← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Riko hannun na muka bishi wurin da motocin shi suke Yana Rungume Dani a gefen kafadar shi Yana Rada min wai nayi mishi Rowa ta girki na Wanda yaso ya dandana yaji zakin hannu na Wanda inda yaji zakin hannun nawa to da kwana yayi Amma yanzu zaije ya fadawa igwai Yana son nazo nayi mishi Zaman daki sai yaji girkin nawa...

Nayi maza na hade fuska don nasan abinda Yake nufi da zaman dakin da zanje nayi mishi wato dai inje in samo ciki Wanda zai tabbatar da Auren mu kamar yadda Al adar take abinda kuma nakejin ba zai taba yuwa ba Kuma zai yuwu ba don Haka nace mishi

"Ba Zan Zo yi maka zaman daki ba karma kace Haka in dai girki ne zanyo shi na sako maka mota akawo maka shi har gida.......

Ya katse Ni Yana murmushi
"Ai ba girkin kawai nake so daga gareki ba my love ganin da nayi Miki a yanzu ya nuna min kuskuren da nayi Ina da kamar ki Amma ace na barki kina nesa Dani sai dai nayi ta ganin ki a cikin bacci na da mafarki na? Ki saurari aike na cikin satin Nan Zaki iso min zaman dakina ya Miko min wata jakar fata me zanen Ado irin na tambarin sarautar su yace igwai ne ya ce akawo min kafin ya Kuma Miko min wata ita Kuma jakar Leda ce ta wani kamfani ita Kuma mamar shi ce tace ya kawo min shi kuma hannu na ya Kama ya saka min wani tsadadden zobe na zinariya Mai Daraja wadda itama ajikin zoben tambarin sarautar tasu ne amma anyi wa zoben harafi guda biyu na farkon sunan mu wato j & g don Haka ya fada min shi Kuma ga tashi kyautar Nan ya Kuma sumbaci yatsun nawa bayan ya gama saka min zoben
Fadawan dake biye dashi a baya suka kwashi kayan nawa suka Rike Wai su Kai min gida
Har na juya Zan koma gida don hankali na Yana wurin Umar bayan nace mishi yayi min godiya wurin mama da Kuma igwai akan abinda suka bani sai kawai naji ya Ruko min hannuwa Yana min kallon tsakiyar idanu Wai Haka Zan barshi Ni ba Zan bashi abinda zai Rika tunawa Dani ba?
Na bishi da manyan idanu na don ban San abinda Yake nufi ba sai kawai naji ya jawo Ni cikin motar Yana hada tsinin hancin shi da nawa inda na Gane abinda yake nufi Wanda Kuma banajin zai sameshi don ba Zan iya yi mishi yadda zai gamsar dashi ba tunda banayin shi Amma ko hakan da na Raya a zuciya ta ya juyo Koko Alamar hakan ya gani shiyasa Bai Bata lokacin jira na ba ? Oho sai kawai na tsinto bakina a cikin nashi na Kuma kasa kwacewa sai da ya sakeni Don ya so hakan. Na fito motar Ina Jin wani Abu Yana min yawo a jiki saboda irin hakan bata taba faruwa Dani ba a son Raina ko Akasin hakan irin na yau don Haka wannan Rayuwar bakuwa ce a gareni

Wannan shine bankwanan da mukayi da yarima Gibson ya tafi Yana min wani kallo Wanda nakejin don ya cuceni ne ya hada bakin shi da nawa yake min shi

Na kawowa Amaka kayan da ya bani da zoben shi da kyautar igwai da kuma ta mah wato uwar yarima Gibson

Amaka ta Rafsa guda Mai tsananin karfi tana Rawa Wai anyi min kyauta sai Kuma ta SHIGA budewa tana gani inda Ni Kuma na sulale zuwa wurin Umar Wanda na hango shi ya fito daga gidan su Grace Yana tsaye jikin bangon gidan Ina karasowa ya Soma fadin wannan Kuma waye Haka yazo wurin ki Justina? Gaba na ya Fadi Jin Ashe yaga duk abinda ya faru tsakani na da Gibson sai ban boye mishi ba na sanar dashi shine Wai mijin da iyaye na suka zaba min....

Ya dube Ni Yana Fadin Ashe Ni Kuma igiyar Ruwa na Kama kenan Justina tunda har anyi Miki miji?
Nima na dube shi nace
"Kana Sona ne kenan? Yace kwarai kuwa sai dai nasan Babu ta yadda Za ayi na sameki tunda har iyayen ki sunyi Miki miji Kuma ko da basuyi Miki miji ba ba lallai ne su bani Auren ki duk da tazarar dake tsakanin mu Amma nayi nufin na fahimtar dasu idan suka ki bani Auren ki saboda tazarar mu to Kuma gashi ma Ashe an bada ke ga Dan gidan sarauta Kinga kuwa abinda ba zai taba yuwa ne ba su tada wannan alkawarin.....

Nayi saurin tarar shi Ina fada mishi nifa dama ba Wai son Gibson nake ba Ni shi kadai nake so don nayi alkawarin ba Zan taba Auren Wanda muke addini Daya dashi ba sai Mai salla Zan Aura ko da banyi salla ba ina son anayin salla a gabana Kuma ma Ni gaskiya Al adun da akeyi ne wurin Auren mu ba suyi min ba da ya nemi ba asi na Kuma fada mishi ya Jima Yana kallo na kafin yace zamuyi magana yanzu na SHIGA gida tunda yayi maraice zamuyi waya.

Na Raka shi har Baki hanya inda Kuma muka gamu da Maazi Nkem ya karyo kwana ya Kuma ganmu Ni da Umar sai dai da sauri nayo baya umar Kuma ya tafi abinshi

Kayan da Maazi Nkem ya Tara's Amaka ta baje tana ta kambama su su suka dauki hankalin shi inda Amaka ta sanar dashi zuwan yarima Gibson Wanda ya kawo min wannan kayan sai ya Kira wayar igwai yayi godiya ya Kuma ce wa sarkin bashi gari ne sai yanzu ya dawo ya samu sako in yarima Gibson ya dawo ayi mishi sannu

Ban san yadda suka Kare ba Maazi Nkem da Amaka da kayan Gibson

Washe gari da naje makaranta nake fadawa nafisat da fauziyya yadda mukayi da Umar Wanda yazo takanas don ya fada min Yana Sona amma Kuma Yana tsoron iyayena mussamman da na fada mishi an bawa yarima Gibson Aurena lokaci kawai ake jira
fauziyya tace gaskiya Justina Lamarin ku fa yazo da Rudani ke ba Kya son yarima Gibson su Kuma iyayen ki shi suke so Umar kike so Umar kuwa Babu ta yadda Za ayi iyayen ki su bashi Auren ki yaya zakuyi kenan? Nima abinda nake tunani kenan a Rai na Ina son nayiwa iyayena biyayya Amma Kuma gaskiya bana son Auren Gibson sai Umar Wanda Kuma na tabbatar iyayena ba zasu taba yarda da Auren mu ba Koda kuwa shi shi kadai yayi saura a Duniya Yaya zamu Kare kenan? Dukkan su sun bani shawarwari Akan nayiwa iyayena biyayya kuma na Roki Allah ya zaba min ALHERI

Na dawo gida jikina a sanyaye inda na makala hearphon a kunne na Ina sauraron karatun Alkur ani Wanda na ji nutsuwa tana sauko min har ma bacci ya kwashe Ni kuma cikin Rashin sa a wayar hearphon din ta zare daga jikin wayar Wanda Ni na zare ta saboda matsewar da nayiwa wayar garin bacci ai kuwa Kira ar ta fito tar ta cikin bututun sauti na wayar Amaka dake zaune kusa Dani ta dubeni ta Kuma dubi wayar dake ta amayar da sauti cikin fusata Amaka ta fincike wayar ta kwantara ta da kasa ta watse Ni Kuma ta sharara min Mari Wanda na farka a gigice Ina zare idanu

"Wato Ashe Baki Daina sauraren wake waken Nan ba ko? Nace Mata karatu ne fa ba wake wake ba....
Ta Kuma kwada min Mari kafin ta shakeni tana fadin Wallahi kasheni zatayi ba Zan jawo Mata abin kunya ba tunda dai na zabi dabi ar masu salla nace ita ta burgeni to gara kawai ta kasheni ta huta don Bata da idon duban Yan uwan ta da suka Rayu cikin addinin su Kuma Wai ace Ni Yar da ta Haifa na ce addinin ta ba na gaskiya bane gara ace ita din ta kasheni da dai nayi Mata wannan wulakancin

Ai kuwa da gaske Amaka take don tun Ina iya shaida abinda ke faruwa har naji numfashi na Yana kokarin daukewa daga gabgar jikina zuwa wata Duniyar Wanda ban santa ba
Ban San ya akayi ba sai naji Emmanuel Yana kwata ta daga hannun Amaka Wanda tace dawa Allah ya hada ta ba dashi ba? Sai ta Rufe shi da duka Wai shike Goya min baya don Haka gara ta kashemu Ni dashi sony kadai ya isheta Rayuwa tunda shi ai me son addinin nata ne. Emmanuel dai dayake namiji ne ya kwaci kanshi hannun Amaka ya Kuma fice ya bar gidan inda Maazi Nkem ma ya dawo yaji labarin abinda na aikata bindigar shi ya kafa min a goshi Yana fadin zai kasheni wallahi da dai ace musulunci nake kwaikwayo . Da kyar baban Grace ya Basu magana suka hakura Amma fa Nasha jibga wurin Sony sai da yayi min laga laga kafin ya barci jiki duk jini da cuwuka Amma wani abun mamaki da na kwanta bacci sai gani dai wurin Nan Ina salla har ana Miko min kyautar littafin da naga mafi yawan su suna budewa suna rero Kira a irin wadda nake so da saurare abinda Kuma yasakani kudurewa lallai sai nayi sallar Nan Kuma sai nayi karatun Nan da nake yawan saurare sai kawai na diro daga Kan gadon nayi wanka da Ruwan zafi na gasa jikina ko Mai ban saka wa cikina ba na fice daga gidan...................

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran

Hadiza Bara'u Gidan iko ne sunana ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
37//38
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ne ga duk inda masoyan ANNABI MUHD S A W suke afadin Duniya Allah ya karawa ANNABI Daraja da wasila da fadeela

Sadaukarwa ga iyalan marigayi Alh Ali Mai chanji marnar gangare Allah Ubangiji yayi mishi Rahama yasa kwanciyar shi hutawa dashi da dukkan musulmin duniya

Fatan ALHERI gareku masoyan Rubutun Gidan sannun ku da kokari littafin GARWASHI na jinjina muku🥰

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Chapter 17 · 0% Book details