← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayatar wa gareku masoyan littafin GARWASHI hakika kun cancanci yabawa Gidan iko na godiya Allah ya Kara daukaka

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

...........Da sauri na Danna stop na kashe Gaba na na balli balli ganin mazuran da Sony ke min
Kafin ma na fito daga motar sai ji nayi ya shakoni ya finciko daga motar Yana kwada min wani Mari da faskeken hannun shi me kama da faranti

"Wato dama abinda Amaka ke Fadi akan ki gaskiya ne har kin Soma kawo Mana su cikin gida?
Ganin da gaske Yake zai jibge Ni ya barni da ciwon jiki don bashi da kirki wurin duka shiyasa ma Amaka ke bashi go ahead din ya jibgeni in nayi laifi akasin Emmanuel Wanda baya da zafi akan komai kuma ko laifi nayi akace ya jibge Ni afuwa ma shi Yake nema min akasin wannan marar kirkin Sony don Haka nayi nufin kwacewa in gudu Amma sai na Gane Bai Rike Ni don ya saki ba ya Rike Ni ne don ya Nadi banza don Haka nasoma kicin kicin kwacewa shi Kuma ya Soma kwada min Marika Yana masifa inda nayi RAM da hannun shi na Galla mishi uban cizo Wanda ya tilas ta shi sakina na kuwa auna aguje na fada daki na maido sakata Ina kuka

Inajin shi Yana zuba Ruwan tijara Wai su zamu kunyata duk kokarin su Amaka da Maazi Nkem da suke Rike da addinin mu sau da kafa sai nice shegiyar da Zan nuna musu addinin nasu ba na gaskiya bane? To yau sai ya karya min kafa guda

Inajin shi nayi shiru don nasan sai su Amaka sunfi shi shafawa akan Lamarin Ni kuwa gani da wata irin zuciya wadda duk abinda take so to son shi kawai takeyi . In nace so to Ina nufin so Haka Kuma duk abinda take ki kinshi take da gaske in nace ki to ina nufin ki shiyasa naji Arai na su daiyi su Gama Amma babu Mai canja min Ra ayi na ai wuya Bata kisa sai kwana ya Kare

Sony Yana zaune falo Yana fada madam Amaka da Maazi Nkem suka shigo suka same shi Yana tijara maazi Nkem ya tambaye shi abinda Yake wa fada ya Kuma kwashe abinda ya sameni inaji
Amaka ta daki kirji tana fadin Kai me kake cewa my son? Ya sake maimaita mata abinda ya ji ya Kuma gani sai kawai Amaka ta kwasa aguje ta Soma dukan kyauren dakin tana fadin na bude ko ta karya kyauren ta shigo wato banji maganar da ta fada min ba ta Kar na sake nayi kawance da hausawa shine ma don na Raina ta na shigo mata gida da Yan wake waken masu salla na kunna Mata ? Wato na Raina ta ko? To na fito Naga yadda zatayi Dani

Da dai ta gane ba Zan bude ba sai ta juyo Kan Sony ta Rufe shi da duka tamkar shine yayi Mata laifin Wai don me ya barni Bai yi min laga laga ba? Ya nuna Mata cizon da na Galla mishi Wanda yake digar jini
Shi kuwa Maazi Nkem ya gama mutuwa daga zaune ba Kuma komai yake takaici ba sai don in igwai yaji halin da nake ciki Dole ne su fasa Aure na su Kuma sun kwashi Rayukan su sun Dora Akan Aure na gidan igwai

Duk Ina Jin su nayi bakam don nasan bude dakin daidai Yake da tarbar damusar dake Jin yunwa Amma Kuma ga mamaki na sai naji ana sako makulli za a bude sai Kuma na tuna Ashe fa akwai safaya na makullan don Haka sai nayi maza na fada ban daki na Rufe inda Nan ma ban tsira ba Amaka ta cakumo Ni ta fito Dani sai Huci takeyi inda Kuma na Gane Kashi na ya gama bushewa

Shake Ni Amaka tayi da duka karfin ta tana fadin
"Gara dai na kashe ki da kija min abin kunya ace yata ta koma salla Ni kuwa wace Riba naci ? Saboda kin Raina Ni na hanaki gaisa wa da su shine kike shigo min gida da Yan wake waken su kina kunnawa to fada min addinin da Kika zaba? Fada min nace ! Ta fada da Amon murya

Ni Kuma naji Shaka sosai don na yarda na Amince Amaka kasheni din zatayi don bata shakeni don na Rayu ba A a sai dai don ta Mikani lahira Wai ko zata huta da Bakin cikin da nake Shirin jawo Mata
Maazi Nkem ne ya dakawa Amaka tsawa Yana fadin
"Zaki kashe min yarinya ne ko Yaya? Da sauri Amaka ta sakeni inda Emmanuel ya kamo Ni ya taso Ni Yana min sannu
Maazi Nkem ya Rufe Amaka da masifa Akan kokarin kisan da take Shirin yi

Maazi Nkem ya kamo hannu na ya wuce Dani dakin shi Yana maido kyauren dakin ya Rufe kafin ya fuskance Ni

"Gaya min abinda kike nufi shin Zaki bar addinin mu ne na iyaye da kakanni Koko Yaya? Sanin da nayi mishi shima ba son hausawa da musulunci Yake ba sai na kadaa kaina Alamar A a karatun ne dai yake burgeni sai kawai naji shima Maazi ya Rufe Ni da duka Amma na makale ajikin shi Ina fadin kuskure ne ba Zan sake ba kafin ya saurara min Yana Huci

A Ranar Hana Ni abinci sukayi Kuma sukace idan suka sake ganina da hausa man ko waye to Zan fadawa Yan garin mu

Kasset din CD CD dina kuwa duka Amaka ta kwaso su ta saka guduma ta dandake su Redion cikin motar ma sai da ta saka Sony ya cire ta Wai taga gidan uban da Zan Kuma sauraran karatun

Allah cikin ikon shi aka janye strike muka koma makaranta na samu su fauziyya da sumayya na cewa fauziyya ta tura min karatun Nan ta kuwa tura min masu yawa naci gaba da Jin abuna ta cikin hearphon inda Kuma naci gaba da mafarkai Akan wannan kayataccen wurin muna salla wani lokacin ma har littafi nake ganina na bude Ina karatu inda Kuma wata da mukeyin sallar a tare tace na Daina saka kayan da nake sakawa Allah baya son irin Haka in Rika saka irin nasu wato doguwar Riga in Kuma Rika Rufe jikina don Yana da matukar Daraja in son samu ne ma in Rika Rufe fuska ta Nikabi
Abinda ya bani mamaki bayan na farka daga wannan mafarki shine matar da taba Ni wannan shawarar ba fa da hausa tayi maganar ba ba Kuma da yaren mu na Igbo ba da wani harshe Mai matukar Dadi Kuma maganar sai ya zamo tamkar irin karatun da nake saurara kalar maganar Tata Amma Kuma Wai na fahimci abinda take nufi sai kuma na yanke shawarar siyo kayan Nan da matar Nan ta shawarce Ni Amma Kuma sai zuciya ta tambaye Ni to ta Ina Zan Soma saka kayan Nan? Ba dai Nan gidan da sony da Amaka suke ba? Ashe kuwa da sauran kallo

Ana Haka NE auren Sony ya taso muka SHIGA sabgar bikin shi da Amaryar shi sisiliya wadda ta Jima tana dakon son shi

Na SHIGA kasuwa don na siyowa Amaka Ashoke Wanda zata Rabawa kawayen ta tunda tuni dama aka tanadi less din Ashoke ne babu don Haka na nufi kasuwa cikin mota ta inda tun kafin na Kai na Soma Jin kaina Yana juyawa Alamar dai ciwona zai tashi kenan don gaskiya tunda na Soma sauraren karatun Alkur ani ya Dade Bai tashi ba don Haka a yau sai naji Alamar zai tashi kamar na koma gida na fadawa Amaka ba Zan iya zuwa ba Amma Kuma sai Naga ai na kusa cimma kasuwar kawai na karasa in yaso in na suyo Mata Ashoken in baro motar na hawo ta haya don na tabbatar ba Zan iya tuko ta na nadawo ba in yaso ko Emmanuel ne yazo ya daukar min

Haka kuwa na karasa kasuwar cikin shigar kana nanun Kaya da dogon takalmi high hill sai dogon gashi na da ya Sha gyara sai kyalli yake har ya sauko Kan kafada ta
Na fito daga motar Ina karajin kaina Yana juyawa . Abinda kawai na sani na Kuma Rike shine na San lokacin da na maida kyauren motar na Rufe daga Haka ban Kuma sanin abinda ya faru kaina ba anan aka makenk na Fadi kasa a tsakiyar kasuwa. Kuma wannan lamarin shine mabudin bude kofar kaddarar da ta hado Ni da mahaifin ku Umar faruk har zuwa lokacin da kaddara tayi Aikin ta ta kaddaro kaddarar da faifan kaddarar ya bude har zuwa inda ake a yau a Kuma yanzu.................

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku

Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿🥰

🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
31//32
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga Ahalin gidan ma aiki da duk masu kaunar shi da gaskiya suka Kuma bisu da kyautatawa

Tukwici ne ga Hadiza ta maman Aliyu da hafsat da Zainab sani maman jinio da Zahra

Fatan ALHERI ga Maryam Bara'u Mero Allah ya gyara min ke

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Chapter 14 · 0% Book details