Sashe 15
Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
.. .......Ina kwance shame shame a tsakiyar kasuwa inda aljanu na suka buge Ni na Kuma Fadi babu Alamar motsi ko numfashi Amma abin mamaki babu Wanda yabi ta kaina bare ya kawo min dauki koda ta mayar Dani inuwa ne Amma kowa sai ya wuce Ni abin shi Amma Kuma ga faruk abin ba Haka Yake ba don Akan idon shi hakan ta faru ya Kuma jira yaga Ni ko wani daga cikin yarena ko zai tallafa min Amma kowa sai dai ya kalleni ya wuce don Haka ya karaso a kaina ya Kuma fahimci matsalar tawa ta bugun iska ce don Haka sai ya Soma tofe Ni da ADDU OI cikin ikon Mai sama kuwa sai naji tamkar ana zuba min Ruwan sanyi Wanda ya farkar Dani daga wannan wahalar. Na bude idona Ina kallon shi inda naji Yana karanto wani karatu Wanda na taba Jin irin shi a Bakin Mai karatun Nan wato sudais. Ga mamaki na Sai naji tamkar ana zare min wani Abu marar Dadi ajikina ana kuma mayar min da wani sasaanyan Abu Mai sanyi har zuciya ta
"Sannu yayi min cikin sanyin murya na amsa da yauwa Ina kallon shi da irin kulawar da ya bani alhalin shi din ba yarena da addinin na Daya dashi ba Akasin su Wanda na fito a yare da addinin na dasu din Basu kula ba sai Wanda Amaka Bata son nayi mu Amala dasu to Ni kuwa saboda Allah ya za ayi na mance da hausawa ko na Daina kulasu alhalin su din suna min karamci tamkar dai a cikin su nake?
Ya dauko min key din mota ta da na watsar a can gefe ga Kuma Yar jakar post dina da kudina suke ciki itama na watsar sai shine ya tattaro min su ya bani Yana fadin Zan iya tuka motar ? Na ce mishi ba Zan iya ba ya Kuma tambaya ta me Zan siya? Na fada mishi na Kuma nuna mishi shagon da Zan SHIGA idan na koma gida Zan turo Yaya na ya daukar min motar. Ya Miko min key dina da jakata na karba Ina mishi godiya da irin taimakon da yayi min yace babu komai Wai yiwa Kaine
Na SHIGA shagon da Zan siyi Ashoken Ashe Wai shine Mai shagon na siya na biyashi inda yayi min sauki ya Kuma fada min gaskiya Akan Wanda na Fara zaba cewa quality din su ba na sosai ba inda ya nuna min Mai kyau na Kuma siya muka Rabu Ina Mai farin cikin haduwa ta da shi da Kuma irin taimakon da ya bani ba tare da ya duba koni wacece ba ya taimake Ni babu kyama babu duba addini
R
Tun daga wannan Rana sai nayi sabo da Umar faruk sabo kuwa Mai yawa har ta Kai duk abinda Zan siya to wurin shi Zan siye shi kuma na lura Yana da sani sosai ta fuskar addini sai na Kara kusantar shi don na Soma fada mishi abinda nakeji Akan addinin su shi Kuma Yana fada min ita Rabauta in Allah ya Rabautar da bawa ko a ki ko aso sai yayi .Kuma a yadda ya fahimci lamarina mahaifa na basa so Kuma su iyaye biyayya ake musu a duk abinda sukayi umarni . Haka yayi ta bani shawarwari Akan nayiwa iyayena biyayya Bai taba fada min na bijire ba sai naji ya Kara burgeni lamarin shi Kuma ya tsaya min Arai na kasa mantawa dashi
Musayar lambar waya da mukayi dashi wani lokacin nakanji kamar na kirashi Amma Kuma sai naji Yana min kwarjini tsoro Kuma ya kamani ince to in na kirashi in ce mishi me?
Duk yadda naso na yakice shi na kasa Domin kuwa sai mafarkin shi nakeyi Wai muna salla a tare dashi a kayataccen wurin Nan
Ban Ankara ba naji zuciya ta taja Ni na afka a soyayyar Umar faruk Wanda na kwana biyu ban je shagon shi ba don Ina tsoron yace baya Sona tunda Ni din ba jinsin sa bane kuma ba yaren shi bane me yuwa ma yafi Amaka tsanar mu Amma Kuma nasan daga gareshi dai ba Zan samu hakan ba sai dai ko ta bangaren iyayen shi don na tabbata yadda Amaka Bata Sona da hausawa Haka shima Umar din Koda shi ya Soni to iyayen shi ba zasu Soni ba kasancewar Ni din ba yaren shi bace tuna hakan da nayi sai ya jefa Ni a cikin Rudani
Ban boyewa kawayena ba na makaranta sai da na fada musu abinda Yake damuna Akan Umar faruk inda sumayya tayi ta min dariya tann fadin
"Kai Justina kin SHIGA hannu gaskiya Amma Kuma lamarin naku da mamaki don yazo ne akarkace don in har naki iyayen sun yarda da Auren musulmi to shi nashi ba zasu yarda ba Amma kiyi ta ADDU A in da ALHERI Allah ya tabbatar ya Kuma kawo hanya Mai sauki ta tabbatuwar lamarin
Ita kuwa nafisat Rabi u cewa tayi da ace dai na musulunta ne abin zaizo da sauki Amma Kuma Yaya nake ganin iyaye na zasu karbi musulunci na?
Sai Kuma na hango Ranar da za ace wa Amaka gani na musulunta bana ko shakka bindigar Maazi Nkem zata dauko ta harbeni don ita da kanta take fadin zata kasheni ne in dai nace Zan biyewa hausawa bare Kuma ace na SHIGA musuluncin da ta gama tsana a Duniya. Ban boyewa nafisat yadda Amaka ke tsanar musulmi ba ita Kuma tace gaskiya Akwai matsala. Na SHIGA damuwa ba kadan ba inda duk suka Gane na Gama kamuwa da soyayyar Umar faruk inda Kuma waya ta tayi Kara na duba sai nayi Arba da sunan Umar faruk Yana yawo Akan screen din waya ta na yi saurin nunawa nafisat nace Mata gashi Nan ma Yana kira tace dauki Kar ta tsinke shima dai ga Alama ya kamu sai dai kafin na daga har Kiran ya tsinke Amma ba a Jima ba wani Kiran ya sake shigowa na daga Ina mishi sallama ya Kuma amsa Yana fadin Ranki yadade Justina shikenan kin barni ina ta jaje har gidan Redion BBC? Nayi murmushi nace ai kuwa baka Zo gidan mu ba da baka Kai Cigiya ba.....
"To ai ban San gidan naku ba tunda Baki fada min ba don Kar na kawo Miki ziyara......
"Idan kuwa zaka Zo me zai Hana na baka address?
"To abani address din sai nazo tunda ke kin min yaji. Murna ta cikani na Kuma tura mishi address din ya Kuma fada min Ranar da zai Zo zai kirani
Kawaye na sun bani shawarwari Akan kame kaina da Kuma kiyaye abinda zaisa Umar faruk ya janye jikin shi akainan don yadda sukaji muryar shi da kalaman shi kamar Babu yaudara Ni Kuma sai na fada musu sanadin haduwar mu dashi da irin taimakon da ya bani inda su duka sukace zasu so ganin shi don ya burgesu da Haka dai muka Rabu na dawo gida Ina ta dokin Ranar da Umar zai kirani yace min gashi Nan Zuwa don ban San irin tarbar da zanyi mishi ba
Kwana biyar da yin hakan sai ga Kiran nashi ya shigo waya ta na dauka Ina gaishe shi Ina Kuma tambayar shi Allah ya sa dai yau zai Zo? Ya Kuma tabbatar min da kwarai kuwa yau zaizo da misalin karfe biyar na yamma nace to Ina jiran zuwan shi
Karfe biyar kuwa na bugawa sai ga manyan motocin gidan igwai yarima Gibson ya karaso kawo min ziyarar ba zata a zatona bakona ne Umar faruk don Haka na fito tarbar shi cikin murna Amma Ina zuwa sai Naga Akasin hakan wato yarima Gibson cikin SHIGA ta nuna shi din jinin sarauta ne saboda kurewa da cinyewa ta fannin kyau da gayu inda Kuma naji kamar na fasa ihu ko in Fadi kasa In ta Rusa kuka .......
Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669
Labarin GARWASHI daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu
Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰💃🏿😂
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
33//34
Hadiza Bara'u Gidan iko
Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne
Godiyar har kullum ga Ubangiji Wanda ya yarje min komai cikin sauki da fuwacewa salati da Aminci da taslimi ga Annabi MUHD S A W da Ahalin gidan sa madaukaka da duk Wanda yabisu da kyautatawa
Tukwici ne ga Hafsat Bara'u ba Duhu Allah ya bada ilimi me Amfani
Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
..........Duk murmushin da yarima Gibson ke jifata dashi na Jin Dadin ganina hakan Bai sa naji nayi farin cikin ganin shi ba sai ma wani turiri da naji zuciya ta nayi don Ina ganin zai kawo min cikas akan zuwan Umar