← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun cika filin jirgin da kukan mu Ni da Amma kafin aminin Daddyn wato Alh Mustafa ya katse ammi da wata tsawa Yana zare Mata idanu abinda yayi matukar Bata mamaki don ta hango wani Abu Mai Kama da tsanar ta fal idon shi abinda Bai taba nuna Mata a lokacin Rayuwar mijin ta ba akasin zolaya da kambama ta wurin iya kula da abokin shi.......

"Ke da Allah saurara Mana Haka Nan tsiyar tubabbu kenan ko zasuyi shekarun Annabi huhu a cikin musulunci sai sun nuna maka asalin su da jinin jikin su mu a addinin mu na musulunci kukan mutuwa haramun ne kar ki sake daga Mana murya anan ja daga baya ki Kuma matso da mota mu saka shi mu wuce gida dubi da Allah yadda Kika Tara Mana mutane sai kace akanki aka Soma Rasa miji

Ni da ammi muka bishi da jajayen idanun mu cikin wani madaukakin mamaki kafin jiki a sanyaye ammi ta Mika mishi key din tana fadin Bata da nutsuwar iya tuki don Haka sai ya amsa ya matso da motar aka sako gawar mahaifina muka shigo mota ya tuko shi da wannan mutum da bamu San ko waye ba muka nufo gida muna sake sabunta kukan mu

A falo aka shimfide gawar Daddy inda Alh Mustafa ya cewa ammi ta buga waya can kauyen su Daddy ta sanar dasu

Jiki na kyarma tare da bugun zuciya ta Soma neman layin yayar mahaifina wato Yaya Badura cikin sa a Kuma ta sameta Amma sai da tayi Ringing sau biyar kafin Yaya Badura ta daga tana fadin

"Waye? Ammi taji wani sabon kuka ya kwace Mata tace
"Yaya Badura nice Aminatu........

"Na Gane muryar ai meye Kuma kike min shaken hanci (kuka)?

Ammi ta Kara saka kuka tana fadin
"Faruk ne Yaya Badura don Allah kuzo kuce mishi ya tashi Kar ya tafi ya barni bani da gata sai Allah sai Kuma shi.........

"Ke aniyar ki ta biki yar arnan dawa fatan da kike mishi kenan ya tafi ya bar Miki dukiya ko? To ki kwana da Shirin ciwon Kai idan ya samu ummaru na Rantse Miki sai kin bar Duniyar Nan bakar kaddara kawai. Kukan ammi ya Kara tsanani saboda Jin masifar da Badura ke Mata ita Kam Tata ta sameta

Badura tana sabe da wayar a kunnen ta tana sauraren kukan Ammi Bata kashe ba sai da ta tsinto muryar Alh Mustafa Yana waya Yana fadin Alh faruk ne Allah yayiwa Rasuwa sai kawai Badura ta kwantsama uban ihu inda mutanen gidan suka taru kanta tana fadin matar ummaru ce ta kirata tana kuka Kuma taji ana fadar ummaru ne Allah yayiwa Rasuwa.

Kan kace me ? Sai gasu kwai da kwarkwata sun ciko mota mazan su da Matan su Yara da manya sunyi dirar mikiya agidan Abu ga jahilcin kauye sai gidan ya amsa sunan shi wato gidan makoki don kewaye gawar sukayi suna ta gurzar kuka har da masu tashin aljanu wato Yaya Badura Wai ta Rasa Dan uwa me kaunar ta da daukar takalifin ta

Ahaka aka shirya Daddy akayi mishi sutura aka yi nufin sada shi da makwancin sa har aka bukaci ammi tazo tayi mishi sallamar bankwana. Ta kuma taho idonta na zubar HAWAYE ta sunkuya tana mishi ADDU AR samun kyakkyawan makwanci da samun Rabon Duniya da tana Kuma fatan can tafiye mishi wannan kuntatacciyar Duniyar marar mutane masu Adalci Adalcin da suke kasa yiwa kawunan su bare suyiwa wani.....

Kawai sai ji tayi an finciko ta an cillo waje
Ta dago idonta tana Kuma Jin zafin hannunta da ya bugu da Bakin kofar ta kalli yagana sai bude manyan hantunan ta takeyi Wai afusace take

"Uban me Kika sani acikin musulunci da musulmai da har kike wani mimi mi da Baki ADDU A kike son nuna Mana kin iya ne? Ai Baku gada ba bare kiyi abin kuzo mugani tuban Taki ta muzuru tuban ganin abin Duniya? Da Allah fice anan Kar kisa ayi mishi azaba akan tsayuwar ki Akan shi kayan kazanta dake iyalan oduduwa da fafaroma

Jin abinda ya kumbo na yagana ke fada tana tada murya yasa na kamo ammi dake HAWAYE muka fito yagana na Rako mu da wani matsiyacin tsaki

Sallamar bankwana da banyi da mahaifina ba sai dai na Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa don lokacin da Naga an fito da mankarar dake dauke da gawar shi ban sake sanin abinda yayi kantafi da Rai na da nutsuwa ta ba sai dai farkowa nayi naganni a Kan cinyar ammi tana shafawa fuskata Ruwa na kumayi nasarar ganin fuskar ta da ta kumbure saboda kuka Kuma har yanzu idaniyar ta Bata kafe da zubar Ruwan HAWAYE ba.............

Wannan labarin na kudine ga Mai son cikakken labarin zai biya 300 ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Labarin GARWASHI daban yake da sauran littatafan gidan iko Kar ku Bari abaku labari

Gidan iko sunan ke muku fatan ALHERI🥰💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
5//6
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Har kullum godiya ga Ubangiji ta zamo Dole Akan yadda ya sauwake Al amura masu yawa agareni Allah ka Kara dubun dubatar salati ga shugaban halitta Wanda nake fatoh shiga cikin ceton shu Ranar alkiyama

Masoyan Rubutun Gidan iko babu yadda Za ayi na manta ku kun Kai har kun wuce a gareni ba don na iya ba kuke yabawa tare da ADDU AR fatan ALHERI gareni har da iyayena ko nayi nufin aje alkalamin don bawa kwanya da zuciya hutu sai naji fatan ALHERIN ku nake bukata sai na girgije na Soma sabon typing🥰

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

..........Zaman makokin mahaifina shima wata makaranta ce guda da za a dauki Darasi Kuma irin Darasin Nan da Duniya ce kadai Kan koyar da irin shi Amma ba Wai mutane irin dangin mahaifina ba

Zaman makokin ya kasu Kashi biyu NE a cikin gida yayin da akeyin guda Daya a waje wurin mazan...
Ko dayake can din ma biyu NE akeyi inda dangin mahaifina suka kafa majalisar su ta Yan uwa Kuma dangi yayin da Alh Mustafa ma shi da jama ar da suka San shi da marigayin mahaifina da mu amalar su suna kammale wurin Alh Mustafa inda Kuma su kawu madu da kawu gide suke tasu majalisar ta Yan uwan Daddyn in sunzo wurin su suke sauka kamar yadda a Nan ma cikin gida zaman ya kasu Kashi biyu . Su Yaya Badura da yagana suna falon Daddyn inda yagana ce tazo ta ce da ammi ta Bata key din dakin Dan uwan ta Bata Kuma ja ba ta Bata sai dai da Yake Kan nasu babu komai sai handama da babakere babu Arabi ba Boko sai hadama da son Azurta Kai yasa basu waye da komai na maraya ba kasancewar ko acan garin nasu na Maiduguri kauye ne sosai shiyasa ma da yagana ta karbi makullin ta kasa bude uwar dakin Daddyn sai suka tare a falon yayin da ammi ke falon dakin ta Kuma makotan tane Wanda suke gaisuwar mutunci tare da ita musamman mama da suke ga gida ga gida Kuma ta mayar da ammi yarta saboda ko shawara da ita ammi keyi shiyasa take tare da ita Kuma mutanen unguwa ma duk da kasancewar unguwar ta G R A ce irin Rayuwar kowa tashi ta fissheshi ake ba Ruwan kowa da kowa yasa dai daiku sukan gaisa ayi barka ko gaisuwa inda can Kuma wurin su Badura duk Wanda zaizo daga Maiduguri Kai tsaye wurin su yake yada zango

Ranar farko ta mutuwar Badura da yagana ne a cikin kichen suna faman dorawa da saukewa na abinci Wanda yagana ta karbo Dan makullin store Wanda ke shake da kayan abinci suka SHIGA sabgar gaban su na gurkawa da Rabawa Amma ko cokali guda ammi Bata gani da idon ta ba bare ayi Mata karar miko Mata ita da jama ar da suke zaune sai fa mama ce ta saka yarta ta dafo wake da shinkafa aka kawo Nan ammi da sulaiman don ni dai Kam ban zaci ko da dimuwa Ruwa ya ratsa makoshi na ba bare abunci Wanda su yagana ke faman hadidiya

Sai bayan Isha I ne kawu madu da kawu gide suka nado tabarmin suka shigo ciki inda kawu gide ya Soma bude fridge din dake kicin yayi Arba da Naman kaji da na shanu ya kuwa kwalawa yagana Kira ta karaso inda ya Rufe ta da masifa Wai ga nama cike da na ura Amma tayi musu abinci babu nama? Ta ke ya Bata umurnin yi mishi farfesun Naman saniya a take Kuma yagana ta hau aikin dahuwar Naman

Haka kawu gide yayi ta zaga gidan Kuma duk abinda ya gani sai ya bude ko Kuma ya nemi sani har yagana ta gama hada farfesun yace yaga fridge a kofar falon ammi taje ta duba in lemu ne ta kwaso musu

Haka suka baje tamkar wadan da suka Zo dinner ba mutuwa ba

Ammi dai tana kallon su inda mama ta kula da take taken Yan Daddy din dama ta San komai sai ta bawa ammi shawarar Kar ta sake tace zata tanka musu duk irin abinda kuwa zasuyi Kar tace musu ko uffan tunda dai Ya'yan ta uku ne Kuma babu Yan uba bare a nemi tada Mata hankali da wani Rabon GADO in aka Gama sadaka dai dolen su su tafi su barta da Ya'yan ta ammi kuwa ta amsa da to
Chapter 2 · 0% Book details