Sashe 20
Gov's Wife Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Waye finance commisioner É—in?" Bilkisu ta tambaya a kiÉ—ime
" Tijjani Bukar"
Shiru Bilkisu ta yi na sakan biyar tana nazarin waye ma Tijjani Bukar a jahar, kafin ta tuno waye COS ya cigaba da bayanin sa " bana tunanin Gwamna zai chanja sunayen da ya bayar, abu É—aya zamu iya yi yanzu"
"Mi kenan?" Bilkisu ta tambaya a zaƙale
"mu yiwa speaker na House magana akan ya rejecting nominees É—in da Gwamna ya bayar "
"Zan same shi anjima"
COS na gama waya da Bilkisu Mr Paul ya shigo ofishinsa ya jefa masa wata takarda.
"Commissioner of youths and sports, is this some kind of a joke?"
"Mr Paul calm down. Boss lady ta san da maganar zata yi wani abu a kai"
"Ka gaya mata tayi duk abinda ya dace, idan ba haka ba bakina ba zai yi shiru ba"
Daga haka ya juya ya fice. COS ya furzar da iska ta baki yana tunanin mafita idan har Speaker bai amince da maganar su ba.
***
A yau ne ranan da majalisa suka yi zama kan amincewa ko rashin amincewa da sunayen sabbin Kwamishinoni da Mai girma Gwamna ya kawo.
Cikin 'yan kwanaki biyu kacal Hajiya Bilkisu Kachallah ta yi sintirin zuwa wajen speaker da deputy speaker na House of assembly yafi sau uku. Wasu mahaukatan kuɗi ta fitar dan a rabawa members na House ɗin saboda su ƙi yarda da sunayen da aka turo. Sai dai abin mamaki tun kafin a gama zaman COS ya kirata ya faɗa mata mummunan labari kan cewa Speaker ya amince da duka sunayen kamar yadda Gwamna ya turo. Bilkisu suman tsaye ta yi ta kasa koda jan numfashi ne na wasu daƙiƙu.
Mi yake faruwa? macijinta yanzu ba kowa yake tsoratarwa ba shi yasa ta yi ƙoƙarin toshe bakin speaker da kuɗi amma duk a banza.
"Kana nufin Tijjani Bukar shine Kwamishinan kuÉ—i?"
"Yes"
"Ba zai yiwu ba Lamara. Tijjani Bukar da Saifuddeen ra'ayinsu ɗaya ne, yama fi Saifuddeen bahagon aƙida"
"Akwai ƙaramar matsala fah"
"Miye kuma!"
"Mr Paul ya resign"
"Ya yi me ?"...
*
Asiya Kachallah tana zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karanta wani littafi Bilkisu ta shigo falon fuuu kaman wata iska.
" Ki cire hannun ki a Gwamnatin Saifuddeen. Babu ruwanki da mulkinsa"
Asiya bata É—ago ba ta cigaba da karatun da take dan tana jin daÉ—in littafin dake hannunta. Bata ankara ba ta ji an wafce littafin hannunta anyi jifa da shi, sai a lokacin ta É—ago ido ta kalli Bilkisu da ke tsaye kanta tana surfa masifa.
"Ki tattara ki koma Kachallah House kafin yamma,"
Maimakon Asiya ta yi magana sai ta saka murmushi, irin murmushin rainin hankali É—in nan.
Har Bilkisu ta bar falon bata dena murmushin ba domin tun ba a fara komai ba har Bilkisu ta fara karaya. Lallai idan haka ne kuwa komai zai zo musu da sauƙi.
Bilkisu na barin falon Asiya ta yi kiciɓus da M Sani dai dai zata je ta shiga mota.
"Boss kin ga rashin mutuncin da Uncle yayi min ko. Shiyasa nace mu kawar da shi lokacin da yake jinya, you should be the governor"
"Ya isa!" Ta daka masa tsawa. Ta ya zai mata magana irin wannnan a gaban excorts É—inta. Mota ta shige ta barshi tsaye a wajen baki buÉ—e.
Duk wani shige da fice Bilkisu ta yi dan ganin an sauke Kwamishinan kuɗi amma abin ya faskara. Dr Tijjani Bukar malamin jami'a ne da yai suna sosai a jihar, abokin Gwamna Saifuddeen ne ƙut-da-ƙut tun lokacin yana koyarwa a jami'ar Congo.
***
A yau safiyar Asabat Gwamna Saifuddeen yana karyawa tareda iyalinsa aka bugo masa waya daga Fada.
Yana ajiye wayar Asiya ta zuba masa ido tana jiran ƙarin bayani dan ta ji yana ta'aziyya a wayar.
Gwamna yace "Allah ya yiwa Mai Martaba rasuwa"
Asiya da Mahira suka haÉ—a baki wajen faÉ—in Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun.
Tea kawai ya kurɓa ya fita saboda Alhaji Sani na jiransa za su wuce chan Fada.
Bayan fitarsa Asiya da Mahira suma abincin fita yai musu akai dan haka sai kira suka yi aka tattara abincin...
Rasuwan Sarkin Congo ya zo da alhini dayawa. Jama'a da dama sun ji mutuwar sarkin a jikinsu saboda Sarki ne adali kuma uban ƙasa da kowa ke alfahari da shi.
Bilkisu Kachallah na jin rasuwan ta ji ƙishirwan sarauta ya tasan mata. Idan har aka naɗa mahaifinta sarki zata ƙara samun wani daraja a idon mutane musaman wanda suke gani kaman tauraron Asiya ke haskawa a wajen Gwamna Saifuddeen.
Bata jira anyi kwana uku ba ta tuntuɓi Gwamna da maganar naɗa mahaifinta wato Alhaji Sani Kachallah.
"Bilkisu idan Allah yayi Baba zai yi sarautan garin nan babu makawa sai yayi, idan kuma har Allah bai rubuta ba then babu yadda zamu yi domin babu alkhairi a cikinsa"
"What do you mean Saifuddeen!. Yes ka gaya min mi kake nufi da wa'azin da ka fara kaman an naÉ—a ka limamim masallacin anguwa"
"Ina nufin ki sa a ranki cewa Allah ke bada sarauta, idan bai bawa Baba ba ban isa na bashi ba"
"Oh please cut this bullshit. You are the governor of this state, kai ne ke da damar naÉ—a sarki a jihar nan. Yanzu butulcin da za ka yiwa Baba kenan bayan duk irin gatan daya maka a duniyar nan"
Gwamna Saifuddeen ya dafa kafaɗar Bilkisu cikin sigar lallashi yace " i'm sorry my dear, ba zan zaɓi Baba a matsayin Sarki ba har sai idan ya chanchanci hakan"
Wafce hannunta tayi da ƙarfi tana faɗin " i will fight you with everything i have Saifuddeen, ko ka naɗa Baba Sarki ko kuma jahar nan ta maka zafi"
daga haka ta fice daga É—akin yana jin yadda tsinin takalminta ke buga tiles kaman zai tsaga shi.
Bai yi mamakin maganganun Bilkisu ba tunda a baya tayi yunƙurin saka shi tsige Sarki lokacin yana raye.
Asiya ce da kwana dan haka ya wuce ɗakinta ko zai samu nitsuwa. Ganin bata ɗakin yasa shi zama kan gadonta yana jiranta. Kusan minti huɗu sai ya ji ƙaran buɗe ƙofar banɗaki, sanye take da bathrobe kalar ruwan ƙwai, gashinta ƙunshe cikin towel data ɗaura kamar turban.
Gwamna ya ƙura mata ido cike da kewarta, tunda aka yi rasuwan nan ba su yi ƙwaƙƙwaran zama na minti goma ba.
Da hannu ya mata alamar ta zo ta zauna a cinyarsa, tana zama ya kwantar da kansa akan ƙirjinta, a hankali ta sa hannu ta fara shafa gashin kansa tana ɗan hura masa iska a kunne.
Kusan minti biyu suka yi a haka kafin yace " Bilkisu na so na zaɓi Baba a matsayin sarki, Baba baya cikin candidate ɗin da mutane suka fi so"
Asiya ta ja numfashi sannan tace "ka yi istikhara, sannan ka nemi shawaran mutanen da kake tunanin za su baka shawara ba tareda son zuciya ba, ina ga idan ka yi wannan Allah zai shige maka gaba akan zaɓin da za ka yi".
Gwamna ya ɗago fiskarsa ya ƙurawa Asiya idanu tabbas yanzu ne ya san yayi sa'ar mata ta gari.
"Wannan kallon fa?" Asiya ta faÉ—a tana É—aga masa gira.
"I love you"
Ba tareda ta shirya ba, wani ƙasaitaccen murmushi ya kuɓuce mata. Tana jin daɗin kalaman nan musamman a lokutan da take ganin zahiri a idanunsa cewa sonta yake bilhaƙƙi.
"I love you nace fah! Ba zaki amsa min ba"
'Yar dariya tayi sannan tace " kai Gwamna ne ni kuma Saifuddeen nake so"
Hannunta ya riƙe dai-dai tana ƙoƙarin tashi.
"A gida da waje Saifuddeen naki ne"
Asiya ta shige jikinsa tana murmushin jin daÉ—i...
***
"Banyi mamaki ba da aka ce Gwamna ya kori kwamishinoni da kika kawo, amma kuma hana mahaifinki sarautar Sarki wannan ya wuce tunanina. Gaskiya ki tashi tsaye akan yarinyar nan idan ba haka ba kan ku ƙarisa tenure ɗin nan za ta sa shi yai waje da ke" Madam Bintu ta ƙarisa maganar tareda kurɓan juice dake hannunta.
"Yanzu miye abinyi Bintu?"
"Ke kin fi yarda da mutanen India ni kuma malamai na baƙaƙen fata ne, idan za ki gwada aikinsu to sai na raka ki"
"As long as zan samu biyan buƙata ban ƙi muje ko'ina ba. Duk aikin da aka min ya dena yiwa Saifuddeen tasiri, ita kuma shegiyar tun asali ma maciji na tsoronta yake.
"Yanzu yaushe zamu je?"
"Duk sanda kika shirya First lady"
"A matse nake Bintu, ba zan yarda a naɗa wani Sarki ba matuƙar Baba na raye a doron ƙasa"
"Gimbiya Bilkisu!" Madam Bintu ta faÉ—a da shewa. Bilkisu tayi murmushin jin daÉ—i.
***
Bilkisu Kachallah ba ta yi tunanin akwai irin wannan ƙauye ba a jahar Congo, kafin su isa ƙauyen ba ƙaramin jigata suka yi ba. Tafiya ce suka yi a machine na kusan awa biyu sannan daga ƙarshe da zasu je jejin da bokan yake sai da suka yi tafiyar ƙafa itama ta kusan awa ɗaya.
Shiga ce suka yi ta ɓadda kama kamar yadda Madam Bintu ta bada shawara, da wuya ka kallesu a yadda su ke ka gane cewa Hajiya Bilkisu Kachallah ce uwargidan Gwamna da kuma babbar aminiyarta fitacciyar 'yar kasuwa wato Madam Bintu Chadi.
Rashin kwalliya dama zafin rana sun saka fiskar Bilkisu ta jeme ta kuma ƙara tsufa. Saboda akwai ƙura a hanyar babu wanda ya san cewa ɓoye matsayinsu shine dalilin daya sa ko sau ɗaya basu cire nose mask da suka rufe fiskar su da shi ba.
Babu abinda ya fi ƙona ran Bilkisu cikin tafiyar da suka yi irin rashin samun abinda suka je nema. Bokan kamar yadda Madam Bintu ta faɗa hatsabibine sosai domin kuwa suna zuwa ya sanar da su abinda ya ke tafe da su sannan ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya yiwa Bilkisu kowanni irin aiki ba, ya ƙara da cewa koda ta je wani wajen daban baya tantama cewa ba za a iya yi mata kowanni irin aiki ba.