Sashe 3
Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa ya watse saboda Dare aka barmu yamu yamu inda ammi tayi nufin budewa su kawu gide bos kwata don su kwanta Amma sai lamarin ya juye tamkar bakar magana ta fada musu yagana da Badura suka ce Ina wuta su jefa ta duk suma kawu madu da giden ba mutunci ne dasu ba Wai su da gidan Dan uwan su har sai ta nuna musu iko? To ba kwartanci sukazo ba don su ko Matan Duniya sun Kare sai ita to zasu hakura da mata bare tayi tunanin zasu iya duban ta a mace bare wani Abu da dan uwan su Yake ganin ta burgeshi shima kahuwa tasa shi Auren ta da ya biye tasu to da ya barta ta Rayu da irin jinsin ta iyalan oduduwa da fafaroma cewar yagana kenan wadda ta zarta su kiyayyar ammi
Tun daga Ranar ammi Bata Kuma SHIGA hurumin su kawu da Yaya Badura ba iyakar dasu gaisuwa shima ba amsawa suke ba in ma sun amsa to zaka samu idon wani ne a wurin shima sai sun bita d kallon wulakanci
Sai da akayi kwana bakwai kafin Alh Mustafa ya Tara mu mu duka Ni da ammi da sulaiman yayin da Yaya Abdullahi yake can Egypt Yana karatu Kuma har yanzu Bai San abinda ke faruwa ba don ammi tace cikin jarabawa yake ba zata sanar dashi ba Kuma mama ma haka tace Kar a fada mishi don Haka Babu shi a cikin taron da aminin Daddyn yayi Mana wato Alh Mustafa da Kuma kawu madu da giden da Badura da yagana
"Dama na Tara ku ne don na sanar daku wani Abu da Baku sani ba in Kuma saukewa Umar wani nauyi dake kanshi saboda babu wani nauyi Akan mamaci me hadari irin bashi ba Kuma bashin komai ne Akan shi sai bashi da nake binshi na kudi har million goma Sha biyar don Haka idan an nutsu sai a biyani kudina don Kar su SHIGA cikin gadon Yara !
Ni da kaina da Yan kananun shekaru na nasan mahaifina shike bin Alh Mustafa kudi na Wanda ya ambata wato million Sha biyar Amma a yau da kasa ta shafe ji da ganin Daddyn sai gashi Yana fadin shi ke bin Daddyn alhalin shike taimakar shi a ko yaushe Kuma ko ina.....
Ban Kai karshen tunani na ba naji ammi ta dauki kabbara tana fadin .
"Ko ka manta ne Alh Mustafa sake tunawa kamar dai shine yake binka wannan kudin ai ka manta a gabana akayi hakan ? Fadin Haka da ammi tayi Ina wuta ya jefa ta ....
"Kina nufin sharri nayi mishi kenan bana binshi zanzo nace Ina binshi? Kina Ina lokacin da na biyashi wancan kudin da kike neman kala min sharri?..........
Kawu gide ya Soma bawa Alh Mustafa hakuri Yana kwantar da Kai da Rarrashi. "Rabu da ita Alh waye Bai San tsakanin ku da ummaru ba ? Dole ne ma duk abinda ke tsakanin ku sai ta sani? Ko Ni ai nasan da wannan bashin don ya fada min Ni nayi zaton ma sun Kai million ashirin
Ammi tayi murmushin Alh Mustafa na fadin ai ya bashi million biyar ne shiyasa suka koma Sha biyar.......
Kar ka damu Mustafa ai yanzu ma za ayi ta takare don duk wani Abu da Yake mallakin unmaru ne yanzu zata fiddo shi ta bamu a fitar maka da kudin ka saura kuwa a mu wuce dasu mu ajewa Yara ya Rage nata ta bar yaran hannun mu Ruwan ta ne Kuma ta komawa arnan iyayen ta dasu duk Daya Wai anyiwa tuwo barin Mai Amma dukiya Kam yau zamu karbe komai ku tafi da ita
Haka ammi ta kwaso kaf wasu kaddarori da tasan mallakin marigayi ne ta zube Agaban su Abu Daya take Jin ba zata yarda ba shine su karbe Mata Ya'ya Amma dukiya bakuwa ce Kuma Arzikin Ya'yan ta ba GADO kawai Yake ba Yana can a tsakar Allah
Gaba Daya suka dauki hayaniya Wai ba iyakar abinda ummaru ya mallaka ba kenan ta boye wasu abubuwan Kuma sai ta fiddo su. Ammi ta Rantse Bakin Ranta Amma Basu yarda ba hatta sarkokin zinariyar ta sai da yagana ta kwaso
Haka suka shiga kasafin son zuciya aka Fara sallamar Alh Mustafa da kaddarorin da yayiwa siyen son Rai a matsayin kudin shi yayi musu sallama ya wuce ya barsu da kasafi
Abin mamaki da nuna tsantsar jahilci shine yadda sukayi kason na maza biyu mace Daya Amma babu tumunin takaba ga ammi sai uwa da Uba da suka Dade da Rasuwa Amma su an fitar musu da nasu kason duk da suna kasa🤔 Wai tumunin takaba sangarta mace ne Banda Alfarmar da akayi mata a cida ita a cida Ya'yan ta ga Kuma gadon su sai Kuma anyi wats bita da Killin Bata wani Abu alhalin ga Wanda sukayi silar zuwan shi Duniya ko sun faku ai akwai magadan su
Ammi dai Bata CE musu ko uffan ba suka Gama kasafin su sukayi haramar tafiya gida inda suka jide abincin dake store suka Kuma kwashe suturun marigayin da duk wani Abu dake cikin dakin shi sai da suka jide shi kaf hatta kujeru da gadon dake dakin shi da TV sai da su Badura suka kwashe komai kafin suka fice zuwa gida inda Kuma Ni da ammi mutuwar ta da wo Mana sabuwa mukayi ta kuka lallai Wanda Bai hadu da Rashi irin namu ba lallai Bai San bakin cikin dake dukan zukata ba musamman dangi irin namu marasa tausayin Kai da tausayawa wani.
Tun daga wannan Rana muka Soma karbar kaddarori mabanbanta Wanda karfin imani ne kurum ya Hana mu hadiyar zuciya. Tun daga wannan Rana na Soma mafarkin ido nayi bankwana da duk wata daula da Jin Dadi da na Budi ido acikin ta nayi bankwana da burin fita waje karatu kamar yadda Dan uwana Yaya Abdullahi yayi. Nayi bankwana da gayu irin na Yar gata nayi bankwana da cima irin wadda uba me so da kauna yakewa Ya'yan shi tattali natyi bankwana da suturu na kawa da yayi Wanda mafi yawan mutane suke Fara gani ajikina. Nayi bankwana da ...da...da ... Bankwana da abubuwa masu yawa na Kuma sauya daga wata Fatima Zahra ta da can a wani Dan TAKAITACCEN zamani da tarihin sa bashi da tsayi zuwa wata Rayuwa ta da ban wadda ta fahimtar Dani kasuwar da kaddarori sukayi a Duniya. Ba don na Isa hakurin ba ba Kuma don na iya ba sai don tilas na iya jurewa Amma idan abubuwa suka isheni sai na Rufe kaina a daki nayi kuka na ma ishi na share HAWAYE kafin nace "Ashe dai mutuwa itace Mai tona Asiri?
Watan Daddyn mu biyu da Rasuwa Yaya Abdullahi ya samu hutu ya Kuma taho ba tare da ya sanar damu zuwan shi ba don duk lokacin da sukayi waya da ammi yakan yawaita tambayar ta Wai Ina Daddy ne baya kiranshi Kuma layin shi baya tafiya Amma ammi Bata bashi amsa sai dai ta shashantar da tambayar tashi shi kuma ya taho ba tare da ya sanar ba sai ganin shi mukayi kamar daga sama ganin shi ya sake dawo min da mutuwar sabuwa don nasan a yau abinda ammi take boye mishi zai fito fili fitowar da zamu sake jajantawa kanmu mu Kuma tausayawa kanmu..........
Littafin GARWASHI na kudine ga Mai son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN akan wannan layin 08035191669
Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari a Baku labari gidan iko shine sunana kecewa saduwar ALHERI🥰
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
7//8
Hadiza Bara'u Gidan iko
Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne
Littatafan Gidan iko
Jan kunne
Wuka a makoshi
Zan fasa kwai
Sai A lahira
Mugun kulli
Matar sarki
Dukkan su zaku iya samun su a kasuwa saboda published ne
Dole na gaishe da masoyan Rubutun Gidan iko musamman masu ADDU A da fatan ALHERI Ubangiji ya fini yabawa
Sai haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria a ko yaushe Kuma ko Ina ALHERI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
.........Jikin ammi yayi matukar sanyi ganin Yaya Abdullahi ba sanarwa . Ni kuwa kuka na ne ya bayyana mishi wani Abu ya faru ko Kuma zai faru. Ina durkushe Agaban shi Ina faman Rera kuka na kasa dago Kai na dubeshi kamar yadda ya kasa Rarrashi na ya kuma kasa tambaya ta ba asin kukana.
Ammi ta zuba Mana ido tana Raba Mana kallo itama ta kasa tsayar da nata HAWAYE
Sulaiman ne yake fasawa Yaya Abdullahi Rasuwar Daddyn Kan shi tsaye Kuma ya fadin hakan saboda kuruciya Kuma shi tunda yayi kuka lokacin da za a fitar da gawar Daddy Bai Kuma sai dai ya kalle mu munayi Ni da Amma har wani lokacin nake tambayar kaina juriya ce ga sulaiman koko kuruciya? Sai na Gane jaruman Duniya sune Wanda basa taba Barin damuwa ta kassara musu farin ciki ta hanyar nuna komai ba komai bane . Sune Kuma Basu yarda damuwa ta kawo musu cikas ko tazgaro ba don suna ganin abinda ya faru ya faru babu Kuma me iya dawo da bara ta dawo bana in ba Allah ba sai su murje komai ya Zama ba komai ba su fuskanci abinda ke gaban su manta da wani tabo da kaddara ta kawo musu in ma kaga sun tuna to sun waiga baya ne don hango wani abun ba wancan ba sai yayi clation da shi
Duk juriyar da nasan Yaya Abdullahi da ita da jarumta irin ta maza Amma kukan da yakeyi Ni kaina sai da na tausaya mishi domin ko kalaman da Yake fada ne Dole su saka Mai imani zubar HAWAYE mussamman da na tuna burin mahaifin mu Bai wuce ya inganta Rayuwar mu da ilimin da zamu zamo abin alfahari ba mu Kuma zamo ya fita hakkin mu da kowane irin gata da gatantawa
"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Yake ta maimaitawa Yana fadin
"Shikenan Rayuwa ta juya Mana baya burina na son karatu ya Rushe duk yadda nake son karatun Nan Dole Zan barshi
"Shikenan SHIGA UKU ta samemu ammi Ina tausayin kaina Ina tausaya Miki.