← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciya ta naji ta karye saboda tausayin ammi na dubeta sai zufa take a tsakiyar Rana inda wahala ta sauko Mata da wani irin tsufa tamkar ba itace Yar gayun Nan da Daddy ke kambamawa a fagen kyau.

Haka muka ci Dan waken Nan Amma Kuma kamar hadin Baki mu duka ukun muka kware da Rudewar ciki muna ta zagaya bandaki Ni da Yaya Abdullahi da sulaiman ammi ta Rude ta fito ta siyo Mana magani flajin kafin muka samu afuwa

Zaman Shirun da Rashin abinyi yasa Yaya Abdullahi yanemi shawarar ammi Akan ta barshi ya dauki motar ta ya Soma sufurin ko don kudin hayar da ke kusanto mu Dole ammi ta yarda Yaya Abdullahi ya Soma sufuri zuwa Kano ko funtua duk inda dai ya samu fasinja a Haka muka samu Rufin Asiri Mai yawa Ashe wannan Jan motar na Yaya Abdullahi shima wata kaddarar ce ke Shirin sauka Akan mu kaddarar da zata girgiza mu fiye da kaddarorin da suka Riske mu a Baya.............

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Wannan labarin na GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku

Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
15//16
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga Yan kungiyar kainuwa writes associated Gaba Daya kaf Ranka takaf ban cire ko guda ba Allah ya Kara daukaka

Sadaukarwa ta biyu ga dukkan musulmin da Ubangiji ya jarabta da kuncin Rayuwa Allah ka fidda bayin ka daga kunci da talauci ka maye da gurbin Arziki

Ban manta masoya ba har Abada kuwa ba Zan manta Babu abinda yafi a furta maka ana kaunar ka musamman Irina da ban Kai ba ban Kuma iya ba

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

........... Wannan wahalar da Yaya Abdullahi ya samu kanshi a Rana tsaka ta Jan mota da sufuri tayi matukar tafiyar da kumarin jikin sa

Ya Kara dafewar fata ya Kuma Kara Rama Akan wadda ya samu Kai acikin ta Amma da Yake jarumi ne sai ya nuna min bafa komai bane wannan duk na lokaci ne Kuma zai wuce da yardar Ubangiji shi lamarin Rayuwa guda biyu NE ko dai ya wuce ya barka ko Kuma Kai ka wuce ka barshi

Haka ya fada min a lokacin da nake kokawa halin da Naga ya SHIGA na wani sauyin saboda sanin da nayi mishi na Bai taba SHIGA wani hali na Rayuwa irin wannan ba bare nayi tunanin sabo Amma Kuma Dole na gamsu da bayanin da yayi min don a sanin da nayi mishi Yana fatan ganin ya fita hakkin mu Akan komai Kar dai muce muna son kaza to kuwa zaiyi kokarin sama Mana abinda muke so inda Kuma na Gane a kokarin Yaya Abdullahi so Yake a Dole sai ya maye Mana gurbin Daddy da muka Rasa Nima sai naji zanso hakan Amma Kuma gaskiyar magana nafi son naga Yaya Abdullahi shima a huce Amma ba cikin wannan wahalar ba to Amma ya muka iya tunda haka alkalamin kaddarar mu ya zano Mana?

Na dawo makaranta kenan na iso kofar gidan mu inda na hango motar Yaya Abdullahi a kofar gida inda na SHIGA tunanin yau kuwa ya dawo da wuri na SHIGA gidan da karsashi na inda na samu Ammi ta zabgo tagumi cikin damuwa sai naji hantar cikina ta kada

"Anmi lafiya dai ko ? Na fada murya ta na Rawa don naji ajikina ba lafiyar da na tambaya ba......

"Lafiya Lau Zahra Abdullahi ne dama ya dawo babu lafiya Kuma gashi babu kudi a hannu na bare na Kira likita Amma tashi kije gidan maman Nana ki aro min ko dubu Biyu ne dama gareshi nake saka Ran samun kudin idan ya dawo to jiki da jini yau lafiyar Taki......

Kafin ma Ammi ta gama zancen ta na wuce kuryar dakin Yaya Abdullahi Wanda na samu Yana ta kelaya uban Amai tsanwa Shar Alamar kumallo ne babu komai a cikin sa

Na matsa kusa dashi Ina mishi sannu kafin na Kama shi na jingina shi jikin filo na fito da sauri na dauko kokon da na Rage da safe na kuza mishi Ruwa ya Zama farau farau na dawo na bashi ya dan Kora ya koma ya kwanta na kwashe Aman kafin na fice zuwa gidan mama na fada Mata sakon ammi ta kuwa bani kudin har ma ta zubo abinci Mai yawa a kula tace na kawowa Yaya Abdullahi Kuma nace tana duba shi kuma zata Zo duba jikin nashi

Na kawo wa ammi kudin da sauri Kuma tace na Kama Mata Abdullahi mu Kai shi Asibiti
Na kamo shi muka fito ammi ta bude motar muka SHIGA kasancewar ta iya mota yasa Kai tsaye muka nufi Asibiti aka duba yaya Abdullahi akayi mishi gwaji sakamakon na malairia ne da da Kuma Rashin Samun hutu sai Kuma ulcer dake neman Kama shi don Haka aka shawarce mu da bashi cikakkiyar kulawa da Kuma samun hutu kafin aka Rubuto magunguna muka dawo gida

Dole Yaya Abdullahi ya zauna a gida ba don ya samu hutu ko kullawar da likitan ke magana akai ba sai don ya samu afuwar jiki ya koma bakin aiki a ganin shi talaka irin shi wane hutu zai nema Wanda sai ya fita ya samo ake bukatun Rayuwa.

Zuwa wannan lokacin duka duka shekarun shi fa ashirin da biyu NE don dai Jin Dadi da kuma jikin girman yasa ya Zama wani babba Amma yanzu da Rayuwa tayi sauyi duk wannan jikin nashi ya zube ya koma Dan kadan don shekara bakwai ne tazarar dake tsakanin mu Ni da kaina na Gane Yaya Abdullahi Yana bukatar hutu don Haka sai zaman jinyar shi ya Kara budo Mana wasu shafukan a cikin littafin da Yake Rubuce da tarin kaddarorin mu inda Yake Shan magani Amma sauki sai ga Ubangiji da Kuma godiyar Nan dai a gareshi

Muna cikin jimamin jinyar Yaya Abdullahi sai ga haj ladi matar da muke haya a gidan ta ta doko Mana sallama har ga Allah mun manta da cikar wa adin kudin ta saboda jinyar Yaya Abdullahi

"Masu gidan suna Jin sallama ko kuwa duk cikin Rainin da ake shirin kawo min ne anaji na Ina kwada sallama ake yi min banza?

Ammi ta amsa Mata da bamuji bane hajiya sannu da Zuwa shigo ciki......

"A a ba sai kin sakani a daki ba don ba dogon turanci ne ya kawo ba kudina na biyo karba bani kawai na wuce in har Babu Raini a cikin lamarin naku

"Kiyi hakuri hajiya Wallahi babu Raini a tsakanin mu yaron wajena ne babu lafiya kingan shi Nan kwance dama shine me biyan kudin don Allah hajiya ki Kara hakuri Zan kawo Miki kudin ki har gida da Ubangiji ya yaye wannan ciwon ne ya kawo hakan...

"Ke Yar Nan Kar kice Zaki kawo min kalaman karya ki fake da karsana ki harbi guzuma
"Don anji nayo sallama ne ake nadewa a gado ace ba a lafiya? In dai lafiya ce waye Mai lafiya a yanzu? Nima ba ita gareni ba Amma nake mazewa nayi harkokina Ni da har hauhawar jini ma gareni Amma ban nade a gado ba sai wannan katon ne akwance Wai baya lafiya? To ki kiyaye Ni don bani da Dadi ko da gishiri Zan Baki watan gaba ki kawo min kudina don ba Zan lamunci a zaune min gida akasa biyana haya ba yo yaushe ma ake haka ? Nan gaba kuwa ai mutum zai iya cewa gidan nashi ne to a fita idona na Rufe don in na Rufe da mutum a ciki ba zai fito ba yayi ta Zama kenan

Da haka ta fice daga gidan tana zuba Ruwan tijara

Ammi ta dafe kanta tana SHIGA wani zuzzurfan tunani Haka na fice zuwa makaranta zuciya ta a kuntace ban iya dorar da duk wani darasi da akayi a makaranta ba saboda zuciya ta tana wurin daban Akasin gangar jikina dake cikin ajin amma zuciyar Bata cikin ajin Haka na dawo inda na iske motar Ammi dake kofar gidan mu an Mata pentin taxi Amma sai ban dauka wani Abu ba azatona ma ba motar ta bace na SHIGA gida na iske Yaya Abdullahi Yana ta amai inda ammi ke fada min magungunan shi ne suka Kare babu Kuma kudin siyen wasu shiyasa ciwon ya koma sabo Dal Dole aka SHIGA kame kame

Washe gari naji Ammi na cewa sulaiman Kar yaje makaranta ya tsaya ya kula Mata da gida da Kuma Yaya Abdullahi. Ban tambaye ta inda zataje ba NASA Kai na fice zuwa makaranta inda yauma ban kula da kalolin darussan da aka koyar damu ba saboda tunanin Rayuwa har aka tashi na taho Ina zancen zuci har na kawo bakin titi Zan tsallake Ina hanga dama na da hagu na don kiyaye ban fada wa abin hawan da ke son wucewa ba inda Kuma na hango wata taxi tayi parking a gabana Ina dubawa sai Naga Ammi a mazaunin direba sai wasu Mata dake baya da Kuma wata mace a gaba

Gabana yayi masifar faduwa inda najiyo Ammi na fadin
"Shigo muje Zahra har an taso? Na bude bayan inda ke da wurin zaman mutum Daya na zauna na Rufe motar Ammi taja motar muka wuce Ina cike da tarin tambayoyi shin ammi mota ta koma ja ne? Ko kuwa wadan Nan matan Ina zata kaisu?

Matan Nan na cikin mota suka katse min tunani ta hanyar fadin

"Ai Ni Wallahi baiwar Allah kin burgeni don wannan Rayuwar babu nakasasshe sai kasasshe Haka Kuma Babu maraya sai Rago tunda har Ubangiji ya Azurta ki da motar nan Taki ce ta kanki da ki tsaya bawa mutanen wannan zamanin marasa Amana suna cutar ki gara ki tuka abinki tunda ma Allah yasa kin iya don Ni Wallahi zaburar Dani kikayi don Zan cire tsoro Nima na koyi motar Nan don tsaro ba don tsoro ba . Dayar matar dake gaba ta karbe maganar da cewa
Chapter 8 · 0% Book details