← Book details Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 48

Sashe 29

Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sati uku aka gama tattara masa duk wani bayani daya ke so, bai yi mamaki ba da ya ga labarin aure da saki tsakanin M Sani da Scott Green.
Sai dai abinda ya bashi mamaki kuma ya ja hankalinsa shine maganar luwaɗi da ƙananan yara da aka ce yana yi. A kan wannan maganar ne ya fitar da maƙudan kuɗi dan ganin an kawo masa sahihin labari da shaida akan fyaɗe da yake wa ƙananan yara maza.
Lokacin da aka kawo masa labarin Almajiri Sa'idu ya so ya shigar da ƙara amma daga baya wata zuciyar tace ya tura bayanan daya tattaro ga Asiya.

Hakan da yai kuwa ya zamo masa alkhairi dan Asiya na samun tabbaci akan labarin ta tura zuwa ga hukumar Human rights.

Mr Lamara ya ɗau waya ya danna wasu nambobi sannan ya ƙara wayar a kunne.
"Begin the process"
Kaɗai abinda ya faɗa kenan kafin ya ajiye wayar, can ƙasan ran sa yana ayyana yadda ahalin Kachallah zai tarwatse kwanan nan.

***
Alhaji Sani Kachallah ya zubawa abincin dake gabansa ido. Tun jiya da Gwamna ya bar wajensa ko ruwa bai sake haÉ—iya ba.

Matar sa dake gefe ta ajiye cokalin dake hannunta tace " Alhaji wai mi yake damun ka ne? Tun jiya na lura baka cikin hayyacin ka. Ka san dai gargaÉ—in da likita yai maka akan yawan tunani"

Ta ƙara da cewa "akwai abinda Saifuddeen ya maka ne? dan na san a duniya maganar sa ce kaɗai ke ɗaga maka hankali" ta ƙarisa maganar da muryar da ke nuna takaici.

Maganar Saifuddeen ta jiya ta faÉ—o masa.

"Baba na juma ina zargin waÉ—annan abubuwa amma na kan tirsasa zuciyata hana irin waÉ—annan zargi. Zan dakatar da Asiya daga fitar da waÉ—annan takardu amma ina so kamin abu É—aya"

Cikin karyayyiyar murya wacce ta fitar da ainihin rauninsa ya ƙarisa maganar

"Baba ka ƙarasa aikin daka karɓa sannan duk wata ka dinga kwatanta wani kaso na kuɗi kana mayarwa cikin asusun jiha"

Har Gwamna ya fita daga É—akin bai iya motsin kirki ba.

Tun jiyan kuwa har yanzu bai san mi zai yi ba.

***

Sai da Bilkisu ta gama shiryawa tsaf zata wuce Abuja gameda maganar Madam Bintu aka kira wayan ta. Ganin wacce ke kiran ne ya bata mamaki, tun maganar bikin Halima ba ta mu'amala da kowa cikin 'yan uwanta idan ka cire mahaifiyarta sai kuma wasu cousins nata da suka raɓeta saboda kwaɗayi.

"Rufaidah" ta kira a hankali kamar dai ta san mi za ta faÉ—a É—in.

Raunanniyar muryar da tayi magana da shi ya bata tabbacin Rufaidah ta ga hotunan da Saifuddeen ya nuna mata jiya.

"Ina so...ina roƙon ki da Allah"
Muryarta ya sarƙe saboda kuka daya fizgeta.

"Rufaidah kina jina? Zan yi komai don ganin..."

"Dan Allah ki bari a hukunta Muhammad. Idan kika saka hannu aka lalata shari'ar nan zan tsinewa Muhammad kuma ba zan taɓa yafe miki ba"

"Rufaidah tsaya ki ji..."

Katse wayar da Rufaidan ta yi yasa ta ajiye wayarta ta miƙe ta isa wajen tv ta ɗau remote ta ƙara volume sannan ta shiga chanja tasha. Babu tashar da ta kawo rahoto akan M Sani shiyasa tayi tunanin ko dai Rufaidar ce take tunanin kai ƙaran M Sani.
Ba ta bar wajen TVn ba kiran Mr Lamara ya shigo wayarta.

Ta kira duka nambobin M Sani da take da shi amma har yanzu babu wanda ya shiga.

Ashe ma an jima da shigar da ƙaran M Sani ashe dama bibiyarsa ake yi dan ai mishi kamun talala.
Bata gama farfaɗowa daga shock ɗin abinda Mr Lamara ya faɗa ba tashar Congo News suka nuno hoton M Sani hannunsa cikin ankwa daga shi sai gajeran wando da singlet fari, fiskarsa tayi ja, gefen kumatunsa ya kumbura suntum kaman an saka ƙaramin ball, ga uwa uba jini dake fita daga hancinsa.

"An ce yaran boarding school yake ɗaukowa ya biya su kuɗi yai luwaɗi da su. An ce an kama shi ne yana yiwa wani yaro ɗan shekara shabiyu fyaɗe. Boss Lady ina ga kada ki saka hannun ki a wannan shari'ar domin zata goga miki baƙin fenti"

Maganar Mr Lamara ya dawo mata. Ta sa hannu biyu ta riƙe goshinta tana sauke ajiyar zuciya, ta sani yanzu kam babu maganar zuwa Abuja...

*

Gaba É—aya zuri'ar Alhaji Sani Kachallah sun jijjiga da wannan batu na kama M Sani.
Rufaidah kam tun da ta gama waya da Bilkisu hankalinta ya ƙara tashi, ƙarshe aka wuce da ita Asibiti saboda suma da ta yi. Likita yace jininta ne ya hau sosai.
Sun mata duk wani taimako na gaggawa amma duk da haka da ta farfaÉ—o ta tuno abinda ta gani a talabijin sai hankalinta ya tashi ta sake suma.

Gwamna da kansa ya je duba Rufaidah a Asibiti dan shima sai a TV ya samu labarin an kama M Sani. Ban da Bilkisu da yai wa maganar M Sani saboda yana zargin ko tana da masaniya akan abinda yaron ke aikatawa ko Baba bai faÉ—awa ba, ya yi tunanin gayawa Baba amma sai ya fasa saboda irin tashin hankalin da Baba zai shiga idan ya ji labarin abinda jikansa ke yi.

Zuwan Saifuddeen ya yiwa Rufaidah daɗi musamman da ya ɗau mata alƙawarin cewa zai bari hukuma tayi aikinta akan shari'ar M Sani. Sai dai duk da haka uwa uwa ce, abinda ɗan nata ya aikata ya raunana mata zuciya ikon Allah ne kawai yasa baƙin ciki bai kashe ta ba.
Dai dai Gwamna zai tafi Alhaji Sani, Halima da kuma Yazid ƙanin M Sanin suka nufo ɗakin.

Gwamna ya gaida Alhaji yana masa sannu da zuwa. Bai iya karanto komai a fiskar Baba ba hakanan ba zai iya fassara kallon da Baba ya mi shi ba.

Ya so tsayawa su gana da Baba amma kiransa da aka yi a waya yasa shi barin Asibitin cikin gaggawa.

Minti huÉ—u da tafiyarsa shima Alhaji Sani aka kira wayar sa ana faÉ—a masa wani zance da ya firgita shi fiye ma da labarin kama jikansa da aka yi.

Ya san wacece Bilkisu, ya san mi zata iya aikatawa, kuma babu shakka ya gane sarai ma'anar furucin da ta yi. Sai dai har ga Allah yana fatan abinda yake tunani ba gaskiya bane.

*

Daga inda Asiya ke kwance saboda zazzaɓi da ke damunta tun jiya ta ɗan sa hannu ta lalubo wayarta dake ringing tun ɗazu wanda shi ya tada ta daga baccin da take.

Kafin ta É—auko wayar har ta yanke, ganin numbar Badawiyya yasa ta danna kira ta É—ara wayar a kunne.

"Ban gani ba, yanzu...to barin duba"
Tana faÉ—in haka ta katse kiran ta duba bidiyon da Badawiyya ta turo mata.

Bata yi mamakin ganin Bilkisu tana press conference ba infact bata yi mamakin jin kalaman Bilkisun ba inda take Allah wadai da abinda M Sani ya aikata tareda alƙawarin ɗaukarwa yaran da aka ciwa zarafi lawyer.

Lokacin da wani ɗan jarida ya mata tambaya akan ko tanada masaniya akan halin M Sani duba da cewa shine na hannun damanta tun daya dawo ƙasar bayan karatunsa a ƙasar waje, sai kawai Bilkisu ta fashe da kuka, ƙarshe ta zaro hankici ta fara goge hawaye tana faɗin Allah ya isa idan har tana da masaniya akan abinda M Sani ke aikatawa. Ta haɗa da cewa M Sani ya cuceta, ya cuci zuri'ar Kachallah gaba ɗayan su.

Asiya ta ajiye waya ta tashi zaune dan ta gano lauje cikin naÉ—i a maganganun Bilkisu...

23

***

Kamar Gwamna zai tashi sama haka ya fice daga cikin asibitin da sauri, hatta securities na shi da gudu-gudu suka dinga binshi a baya dan saurin da ya ke yayi yawa.

Mr Lamara ne ya kira shi ya sanar da shi Bilkisu ta shirya hira da 'yan jarida a gidan Gwamnati kan maganar kama M Sani da aka yi.
A cikin mota ya buÉ—e waya yana kallon maganganun da Bilkisu ke yi.
Wacce irin zuciya ce da Bilkisu? Ya tambayi kansa yafi a irga.
Ya samu labarin bata je ta duba Rufaidah ba balle ta mata jaje.

Da tunani kaca-kaca ya isa gida wanda kafin ya isa an riga an gama brief press conference É—in da aka shirya na minti talatin.

Bilkisu na magana da wasu maza biyu Gwamna ya shigo falon.
"In my room now" ya faɗa cikin fushi sannan ya bar falon ƙirjinsa na bugawa da ƙarfi.

Ba ta bi ta kansa ba sai da ta gama bawa assistant ɗinta umurni sannan ta wuce ɗakinta ta shige banɗaki. Ta riga ta ɗauki alƙawarin yin watsi da duk wani umurnin Saifuddeen, daga yanzu za ta yi abinda ta ga dama ne a lokacin da ta ga dama.

Wasa-wasa kafin Bilkisu ta amsa kiran Saifuddeen sai da ta ɗau kusan minti hamsin, ta shirya cikin wani kayan bacci riga da wando mai tsantsi kalar baƙi.

A tsaye ta same shi yana waya har lokacin kayan daya shigo da su ne a jikinsa. Ta zauna akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya.

Kusan minti shida yana waya kafin ya kashe ya juyo ya kalleta.

"Bilkisu" ya kira sunan ta da murya daya ke nuna tsantsan damuwa.

"Mr Governor" ta amsa kamar yadda yanzu ta ke kiransa.

"Kin ko san implications na abubuwan da kika faÉ—a kuwa?"

"Mi na faÉ—a daya wuce gaskiya, ko kana tunanin ina sane da abinda É—an Rufaidah ke aikatawa ne"

"Ɗan Rufaidah!... Bilkisu yau Muhammad kike kira da ɗan Rufaidah. Kin manta cewa tunda ya dawo ƙasar nan ke ce uwar da ke goya shi"

"Bacci nake ji Mr Governor idan kana da abu mai mahimmanci da zaka faÉ—a to, idan kuma babu zan wuce É—aki"

" Bilkisu Rufaidah yayar ki ce, kuma duk rashin jituwar dake tsananinku bata chanchanci wannan rashin mutuncin ba"

"Shikenan dama?" Bilkisu ta faÉ—a da sigar ko oho da abinda ya faÉ—a

"Daga yau na hana ki yin hira da 'yan jarida directly or indirectly"

Miƙewa tayi tana dariya ƙasa-ƙasa, tana mamakin ƙarfin gwiwa irin ta Saifuddeen.

"Ba ka isa ka hana ni komai ba Mr Governor"
Ta faÉ—a cikin É—aga murya.

Abinda ya karanto a idanun Bilkisu ya tabbatar masa cewa akwai babbar matsala anan gaba, mamaki da fargaba suka mamaye shi lokaci guda...

***
Chapter 29 · 0% Book details