← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Abdullahi Yana sunkuye Agaban su kawu madu Wanda ke fadin abinda ya kawo su Wai kaf dukiyar da mahaifin mu Yake ciki Yake juyawa gadon da iyayen su suka mutu suka bar musu ce shi Kuma saboda shine Mai nasibin siye da siyarwa sai Yaya Badura tace abar mishi ita ya juya tunda abin duk na gida ne in yaso idan ta yadu tayi harshe sai a fidda kowa to akan hakan ake sai Kuma ga Ajali ya Riske shi ya mutu da nauyin dukiyar su don Haka suka Zo don a sake lissafi da dai sunyi hakuri sun barwa marayu to Amma daga baya da suka tuna da gidan Nan da Kuma motocin marigayin shine suka Zo karbar hakkin su dama su shi Abdullahin ne suke so suyi magana dashi saboda shine namiji Kuma Dan su don ta ammi ba ta isa suyi wannan maganar da ita ba.

Mu duka mukayi Duff tamkar babu kowa a wurin

Yaya Abdullahi ne ya dubi Ammi yake cewa
"Ammi kinji abinda sukace.......
"Ubanwa yace ka sako Mana ita? Cewar kawu gide

"Harkar Wanda suka shafi musulmi ne ba harkar Yan lahadi ba kaima abinda yasa muka sako ka don Dole za a kiraka jinin mu Kuma ba Wai shawarar ka muke nema ba Kar kace zaka wani daga Mana hanci Umarni ne ba shawara ba Bari kaji abinda muka Zo dashi

Ya dubi kawu madu Yana fidin
"Munzo ne mu debe ku mu wuce daku can maiduguri ita Kuma wacan kayan banzan mu sallame ta ta komawa kafuran iyayen ta dama mu bama maraba da shigowar ta cikin Ahalin mu sunan ku dai uban ku ya gama Bata muku shi tunda ya gama jinin ku da ahalul kitabi mu kuwa yaya zamuyi da ku tunda mahaifa ta hado mu dashi muma sai dai mu kalli Allah kawai Amma in Banda zumuncin Allah yaushe irin haka zata faru har ka kalli Ahalin mutum ? Gabana naji yayi wata faduwa Jin abinda kawu gide yake fada ba Wai komawar mu kauyen ne takaici na ba a a tadda Yake aibata uwata wadda ta zabi shigowa cikin su don an kwadaitar da ita hasken musulunci Amma su da suke musumai sune suke tozartata tamkar dai ace Ridda tayi daga musulunci ta koma inda ta fito wato addinin ta na kirista

Agaskiya idan dai har zai zamo mutanen dake amsa sunan musulunci irin dangin mahaifina ne to na tabbatar da duk Wanda ya shigo cikin musulunci da gudun shi zai fice ya bar addinin duk yadda yake son shi kuwa saboda Rashin nagartar wadan da ke amsa sunan musulunci har ma yayi zaton abinda yaji ko ya gani Akan musuluncin ba Haka bane yaudara ce

Ammi da tunda taji abinda suka fada ta Fara kuka da iyakacin karfin ta don ta San Bata da karfin fada dasu Kuma in har aka Raba ta damu to ta gama SHIGA UKU don Haka ta dire duka gwiyawun ta akasa tana kuka ta hade hannuwan ta wuri Daya Alamar Roko akan kar su Rabata da Yayanta ita ta yarda in ma gidan ke Basu so su ganta ciki zata tashi Kuma zata bar musu Amma don Allah Kar su Raba ta Ya'yan ta

Kukan da ammi keyi yayi masifar kada hantar cikina har naji koma me za ayi ba Zan taba barin a Raba mu da ammi ba don da iyakar gaskiyar ta take kuka tana Rokon su fuskar ta ta baci da Ruwan HAWAYE sai ahi take musu da Roko Amma babu Wanda ya kulata sai ma harara da suke jifarta da ita tamkar idanun su zasu zubo kasa........

"Mun fa gama magana babu wani tsari da Zaki kawo Mana baccin da muke tsoron bar Miki Ya'yan don kar ki mayar dasu kafurai ai da har su zamu bar Miki ki koma can Legos ki mayar dasu kafurai duk matsalar kuce ba tamu ba. Cewar yagana

Yaya Abdullahi yayi magana cikin wani sanyi Wanda ke nuna cikin firgici yake firgicin da na tabbatar na ganin Ammi a wannan halin ne

"Kuyi hakuri kawu da dai Ni kukace na dawo Maiduguri ne to da zanyi alfahari da hakan Amma Zahra da sulaiman idan aka maida su can gaskiya inajin Ni kaina banyiwa kaina Adalci ba Kuma ma na lura Ammi Bata son Rabuwa da su don Allah ku bar maganar Raba ta dasu ..........

"Kai fita idona na Rufe kaji in ka kuskure na Rufe idona kana ciki akwai matsala mun Gama magana ba shawarar ku muke jira ba.......

"Wai shima Nan haka da shi ya iya iya shege? Cewar kawu gide da ya tari nunmfashin madu.....

"To ai matsalar gwamutsa jini kenan ka dai gani sai kace wasu tsararrakin shi muna magana yana mayarwa bafa kunya garesu ba musamman waccan me idanun uwa anyi barin kwai a titi kawu gide ya fada Yana Nuna ni......

"To yaushe zasuyi kunya dama uwar su Bata wanye da banbance Haram da halak ba? Bata wanye da tsarki da kafurci ba? Cewar yagana

Haka suka ci gaba da cin mutuncin mu da cin fuska tas suka yage fuskokin mu kafin suka bukaci mu tashi mu gado kayan mu mu wuce Maiduguri inda Kuma tashin hankalin ammi ya karu tayi ta kuka me sauti tana Kara Rokon su da suyiwa Allah da ANNABI su bar Mata mu Amma kamar ba Allah take Rokon su ba inda Kuma yaya Abdullahi ya Gane ba irin su kawu gide akeyiwa kawaici ba don Haka ya fada musu gaskiya ba zamu bisu Maiduguri ba tunda Ammi Bata so......

"Kai kace me? Kawu gide ya fada Yana zaro kwala kwalan idanun shi

Ya kuwa sake maimaita mishi abinda ya fada na ba zamu bisu Maiduguri ba........

"Karya kakeyi Wallahi uban ka ma Bai Isa na yanke hukunci ya Musa min ba bare Kai kayan banzan da Bai Kai na wofi ba ko Kuna so ko Baku so gaku can kunje Maiduguri ubanku ma da can yake tutiya da alfahari. Ya fizgo hannun sulaiman dake kankame da ammi kafin Jin ana Shirin Raba su nima Kuma yagana ta finciko hannuna ta Rike Alamar dai da gaske suke Shirin tafiya damu.......

"A a ku sake su ai daukar duka hutawa tunda Haka suka shirya su da Uwar su ai bayan tiyar akwai wata cacar tunda ba zasu biyo mu ba ai mu bar su dama don kar a zagemu ne ace saboda kasa ta Rufe idon unmaru ne muka yada su kasan mutane ba iya musu ake ba yanzu ne zakaji ana ga zance ga magana sai dai Yaya zasuyi damu akan dukiyar gadon mu dake hannun sa?

Ya fada Yana kallon Ammi

Cikin shesshekar kuka Ammi tace
"Ku kasa dukiyar yaran Nan sake hannunku uku ku dauki Daya sauran biyun sai ku Adana musu......

"Yo har nawa ne abinda muka karba da kike fadin mu dau kaso Daya mu aje saura? To dukiyar dake hannun mu Bata Kai Daya bisa goman abinda muke bin ummaru ba shekara nawa Yana juyata ?.....

"Kawu kuje ku Rike ta duka mun bar muku a matsayin dukiyar ku. Cewar Yaya Abdullahi.

Yagana ta watso mishi wani shegen kallo tana fadin
"Ko gidan Nan aka hada Mana dashi ba a biya mu ba don Haka asan dai yadda Za ayi don ni ban yarda iyakar dukiyar da ummaru ya Tara ce matar can ta kawo ba......

"Gida ma ai ya zamo wajibi mu karbeshi mu saka shi kasuwa in yaso sauran cikon mun yafe tunda abin duk na gida ne Kuma Dan Uwa ne.

Wannan magana ta kawu gide itace ta kawo karshen jayayyar akan gidan da muke ciki sun kwace shi a matsayin kudin da suke bin mahaifin mu Wanda ko Ni na San Babu wasu kudin su a hannun shi. Mutumin da ya kasance cin ka da Shan ka duka shine in ma jari sukayi kukan ya karye shine Mai tada shi Amma yau saboda kawai mutuwa Mai tonon Asiri sunga babu shi shine har suke fadar Wai gadon su Yana hannun shi bayan sun karbe komai namu na Kuma mahaifin mu Dan gidan da muke ciki ma yau shi ya tsone musu Ido har suna fadin shima nasu ne Anya kuwa idan dai har haka zumunci ya koma ba Dole asha wuyar Rayuwa ba🤔?

Ban zaci Rashin mutuncin nasu ya Kai inda ya Kai ba sai da Naga kawu gide yayi tsaye akan Yaya Abdullahi Wai ya bashi takardun gidan Ammi Kuma tace ya dauko su suna Nan dakin Daddyn cikin akwatin takardun shi Dole kuwa Yaya Abdullahi ya dauko su ya mikawa kawu gide suka fice suna fadin tunda mun zabi Uwar mu akan su to mu sani da Uba ake Ado Riga ko a kasuwa sai a siyo Kuma duk Dan da yarasa Rigar Uba yayi asara Kuma har abada a tsirara yake yawo Kuma tunda muka kisu to Kar mu sake mu nemesu mu Riki dangin uwar mu in yaso mu dauwama a cikin musulunci ko mu koma kafurai duk Daya Wai anyiwa tuwo barin Mai Kuma sun bamu notice na kwana talatin mu nemi wurin Zama don zasu saka gidan kasuwa su siyar da Haka suka fice suna aibata ammi da Dan uwan su dake kwance kushewa Wai shi ya ja musu ya jajubo musu Ahalin oduduwa da fafaroma

Ban taba tsintar kaina cikin tashin hankali ba tun bayan Rasuwar Daddy sai a yau da na Gane gidan Zama ma zai gagare mu bare abin kaiwa abakin salati sai Kuma na Gane shi bawa Yana zuwa Duniya ne kawai don ya karbi kaddarorin sa kyawawa ko Akasin hakan kamar dai mu da muke tsaka da karbar namu kaddarorin masu saka idaniya zubar HAWAYE..................

Labarin GARWASHI na kudine ga me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Labarin daban yake da sauran Kar ku Bari ayi Babu ku sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
11//12
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne
Chapter 5 · 0% Book details