sai kalaman suka mata nauyi a baki ta kasa faɗin komai. Duk yadda tayi yunƙurin magana sai hawaye ya zubo wannan ya bashi damar rungumeta jikinsa sosai yana bubbuga bayanta.
Kusan minti biyu suka yi a haka kafin Asiya ta zare jikinta ta goge fiskarta da kyau sannan tace
"Alfarma É—aya nake nema a wajen ka" Gwamna ya zuba ido yana kallonta
"Dan Allah ka bari na gudanar da shirin nan koda ba da tallafinka bane"...
20
***
"Asiya"
"Asiya"
Badawiyya ta sa hannu ta dafa kafaÉ—ar Asiya wacce tunda ta dawo daga ofishin Gwamna bata yi magana ba.